Showing 96001 words to 99000 words out of 112768 words

Chapter 33 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

da danta" "ba wani kishi, naga an fara nunamun wariyar launin fata ne tun yanzu".

Dariya yayi, ya dauketa suka haura dakinshi
Taimaka mai tayi, ya cire kayanshi ya daura towel.

Taso ta Kuma yin wanka ya hanata wai zatayi mura, dole ta dawo gefen bed ta zauna

Yana fitowa yayi sama da ita, tsakiyar gadon ya kwantar da ita Shima ya kwanta gefenta tareda janyota jikinshi. Dan turashi tayi ya kwanta yana kallon ceiling, ta kwanto kan kirjinshi.
Hannunta ta tura cikin sumarshi tana yamutsawa, ta hade bakinsu tashiga aika mai da hurt kisses. ta shiga yawo da hannunta duk inda ya kai a jikinshi. Sosai ya rudemata ita taja ragamar komai suka lula wata duniya.................






*>?p? AMINIYAR ANGO >?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD*
*AMINIYAR ANGO*


*Page 56*


Seda komai ya lafa, ta kwanta luf a kirjinshi. Tashi zaune yayi da ita ajikinshi tayi saurin takara binne kanta a kirjinshi.

Lakace hancinta yayi yace, "Kyaji dashi, irin ta Allahn nan" dan waro ido tayi tana dariya, "Toh da takace?".

Dage kafada yayi, yana murmushi ya dauketa suka nufi toilet. Cikin bath tub ya tsomata Shima yashiga.

Tare sukayi wanka suka fito daure da towel, suka haye gado suna manne da juna har bacci ya daukesu.

Sharp sharp suka kammala breakfast suka fice, saboda sun so su makara

Yana driving hannunta na cikin nashi, yana shafawa da dan yatsan shi yace, "Nidai bana son zuwa shagon tailorn nan, kinsan shagunan tailors ba'a rabasu da Maza"
murmushi tayi har dimple din ta na lotsawa kana tace, "Kai hearty! Kai kam kacika kishi, ina ruwana da wasu mazan bayan ina tare da nawa namijin mazaje, daya tamkar da dubu".

"Meze sa bazanyi kishin abinda nake so ba, ko bakisan kauna ke haifar da kishi ba?"

"Uhmmm nasani, amma dai yanzu da katon ciki a gaba kasan babu namijin dazeyi attem?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? pting tsaida ni".

"Amma ai zasu kalleki, kinsan ido ba'a mai shamaki. Gashi ba iya sa facemask zakiyi ba"

Ita dai batace komai ba, dan tasan tunda yafara tsiro maganganun nan, da wuya idan be canza shawara ya hanata zuwa ba.

"Wane riga zaki bada measurements tunda, kayanki duk sunyi kadan?"

With full confidence tace, "Idan ya kalleni da kyau, nasan zeyimun wanda bazan takura ba, Kuma zance yayimun dogayen rigunan masu fadi. Kasan wasu tailors din sunada basira ko babu measurements dasun Kalle ki zasu miki din........" Tsawan da yamata yasa ta saurin hadiye maganan, ta zare hannunta daga nashi, tana matsawa.

"Kufa mata na lura bakuda tinani, se kije ki tsaya gaban wani kato yana kare miki kallo" yakarashe maganan yana jan tsaki

Cikin rawar murya tace, "Bafa haka nake nufi ba, da yamiki Kallo daya sh...."
"Kinyimun shiru ko kuwa? In kuma jin kin kara mun maganan tailor anan kiga yadda zanyi dake" ya fada yana kwafa.

"Bafa ni kadai zan je ba, nida Aesh...." "Will you shut up, koke dawa zakije na soke zuwan, ki bari da yamma idan nadawo muje tare ki kai, idan haka yamiki fine, idan kuma be miki ba zan sa scissors na yanka atamfofin falle falle, kidinga hadawa da t shirt"

Kauda kanta tayi ta koma tana kallon waje, bata Kuma cewa komai ba, dan tasan yagama magana.

Bakin gate ya sauketa tace, "I'm so sorry" tafada tana fita daga motan tashige ciki, yabi bayanta da kallo yanajin yanayin data fita be mai dadi ba, Ya jima yana kallon gate din kan yaja motar yabar gurin.

Itama haka ne a bangarenta, tunda ta zauna a seat take tinanin yanda suka rabu duk abin se ya dameta, duk da tabashi hakuri se take ganin kamar har lokacin fushi yake. Wayanta ta zaro tana kokarin dialing numbern shi sega kiranshi ya shigo, seda ya kusa katsewa tayi picking tareda furta

"Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh"
"Wa alaekumussalamu warahmatullah wabarakatuh, bloody! Wai fushi kikayi?" Girgiza kai tayi kana tace, "No! nikam meze sani fushi?"

"Fushi kikayi mana ai na gani a idanunki, I'm sorry I don't meant to hurt you. You know I LUV YOU, and you know kauna ita ke haifar da kishi ko?"

Kai ta jinjina kan tace "Uhmmm" "toh kaunarki ke sawa inji duk namijin daya kalleki kamar na shakoshi har seya dena numfashi" batasan sanda murmushi ya kwace mata ba

"Nidai babu ruwana idan kayi kisa, kanaji kana gani wacce kake kishi akanta za'a rabaka da ita a kaika prison a kulle, Kuma ni ba binka zanyi ba".

"Kinma isa? Kafata kafarki, kina tinanin zan iya rayuwa a inda bakya nan ne? ko mutuwa bazan so ta daukeki tabarni ba".

"Banyi tinanin maganan ze batama rai ba, I'm sorry"

"Komai ya wuce, idan kuntashi ku biya gidan su Zainab din, amma karku jima zan dawo da yamma muje wajen tailor"

"Thank you so much sugar pie"

"Ki gaidamun da my baby" murmushi tayi tace, "yana jin Abbanshi, bye bye".

Su Aesha da tun dazu suka shigo ganin tana waya yasa basuyi mata magana ba, seda tagama Aesha tace, "Uhmmm munga Romeo da Juliet"

Bata kulasu ba ta dauko hand out tana dubawa.

10am suka fito saboda lecture daya garesu, a jere suke tafiya har bakin gate, kan sukayima juna sallama.

"Sister yanzu ina zamu fara zuwa? Gidan su Aunty zeeee ko wajen tailor?"

"Gidan su Aunty zeeee" tafada a takai ce.

Driver tafadama inda ze kaisu, ya dauki hanya dan zuwa yanzu yasan gidan su zeeee sosai

Bakin gate ya ajiye su, ya juya. Knocking sukayi me gadi ya leko ganinsu yasa shi washe baki dan ya ganesu sosai, Kuma zeeee tayi mai introducing dinsu.

Gaisheshi sukayi kan suka karasa ciki. Zaune suka samu Ammi da Rumaisa a parlour aiko tana ganinsu ta karaso tayi hugging dinsu, tana kwala Kiran Aunty zeeee

"Ke kam Rumaisa bazaki dena shirme ba, ba zakije ki kirata ba sedai ki cikama mutane kunne" murmushi tayi ta riko hannunsu suka karaso kusa da Ammi suka rissina suka shiga gaisheta, Fuska sake ta amsa cike da kulawa.

Dasaurinta ta nufo parlourn Jin Kiran da Rumaisa ke kwala mata "lafiya kike kwadama mutum kira kamar makauniya" tayi maganan cike da Jin haushi.

Hango su Aesha da tayi, yasa ta sakin murmushi tana karasawa gangansu, Tareda musu sannu da zuwa.

"Wata sabon gani, yaushe rabonku da gidan nan? Gara Aesha ma mun hadu gidan Aunty Suhailat ranan sunan Aadil, amma Muhibbah kam ma ko ranan bamu hadu ba"

"Ranan ina ciki banajin dadi, se daga baya Aesha ke cemun kunzo" ta karashe maganan tana zare gyalen jikinta ta ajiye a gafe tareda jingina bayanta jikin kujera tanayin balance.

Tana kokarin yin magana idanunta suka sauka kan cikin Muhibbah, baki sake take kallonta, mamaki yakasa boyuwa akan fuskarta murmushi ta danyi kan tace "Eyyyaaa sannu" tayi maganan har lokacin idanunta na kan cikin.

Mikewa Ammi tayi ta shige ciki, tabasu guri suji dadin firar su

Kayan motsa baki Rumaisa ta kawo ta jere a gabansu, tana zama gefen zeeee idanunta suka sauka kan cikin Muhibbah. Kallon Aunty zeeee tayi suka hada idanu, seta basar suka cigaba da firansu.

Kasa hakuri tayi ta duba Aesha tace, "Nikam dama Muhibbah nada aure? Kuyi hakuri, fatan tambayan baze bata muku rai ba"

Dariya Aesha tashigayi harda rike ciki "Laaa Auty zeeee wai dama baki taba sani ba?" "Wllhi bansaniba, duk idan naje gidan Ummi a gidan nake ganinta, Koda yaushe Kuna tare. Kuma Koda wasa ko cikin fira yayanku be taba sanar dani ba"

"Maybe yayi tinanin kinsani ne shiyasa be sanarmiki ba, duk lokacin da zaki zo itama zuwa takeyi gidan Ummi ko Kuma idan mun dawo school seta tsaya se idan kun tafi ta koma gidanta"

"iKon Allah bantaba sani ba se yau, shima bancin ciki da bazan saniba".

"Ko babu ciki zaki sani Aunty keda kin kusa dawowa family MUHAMMAD SHU'ABU BICHI, kinga ko ai dole zaki sani".

"Eyyyaaa sannu Muhibbah, Allah ya raba lafiya" ita dai murmushi kawai take


Sun jima a gidan har Muhibbahn tayi bacci ta tashi, se wajen 3:30 tace su tashi su tafi

Se a lokacin Ammi ta fito sukamata sallama "Aesha ki gaida Ummin taku, Muhibbah Allah ya raba lafiya".

"Zataji Ammi" ita dai Muhibbah akan lips ta amsa da Ameen! A kunyace ta fito daga parlourn.

Tana karasawa gida tayi wanka tazo ta tada sallah, seda ta idar da sallah ta nufi wardrobe ta dauki doguwar riga tasa duk da tanajin ta matseta. Babban gyale ta yafa ta dauko jakanta ta nufo parlour.

Zamanta keda wuya taji karan takalmi alamun takun mutum
Kallon gurin da take jiyo motsin tayi, ta hangoshi yana taka staircase kanshi a kasa.

Shirye yake cikin hadaddun kananun kayanshi, da mamaki take kallonshi har ya karaso ganganta. "Hearty! Yaushe kadawo?" Tafada tana mikewa.
Murmushi yayi yana riko hannunta cikin nashi

"Let's go" abinda yace kenan suka fice.

Bakin shagon tailorn yayi parking, ya fito ya bude bayan booth ya dauko kayan kafin ya karasa yaran shagon sukayi saurin karbanshi.

Hannu yaba tailorn suka gaisa, kan yace,
"Dogayen riguna zakayi gaba daya, babu measurements kawai kayi su da fadi sosai yadda za'ayi balance a ciki" "okay toh shikenan babu matsala, nan da 3 days za'a kammala in Sha Allah".

Sallama sukayi ya juya ya fice daga shagon, yashiga mota yaja yabar arean.

Kallonta yayi ya dagemata gira, tayi murmushi har dimple din ta na lotsawa tareda kwantowa kan shoulder dinshi tana kashe mai ido daya"

Yatsa ya dora kan dimple dinta yace, "Allah yasa babyn mu ya dauko beauty point din nan naki, I like it"

Fadada murmushin ta tayi, "Ba kaima kanadashi ba" "Uhmmm! Nawa a side daya ne, ke kuma a side biyu duk kinadashi, ko murmushi kikayi seya lotsa".

Fira suka cigaba dayi bata an kara ba se gani tayi sun shigo unguwarsu Abba, murmushin farin ciki tashigayi.

Horn yayi aka wangale mai gate ya kutsa cikin gidan

Fitowa yayi, yazagayo ya bude mata tafito ya gimtse hannunta cikin nashi suka nufa ciki.

Daga kan dazatayi ta hango Fu'ad suna nufo inda suke tsaye jikinta ne ya soma rawa, a tsorace tace, "Nashiga uku na, ga ya Fu'ad nan yau na kade. Yanzu me zance mai?"

Dariya ma tabashi yadda yaga duk ta rude "Abinda ke tsakaninmu zaki fada mishi mana ko kinada abin fada bayan wannan?" waro idanu tayi "Tafdi so kake jikina yayi tsami kenan? Cewa zeyi meyasa ban turaka gurin Abba ko Kuma daddy ka nemi izini ba, na fara tsayuwa da Kai".

Fuska a sake yakaraso ya mikamai hannu suka gaisa, duk da yayi mamakin ganinshi tsaye da Aesha sedai ko a fuska be nuna ba, Muhibbah ce ta gaisheshi ya amsa cikin kulawa suka shige ciki, shikuma yabi Muhibbah da kallo ganin katon ciki a gabanta.

"Mrs M! Duk kin wani daga hankalin ki gashi yaganmu bece komai ba" "Nidai zan shiga daga ciki, ba'a gane kan ya Fu'ad yanzu se in shiga kaji wani labarin, zamuyi waya" tana Kai nan ta juya tana daga mai hannu ta shige ciki.


***********

"Ammi! Ashe Muhibbah matar aure ce, duk zuwan da suke bamu taba sani ba"

"Nima ban kawo tanada auren ba se yau da idanuna ya kai kan cikin, fatan mu dai Allah ya sauketa lafiya" "Ameen ya rabbi" ita dai zeeee na kwance tana chatting da farin cikin ranta, tanajinsu bata ce musu komai ba.

***********

"Miye alakarki da wanda na ganku tare yazu?" Yayi mata tambayan kamar be taba sanin wanda ya ganta dashi ba.

Ummi ta kala, ita ko ta dauke kai, dan tunda ta fito da mayafi ta tambayeta ina zata tace wani course mate dinta ne yazo zata bashi book dinshi, tace babu ruwanta idan Abba ko Fu'ad suka zo suka sameta

Murya na rawa tace, "B...a..bu komai" "Toh kar inkara ganinki dashi".

Saurin gyada kai tayi kana tace "Tom"

Muhibbah tace,
"Kaima Yaya tunda kaganshi a gurinta ai kasan da dalili ko" "toh gaban kanta takeyi? Izinin wa ya nema? Saboda haka kar na kara ganinta tsaye da shi".

"Kayi hakuri, ze nema in Sha Allah" be kuma cewa komai ba, ya janyo wayarshi yashiga operating.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin Muhibbah ya shiga wata tara a Koda yaushe zata iya haihuwa, duk yadda yaso ta dena zuwa school taki tace babu amfanin zaman gidan zuwa makarantanma exercise ne.

Zuwa yanzu duk course mates dinsu sun san matan aure ce saboda yadda cikinta yayi Kato a gaba kamar kwallo duk da babyn yayi kasa alamun yana gab da fitowa.

Kullum hankalinshi na kanta se yazo school din sau biyu kafin su tashi, kawai dan ya dubata. Ko ya tafi baya 1 hour be kirata ba, ko tace kalau take, seya kira Aesha yakara tabbatarwa. idan suka tashi school ma gidan Ummi take tafiya se yamma yazo ya dauketa.

Rigunan da aka dinkamata take zunbulawa taita yawo a ciki, sunyimata yawa sosai amma tafi jinta comfortable aciki, su Aesha dasu Umaina idan suka Kalli fadin rigunan suyita mata dariya, tun tana tankasu harta dena bi ta kansu.
Su ummi ma hankalinsu na kanta kullum addu'arsu Allah ya sauketa lafiya, haka mummy hankalinta na kan autan ta kullum seta kirata sau 3 sau 4.

Ita kam Muhibbah tafisu shiga damuwa, A tsorace take kullum gabanta cikin faduwa yake kawai daurewa takeyi.

Wata ranan Sunday da dadare labour ya tashi mata, tana sanye da vest da mini skirt suna zaune suna fira, ta soma jin changes a jikinta amma seta daure saboda bata so ya daga hankalinshi tasan idan ya fahimta yanzu duk ze damu kuma ba wani sosai bane ciwon.

Jin ana Kiran isha'i ya mike yayi pecking goshinta ya fice, tayi murmushin yake tana mai bye bye

Kokarin mikewa ta fara taje tayi sallah, taji mararta ta murde, da sauri ta zamo kasa ta tsugunna, tun tana Jin ciwon kamar wasa wasa, a hankali ta soma jin bayanta na rikewa, mararta na tsananta ciwo.

Bakinshi dauke da sallama ya shigo parlourn nishin ta yasoma jiyowa, da sauri ya Kalli inda ya barta ai ko ya hangota durkushe tana murkususu

A guje ya karasa ya rukota "Heebbah! Lafiya? Meke miki ciwo?" Takasa magana se jujjuya Kai take tana nuna mai bayanta.

Cikin tashin hankali ya dauketa cilak ya fice daga parlourn, ko tinawa da wani hijjab beyi ba yasata gaban motan Shima ya zagaya yashiga ya fige motan a guje ya fice daga gidan, yana driving yana shafa fuskanta cikie da tausayawa, gani yake driver baze mai gudun da yake so ba shiyasa ko takanshi be biba.

Tun daga nesa yake horn me gadi ya wangale mai gate ya danna motan ciki, ya fito ya dauketa yayi labour room da ita doctor fareeda ta mara mai baya.....................






*>?p? AMINIYAR ANGO >?p?* *>?p? Aminiyar ango >?p?*[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD*
*AMINIYAR ANGO*

*Page 57*



Kan gadon ya daurata ta rikeshi gam tana hawaye tana cije lips
"Hearty marata wayyo Allah bayana, kuguna ze cire nashiga uku na"

Fuskanta kawai yake shafawa yasa hannunshi biyu yana gogemata hawayen, yama kasa magana dan ji yake shima kamar ze zubda kwalla.

"Sir please bari na dubata" doctor fareeda tafada tana karasowa inda suke, shi gaba daya ma ya rasa ta ina ze fara se da doctor tayi magana kana yafara kokarin zare hannunshi daga nata, takara rikeshi.

Kanta ya shafa yasa hannu ya tallabo habarta, idanunshi yasauke cikin nata cike da tsananin tausayawa yace, "Sorry dear, ki bari doctor ta dubaki, ko bakya so mararki tadena ciwo?" Saurin gyada mai kai tayi.

Yayi pecking goshinta cikin dubara ya zare hannunshi daga nata, ya matsa baya yana kallonta zuciyarshi gaba daya ta karye, duk da shi ba mace bane amma ya karba haihuwan dubannin mata yasan irin wahalar da suke Sha

Hand gloves tasa ta karasa ganganta "Sorry madam, dan kwanta mu gani" tafada tana taimaka mata ta kwanta.

Skirt din jikinta ta janye sama, ta kai hannunta tana kokarin zame pant din, tayi saurin mikewa tana ja baya ta jingina da bed din tana zare ido kamar mara gaskiya.

Girgiza kai tayi, tayi murmushi, idan da sabo tasaba ganin irinsu Muhibbah, se aita fama dasu su kafe. amma idan labour yayi labour har riga suke cirewa tsabar azaba. Tasan yanzu duk wasan kwaikwayo ne shiyasa har tasamu daman abubuwan nan amma kuka na gaba.

"Doctor ina ga sena nemo wata ta tayani ni kadai bazan iya da madam ba" beyi magana ba yakaraso ya rike hannayenta yana mata dubara hade da kalamai masu kwantar da hankali, a haka har doctor ta samu ta rabata da wandon ta dubata, tako saki kara.

Hand gloves din ta zare ta zuba a sharp box tace, "doctor ta kusa, yanzu 8cm remain 2" jinjina kai yayi, ta juya ta fice.

Bata jima ba tadawo hannunta rike da kayan aiki, tazo ta rike hannunta tafara neman vein da mamakinta batayi darun data saba ba se hawaye kawai ke bin kuncinta. Shikuma yana zaune kan stood dake gefen bed din, ya gimtse dayan hannunta cikin nashi, dayan hannunshi kuma yanata aikin share mata hawaye hade da rarrashinta da karfafa mata guiwa.

Drip ta dauramata ta kawo wata allura (Oxytocin) ta zuba cikin drip din.

Tana kwance lamo kamar me bacci, ciwon maran ya lafamata. Ruwan natafiya da dan sauri dan har yayi rabi, kamar an tsikareta ta tashi zaune tasa hannu ta fisge canularn tasaka ihu.

Cikin kidima ya rike hannunta da jini ke faman zuba yace, "Heebbah! Ya akayi? Meyasa kika cire drip din gashi kinsa jini nabin hannunki" yafada hankali tashe.

Ita bama ta hannunta takeyi ba dan bata fahimtar abinda yake fada, kuka me sauti ta fashe dashi "Yaya marata, innalillahi wa inna ilaehi raji'un........"

Yana rike da ita a jikinshi duk ya kidime, se doctor fareeda ce ta karaso ta kwantar da ita ta duba taga ta kai 10cm "madam push, ga babynki nan na neman hanyan fita" nishi tashigayi iya karfinta, kuka take amma hawayen sun kafe tsabar azaba.

"Yauwa madam push, ga kan babyn nan" "doctor kibarni na gaji"
"Sorry madam ki daure, kin kusa" tafada cikin kulawa.

Nishi tacigaba da yi, baby ya doso a lokaci daya kuma mararta ta wani murde, A zabure ta zira kafarta kasa tana kokarin sauka daga gadon.

Da hanzari suka rikota tasaki kuka me sauti, "bayana, kuguna Wayyo Allah marata. Mummyna ki haifemun Allah yabiyaki da gidan aljannahtul firdaus, kai innalillahi wa inna ilaehi raji'un........."

Shiko baby burinshi kawai ya ganshi a waje dan ya gaji da rayuwar duniyar su, se neman hanyan fitowa yake

"Yaya mutuwa zanyi, ka kiramun mummyna, wayyo Allah na dan Allah ka kiramun Ummi da sister, Ko munada rabon sake ganawa kafin na mutu, bazan iya ba"

"Heebbah zaki iya" Kai kawai ta girgiza dan tagama sarewa da lamarin duniya

Be

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login