Showing 102001 words to 105000 words out of 112768 words

Chapter 35 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

Yaya ya leko yaga bamu tafi ba, yace muje mu kwaso kayan baby" tana maganan tana tafiya. Bata jima ba tadawo sanye da hijjab, Suhailat ta ajiye Aadil suka fice dasauri gudun ya motsa Ummi tace dole seta tafi dashi.

Hannu ya Kai ya shafi kumatunta yana murmushi yace, "'yan mata na how far" yafada yana dage mata gira

Hararanshi tayi tana turo dan karamin bakinta, dariya me sauti yayi, yakama hannunta yayi pecking yace, "Ammi kawo babyn kiyi break fast" langwabar da kai tayi ta make kafada tana kare matse yarinyan ajikinta

Murmushin gefen baki yayi yasa hannu ya karbeta, Muhibbah ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana gyara rigarta batare da ta kalli ko gefen da yake ba.

Kallonta yayi yana murmushi me sauti ganin yadda take sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta kubuta daga wani hali "Hayateee! Da alama babyn mu batada rigima kalli daga Shan nono har tayi bacci" Dan kallan babyn tayi tace, "Uhmmmm"

Kwantar da babyn yayi, ya riko hannunta ya zaunar da ita kan center carpet ya zauna kusa da ita ya ajiye tray din a tsakiyar su. Plate ya dauka yayi serving dinsu, pepper soup ne na beef head, se jallof din shinkafa dataji beef meat ga bread a gefe.cup ya dauka ya hada tea me kauri ya jeresu a gabanta ta bisu da kallo a ranta tace tafdi duk wa innan abincin ne Ummi ke cewa Karna rage ko kadan.

Shinkafan ya soma bata tana karba, kadan taci tace ya isheta, kana yashiga bata pepper soup din hade da bread, taci sosai tasha tea seda yatabbatar ta koshi tana kokarin amai kana ya kyaleta Shima yaci.

Tana kokarin tattare kayan dasuka ci abinci yayi saurin riketa "Blood! na huttasheki bari a turo mairo tazo ta kwashe...." kafin ya rufe baki su Aesha da Suhailat suka soma shigo da kayan baby dana Muhibbah, baki sake take kallonsu duk yadda taso ta share kasawa tayi tace, "Aesha wa innan kayan dakika dibo fa? Se kace nadawo nan kenan da zama?? Harda gadon baby, haka akwatin zuwa asibiti dakika hada kika cikashi kamar masu zuwa gidan biki harda sa pampers pack daya" tayi maganan tana dariya

Itama dariyar tayi "Toh nasani ko twins ne naje nasa kaya ace se na karo" tsaki taja "Abinda yafi twins, ai ko ke zaki shirya kayan nan tunda ke kika lodosu" "Bakida matsala maman baby indai wannan ne angama" mikewa yayi, ya dauki 'yarshi ya fice daga dakin.

Ita da Suhailat suka shirya kayan, suka ajiye komai a mazauninshi, Ummi ce ta turo kofan tashigo ta dubi Muhibbah tace, "Sannu Muhibbah ya karfin jikin?" Murmushi ta danyi tace, "Dasauki Alhamdulillah"

Kai ta jinjina "toh taso ayi wanka" tafada tana nufar toilet din, Aesha kuma ta tattare kayan dasuka bata ta dauki tray din suka fice. Cikin sanyin jiki ta cire kayanta ta daura towel ta nufi toilet, hango ruwan zafi na tururi da tayi yasa gabanta faduwa amma ta daure ta karasa kusa da Ummin, a kunyace ta zare towel din ta tsugunna.

Towel ta tsoma cikin tafasashen ruwan ta ciro ta daura a bayan Muhibbah aiko tafasa ihu ta mike a guje ta koma karshen toilet din tasaki kuka me sauti

"Muhibbah lafiyarki?" "Ummi a surka ruwan please yayi zafi dayawa" "Kintaba ganin an surka ruwan wankan me jego ne? Ruwan da seda na barshi yasha iska, da iyye ce zata miki da kin gane Allah daya ne, ni dama ita tazo take miki kuyi ta dramarku ina gefe" kafada ta make tana turo baki.

"Kizo muyi mu gama ayima baby, anjima kadan zakiga gidan nan ya cika da 'yan barka"
tayi juyin duniya tazo ayi wankan amma fafir ta kafe ita fa se an surka, ganin bazata iya da lamarin Muhibbah ba yasa ta fice tabarta cikin toilet din.

Parlour taje tasanarma Fu'ad, ya mike yabama Aunty Maiminatu babyn yabi bayan Ummi suka koma ciki, can karshen bangon toilet din ya hangota ta dauki towel ta daura tana ganinshi ta matso kusa dasu tana matsar kwalla yace, "Ummi dan Allah ki bari na zane yarinyan nan ko zata shiga hankalinta" "baza ayi haka ba, zata dena harda yarinta, abi komai a hankali" towel din ta zare ta tsugunna batareda tace komai ba. Kwafa yayi ya fice ya koma bakin gado ya zauna, dole ta tsaya Ummi ta gaggasamata jiki babu daman raki se hawaye kawai ke bin kuncinta. "tashi ki shiga cikin ruwan" dan waro idanu tayi, a zuciyarta tace nashiga uku na yau dai so ake sena mutu za'a kyaleni, ganin ta tsaya taki motsi ta kyaleta bata Kuma magana ba ta fice, ta turo Fu'ad ta bar dakin.

Bataji zuwanshi ba sai ji tayi yayi sama da ita, be direta ko ina ba se cikin ruwan ta zabura zata mike ya maidata, yana shafa bayan ta, ya tsuguna ya tallabi kanta ya sauke lips dinshi saman nata yashiga aikamata da french kisses, ya tura hannunshi cikin gashinta yana ya mutsawa, Tuni tamanta tana cikin ruwan zafi ta biyemai, Sun jima a haka kafin ta sabule bakinta tana binne kanta a kirjinshi, yayi dariya tareda nadota a towel suka fito.

Shida kanshi ya shiryata ya kwantar da ita yaja blanket ya lullube iya chest dinta, yayi pecking goshinta ya fice tabi bayanshi da kallo tana murmushi, ta runtse idanunta baccin gajiya yayi gaba da ita.

Har su Ummi suka shigo dakin akama baby wanka aka shiryata bata san wainar da ake toyawa ba tayi nisa a baccinta tsabar gajiyan daren jiya

Ba ita ta farka ba se 1 brush tayi ta nufa parlour, kan kujera ta zauna ta gaisa da mutane anata mata barka sedai ta danyi murmushi.

Baby na hannun Aunty Maiminatu, ta kuramata idanu a zuciya take mamakin hakurin yarinyan tun safe da tayi feeding dinta bata karajin kukanta ba, su kuma basu kawomata ita ba

Kallon da taga tanama babyn yasata yin murmushi tareda dauramata yarinyan kan kafafunta, kasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta.

"Muhibbah ni kike Jin kunya? Rike 'yarki itama tana so taji dumin mamanta ai tamayi kokari, na kai miki ita na ga baki tashi ba" murmushi ta danyi tasa hannu ta rike baby.

Ta gefen ido ta Kalli Aunty Maiminatu, ganin hankalinta baya kanta, ta mike da yarinyan a kafada tashige daki. Kan kafafunta ta ajiyeta tana kare mata kallo tanajin yadda kaunarta ke ratsa jini da jijiyarta bataji ko kuda zata bari ya tabamata diya indai ba bisa kuskure ba.

Hannu ta kai ta shafa kumatunta ta saki murmushi tanajin sanyin dadi, yarinyan na shirye cikin kayan sanyi masu taushi pink color se tashin kamshi take.

Mutsu mutsu ta farayi, ta dan jijjigata aiko ta bude idanu dan dama ta gaji da baccin, pecking kumatunta tayi tana dariya tace, "baby na kintashi? kinajin yunwa?? zaki sha nono???" Tayi maganan tana Kai hannu ta zuge zip din rigarta, tashiga feeding dinta tareda runtse idanu tana Jin azaba amma ta daure saboda tasan tanajin yunwa kawai dan batada rigima ne. Tana koshi ko ta koma baccinta, tana kokarin kwantar da ita su Umaina suka shigo da murnarsu, sukayi hugging din ta ta saki dariya tana gyara zamanta.

Ramlat tace, "Da safe Aesha ta kira take fadamana kin haihuwa, dah kamar zamu tawo, Umaina tace mudai bari a tashi ma tawo" tayi maganan tana daukar baby

Umaina tace "kinga baby 'yar lukuta, tubarkallah masha Allah, Allah ya rayamana ita akan sunna" Ameen duk suka amsa dashi

Ba Muhibbahn ba, ba Aesha ba duk su hudun suka shiga shirme, nan ciki aka kawo musu lunching suka hadu suka ci suka dora daga inda suka tsaya, Umaina kam sunki ajiye baby data fara bacci se sun san yadda sukayi suka tasheta wai sunfi son suga idanunta a bude saboda ta gane su da kyau a school karta dinga yimusu kiwa, ita ko kamar tayi satikai se binsu take da kallo da ta gaji tasa kuka su kuma su shiga rarrashi amma sunki bada ita, se yamma suka wuce Aesha ta rakasu compound tasa driver ya maidasu gida.

Kwanaki nata tafiya har jibi suna, mutanen KD sun hallara gidan Ummi................



*Dan Allah kuyimun uxuri idanuna sun sani gaba, kunburin ya rage amma zugi yakemun sosai, ga kaikayi, bana jure kallon hasken screen, wannan page dinma inayi ina ajiye wayan a hk dai na lallaba nayishi sbd jira bb dadi*




*>?p? AMINIYAR ANGO >?p?*[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD*
*AMINIYAR ANGO*


*Page 59*


Suna zaune a halin gidan suna fira cike da so da kaunar juna, Aesha naba Aunty Asma'u labarin darun da akayi da Muhibbah wajen feeding baby da dramar da akasha wajen wanka, anata dariya.

Asma'u tace, "Ai nasan za'a rina, indai raki ne daga kan Muhibbah an gama, Allah kadai yasan dramar da akayi da ita wajen labour, saboda sanin ragwantan ta da mummy tayi kullum hankalinta na kanta, tunda Muhibbah tashiga watan haihuwan ta batada magana se na autan ta" baki ta tura tace, "Aunty! Bakiji azabar dana keji bane, har yanzu idan ina fedding dinta inajin zafi dauriya kawai nakeyi, Amma baki ga dauriyar da nayi bane wajen labour, ki tambaya hearty kiji ko kuka ma banyi ba". Tun dazu dasu ke firar su be ko dago Kai ya kallesu ba, se da yaji Muhibbah tace ko kuka batayi ba a labor room, hada idanu sukayi ya mata kallon babu kyau karya. Murmushi ta sakarmishi ta kauda kai gefe.

Dariya sosai sukayi, Aesha ta harareta ta tabe baki kana tace, "Wllhi idan duk jikina kunne ne bazan yarda ba, kedin ce zakice kin haifo yarinyan nan ko tarinki ba'a ji ba? Ah gaskiya ki canza wata maganan amma wannan bata Karbu ba". Aunty Asma'u tace, "Ai bama se kin rantse ba Aesha, wacce gurin feeding seda aka kwashi 'yan kallo da ita inaga Kuma labour, Allah kadai yasan abinda ya faru" "Wllhi Aesha kin rainani, kinga gadon baccina, ko kin manta ni yayarki ce?" "Tafdi yayata a ina? 3 months fa kachal kika bani, ta ina kika zama yayata"

"Ko da yini daya ne dai na rigaki shan iskan duniya, Kuma yayanki nake aure kinga karewan yayama, Auntyn ki ce nii" tsaki taja tace, "Kyaji dashi"

Ganin Ummi ta mike ta musu seda safe, shima ya mike yana duba agogon dake manne a bangon parlourn, 30 minutes after 9, kallonta ya danyi yace, "Bakijin bacci ne?" Ya fada yana daukar baby ya nufi bedroom. Bata kulashi ba tace, "Aunty ko hauka nayi a lobor room kar kuga laifina, Ashe haka akeshan wahala wajen nakuda? Wllhi da ace yara sun san abinda iyaye ke ji tunda ga daukar ciki har zuwa haihuwa, da ko wuta iyaye sukace yaro ya shiga bazeyi musu ba bare ya tsaya jayayya dasu, Ya Allah tukuicin aljannah firdaus ga mahaifiyar da tayi silar kawomu duniya, sannan tukuicin aljannah firdaus ga mahaifin daya sha wahalar rayuwa sabodamu ya hayyu ya qayyum".

Dariya sosai sukayi harda rike ciki kana suka amsa da Ameen ya rabbi, Suhailat tace, "Muhibbah fa anci kwakwa, haihuwa yakin mata" tayi maganan tana cigaba da kyalkyala dariya. Numfashi ta sauke kana tace, "Bari kawai Aunty Suhailat, nidai kam nayi auta daya ta isheni, bana fatan na Kuma daukar wani cikin ina bazan iya ba"

Harara maimunatu ta watsamata tace, "Ai indai ciki ne, kima shirya dan kafin kiyi arba'in kin dau wani" gabanta ne ya fadi ta waro idanu tareda fadin "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, Aunty wane irin kafin inyi arba'in na dau wani cikin?" tayi maganan kamar zatayi kuka duk ta rude kamar wacce akace tana dauke da cikin yanzu haka a jikinta.

"Miye na salati, ba ke dadi miji ba ko suna ba'ayi ba amma koda yaushe Kuna nanike da juna, Ki bari yamiki wayau tun baki arba'in ba ki fara sabon laulayi, ni banga amfanin dawo dake gidan nan da Ummi tayi ba duk ta takuraku, nace mata da anyi suna ta tattara ta maidaki gidanki, tace saboda wankan baby da kula dake baze yuwu tabarki ke kadai da danyan jego ba ki cuce kanki kiki shiga ruwan zafi, zuciyarta bazata nutsu ba koda ta nema miki tsohuwa saboda tasanki da rikici, iyye Kuma tace se bikin ya Suhail zata zo" kafin tayi magana Asma'u tace, "Ki barta yaro be san wuta ba se ya taka, Muma ba duk hakan ce ta faru damu ba a farko, muna goyo muna laulayi, kuba Romeo and Juliet ba Allah yakara dankwan kauna, Allah yakawo twins nanda 9 months mu dawo suna".

Idanunta ne suka kawo ruwa, cikin sanyin murya tace, "Wllhi Aunty babu abinda mukeyi, shi yake zuwa da kanshi bani nake kiranshi ba, kuma ma ai banida tsarki bare kuyi tinanin wani abu" tayi maganan hawayen idanunta na silalowa

Kafadarta Aunty Maiminatu ta dafa "Ai kwanan nan zakiyi tsarkin wasu basa jimawa, ya danganta da yanayin ki, wasu matan basa 2 weeks jini be dauke musu ba, ki fahimce ni bance kunayin wani abu ba, ai ba laifi bane ma dan kunyi wani abu ina mata da miji ne keda dashi?" Kai ta jinjina.

"Abinda nake so ki fahimta shi fa namiji babu ruwanshi, ya dinga miki dubara kenan har seya samu abinda yake so ya kunsa miki ciki daga karshe yabarki da wahala, befi yabiki da sannu ba, ba ina nufin daukar ciki wahala bane, amma kina da karamin goyo kina laulayi ya kike tinani kema kinsan lamarin is not easy". Seda taja fasali kafin taciga da magana "ni bance ki daga hankalinki ba, Kuma bance karki ba mijinki kulawa yadda yadace ba, amma karki bari yamiki wayau. Yanzu jikinki a bude yake zaki iya daukar ciki akoda yaushe, bance miki karkuyi romancing juna ba amma kiyi taka tsantsan, nidai shawara nake baki ba umarni ba".

A kunyace tayi kasa da kanta tana wasa da yatsunta kamar zata ballasu, Asma'u tace, "Kibarta idan kunne yaji gangan jiki ya tsira, yanzu ba lallai ta gane yaren ba se tsautsayi ya hau kanta ga baby ga ciki, muna shagalin bikin ya Suhail ita kam tana kwance".

Aesha na dariya tace, "Kuma wllhi bikinmu zamusha, se ma munso idan munzo wucewa mucemiki sannu, nayi miki mutumci ne ma na daukamiki baby"

Duka ta Kai mata tana harararta, Suhailat tace, "Kinga Aesha! Allah ya kaimu aurenki kema bamusan abinda zakiyi ba" Muhibbah zatayi magana taji kukan babynta kafin tayi wani yunkuri tajiyo muryan Fu'ad yana kwada kiranta "Heebbah! Fateema!!" baki ta dan tura ta zira kafafunta kasa tana sa takalmi, ta mike tayi musu seda safe, suna mata dariya suma suka mike suka nufi bedroom.

Da sallama akan lips dinta tashiga dakin, tazauna gefenshi takai hannu ta karbi babyn tafara feeding dinta. "Firan me kukeyi haka kika barni tun dazu ina zaman jiranki?" A dan tsorace ta kalleshi, a ranta tace kar dai ace yaji maganganun da mukayi dasu Aunty.

"Ina magana kinyi shiru" murmushi tayi tace, "Firan rayuwar duniya mukeyi, kasan idan 'yan uwa aka hadu se aji kamar kar a rabu" "Toh sannu me 'yan uwa, yanzu Kam lokacina ne, gobe seku daura daga inda kuka tsaya" dariya tayi tace, "bazaka tafi gida bane?" Tayi maganan tana duba wayanta taga 5 minutes after 10.

"Uhmmm yau anan zan kwana" bata ba maganarshi muhimmanci ba ta kwantar da yarinyanta ta fara shirin kwanciya. Daukan babyn yayi, ya dauki dabino ya tauna ya lasamata a baki yamata kuduba. Seda tagama shirinta tsaf ta hauro bed din, ya dauramata yarinyan kan kafafunta ya kai hannu ya shafa kumatun babyn yace, "My little zahrah" kallon rashin fahimta tabishi dashi, dama tun tuni take so taji sunan yarinyan amma ganin beyi mata maganan ba yasa tabari zuwa ranan suna tasan dole zataji. Kai ya jinjina yace, "Fateema, kuma Ammin Fateema" shiru tayi, dan duk tinaninta sunan Ummi ko na mummy ze sa, ajiyar zuciya tasauke tace, "Amma hearty ya akayi kasa mata fateema, bancin suna na ne, kuma nima takwara akayima iyye" gira ya dage yana dan murmushi yace, "Nima masoyiyata nama takwara, kinsan dai bana wasa da alkawari" Kai ta gyada

"Kintina ranan da kika rokeni alfarman nayi miki alkawari, ko bayan mutuwarki zanyi miki takwara?" Murmushi me sauti tayi tace, "Uhmmmm, amma ai cewa nayi idan bana raye, Amma yanzu ai ina raye, Meyasa kayimun takwara?" "Saboda ina kaunar me sunan, Kuma haka zalika ina kaunar sunan ta dalilin me sunan. Idan duk 'ya'yana zan samusu fateema sunan baze taba gundurana ba, saboda sunanki ne habeebtee" yayi maganan yana jan hancinta. Jikinshi ta fada tana dariya hade da hawayen farin ciki, yasa hannu yana ya rungumeta yana bubbuga bayanta, kana ya dagota ya rungumeta ita da babyn, yasa harshenshi yana sharemata hawaye.

"Banaji akwai macen data kaini dace, samun miji kamar ka sai wacce ta taki sa'a, ina alfahari da kasancewar ka miji a gareni kuma uba ga Little, ina taya kaina murnan samunka matsayin abokin rayuwa, Anta Hayateee wa farhatee, uhibuku hubban kaseeran, I LUV YOU WITH ALL MY HEART"

"LUVS YOU TOO MY ONE".

Daga haka ya karbi babyn ya kwantar kan bed dinta, ya koma gadon ya janyota jikinshi ya matseta yashiga yawo da hannunshi a jikinta yana wasa da gashinta, yasa hannu ya tallabi kanta ya daura lips dinshi saman nata yana kissing dinta cikin kwarewa, hannunshi ya tura cikin rigarta yashiga yawo dashi, tayi saurin rike hannunshi ta sabule bakinta daga nashi tana sauke ajiyar zuciya tace, "Yaya katashi ka tafi gida, dare yanayi"

"Anan zan kwana" yayi maganan yana kara matseta a jikinshi

Kamar zatayi kuka tace, "Dan Allah hearty nidai katafi kar wani ya kamamu mun kwana tare muyi abin kunya, idan ma bazaka gida ba ko dakin ka na nan gidan ka tafi ka kwana please"

"Kamarya kar wani ya kamamu, wani sabon muke aikatawa ne? Ko ba ma'aurata bane mu??" "Uhmmm nasan mu ma'aurata ne, amma kaga be dace ba ko ummi idan taganmu zata iya yin fushi tace da anyi suna na tattara na barmata gidanta" "Kinga ni da zatayi haka ma wllhi da naji dadi, koke nasan a ta kure kike, bamusamun sakewa, ni dama dan babu yadda zanyi ne shiyasa kike zaune gidan nan amma banaji zan iya bari har kiyi 40 days a nan" shiru tamai saboda ta fahimta ta matsa da koranshi fada zasuyi kuma taja ya kafe cewa a dakin ze

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login