Showing 69001 words to 72000 words out of 112768 words

Chapter 24 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

bakinta daga nashi tafara kokowa da numfashinta a wahale taja dogon numfashi ta sakeshi tareda sakin razananniyar karaaaaa............ *>?p? Aminiyar ango >?p?* *>?p?Aminiyar ango>?p?* *Aminiyar ango >?p?>?p?>?p?*[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*

*Page 45*


A sanyaye ta karasa parlourn har lokacin su Ammi na zaune Rumaisa na ganinta ta mike da fara'arta

"Kunga uwar gidan doctor, daga ke ba Kari"

Batace mata uffan ba tazauna kusa da Ammi ta kwantar da kanta kan cinyar Ammin

Ganganta Rumaisa ta karaso ta tsugunna "Aunty zeeee lafiya kuwa? Ko wani abun dr yamiki ne?" Tayimata tambayar a sanyaye cikin kosawa da Jin amsanta

Kai kawai ta girgiza tama kasa magana

"Zainab lafiya kike kuwa? wani Abu ne yafaru?" Tayi tambayar cikin kulawa

A raunane tafara magana "Ammi nashiga uku na zuciyata na neman tarwatsewa Ashe da gaske doctor nada mata" shiru tayi tana nazari, Rumaisa ta dafata "Haba Aunty dan Allah ke miye hadinki da matarshi nabaki shawara ki cire hankalinki kan matarshi ki fuskanci yakin dake gabanki na mallakar zuciyarshi, da matarshi zaki zauna ne ko dashi?"

Wani abu me daci ta hadiye kan tace "Dashi zan zauna Rumaisa amma bakiji yadda zuciyata ke neman tarwatsewa ba"

Ajiyar zuciya Ammi ta sauke "Zainab idan zaki kwantar da hankalinki ki kwantar namiji mijin mace hudu ne, ko mara mata kika aura baki da tabbacin ze rayu dake ke kadai har karshen rayuwa keda baki shigabama kike kishin shi toh ita matarshi Kuma ya kike tinanin zataji idan labarinki ya risketa ki kwantar da hankalinki kiyi addu'ar zabin mafi alkhaeri"

Kukan da take dannewa ne ya kufcemata "Ammi ni damuwata ba iya matarshi ba ne, Dr ya fadamun bashida ra'ayin zama da mata biyu dana ce na amince zan zauna dashi a haka cemun kawai yayi zeyi tinani abinda ya yanke ze kirani ya fadamun kinga kenan Ammi banida tabbacin zan samu gurbi a zuciyarshi ko aa" ta kare maganan cikin kuka, kuka take sosai kamar zata shide.

Dago ta tayi ta daurata kan kafadarta tana dan bubbuga bayanta alaman rarrashi "Ki fawwala wa Allah komai karkisa damuwa a zuciyarki duk abinda ubangiji yayi dai dai ne ba komai muke so muke samu ba ki dauka wannan na daga cikin babin kaddararki dan haka kisama ranki hakuri da juriya mu kuma jira kinji ko?" Kai kawai ta gyada badan tana wani fahimtar abinda mahaifiyar ta ta ke fada kuma har lokacin takasa tsaida kukanta.

Hannunta Rumaisa ta kama "Aunty please ki dena kukan nan wata bata taba auren mijin wata kiyi hakuri idan har mijinki ne ko ana mazuru ana shawo se kin mallakeshi, sannan mujira muji feed back daga gareshi ki tashi muje daki" ta karasa maganan tana sharar kwallan tausayin 'yar uwarta.

Kamata tayi suka karasa daki Ammi tabi bayan su da kallo tanajin tausayin 'yarta na taso mata.

Kan bed ta kwanta tana Jin wasu sabbin hawaye na zuwan mata, a gefenta ta zauna "Dan Allah sis ki cire damuwa a ranki babu abinda ke saurin illata bawa kamar tinani" tayi maganan tana mika mata cup din hannunta, karba tayi ta dan kurba ruwan ta Mika mata cup din.
Murmushi tamata kan tace "Ki kwanta kiyi bacci zuwa safe zaki samu saukin abinda kikeji in Sha Allah" bata bata damar magana ba ta mike ta fice.


*********

"Innalillahi wa inna ilaehi raji'un Ummi, Abba, daddy ze kashe muku niiii, wayyo mummy na ashe bamuda rabon sake ganin juna ashe sallamar karshe mukayi, dan Allah Yaya kabarni zaka kasheni nashiga uku na....."

Sambatu take tana Kuka sosai harda shidewa amma shi inaaa bema san tanayi ba jin kukanta na hawa mai kai yasa ya hade bakinsu, tun tana iya gane abinda takeyi har ta fara fita hayyacinta bazatace a duniya take ba ko a lahira ko motsi ta kasa se jujjuya Kai kawai take

Gefe ya mirgina ya kwanta ya janyota ya kankameta yana maida numfashi ya kai 10 minutes a haka kafin yatashi zaune ya janyota jikinshi ji yayi jikin ya dan saki se kokowa take da numfashinta dasauri yashiga jijjigata "Keeee!" Shiru babu amsa

"Bude ido ki kalla yayanki, dan Allah ki bude ido ki kalleni please" ganin har lokacin idanunta a rufe suke yashiga kiranta "Fateeee! Heebbat!! Bude idonki ki kalleni"

Wani hawaye me dumi yaji ya digo mai a kirji ya kara kankameta "Heebbah! Please kidena hawayen nan ki bude ido ki kalla yayanki, kina jina" tana jinshi amma bataji ko yatsanta zata iya dagawa se hawayen azaba ke faman zarya a kuncinta. Jin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya yasa shi mikewa da ita

A hankali ya kwantar da ita kan pillow ya daura towel ya shige toilet wanka yayi kan ya hadamata ruwan zafi ya diga detol a ciki yazo ya dauketa cilak ya tsomata cikin bath tube din a zabure ta mike tasaki uban kara, dannata ya kumayi ciki ya riketa dakyau se ihu take amma yaki sakinta seda yaji ruwan ya huce ya Kuma zuba wani na zafin yasata ciki tana kuka tana cije lips seda ya zubar da ruwan ya hada me dan dama dama ya maidata ciki Shima ya shiga, wankan soso da sabulu yamata tana turjewa a haka har aka gama wankan.

Cikin ruwan ya barta yace tayi wankan tsarki ya fice

Nade bed sheet din yayi ganin ya dan baci da jini ya canza wani ya nufi wardrobe ya dauki jallabiya ya zira

Daker take motsawa har lokacin idanunta a rufe se hawaye take a daddafe tayi wankan tana kokarin fita daga bath tube din taji anyi sama da ita dama karfin hali ne tasan ba iya tashi zatayi ba bare tafiya

Kan bed ya direta yaja blanket ya rufeta kan ya nufi wardrobe ya dauko mata jallabiyarshi yazo yasamata yanaji tana tureshi be ko tanka ta ba sema haurawa da yayi gadon ya rungumota, kuka me sauti ta cigaba da rerowa, bayanta yashiga bubbuga alaman rarrashi

"Ki dena kukan nan haka kar kiyi zazzabi please, yayanki ne ko? Natuba bazan sake ba" banza ta mai ya Kai bakinshi saitin kunnenta

"Allah yamiki albarka Heebbah kin shayar dani ruwan zuma kin daukemun kishin da koda teku zan shanye ko makoshina baze jika ba kin dauke mun cutar data taru a mara na shekara da shekaru, Allah ya biyaki da gidan aljannahtul firdaus Allah ya faranta miki kamar yadda kika farantamun, Allah ya azurtamu da 'ya 'ya na gari *I LOVE YOU*" Yana maganan yana kara kankameta kamar ze maidata ciki.

taji dadin kalamanshi sosai ba kadan ba amma Kalmar daya fada a karshe ne tajishi un expected se take kokonton gaske ne ko mafarki, take kuma tinanin lokacin da yanemi suyi soyayyar kwana daya ya fadomata batasan lokacin da tasaki boyayyen murmushi ba, dg haka bacci ya dauketa.

a ranshi yake raya lallai dan hakin daka raina shi ze tsole maka ido ji fa 'yar yarinyan amma tasa shi ya tafi wata duniya ya Dade yana tina ne tina ne a haka har bacci ya daukeshi.

Se 5:40 ya farka da sauri ya zira kafarshi ya sauka daga gadon yana fadin "Ya Salam" alwala yayi yadawo ya tada sallah seda ya shafa addu'a kan ya mike ya karasa kusa da ita blanket din ya janye yaji hucin zafi ya siraro mai a hankali ya kai hannunshi wuyanta yaji zafi rau dan zaro ido yayi "Ya ilahi" ya fada a zuciyarshi, bacci yaci karfinshi be ko ji dumin jikin nata ba se yanzu.

Dukawa yayi ya huramata iska a kunne yana shafa gashin kanta, motsi ta farayi gashin idonta na rawa amma taki bude idanun

Murmushi yayi "bude idonki mana ko bakya son kallon yayanki ne?" Saurin daga mai kai tayi tana kara runtse ido.

Murmushin gefen baki yayi yafara kokarin daukanta ta ture hannunshi "Na kyaleki zaki iya tafiya?" Kai ta gyada "Toh jeki kiyi alwala kizo kiyi sallah Kisha magani" kokarin mikewa tafara ta sauke kafarta kasa tana takawa tasa kuka me sauti ta koma ta zauna

"Wayyo Allah na Mummy na mutuwa zanyi, kafata ta cire shikenan nazama gurguwa nasan sedai a cire kafar nan batada wani amfani yanzu" da iya gaskiyarta take maganan tana kuka wiwi.

Tsayawa yayi kawai yana kallonta yana murmushi shi wllhi dariya ma take bashi be cemata komai ba ya dauketa zuwa toilet da kanshi yamata alwalan ya dawo ya ajiyeta kan darduman ya zira mata hijjab ya koma ya zauna bakin gado yana kallonta

A zaune tayi sallahn tayi addu'a ganin ta shafa addu'an ya karasa ya dauketa ya kwantar kan bed din ya koma ya nade sallayan.

Jikinta ne yakara daukar zafi hakoranta har hadewa suke da juna jikinta se rawa yake

Da sauri ya fice be jima ba yadawo hannunshi rike da magunguna

Kokarin cire mata hijjab ya fara ta rike hannunshi "Dan Allah kabarni sanyi nakeji" "miye haka, wayace miki idan ana zazzabi ana lulluba?" Jin yayi maganan da dan fada tayi saurin sakinshi, yakai hannu ya zare hijjab din ya jefar kasa ya kare hade fuska yasan idan ba haka ba kan yasamata drip din nan se an jisu.

Canular yafara samata tafara kuka ya girgiza kai ya cigaba da aikinshi drip yasamata ya dura allurai a ciki ya hada dana bacci

Ya kunna AC yakoma ya zauna a gefenta ya gimtse hannunta cikin nashi tun yanajin sautin kukanta can yajita shiru alamun tayi bacci kallonta yayi yasaki murmushin gefen baki ya mike yabata peck a goshi ya fice.

Kitchen ya shiga ya hada breakfast yayi wanka ya shirya ya tsaya gaban mirror yashafa body lotion ya bude wardrobe ya dauki kayanshi ya sa ya feshe jikinshi da turare ya fito rass a angonshi ya karasa kusa da ita ya zauna yana kare mata

Fara ce tass ga dan dogon hancinta dai dai fuskarta yadda ta turo dan karamin bakinta tana faman yatsina fuska yasa murmushi kufce mai kai da gani kasan baccin wahala take.

Hannu ya kai yataba wuyanta yaji zazzabin ya sauka yaja blanket ya lullubeta ya rage gudun AC ya dauko wayanshi ya hado da nata ya fice.

Door bell aka danna yakarasa ya bude mairo ya gani tsaye ya juya tashigo tace "Ina kwana" "lafiya" yafada yana karasawa dining ya zauna ya zuba abincin farfesun kan rago ne da bread se tea befi 20 minutes ba ya mike ya haura daki mairo ta fito tafara gyaran parlourn.

Wayanta ne ya dau kara yayi picking call din yakara wayan a kunnenshi ba tare da yayi magana ba

"Hello!" Jin shiru yasa tace "Banson wulakanci wllhi, ana miki magana kinyi ma mutane banza se kace ke kesamun credit"

"Aesha ya akayi?" Jin muryarshi yasa duk ta dabur ce tama rasa me zatace daker ta bude baki cikin rawar murya
"Dan Allah Yaya kayi hakuri bansan kai bane" "tambayr da na miki kenan?"
Yayi maganan a kausashe

"Da.... da....ma naga Muhibbah bata shigo school bane har yanxu shine nace bari na kirata naji ko lafiya" tayi maganan a rarrabe.

"Bata da lafiya bazata samu shigowa ba" kit ya yanke kiran.

Wayan tabi da kallo tana ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseran gudu, masifar ya Fu'ad se shi tafada tana toshe baki kamar tana gabanshi juyawa tayi ta koma class.

Ganin drip din ya kare yasa ya cire mata ya koma ya zauna

Yana zaune bakin gado kanshi kasa yana operating wayanshi yasoma jiyo kukanta

Juyowa yayi ya kalleta yana dafe goshinshi a hankali ya furta "ya Salam, yarinya se kuka kamar 'yar baby tayi kuka hakanan ma bare yau da dalili"

Karasawa yayi ya yaye blanket din ya zauna ya dagota ya dorata kan cinyar shi "Kinyi bacci da kuka ba dole ki farka da kuka ba, ya jikin? Me ke miki ciwo?" Kala bata ce mai ba "Kanki ke ciwo? Ko kafar ce har yanzu ke zafi?" Saurin daga kai tayi, takara ma kukanta sauti

"Yaya shikenan ka lalatamun kafa nazama gurguwa" hancinta ya dan ja "Injiwa muje nakara gasa miki ita zata warke" mikewa yayi da ita ajikinshi ya nufa toilet ruwan zafi ya hada ya tsomata hade dayi mata wanka ya na dota a towel ya fito dakinta ya nufa da ita ya ajiyeta bakin bed ya dauko kayan shafan ya zauna kusa da ita yafara shafa mata body lotion batasan lokacin da ta waro ido ba suna hada idanu a kunyace tayi kasa da kanta wani mugun nauyinshi take ji ji take kamar kasa ta tsage ta shige

"Wai kunyata kike ji matar Yaya?, zama ki gama gulmanki ki bude idon ne"

Har powder shi ya shafamata ya dauko mata abaya orange colour ya zira mata yanaji tana shagwabar ya kyaleta tasa da kanta yaki kulata.

Sama yayi da ita "Muje ki yi break fast" "Ni ka saukeni na tafi da kafata" "Na hutasshe ki bari na cika ladana" se zilo take amma yaki sauketa, kan kujera ya ajiyeta ya juya ya nufa kitchen bayanshi tabi da kallo yamata kyau ainun sanye yake cikin tsadadden yadin shi me taushi Blue Black yakawo hula ya daura, batasan lokacin da tasaki murmushi ba.

Be jima ba ya dawo rike da tray ya ajiye kan carpet ya daukota yamata masauki akan cinyarshi ya shiga bata farfesun

Lecture daya gare su basu jima ba suka fito daga class suka Kamo hanya driver yazo ya dauketa tayi masu Umaina sallama "Ki gaishar da Fateema Allah yakara sauki idan gobe bata shigo ba in Sha Allah zamu zo mu gaisheta" cewar Ramlat

"Ameen zataji".

Gidan Muhibbah tace driver ya kaita bakin gate ya ajiyeta tayi knocking me gadi ya bude mata tashigo

Door bell din ta danna Jin shiru yasa ta murda handle din kofar takoyi sa'a a bude yake kutsawa ciki tayi da sallama

"Kai matar Yaya kina ina ne ciwon nan ya isheni se ance ciki gareki se kice aa toh yau nida kaina zan miki tes......."

Maganan ce ta yanke ganin Muhibbah zaune kan cinyar Fu'ad hada idanun da sukayi yasa da sauri ta juya tana furta innalillahi wa inna ilaehi raji'un..............




*>?p? Aminiyar ango >?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*

*Page 46*

https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8



"Zo nan" kamar saukan aradu haka taji muryarshi ya dira a kunnenta sum sum sum kamar mara gaskiya ta juyo ta karasa ta zauna kan kujera, cikin rawar murya tace "Ina kwana"

"Lafiya kalau! Ya school har kun tashi?"

"Alhamdulillah! Eh dake yau lecture daya garemu" Kai kawai ya jinjina.

Ganin Aesha yasa kunya ta kara kamata tayi saurin mikewa ya maida ita zaune, ta bude baki zatayi magana suka hada ido dashi ganin kallon dayake mata yasa taja bakinta tayi shiru dole ta cigaba da karbar abincin, ita dai Aesha tayi kasa da kanta se wasa da yatsunta take jinta take kamar a kan kaya da tasanin zuwanta ta shigayi bata taba tinanin zata sameshi gida ba, taci abincin babu laifi ganin tana kauda Kai yace "Heebbah! Kin koshi ne?" Kai kawai ta gyada.

Mikewa yayi da ita ya ajiyeta gefen Aesha ya juya ya tsuguna da niyyan dauke tray din Aesha ta karasa dasauri ta tattare kayan ta dauki tray din ta nufa kitchen.

A gefen kujeran ya zauna ya gimtse hannunta cikin nashi "Heebbah! Ya jikin yanxu meke miki ciwo? uhmmmm!"

"Kafata" tafada tana marai raice fuska" "oh sorry ze dena kinji ko?"
Kai ta gyada

"In dan fita tunda Aesha tazo ta kulamun dake?" Jin jina Kai tayi ta dan yi murmushi jin yadda yake tambayarta wai ya fita kamar wani yaro

"Yauwa habeebtee bazan jima ba zan dawo, Aesha zata kula dake, idan kafar ta takuraki ki kirani" batace kala ba ita dai binshi kawai take da ido kamar bakon halitta zuciyarta fal mamakin shi jin abun take kamar film.

Aesha ya kwala ma kira tunda ta kai tray kitchen taki fitowa gudun ta takura musu tabarsu su sarara Jin muryar Fu'ad na kwada mata Kira yasa tafito da dan sauri

"Zaman me kike tun dazu a kitchen"
"Babu komai" ta furta a sanyaye.

"Zan fita bazan jima ba zan dawo ki dafa mata abinci, ki kula kafarta na ciwo idan zata tashi ki dan taimakamata idan kinga bazata iya ba just give me a call"

"Toh Yaya seka dawo" Kai kawai ya Jinjina

"Sweety I'm going bakya bukatar komai? Zan iya tafiya? Ko zakiyi wani abu na kaiki toilet? Uhmmm" runtse ido tayi wani abu yazo ya tokare zuciyarta sweety daya kirata dashi se taji kamar Mukhtar dan sunan da yafi kiranta dashi kenan duk inda taji sunan seya fadomata a rai shedan ta kora tayi murmushi

"Yayana katafi abinka idan ina son wani abu ma ga sister nan, Allah yatsare yadawo da Kai lafiya" "Ameen! Me kike so na tawo miki dashi?"

Seda ta dan rausayar da Kai kan tace

"Kanka! idan kayimun haka kagama mun komai" ta fadeshi tana sauke boyayyiyar ajiyar zuciya dan daker ta tattaro jarumta ta iya fadan kalaman.

Murmushi me sauti yayi "Indai nine bakida matsala in Sha Allah, Amma ban dani ki fada me zan tawo miki dashi"

Yaji dadin kalmarta bancin Aisha na nan da sun koma gado ya nunamata zazzafar kauna, ji yayi yana bukatar Koda iya runguma da kiss ne yamata.
Dan kallon Aeshan yayi yaga ma hankalinta na kan wayarta, amma duk da haka baze iya ba.

Kamar bazatayi magana ba can tace "Chocolate" tafada a takai ce

Jan hancinta ya danyi "Sha zumamiya kedai bakya gajiya da Shan zaki, natafi karkiyi kuka kinji take care please" ya fada in a low voice
"Adawo lafiya"

Peck yabata a goshi da hannunta yafice yana murmushi, Kalmar sha zumamiya daya fada yakara tina mata da mukhtar dan baya so take Shan zaki kullum complain dinshi kenan Kuma baya gajiyawa da kawomata kayan zakin duk dan tayi farin ciki hawaye ne yaso zubowa tayi saurin mai dashi tabi kofar parlourn da kallo tana murmushi jinta take kamar a wata sabuwar duniya tanaji duk duniya babu Wanda ya kaita farin ciki.

Seda ta leka taga fitarshi daga gidan kan ta dawo da sauri

"Oh ni matar Yaya irin wannan kauna haka har Ina ya ilahi wllhi kun tashi kaina Omo see love"

"Sa ido mutum na cikin shan soyayyarshi kinzo kin katse mai Jin dadi" tafada maganan da zolaya.

Dukan wasa ta kai mata "Ah ni na hanaku Jin dadinku ne duk soyayyar da kukayi a gabana zakice na hanaku kiji sharri"

"Toh ai kinsan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login