Showing 48001 words to 51000 words out of 112768 words

Chapter 17 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

gas ta zuba man gyada onion da kayan miya ta kawo spices da seasoning ta zuba ta jujjuya, oven taje ta dauko naman Kazan tazo ta juyeshi cikin pot din ta jujjuya ta kawo taliyan dake basket ta zuba ta jujjuya ta barshi for some minutes ya dan kara dawuwa kana ta sauke ta zuba a food flask.

Kwakwa ta fere tayi grating dinta ta zuba cikin blender ta kawo ruwa kadan ta zuba ta zuba condense milk ta kawo hollandia yoghurt ta zuba ta zuba madaran gari tayi blending din su ta tace tasa a fridge.

Wanka tayi ta tada sallahn magrib tana zaune tana azkar seda tayi isha'i ta nade pray mat din ta zare hijjab din jikinta ta tsaya gaban mirror tayi shafa ta kawo humra ta shafe jikinta dashi ta nufa wardrobe ta dauko kaya ta shirya cikin kana nan kaya 'yar karamar riga ce me hannun vest se wando iya guiwa ta feshe jikinta da turare ko hula batasaba ta nufo parlourn kasa.

Yana tashi daga asibiti ya nufa gidan Abba ya gaishe su seda yayi alwalan magrib ya musu sallama a masallacin unguwar su ya tsaya yayi magrib be shigo gida ba seda yayi isha'i yana shigowa be tsaya parlourn ba ya nufi dakinshi, wanka yayi ya shirya cikin vest da wando three quarter ya feshe jikinshi da turarenshi na mufaddal

Ta dukar da kanta tana operating phone dinta kamshin turarenshi ne ya sanar da ita karasowarshi, Kai ta dago ta kalleshi karaf suka hade ido tayi saurin dauke Kai tanajin yadda kirjinta ya buga da karfi daker ta bude bakinta da yamata nauyi tace "S..san. nu da dawowa" tafada cikin dan rawar murya "yauwa" yafada yana Jan kujera ya zauna.

Taliyan ta zuba mishi ta dauki cup ta zuba mai juice din data hada sannan ita ma ta zuba nata ta shiga ci

Taliyan ya faraci yayi 2 spoons a ranshi yace ya akayi yarinyan nan ta iya girki haka baki ya dan tabe ya daga kafada alamun ita tasani ya cigaba da cin abincin shi, juice din ya dauka yana kaiwa baki ya lumshe ido, yaci taliyan babu laifi amma yafi Shan juice din.

Parlour ya koma ya barta nan, muryarshi taji yana kiranta "Keeeee" can kasa taja tsaki kana tace "Na'am" "idan kin gama ki hadomun coffee, kisa lemon kisa sugar kadan".

Batace komai ba ta nufa kitchen ta hada mai coffee ta dauki lemun tsami ta yanka guda daya ta matse a ciki ta zuba 1 tea spoon na sugar ta kawo mishi, karba yayi yafara siping

A kujera ta zauna ta cigaba da danna wayanta dan Allah yasani tsoron dakinta takeyi gidan shiru babu motsin mutane gashi dare beyi sosai ba gara ta zauna a parlourn tunda Fu'ad na zaune Koda baza suyi magana ba dai zataji motsin mutum.

Ko kallon inda take beyi ba itama bata juya inda yake zaune ba

Wayanta ne ya dau sauti me dadi First love sunan daya bayyana akan screen din wayan, cikin shagwaba ta dauki wayan "Hello mummy na" seta sa kuka "Muhibbah miye Kuma abin kuka" "To ba kin manta dani ba, dazu Kuma na kiraki bakiyi picking ba, Daddy Kuma nasan ko na kira a lokacin baya gida" "Rigimar ki tasa naki kiranki nabari sekin dan saba da garin, dazu Kuma wayan bata kusa dani shiyasa".

"Ya Daddy, Shima ya Anas sau daya ya kirani" "Lafiya kalau muke Anas yayi missing dinki bakiga yadda yadawo so silent ba babu abokiyar rikici" "Allah sarki my ya Anas"
"Fatan dai kin dena koke koken banza?" Dariya tayi Bata reda tace komai ba.

"Ina yayanki? Ftn yana lafiya" Seda ta dan kalleshi kafin tace "Lafiya kalau" "Haka ake so, Allah yakara mai hakuri dan seya yi hakuri dake" kukan shagwaba tayi Kai Mummy nidai nake hakuri" dariya tayi sosai "Dama nafi so ki zama me hakuri da juriya a gidan mijinki, duk wani gidan aure cike yake da kalubalen rayuwa idan akayi hakuri se a zauna lafiya amma akasin haka gidan nan ze zama me karancin zaman lafiya farin ciki yanayin kaura ne a rayuwar ma'auratan da basu hakuri da juna, zaman gidan aure yana bukatan hakuri, juriya, uzuri, tausayi, kulawa, so, kauna, biyayya wa innan abubuwan guda 8 suna daga cikin matakan da duk ma'auratan da suka takasu ze kaisu ga hanya madaidaiciya, zaman lafiya ze dore a gidansu sannan farin ciki ze dawwama a rayuwarsu.

Kinga hakuri: Wannan na mutum biyu ne se kin zama me hakuri Shima Kuma se yayi hakuri dake amma idan so samu ne hakurin 'ya mace yafi na da namiji zaki ci ribar hakurin a gaba Koda baki samu wajen miji ba zaki samu wajen 'ya'ya domin akwai matakin da zaki kai yaranki zasu maida ki tamkar sarauniya

Juriya: Ana so ki zama me juriya duk abinda miji ze miki ki jure duk tsananin da zaki shiga a gurin miji ko 'yan uwanshi ki jure komai nada lokaci wata rana se labari

Uzuri: ana bukatan ma'aurata su kasance masu yima juna uzuri, zamantakewar da babu uzuri a cikinta bata karko

Kulawa: yana daukan ma'ano ni, Auren da babu kulawa acikinshi babu tattali baya nagarta ki tattala mijinki kibashi kulawa yadda ta dace yanayin kulawa dashi yanayin kaunar shi gareki
Shima kulawa na mutum biyu ne

Kulawa yana daukar ma'anar kiyayye dukiyar miji ki tattala kayanshi ki tayashi kula da dukiyarshi duk wani abu nashi kiyi kafa kafa dashi

Kulawa yana daukar ma'anar kulawa da kanki kare mutuncinki daga kula wasu mazan daba muharramanki ba kiyaye kanki daga shigan banza ko sa kayan da zasu fidda surarki a waje.

Tausayi: kinsan ma'anar tausayi toh matukar babu tausayi da Jin Kai tsakanin ma'aurata toh zamansu babu inda ze je
Shima tausayi na mutum biyu ne

Biyayya: Shine gaba idan har baki ma miji biyayya duk abinda zaki mishi bashida amfani dan baze ganshi ba ko goyashi zaki dingayi indai baki mai biyayya bashida amfani
Biyayya Yana nufin, duk abinda mijinki yace kiyi toh kiyi iya iyawarki matukar be sabama shari'a ba, idan yace ki bari toh duk sonki da abun nan ki hakura ki barshi se a zauna lafiya
Biyayya na 'ya mace ne.

So: ki so mijin ki domin idan babu soyayya duk abin da na lissafa miki bazaki iya yinshi ba, ki koyama zuciyarki son mijinki
So na mutum biyu ne domin ko namiji idan baya sonki baze iya kyautatamiki ba

Kauna: kauna shine gaba domin so tsuntsu ne ya kan iya tashi daga wata bishiyar zuwa wata amma kauna bata tsufa, Shima kauna na mutum biyu ne

Wannan shine kadan daga matakan rayuwar zaman gidan aure, idan nace zan zayyano su gaba daya a yau zamu kwana zaune bamu gama ba.
Dan haka
ki koyama zuciyarki kaunar mijinki kiyima iyayanki biyayya Allah ze taimakeki kinji ko?".

Kai ta Jin jina tana share hawayen da suka silalomata

Yana sauraron duk nasihar da mummy ke mata se yaji duk jikinshi yayi sanyi.

"Dazu umman Mukhtar da Zarah suka zo yimana ban gajiyan tashin taro" "Allah sarki umma ai ita yakamata aje ama ban gajiya, Allah yabiyata, zan kirata na mata ban gajiya, Amma kinga ya Mukhtar? Ko bashi ya kawo su ba".

"Aa driver ya kawo su, tun kafin biki banji yakara zuwa kofar gidan mu ai" rau rau tayi da ido hawaye sun cikamata ido tace "Allah sarki ya Mukhy na" dagowa yayi ya tsareta da idanu tunda tafara wayan yaji tasa kuka ya daga Kai ya Dan kalleta ya maida kanshi kasa be kara ko kallonta ba se yanzu da yaji tace ya mukhy ta.

Fada mummy tafara mata "Kina matar wani kina Kiran sunan wani namiji ba muharramunki ba, kina so ki hadu da fushin ubangiji ne?" Kai ta girgiza kafin tace "Aa" "Toh kar in Kuma ji kinji ko?" Kai ta Jin jina "Allah yamuku albarka yabaku zaman lafiya, ki gaida yayan naki seda safe" ganin irin kallon daya ke mata yasa tasha jinin jikinta tayima mummy godiya sukayi sallama.
Yana ganin ta gama wayan
Tsamm ya mike tsaye ya ajiye cup din hannunshi akan center table, idonshi ya kada yayi jajir tsabar baccin rai cikin tafiyar shi na takama ya nufota ganin gurinta yake yowa ta mike da sauri tana ja da baya yana binta seda ta kai karshen bango ta tsaya, kirjinta na bugawa da karfi zuciyarta ta tsinke tsabar tsoro hawayen dake kwance a idanunta suka samu nasarar silalowa

Ji tayi numfashinta na kokarin daukewa ganin yazo daf da ita har numfashin su na gaurayuwa dana juna yasa hannunshi daya ya dafa bango se taga kamar ze rungumeta, hancinshi ya kai setin wuyanta yana shin shina lumshe ido yayi Jin wani sihirtaccen kamshi dake tashi a ilahirin jikinta, tsoronta ne ya karu zuciyarta ya tsananta bugu kamar saukar aradu haka taji muryarshi yana magana "A cikin gidana kike Kiran sunan wani Kato a gabana tsabar kin rainani ko? Dasauri ta girgiza Kai "Ya mukayi dake tun a kd? Bance kar in kara ji kin kiramun sunan wani kato ba" runtse ido tayi da karfi dan ta tsani taji yana Kiran Mukhtar da Kato

"Ba tambayarki nake ba" ya fada da dan karfi
Dasauri ta gyada Kai can Kuma tace "K.... Ka...fadamun" "toh iskanci ne yasa kika ambata a gabana ko kunya?" Shiru tayi takasa cewa komai ji take kamar kasa ya tsage ta shige tsabar tsoro "Nace iskanci ne ko raini?"

Tayi Saurin girgiza Kai "Dan Allah kayi hakuri" "Rike hakurinki bakin rai nani ba zanyi maganin bakin rashin kunya".

Ta bude baki zatayi magana taji ya hade bakinsu guri daya...............



*Uhmmmm nayi shiru >???>?? ni nayi nan Muhibbah Allah ya kubutar dake hannun wannan baudaden mutumin*

*Aminiyar ango >?p? >?p?>?p? >?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: =???=???=???=???=???=???
_*SOYAYYAR KWANA ?AYA*_
_BY_
_*FATIMA A MUHAMMAD*_
_AMINIYAR ANGONTA_
=???=???=???=???=???=???
_*TEAM*_
_*ZAFAFAN=?%?DAWA*_
_*JARIRIYAR DAWA*_
_________________________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
________________________

*Page 36*


*Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae*
*Sunada kaya kamar haka....*
*Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....*
*Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt*
*Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted*
*Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......*
*Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol >??*
*Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye

=?G?=?G?=?G?=?G?=?G?=?G? https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t



Kai tashiga girgiza mai hawaye na zarya a kuncinta tana kiciniyar raba bakinta da nashi amma takasa

Hannunshi ya Kai ya zagaye kugunta, hankalinta ya kara tashi tsoronta ya ninku numfashinta yadena fita dai dai, ji tayi kafarta taki daukarta jikinta ya mutu tana kokarin faduwa tayi saurin kai hannunta ta rike kugunshi, seda ya ladaftar da bakin kan ya raba bakin shi da nata ya Kai hannunshi saitin zuciyarta yaji yadda yake bugawa dasauri tsabar tsoro, bakinshi ya kai wajen kunnenta kamar me rada yace "Matsoraciya kawai, kinsan kina tsoro kike rashin kunya? ni babu abinda zan miki bakin rashin kunyan kawai na ladaftar gobe kuma kika kara sena miki abinda yafi wannan, yana Kai nan ya dan tureta ya nufi upstairs"

Tafi minti biyar tsaye a gurin tana kuka kana itama ta haura ta nufi dakinta tana shiga ta rufo kofar da karfi ta murda key, toilet ta wuce ta dinga zira yatsanta a makogoro tana kakarin amai amma yaki fitowa dole ta hakura tayi brush tafito ta kwanta tayi Allah ya isa a ranta yafi cikin kwando, ko miyau taki hadiyewa se ya taru taje toilet ta zubar a haka har tayi bacci da guntun zazzabin daya lallabo ya rufeta.


Yana shiga daki yafada kan bed yayi ruf da ciki yanajin yadda cikin shi ke murdawa se faman sauke ajiyar zuciya yake, mikewa yayi dafe da mararshi ya shige toilet yasakarma kanshi ruwa yajima sosai a toilet din kana ya fito daure da towel ya nufa wardrobe ya dauko rigar bacci ya zira ya kwanta yanata faman juyi har bacci barawo ya saceshi.

Tun 7 ta tashi tashiga kitchen tafara kokarin hada break fast soyayiyar doya da miyan source tayi tashirya dining ta koma daki tayi wanka tashirya cikin doguwar rigan abaya maroon colour

A dining ta zauna ta zuba doyan tafara ci seda ta kusa gamawa sannan ya fito shirye cikin farar t shirt da wandon jeans, kujera yaja ya zauna a kunya ce tace "Ina kwana" "Lafiya" yafada yana kashemata ido daya tayi saurin dukar da kai

Serving dinshi tayi ta mike ta koma parlour dan dama tariga ta koshi, be wani ci dayawa ba ya mike ya fice daga parlourn ta bishi da kallo har yakarasa ficewa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta mike tashiga gyaran gidan.

Parlour ta dawo tayi ta gumi tarasa me Kuma zatayi ta gaji da zama shiru jinta take kamar a freezon karar wayanta ne yadawo da ita daga tinanin data tafi Ummina sunan da taga yana yawo a screen din wayan
Da murmushi ta dauka "Assalamualaikum" "Wa alaekumussalam" "Ina kwana Ummi" "lafiya kalau Muhibbah, ya gidan" "Lafiya kalau Ummina" "Ya zaman shiru, aiki ya miki yawa ko? Bari zuwa gobe za'a samo miki 'yar aiki" Murmushi tayi "Aa Ummi aikin ma babu yawa tunda ba bata gidan ake ba, sedai gidan shiru babu dadi" "Kinga idan aka kawo me aikin zata dinga debemiki kewa kafin ta tafi, Kona turomiki mairo ne? Idan yaso da yamma se driver ya dawo da ita nan saboda nafi yarda da nutsuwarta tafi shekara 5 tana mana aiki batada wata matsala" "Shikenan ummi hakan ma yayi nagode Allah yaja da kwana" "Ameen diyar kirki, Amma se munyi magana da mijinki kinsan baudaden halinshi kar na turota ya korota" dariya tayi tace "Haka ne Kuma ummi" "sekin kara hakuri da yayan naki kinji ko?" Murmushi me sauti kawai tayi batareda tace komai ba "Allah yamiki albarka" "Ameen Ummi, Allah yakara girma" Ameen ta amsa dashi tana ajiye wayan.

Kwanciya tayi kan kujera ta rufe ido tana tino moment din su na jiya bata San ta saki murmushi ba tina yadda duk ta tsure kamar wacce tayi arba da zaki a tsakiyar daji

Sallahn azuhur tayi ta sauya kaya zuwa kanana vest ne se pencil wando se Kai kawo take a dakin ta dauko wayanta ta nufi kitchen cornflakes ta hada madara ta zauna tana Sha a hankali kome ta tina kawai ta mike ta nufi compound

Tana fita ta lumshe ido Jin wani iska me dadi ya ratsata, zagaye compound din tashiga yi tana kallon tsarin gidan tana Jin jina girma da tsaruwar gidan danma bata bi dayan bangaren gidan ba ta zauna a wani chair me kamar lilo dake tsakar gidan

Me gadi da driver na zaune suna kallon yadda take zagaye a gidan har wani bude hannu take tana juyi da tsalle, me gadi yace "Kuruci dangin hauka, ka Kalli yadda madam keyi babu ruwanta" driver yace "Banga laifinta ba, gara tafito tasha iska tunda aka kawota sau daya mutane suka zo gidan nan sedai kaga shiga da fitan oga, ta mori kuruciyarta wata rana baza tayi ba" seda ta zauna a kujeran kana suka shiga gaisheta bata amsa ba se mayar musu da gaisuwan da tayi dan duk cikin su biyun babu Wanda be haifeta ba.

Tana zaune tana Shan lilonta idonta a lumshe kamar me bacci taji an zubamata rankwashi a Kai dasauri ta dafe kan tareda bude ido, ganin shi ne yasata saurin saukowa daga kujeran a tsorace dan bata taba kawowa ze dawo gidan da wuri haka ba.

Tun shigowarshi gidan ya hange ta alla alla yake yayi parking ya karaso inda take

Hanyar parlour ya nufa batareda yace mata uffan ba, A dan tsorace tabi bayanshi ganin shi tsaye cikin parlourn yasata rakubewa a bango inda take ya nufa batayi yunkurin matsawa ba dan tasan ko ina taje seya kamota
Jin hucin numfashin shi daf da ita yasata furta "innalillahi wa inna ilaehi raji'un" can cikin ranta.

Hannunta ya rike da karfi, "Ash" "Me kikeyi a waje?" "Babu komai, nagaji da zaman shiru shine na dan fita nasha iska" harara ya watsa mata ya nunata da yatsa "Da wa innan kayan kika fita, me gadi da?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? driver na zaune suna kallonki ko?"

Girgiza Kai tayi tana zubar da hawaye tace "dan Allah Yaya kayi hakuri banyi wani abu ba fa, kar kamun komai please" takai karshen maganan tana sa dayan hannunta ta toshe bakinta.

Murmushin gefen baki yayi Wanda yakara fito da ainayin kyanshi, murmushin yamishi kyau dan besaba yinshi ba "Me kike tinanin zan miki? matsalar auren kwaila kenan, babu abinda zanyi dake ladaftar dake kawai zanyi tunda bakyajin maganan fatar baki, nanda wani dan lokaci kalilan zan kawo amaryata gidan nan, dan hakama ki kwana da sanin da zaran an dauramun aure zaki kwashe kayanki ki koma kasa Fatan kin fahimta?"

Maganarshi ce ta bata mata rai tace "Dan Allah Yaya ka sakeni nima naje na aure Wanda nake so yake sona, ya mukhtar a shirye yake ya bani duk wani farinc.... " Hannu yasa ya bige bakinta tayi saurin da fewa tana hawaye

"Zaki maimaita abinda kika fada anjima" yana kai nan ya nufi stairs, tana nan tsaye har ya fito rike da wasu files ya fice ya shiga motarshi ya fice a guje dan dama sauri yake wasu files ya manta shine ya dawo dauka.

Da wuri tagama dinner ta shirya dining ta shige daki ta murda key Koda tayi wanka kasa saukowa tayi taci abinci dan kar ta sauka ya ritsata a parlourn.

Kofar dakin taji ana knocking tayi shiru kamar bata dakin Jin alamun ana zira key jikin kofar yasata mike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login