Showing 81001 words to 84000 words out of 112768 words

Chapter 28 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

tashi ba seda tayi isha'i kan ta mike ta nade pray mat din tareda zare hijjab din jikinta

Gaban mirror ta tsaya ta shafa lotion da humra bata shafa komai a fuskanta ba ta nufi wardrobe ta dauko wata riga ta sa ta tsaya gaban mirror tana kare ma kanta kallo batasan lokacin da murmushi ya kwace mata ba se kuma kunya ya kamata tana kokonton fita da kayan amma ta fuske ta dauki turare takara feshe jikinta ta nufi down stairs.

Fridge ta nufa ta ciro juice gudun yayi kankara ta ajiye a dining

Parlour takarasa kan kujera ta zauna ta janyo wayarta ta shiga karatun novel

Yaso ya rasa sallah yana shiga masallacin ana kokarin tada sallah Koda ya fito masallaci seda ya biya mall yayi siyayya kan ya karaso gidan

Har ya tura kofar parlourn ya shiga ya karasa daf da ita bata lura dashi ba saboda hankalinta gaba daya na kan waya habarta ya dago cikin hannunshi a zabure tayi saurin daga idanunta suka fada a nashi boyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke dan ta tsorata tunda bata ji dawowarshi ba

Hawayen dake bin kuncinta ya kai hannu ya dauke tareda zama gefenta ya dagota ya dorata kan cinyar shi ya zagaye hannunshi a kugunta ita kuma ta kwanto da kanta kan kirjinshi tareda gyara kwanciyarta kan jikinshi ta sakalo hannayenta ta bayanshi ta rungumeshi tana sauke ajiyar zuciya

Yana shafa kanta yace "Waya tabamun sanyin idaniyata?" "Babu kowa fa" tayi maganan a sanyaye dan novel din data karanta ya sanyaya mata jiki Kuma ya karamata ilimin rayuwa

"Toh meyasamun Kee kuka haka uhmmmm" yayi maganan yana shinshinan gashinta

Nannauyar ajiyar zuciya tasauke "Wllhi hearty wani novel na karanta *HAIHUWA DA HANJI*"

"Shine yasakamun ke kuka?"
"Allah Yaya book din akwai tausayi ne, a book din zaka san maraici ba karamin abu bane maraici ba dadi duniya ta baci mutane basu dauki zuminci a bakin komai ba ko kai ka karanta se ka zubda kwalla"

"Wannan wane book ne haka bani labari inji" yafada yana cusa kanshi wuyanta yana shin Shinar sihirtaccen kamshin ta.

"Wata yarinya ce fa babanta ya rasu tun tana ciki wajen haihuwar ta kuma Allah ya karbi ran mahaifiyar ta se kakanta mahaifiyar babanta ta dauketa bata wuce 8 years ba Allah ya ma kakar tata rasuwa ta koma wajen innanta kanwar mahaifinta ita ma wajen haihuwa ta rasu shikenan ake kiranta da mayya wai tun tana ciki take maita wasu kuma su ce mata annoba rasuwar kanwar mahaifinta yasa ta koma gun kawunta kanin mahaifinta kawu shima bashida mutum ci yaita zaginta matanshi suke dora mata tallah wannan da safe wannan da yamma Kuma ko kadan bazasu bata ba se dai ta kankare kanzon tukunya taci akwai ranan da ta fita tallah wani daga siyan abincin ta yaci a take a gurin ya mutu nan matasa sukace se sun kashe ta daker aka kwaceta daga karshe kanwar mahaifiyar ta tazo ta tafi da ita taji dadin zama gidan sosai Auntyn ta ta haifa 'yan biyu babu jimawa ta rasu nan kishiyar Auntyn nata ta kwaso jama'ar gari wai ita ta kashe Auntyn nata nan fa ta dauki piya piya ta sha tsabar yadda rayuwa tamata kunci shine wasu sojoji su biyu sun zo wucewa suka ga dan dazon mutane suka karasa gurin dayan sojan ne ya haura Katanga yasameta tana kokawa da numfashinta ya fasa madara yabata kana aka tafi da ita asibiti, anan na tsaya se naji shigowarka" tana labarin tana kuka.

Shima kanshi daya ji labarin seda jikinshi yayi sanyi yakara tsorata da duniya

Hancinta ya ja "yanzu Kuma lokacina ne kibari gobe da rana seki karashe karatun nima zanso inji karshen labarin nan" ya fada yana dauke mata hawayen fuskanta

"Kuma kasan abinda ze kara daga ma hankali?" Ta kare maganan cikin sigar tambaya hade da jimami

Kai ya girgiza kan yace "Aa sekin fada"

"Is a true life story"

Dan zaro ido yayi "Really?" Kai ta jinjina
"Shiyasa labarin ya tabamun zuciyata sosai imagine nake tayi idan nice ya zanyi".

Ajiyar zuciya ya sauke "Ko wane bawa da kaddararshi Heebbah wayanmu ko dubarar mu bazata taba sa mu guje ma kaddararmu ba seta riske mu a duk inda muke, fatan mu dai Allah yabamu iKon cinye jarabawarmu ita kuma Allah yakawo mata mafita irinsu gaba zakiyi mamakin matsayin daza ta taka ita haka rayuwa take baka taba yin nasara ba tare da kalubale ba yayinda kalubale suka tasoka toh akwai nasara na jiranka gaba, Allah yasa mudace"

"Ameen! Ai wannan ko wacce irin nasara ta samu ta can can ceshi wannan uku ban rayuwa haka da kana nun shekarunta" tafada tana sauka daga jikinshi tare da riko hannunshi

"Hearty muje kayi dinner" dan waro idanu yayi se yanzu hankalinshi ya kai kan kayan dake jikinta, riga ce transpered iya guiwa babu abinda be bayyana na jikinta ba

Mikewa yayi yana kare mata kallo yana jin wani abu na fisganshi yana kokarin yin magana tayi gaba tana dariya dole tasa yabi bayanta yaja kujera ya zauna, serving dinsu tayi tana murmushi tana Jin ninkin kaunarshi, ta zuba musu juice din a cup daya ta dare cinyarshi ta shiga bashi abincin a baki ita ma tana ci duk yadda yaso tabari ya ciyar da ita da kanshi ki tayi wai yana mata wayau itama tana so ta hidimta ma mijinta tana Kai mai laumar farko ya lumshe ido

"Wow delicious! bloody kinji dadin abincin nan kuwa?"
"Kai hearty kose ansa ma waigi ne" tafada tana dariya
"Gaskiya gara kisamun waigi kar in fadi wannan dadi har tsakar ka" yafada yana murmushi

Sosai ya karbi abincin juice din ma yasha babu laifi dan bakaramin dadi ya mai ba.

Mikewa yayi da ita suka nufa bedroom dinshi kan bed ya direta da sauri ta sauko tafara balle mai botir din rigarshi tare da mika mai towel ya daura ta juya baya ya karasa cire wandonshi murmushi me sauti yayi "Soon zan cire miki wannan kunyan" ya fada yana nufan toilet.

Dariya tayi ta nufa wardrobe ta dauko mai kaya be san dauriyar da tayi ba wajen balle mai botiran

Gefen bed ta zauna, be jima ba ya fito ta mika mai riga da wando na bacci karba yayi yasa iya wandon ya bata rigan ta maida wardrobe

Gaban mirror ya karasa ya feshe jikinshi da turare kan yadawo ya zauna gefenta kwanto da kanta tayi kan cinyarshi shi Kuma ya riko hannun ta yana shafa bayan hannun da babban yatsanshi dayan hannun Kuma yana shafa gashin ta da be taba gajiya da shafawa indai suna tare.

Wayanshi ya janyo yayi dialing numbern Suhail ringing daya ya daga

"Dan uwa ya akayi ne yanzu nake shirin kiranka"

"Ya ake ciki ne?"
"Uhmmm toh ya zanyi tunda ka gaji da ganina a gwauro zan karbeta kan dole ya na iya ai ba'a maida hannun kyauta baya" ya fada yana dariya

Murmushi yayi
"Kaji dashi dai saura wata rana naga kana rawar kafa a kanta, zan ajiye ma numbern ta dan Allah kayi kokari ka kirata cikin daren nan please"

"Haba rawar kafar me zanyi"

"Kaga ni kam seda safe yanzu lokacin madam ne" yayi maganan yana dage mata gira

Tayi murmushi mara sauti
"Eyyeeee muda bamu da mata mun bani da gori dole nasamu Jafar mu tattauna"
"Idan kunji haushi kar ku bari ku kai Friday baku shiga daga ciki ba" yana kai nan ya sauke wayan yana murmushi

Ita dai tana jinshi amma bata ce mai uffan ba dan bata gane da wanda yake wayan ba

************

Jikin Ammi ta fada ta fashe da sabon kuka hankali tashe Rumaisa ta karaso "Aunty zeeee lafiya? Me aka miki"
Ta fada tana zama gefen su

"Zainab meyafaru? Kiyi magana mana duk kin daga mana hankali"

Dagowa tayi tana kallon Ammi cikin muryar kuka tace "Ammi dr ya gama yanke hukunci baze iya auren mata biyu ba, se dan uwanshi ya hadani dashi"
Bubbuga bayanta ta shigayi kan tace "Zainab ki sani duk abinda kika ga baki samu ba toh ba rabonki bane idan duniya da abinda ke cikinta zasu taru basu isa su hanaki mallakan abinda Allah ya riga ya mallaka miki ba, haka zalika Koda duniya da abinda ke cikinta zasu taru basu isa su miki abinda Allah be miki ba ina nufin basu isa su baki abinda Allah be baki ba dan haka kisani kowane bawa yana da tashi kaddaran, ba komai muke so muke samu ba. Doctor ya cika mutum me halacci ki Karbi kyautar daya miki hannu bibbiyu muyi fatan Allah yasa hakan ya zama na shine mafi alkhaeri kinji ko?"

Gyada Kai tayi tana share hawayen ta kan ta mike ta nufi daki Rumaisa ta mara mata baya sosai takara rarrashinta ta kawomata ruwa tasha kan ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya.

Wayarta ce ta dau kara Rumaisa ta dauko ta mika mata ganin bakuwar number yasa har ta katse bata daga ba Jin an kara Kira yasa tayi picking ta kara a kunne batare da tayi magana ba

"Amincin Allah yatabbata ga gimbiyar mata"

Dan wara idanunta tayi ta kara kallon numbern kan ta sake karata a kunne cikin shakakiyar murya tace "Ameen tare da Kai"

"Lafiya kike kuwa naji muryarki haka ko bacci kike na tashe ki"

"No! Kaina kemun ciwo"
"Eyyyaaa sorry Allah yabaki lafiya"

"Ameeen" shiru ne ya ratsa tsakani na seconds kan yace "Nasan baki gane me magana ba ko"

Daga kai tayi kamar yana gabanta kan tace "Uhmmm"

"Ina fata Dr ya miki bayanin komai"

Dama tun sallamarshi tayi tinanin shi din ne

"Uhmmmm yayimun" abinda ta iya fada kenan

"I'm by name Suhail Abdullahi Muhammad BICHI"
"Zainab Sa'ad" ta fada a takai ce

"Nice name! zainabu abu me ta gwayen suna, Fatan zaki sama mun special place a zuciyarki"

Murmushi me sauti ta danyi ba tare da tace komai ba

"Kinyi shiru gimbiya ta"
"Uhmmm" abinda tafada kenan

"Me uhmmm yake nufi ban gane yaren ba ko fulatancin 'yan yolah ne"
Dariya tayi tace "Aa wllhi ba haka 'yan yolah ke fulatancin su ba"

"Yaren ki ne kenan toh a fassaramun"

Dariya sosai tayi kan tace "Eh" be kuma cewa komai ba yayi murmushi dan yasan kunyarshi take ji, sosai suka sha fira yana zolayanta tana dariya har ta sake dashi

"Bari na barki, kisha magani kafin ki kwanta please, Allah yakara sauki" "Ameen tnx"

"Sleep tight"

Daga haka sukayi sallama

Wayan tabi da kallo tana murmushi Rumaisa da take gefenta tana danna wayanta amma tanajin wasu abubuwan da suke cewa ta matso ta rike hannun zeeee tana murmushi

"Aunty kinga kyautar ubangiji ko?, kina ta addu'a Allah ya mallaka miki Dr daya tashi seya musanya miki da wani, kuma shima da gani beda matsala Kuma shi yanada magana ba kamar dr Fu'ad ba"

"Haka ne 'yar kanwata a alamu yanada kirki Kuma yanada barkwanci" kwanciya tayi tana murmushi tare da yima Allah godiya se murmushi take daren ya mata dadi sosai

********

Daukarta yayi ya kwantar da ita tsakiyar gado ya kwanto kan jikinta yana binne kanshi a wuyanta

"Hearty" "bloody ya akayi"

"Dan Allah kayi hakuri da abinda ya faru a school, wllhi ban taba yi mai magana ba amma nasan nayi kuskure Ina tsoron kayimun fada ne shiyasa ban sanar maka ba" seda ta numfasa kan ta cigaba da magana "Malam Mukhtasir Kuma kai kace mishi kanwarka ce ni shiyasa nima ban fada mishi matarka bace saboda naga baka son jingina kanka dani Kuma ban kai matsayin da zaka nuna ma mutane ni matar ka ba ce"

Be bari ta Kuma magana ba yasa hannu ya toshe mata baki yashiga yawo da hannunshi a jikinta har ya rabata da rigar jikinta, babban yatsan kafarshi ya shiga yimata susa dashi a tafin kafarta ya kai bakinshi yana huramata iska yanayi yana yawo da harshenshi cikin kunnenta zauta ta yake neman yi, a dan tsorace take dan be san yayi kadan ya hakura ba gashi ita kuma tarasa abinda yasa har yanzu ta kasa sabawa bata so ta cika raki ne shiyasa ta daure

Gaba daya ya rude itama ya rudata bakinta ta dora saman nashi tashiga ai kamai zazzafan kiss hannunta Kuma ta cusa shi cikin suman kanshi tana ya mutsawa sosai salonta ke shiganshi a hankali ya ratsata sun jima a haka seda ta fara kananun kuka kan ya kwanta gefenta ya janyota jikinshi yana sauke ajiyar zuciya yana bata peck ta ko ina.

Tare sukayi wanka suka dawo suka kwanta yaja blanket ya rufesu, bakinshi ya kai saitin kunnenta

"Fateema! Ina matukar kaunar ki baki yayi kadan wajen furta irin tarin kaunar da nake miki, ni din mallakin ki ne kuma sirrinki ina sonki fiye da kowa da komai a fadin duniyan nan na mallaka miki ragamar rayuwata se yadda kike so zakiyi dani, idan nace miki tun baki san kanki ba zuciyata ke dawainiya da kaunar ki zakiyi mamaki ko?" Dan ware idanu tayi tana binshi da kallon rashin fahimta

Murmushi yayi tare da jinjina Kai "Tun tasowar ki nake matukar kaunarki Heebbah, wannan labari ne me tsayi kiyi bacci idan mun samu time har dalilin dayasa na nemi muyi *soyayyar kwana daya* zan fadamiki"


**********

Koda ta tashi Jin ranta take a sake nauyin dake zuciyarta duk babu shi tunda tasa son Fu'ad a zuciyarta farin ciki yayi kaura a rayuwarta kullum cikin tinanin shi take amma yau kam Jin ranta take Kal. Wanka tayi ta fice parlour tasamu har an shirya dining zama tayi tana gaida daddy ya amsa cikin kulawa kan ta gaida Ammi itama ta amsa fuska a sake kana suka gaisa da Rumaisa

Suna breakfast suna firan su har suka kammala Daddy ya fice suka bishi da addu'ar dawowa lafiya kan Ammi ta Kalleta

"Zainab wannan farin cikin fa kamar wacce akama kyautar kujeran hajji se zabga murmushi kike tun dazu"

Murmushi kawai tayi ita kanta ta kasa boye farin cikinta

Rumaisa tace "Ammi tino kalaman da wannan dan uwan Dr Fu'ad din ya mata take, yama sunanshi?" Ta fada tana kallon zeeee

Harara ta watsamata "Bansaniba magulmaciya"

Dariya sukayi ita da Ammi "Ah Zainab jiya kin tafi daki da kuka yau kin fito kinata fara'a ai da walaki wai goro cikin miya, Alhamdulillah kice daga yau kuka ya kare"

A kunyace ta rufe fuska tana murmushi.

**********

A dining ya sameta tana ganin shi ta fadada murmushin ta "Good morning my heart"
"Morning blood" ya fada yana zama

Break fast sukayi cike da so da kauna seda suka kammala ya mike "Dauko jakarki na saukeki school"

Jikinshi ta fada ta kankame shi "thank you so much my heart"

Peck yabata a goshi

Da sauri ta haura dakinta ta dauki hijjab ta zira ta dauko Jakarta tare da dialing numbern Aesha

"Hello! Ki sameni school nayi gaba"

Tana zaune dama tana tinanin school din ta mike tayi tsalle

"Dagaske ko wasa?" "Bansaniba nidai nayi gaba" tana kai nan tayi hanging call din ta nufa down stairs

Ta samu har ya fice itama tabi bayanshi ta bude gaban motan tashiga yaja ya fice daga gidan

Har cikin school din yashiga kafin yayi parking ya dauko face mask ya mika mata

Kallonshi ta danyi ganin beyi magana ba yasa ta karba tasa yace "Daga yau duk lokacin da zakije school bana so naga fuskarki a bude se kin shiga class ki cire idan zaki fito Kuma kitabbatar kin mayar. Ko na siya miki nikab ne?" Bata fuska tayi ta girgiza kai "No! face mask din ma ya isa"

"Kuma ban yarda dasa karamin gyale ba idan zaki school kinji ai" Kai ta gyada

"Bakiji abinda na fada bane?" "Naji"

Kudi ya mikamata ta karba "Thank you" tafada tana fita daga motan kan ta dan tsaya tace "Allah yatsare yabada sa'a yadawo mun da kai lafiya"

"Ameen" ya fada yana murmushi seda yaga ta nufi hanyar department dinsu kan ya ja motar yabar school din

Ya dauki hanyar asibiti kenan wayarshi ta dauki kara ganin sunan malam mukhtasir yasa ya cije lips din shi na kasa da karfi kan ya kara wayan a kunnenshi

"Barka da safiya Dr" "Barka dai" yafada ba yabo babu fallasa

"Dama maganan da mukayi ne nace bari na tina ma nasan abubuwa suna maka yawa yanzu haka ka manta"

"Bata taba fada maka tanada aure bane?"

Daburcewa ya nemiyi "Aure Kuma"

"Eh mata ta ce"
Wayan ya kara bi da kallo yaga numbern Fu'ad din dai ya kira

Cikin rawar murya yace "Wllhi doctor bansaniba bata taba fadamun ba"

"Ai gashi yanzu kaji"
"Dan Allah kayi hakuri rashin sani ne"

"Ya wuce" ya fada yana katse Kiran

Se 2 suka tashi driver yazo ya daukesu

"Wai nikam Muhibbah ya akayi kika sa Yaya ya sauko da wuri haka abin ya bani mamaki"

"Oh ni zarah wannan sirri ne tsakanin mata da miji babu ruwanki ke Kam"

Baki ta tabe "Kyaji dashi dai, muma zuwa zamuyi muyi auren nan ko zan huta da gori abu kadan miji miji haba"
"Kin shaka ne?" "Hmmmm muma Allah ya bamu mijin"
"Ameen" ta fada tana dariya

Kamo hannunta tayi "haba 'yar kanwata Kinsan nida ke ba'a jinmu ko sorry"

"Yauwa nikam kin karanta *haihuwa da hanji?*"

"Aa gaskiya ban karanta ba na wace marubuciya ne?"

"*Fatima Muhammad Gurin (Gureenjo)*"
"Gaskiya ban ganeta ba"

"Marubuciyar *Rubutu akan ruwa* littafin Aysha da Emran tana kiranshi da (Abba ko tace Eshran) matarshi Kuma Nainah

"Oh na gane ta kai ta iya novels ba karya kinga rubutu akan ruwan nan yayi dadi, ba akwai su asmy su murad ba"

"Ai ni har yau bana gajiya da karanta rubutu akan ruwa littafin nan yayi dadi nakasa mantashi"
"Wannan ma ya hadu sosai na Afeefah yarinyan na shan uku ba a labarin. Kuma true life story ne"

"Dan Allah fa?" "Wllhi kuwa har hearty naba ma labari nima ban karasa karantawa ba se idan na koma gida"

"Eyyeeee su hearty manja" "Kinganki hmmm bazan biye miki ba nayi magana kice namiki gori"

"Kituromun novel din please" "okay in Sha Allah zan turamiki ta watsapp"

A kwana a tashi babu wuya har su Muhibbah sun gama exams sun koma school suna shiryayen exams din second semester

Soyayya tsakaninta da Fu'ad kuwa ba kama hannun yaro se abinda yayi gaba kullum sabon shagwaba take fito dashi shikuma yana faman tarairayarta.

Suhail da zeeee ma kullum soyayyar su kara karfi take dan suhail yazo sun ga juna Aesha da Muhibbah ma sukan Kai mata ziyara wata rana su dameta ta janyo Rumaisa su zo gidan ummi...................


[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD AMINIYAR ANGO*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login