Showing 36001 words to 39000 words out of 127150 words

Chapter 13 - SANGARTATTCE COMPLETE

01 Nov 2026

230

acikin jakar, da gudu tai wurin tana share hawayen dataji yafara kwararowa, kaman daga sama yaji ance "mena maka kafasa aure na?" dago kai yayi asanyaye ya kalle

ta gani tayi idanunshi sunyi jajir suma harma sun kumbura, kasa daurewa tayi tafashe da kuka sosai tasa gyalenta tana sharewa bata ma damu da mutanen dake shiga shagon siyan abu bama cikin kuka tace "maiya sameka idanunka sukai haka? Mena maka? Maiya sa ka

ce kafasa aure ne kasan illar da hakan yamun kuwa? Inda kasan baka sona maiya sa tuntuni baka fadaba sai a wurin daurin aure? Maisa kamin haka eh?" baki yabude zaiyi magana saikuma yafasa yay shiru taga ya kurama bayanta ido, da sauri ta juya dan taga maiy

ake kallo Ayaan ne acikin mota yay wining glass down idanunshi sanye cikin bakin glasses,

daure fuska yay tamau ya kalleta babu alamun wasa atattare dashi yace "get in" kaman bada ita yake ba ta juya ta kalli Isyaka daya cigaba da hada kaya abinshi kaman b

ashi a wurin tace "kasan yanda nake sonka kuwa shine ka cutar dani haka ko, maiya sa kamin abinda kami..." tsawan dataji yasa takasa karashe maganan datake yi. "are u deaf nace kishiga mota mutafi" yay maganan har lokacin yana zaune cikin mota afirgice ta

juyo tafashe da kuka sosai batare data shiga motar ba mutane sai kallon su suke, bude kofar yayi yafito yana wani irin taku da duk taku daya saitaji har a kokon ranta, da sauri ta runtse ido sabida wani irin mugun tsoron dataji yana shigan ta, hanunta data

ji ya fizga kaman zai katsa yasa ta bude ido janta yayi ya bude mota ya wurgarta ciki kafin ya koma ta dayan side din yanama Isyaka dasuka hada ido wani irin kallo, da sauri Isyaka yadau jakar ya juyama motar baya kirjinshi na bugawa, wani irin dan iskan m

urmushi yayi kafin ya bude motar ya shiga ya bata wuta, kuka take kaman ranta zai fita kanta nakan cinya.

Bai tsaya ko inaba sai gidan dam, wurin babu kowa gashi very peaceful sai iskan bishiyoyin daketa kadawa da kukan tsintsaye dake wucewa, zagayawa y

ay ya bude side din datake har lokacin kanta nakan cinyanta kuka take sosai cikin kakkausar murya yace "fito" ko dago kai batayi ba balle yasa ran zata fito, hakan yasa ya jawota da karfi luuu ta taho zata fada kanshi dan ko karfi daya bataji dan rabonta d

a abinci tun jiya ya matsa gefe da sauri hakan yasa ta zube akasa, wani wahalanlen kuka tasaki ahankali tana share guwiwar hannunta daya bugu da kasa, ya dawo ta gabanta yay wani irin tsugunnawa daya karamai kyau yana karkada key motar dake hanunshi yana

mata wani irin kallo yace "baki da natsuwa ko, bakisan kinada aure ba zakije kina ma wanchan dan kauyen magana" turo baki tai cikin kunci tace "Isyaka na niba dan kauye bane karka sake cemai dan kauye" takarashe maganan tana wani lankawasa wuya gawasu saba

bbin hawaye dasuka zubo mata tsabagen takaici, dagota yay da karfi ya jingineta jikin mota ya kafeta da ido da sauri ta kawad dakai tareda sa bayan hannu tana goge kwallan yace "ke ki natsu fa banason raini ko kadan wlh, auren taimako nayi, na taimake ki d

a mahaifin ki danaga hawan jini na neman kamashi da almajirin chan yace yafasa auren ki" murguda mai baki tayi dan wlh yakaita bango tace "eh almajirin ne aidai Allah ya halicce shi, kuma ahaka nakeson abuna har yanz..." bakinta daya kaima duka da karfi ya

sa tai shiru ta fashe da kuka, hanunta ya kama yakai baya ya murde hakan yasa ta bankare tana ihu. "wayyo Allah na Mama zai ciremin hannu" hadata yay da mota ya matseta danhar jikinsu na gogan juna ya kalli kwayar idonta yace "wlh idan kika sakemin rashin

kunya sai namiki abinda zaki dinga kuka tunda ga yau har ranan daza'a kawoki gidana".....

[7/17, 11:57 AM] +234 814 359 8303: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

33 - 34

Ya ja hanunta ya bude side dinta ya wurgata ciki kafin ya koma mazaunin

driver ya shiga ya yatada motar yabar wajen, duk tacika mai mota da kuka abakin layin su yay niyar sauketa hango su Abba da Malam awaje yasa yawani dakamata tsawa. "ke!" atsorace ta dago kai ta kallai hannu ya daura akan lips dinshi alamun tai shiru hakan

yasa ko tai shiru har yakarasa kofar gidansu, aiko su Abba sukabi motar da kallo parking yay

yafito da sauri ya zagayo ta inda take ya bude mata daidai nan su Walawa dasuka zo wurinta suka fito daga gidansu, murmushi both Abba da Baba harda Baba Sulaiman

duk sukayi hankalin su yakara kwanciya ganin Ayaan da Bilkisu tare. Fitowa tayi daidai lokacin su Walawa sun iso sai kallonshi suke atare suka gaidashi "ango ina yini, ina kukaje kaida Amaryan tun dazu mukaxo fa" murmushin dole ya kakalo ganin su Abba a wa

jen itakuma wucewa tai cikin gida abinta, su Walawa sai uban surutu suke mai yana yake daga baya sukamai sallama rapper kudi yaciro yabasu suka karba sukamai godiya kafin su koma cikin gidan.

Sai bayan azahar suka tafi bayan sun cika gidan da kayan abinci

da kudi duk yanda malam yaso yaki karba kin yarda Abba yayi yace ai yanzu anzama daya kafin su wuce kano kowanensu rai fess.

**************

Tun tanama su Umma, Mama da Baaba kuku asaurareta ana lallabata har yazo kowa yafita harkan ta to uban ma me z

asu iya aure dai anriga an daura saidai kuma abisu da fatan alheri, ganin babu mai sauraron ta danhar su Walawa sunfison Ayaan sunce mezatayi da Isyaka daya wulakan tata ranan daurin aure yace bayaso, tama godema Allah yaro dan gayu yace yanayi, hakadai ta

tattara ta manta da alamarin tacigaba da zuwa school abinta ta dage da karatun exam, Mami na yawan kiranta ganin haka yasa duk Friday saita turama Mami Friday message mai dadi da ma'an hakan ko ba karamin faranta ran Mami yakeba.

Cikin iko na ubangiji ta

fara zana jarabawan ta abinta sosai ta dage tana karatu ta manta zance wani Ayaan da Isyaka, inbama su Walawa sun kirata da matar Ayaan ba wanda yanzu shine sunanta har mantawa ma take ita matan aure ce, kumama wai Matar dan iskan nan maisa sarka da dan k

unne hmm.

Zaune yake akan daya daga cikin kujerun platinum table dake cikin club din wanda aka jerasu mussam sabida mayan, non alcoholic wine mai sanyi waiter ya zubamai a glass cup kasancewar sunsan shi bayashan alcohol, gefenshi wasu maza ne hadaddu g

uda biyu wanda suke friends dinshi tare sukai school, daya daga cikin sune mai suna Fawaz yace "wai kai bazaka je ka dubo matar kaba yanzu more than a month kenan da bikin ku da baka gayyace muba" jan tsaki yayi tareda kara relaxing ajikin kujeran dayake k

ai yanabin wankan dake tashi a club din na Drake, dariya su biyun sukayi banda shi daya wani lumshe ido dayan ne mai suna Paul yace "yo wai tayaya ma wanda zai aureta kace yafasa awurin daurin auren, mekayi Ayaan? I know u have something to do with him say

ing bazai aureta ba" sai a lokacin yadan yi murmushi kadan kafin yawani tabe baki yana girgiza kai yace "nothing much, I just threaten d poor guy, bayan nasa an kamomin shi na kusan harbinshi da bindiga ya tsorata harda kuka fa wai bayason ya mutu yanzu he

's just 25, yadan ban taudayi so saikuma na cikamai aljihu shikenan" dariya sukahau yi dukan su Fawaz yace "shege mugun iche, ashedai kana son yarinyar" da sauri ya kallesu kafin ya murtuke fuska yace "guys banson iskanci, ni" yanuna kanshi yace "ni, ni, m

e fa, inso yarinyar nan wanan yar kauyen? God forbid, Allah ya kyauta, she is not my type infact tamamin kadan as my woman, i did wat i did for Pops, u know he's old yo, so banison abinda zaisa yay breaking down, i gats make d old man happy now" atare sama

rin suka gyada kai suna "yeah hakane, we gats make our Pops happy kam" drinks dukansu sukai sipping atare Fawaz ya kalleshi yace "wat about ur Meram?" kallonshi yadanyi kafin ya maida mai da tambayar. "wat about her?" Fawaz yay yar dariya yace "i mean baka

sonta bazaka aureta ba ita? Me relationship din dake tsakanin ku dont u

have feelings for her" tabe baki yay yace "Gee, get this straight nifa aure ko soyayya bayama ajenda na, infact inda baku tunamin da dat low life girl da Pops yahadani da itaba ninama

manta inada wata so called wife, and Meram, Meram" yakira sunan sau biyu yanadan rolling eyes dinshi saikuma ya tabe baki yace "ina more rayuwana da ita ne kawai anytime am in d mood, babu komi tsakanina da ita, she's just a girl dat love giving her self

to me okay" dariya duka sukayi Fawaz yaciro wayarshi yace "lemme call my babe nima" tabe baki yayi kafin ya mike yaje dance floor yafara rawa abinshi yana sipping wine din glass cup din hanunshi.

Sai gurin sha biyu suka fito daga club din kowa yaja mota

r shi dan zuwa gida. Abangaren shi yay parking yafito yana kwance belt din wandon shi ya bude kofa ya shiga daki, zaune yaga Abba a kujera ga dukkan alamu shiyake jira, dan sosa kai yayi yamaido kofan ya rufo yazo kusa da Abban daya kafeshi da ido dan murm

ushi yayi yace "Pops bakayi bacci ba" yay maganan yana zama tareda daura kanshi akan kafadar Abba, sosai yay niyar mai masifa amma saiya sassauta murya cikin lallashi yace "Boy lokaci yayi da u will stop clubbing, da nabarka ne sabida inama kallon yaro but

yanzu ai ka girma tunda ma har ka ijiye mata, ehen talking of mata wat do you mean ne eh? More than a month yanzu bakasan kaje ka duba matar kaba, ina so gobe goben nan ka shirya kaje" daure fuska yay tamau kaman zai fashe yace "zanje hospital gobe akwai

aikin da zanma wata" "karya kake" Abba yatari maganar shi afadace ya nunashi da yatsa yace "wlh inhar baka tattara komi ka ijiye gefe ka wuce kadubo matar ka gobe ba saina saba maka" ya kamo kunnenshi tareda daye dankunen diamond din daya makala da gum kar

a yayi. "Pops zafiiii" ya dafe kunen kaman zaiyi kuka Abba ya cillar da dankunen yace "wlh karna kara ganin ka dasu, wanan shegiyar sarkar ma kacire, kai ai ba mace bane" turo baki yay yace "sarkan ma ai bana mata bane, baka gani bane Pops namaza ne fa" "I

've said my own, first thing tommorow morning kabar gidan nan kawuce kaje ka dubo matar ka, hakkin ta na kanka be careful" Abba ya wuce yafita yana masifa.

Da gudu take tafiya danyau ko tsayawa karban waina batayi ba daga wurin Baaba, yaune take rubut

a last paper ta Civic education kuma karfe biyu ranane paper bacci tayi babu wanda ya tasheta dan Mama da Umma sunje barka, biyu saura minti goma ta tashi hakan yasa ta zabura tasaka kayan makaranta tafito tana kaiwa bakin titi tasami Bus ta shiga, abinka

da bus sauke dauka ba ita takai makaranta ba wuraren karfe biyu da rabi, sunayen Allah kawai take kira ta shiga makarantar da gudu tai exam hall atsorace takai bakin class din ta tsaya yan aji sai kallonta suke su Walawa dake rubutu suna mata alamu data sh

igo, kallon fuskar invigilator tayi ganin baice karta shigo ba saima wani kallon wulakanci dayake mata irin na kinyi latti kinkuma tsaya awaje dinan yasa ta kwasa da mugun sauri tai cikin hall din, tsayawa tasake yi dan tsoron zuwa ta karbi booklet da ques

tion paper take ganin ya mikomata daga inda yake zaune yasa tai inda yake da saurin ta, zuiiii tai wani irin mugun faduwa sakamakon bawan ayabar dake kasa data taka wani irin mugun ihu tayi dan saida ajin duka ya dauka sakamakon faduwa datayi gabaki daya

ta saitin ciwonta, dan ciwonne ma yafara buga kasa kafin sauran ilahirin jikinta, da sauri shi kanshi invigilator ya sauko daga kan kujera su Walawa ma haka duk aka zagaye ta, Walawa tasamu ta damke da karfin bala'i cikin kuka tace "Walawa na bige ciwona u

hm uhm uhm" wani irin nishi take tana kuka sosai tama kasa magana, invigilator yace "ku kira principal dinku" da gudu yan

ajin aka fita aka kira principal koda tazo tuni Bilkisu tafice hayyacin ta sabida azaba kuka kawai take da ihu, Keke napep principal t

asa aka kira ta dubi dabilan ajin tace "wayasan gidansu?" su Walawa ne suka daga hannu hakan yasa principal din tace "kuzo ku maidata gida wurin iyayenta ku dawo yanzun nan sabida kuyi jarabawar ku" kokarin mikar da ita ake ta kankame Walawa tana ihu "dan

Allah dan Allah nace wlh inna tashi fashewa cikin nan zaiyi" tana maganan tana kukkule ido kaman mai shirin suma, principal tace sudauketa, taruwa sukayi suka dauketa suka saka a Keke Walawa da Aisha shehu suka bita sai gida.

[7/17, 12:04 PM] +234 814 359

8303: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

35 - 36

Yafi minti biyar da parking a kofar gidan nasu amma yaki fitowa saima kallon kofar gidan yake daba kowa dan duk almajiran sun tafi bara, yana sanye da dark blue shadda da akamai aikin hannu

mai shrgen kyau, jumper ne rigar danshi ya tsani tazarce, kanshi ba hula saidai gashin shi dayay lub lub dashi sai uban kamshi yake, tsaki yakara ja ya dunkule hannu ya daki iska "f*ck! hanayinyar dayaji yasa yadan dago kai, yan mata biyu yagani da farare

n hijabi da purple dankwali da purple wando alamun yan makaranta ne sun tsaya gaban keke suna mika hannu suna magana alamun da wani akeken dasuke ma magana, daya daga cikin su yaga ta juya ta shiga gidan su da sauri chan sai gashi tafito da Baba yasa babba

n kaya kanshi da rawani irin ta malamai, magana yaga Baba natayi baya iyaji sabida glass din motar arufe suke fararen hannu yaga an miko daga keken wanda kumbunan hannun ke zagaye dajan lalli dayay jajir, hannun Baba ya kama, ya kara daya ta bayan wuyan sh

i da kyar ta sakko da kafa daya kasa saikuma ta kece dawani irin kuka da shida kanshi saida yaji daga motar, kamota Baba yayi hakan yasa tafado jikinshi tama kasa mikewa da kyau tana neman yin kasa tana wani irin kuka da sauri su Walawa suka taya Baba rike

ta dukansu, hankali tashe Baba ya rikota da taimakon su sukai cikin gida tana mugun kuka, dan tabe baki yayi kafin yace "wats wrong with her?"

Shimfideta Baba yayi akan tabarman dake dakinshi sabida tsakar gida yajiku dan dazu anyi yayyafi, Baaba dasu

Umma suka zagayeta dan bama su dade da dawowa daga barka ba, ganin yanda take ihu tana kuka yasa Malam ya tsugunna ya daga hijabin tareda rigar ya janye farar shimin datasa ya kalli ciwon bugewan datayi yasa wurin yay ja sosai abunku dafara, mikewa tsaye

yay yakalli Mama yace "cire mata kayan nan iska yadan shigeta kotaji dadi, bari naje na nemo taxi abakin hanya saimu kaita asibiti" to Mama tace jiki asanyaye ta tsugunna tana kokarin maida hawayen dataji yana kokarin zubomata, cire hijabin da rigar tayi t

a barta da farar shimin kadai sai kuma wandon makaranta jikinta zata mike ta cafko hanunta tana kuka tace "ina zaki Mama? Dan Allah ki rikeni, Umma, Baba" takirasu duk awahale, dan uban kukan datake yasa ta galabaita, zuwa wajen Umma tayi ta rike, Baaba ku

ma dasu Raiyana duk suka tsaya akanta suna mata addu'a.

Bude mota yay yafito sabida hango Malam dayayi yana shirin fitowa daga gida adan kunyace ya dukar dakai ganin Baba na kallonshi dudda hankalinshi atashe yake hakan bai boye farin cikin ganinshi day

ayi ba, ahankali yace "ina yini Abba" murmushi Baba yayi yace "barka dazuwa saukan yaushe? Yasu Alaji da kowa da kowa" ahankali yace "Alhamdulillah sunce agaishe ku" girgiza kai Baba yayi yace "kaga ikon Allah yanzu hakafa fita zanyi nem mota ahanya, dan m

atar takace ba lapiya yanzun nan daga wajen jarabawan tasu ce aka kawota ma, cha nayi nasamo sai muzo akaita asibiti amma tunda kaga Allah yakawo ka ai sai kadubata" dan murmushi yayi yace "meke damunta Abba?" ajiyar zuciya Baba yadan yi yace "wanan dai ma

tsalar cikin dana fada muku tanada shi, wai bawon ayaba ta taka a makaranta shine fa tafadi, mu shiga ciki ka dubata" gaba Baba yayi yana biye dashi a tsakar gida har dakin nashi, aiko tundaga zaure yakejin ihun nata tsaki yadanja wanda shi kadai zai iya j

in karanta. Sallama Baba yayi ya shiga dakin daidai lokacin ta kara kankame hannun su Mama kaman zata shide tace "Mama Mama wlh zafin yakaru kaman wurin zai farke" dan leko dakai yayi tabayan Baba ya kalleta kitson shiku ne akanta manya da kanana idan akai

babba daga sai ayi karami siriri guda daya, tsawon shikun har bayanta yakai jelar nata lilo sabida yanda take jujjuya kai, dan makalen dan kunnene akunnenta ja, ya gangaro xuwa jikinta dake cikin farin shimi dayabi jikinta gabaki daya saikuma purple wando

n da farar safan makarantar dake kafarta, gashin gaban kanta sunbi zufan datakeyi sun kwanta lub lub idanunta sunyi jajir danhar kumbura sunyi tsabagen kuka, yanda ta kakkame su Mama tarike su kace a nakuda take, ganinshi yasa su Mama duk suka mike tsaye a

kunyace siriki yazo, dukar dakai yay ya gidansu suka amsa sunamai barka da zuwa kafin duk su fita dakin su ka barta akan tabarman tana uban kuka, karasawa inda take Baba yayi ya kalli Ayaan da har lokacin yake tsaye a inda yake kai akasa yace "karaso ka d

ubata Ayaan" kara fashewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login