Showing 12001 words to 15000 words out of 127150 words
irin kankame ta yana wani irin nishi da ita kanta saida taji kaman zata suma wajen tsoro ga jikinshi wani irin mugun zafi, duk wani addu'a dayazo bakinta karantashi tak
eyi tana kokarin tureshi amma takasa sabida wani irin kankameta dayayi fuskarshi akan wuyan ta, sunfi minti goma ahaka ganin gari yasoma duhu sosai dan bamata iya ganin fuskar shi sosai yasa tafara kokarin tureshi danya saketa tatafi gida amma takasa, dank
o motsa hannu takasa, kuka tafashe dashi sosai tace "ka sakeni natafi gida" ganin baimasan metake cewaba saima jikinshi da ko ina ke rawa yanata wani irin nishi ya kankameta yasa tai shiru tana kuka ahankali zafin jikinshi na kona ta sosai, wani irin tsoro
ma taji tanaji yanda takejin kukan abubuwa daban daban awurin tafara karanto addu'o'i tana kuka kasa kasa, jujjuya kanshi taji yanayi awuyan ta yana wani irin nishi kafin yafara bubbuga kanshi akan kafadarta da karfi, tafashe da kuka sosai dan bakaramin z
afi buga kan kemata ba, dena wa yayi kafin ya burkito ya gangaro da kanshi kan kirjinta, ya kwantar da kanshi awurin ya kankameta sosai dan kaman zai shige jikinta yana rawan sanyi, wani irin kuka takeyi gabaki daya yawani irin riketa danko motsi, ko numfa
shin kirki ma bata fitarwa, kuka tacigaba dayi har wani irin wahalallen bacci yay gaba da ita azaunen.
Ahankali yake bude idonshi dayaji sunmai wani irin shegen nauyi ga kanshi dake wani irin fitinannen sarawa, daga hannunshi dayaji yay mai nauyi yay
yadaura akanshi yafi minti biyu ahaka kafin yakara sa bude ido gabaki daya yana karema wurin kallo daya cika da hasken rana, bin gabaki daya wajen yay da kallo kafin ya sauke idonshi a inda kanshi yake da sauri ya janye kanshi daga kan kirjin wata faran ka
kkywan yarinya dayaga ta takure abango gawasu busassun hawaye dasukai layi layi a fuskarta, da sauri ya mike tsaye ganin ajikinta yake yabi gabaki dayan wurin da kallo yana kare hancin shi sabida wani irin wari dayaji wurin nayi, yana komawa da baya da bay
a, champal dayaji akafan shi yasa ya kalli kafar da sauri yaga kafarshi cikin amai yasa yay wani irin ihu "Fuck! Wah! Ewww" yawani yatsine fuska, afirgice ta bude ido jin ihu tabi wurin da kallo kafin ta sauke kanta akan mahaukacin dataga sai kallon kanshi
yake yana mikar da hanunshi sama yana kallon hanun nashi dama duka jikinshi gabaki daya, kokarin tashi tayi amma takasa sabida yanda kafarta yay mugun tsami dan kafarta alankwashe suke daya kankameta jiya, kiciniyar tashi datake yi takasa yasa yajuyo kai
ya zuba mata idanun dayasa taji kirjinta yabada wani irin duma dum! Zuwa wajen yay azuciye yawani irin fizgota har saida tai kara sabida yanda kafarta yay kara tace "wayyo Allah kafata" kawad da kanshi yayi tareda saka hannu daya yana kare hanci saikace ka
shine yazo gabanshi, dan matsawa yay nesa da ita yana kakkare hanci tareda mata wani irin banzar kallo dayasa taji kaman zatai fitsari, nuna ta yay daga sama har kasa da yatsa yace "who d f*ck are u?".
[7/15, 12:18 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦
Maman Abd Shakur
11 - 12
Kasa bashi amsa tai ganin maganin Baba yay aiki gashi yaji sauki, bayan hannu tasa to goge hawayen dasuka zubo ta juya ahankali tana dingisawa batare data sake kallonshi ba ta tsugunna da kyar sabida kafarta tadau hijabi
n ta dake kan carpet tasaka tai hanyar fita daga dakin, wani irin fizgota taji anyi arude tajuyo baiyi watawata ba ya dauke ta da mari mai kyau hakan yasa tafasa wani irin uban ihu ta dafe kuncinta tana wani irin kuka, nuna kanshi yay da yatsa yana kallon
fuskarta cikin husky voice dinshi yace "ke kinsan wayeni ina miki magana and u dare walk out of me, F*ck!" yawani dunkule hannu ya daki iska, Muji da tuntuni yake tsaye abakin kofa ya shigo da sauri yazo wajen dan tun jiya da daddare ake nemanta agida, han
kalin kowa yatashi, dazu dasafe ma su Umma sukazo duba ko agidansu ta kwana, kotadawo da latti tsoro yasa ta kwana amma batanan hankalin Baaba duk yabi yatashi, yanajin haka yadau keke yafito batare da kowa yaganshi ba hakanan zuciyar shi yace yazo yadubat
a anan. Karasa shigowa yay yabita da kallo yanda take kuka sosai ga hanunta akan kuncinta da sauri Muji ya kama hanun ya cire daga kan kuncinta ya kalla yanda wajen yay ja duk shatin hanunshi sunfito, fadawa kan Muji tayi tana sheshekan kuka da kyar ta iya
cewa "mutafi Ya Muji yariga ya warke" Cireta Muji yay daga jikinshi ya kalli Mahaukacin dasu yake kallo, azuciye Muji yace "uban me kanwata tama ka mare ta haka eh adam, butulu kawai, kasan irin dawainiyar datai dakaine mahauka..." da sauri tarufe mai bak
i tana kuka tace "dan Allah nidai mutafi gida, yaji sauki shikenan ai" ture ta Muji yayi hartana neman faduwa cike da masifa yace "wlh karki bari na daura miki wani marin nima, tun dazu na tsaya anan ina ganin abunda yamiki uban wayeshi dazai mareki haka?
aida kinbarshi anan yacigaba dacin abincin bola banza dakiki mai dukan mata" cakumo shi yayi azuciye da idanunshi dasukai mugun ja ya shake Muji sosai, Muji yafara tari abunku daba karfi daya ba, tashi tayi daga tsugunen datake tana kuka tafara dukan kakka
rfan hannunshi da karfi tana kuka. "ka sakeshi, ka saken min wana, wlh ka sakeshi, zaka kashe shi" cire hanunshi daya yay daga kwalar rigar Muji yasa hannun ya hankadeta tafadi kasa, wani irin mukurkusu tayi sabida ciwon ta daya kama mata tafasa ihu sosai.
"wayyo Allah na cikina, Ya Muji zan mutu, zan mutu wayyo" juyo da kai yay ya kalli Muji da tsabagen wuya idanunshi sunyi ja sosai, jijiyoyin kanshi sun fiffito yace "duk randa ka kara haduwa dani watch ur tongue and know how u speak to me, bana tolerating
raini one single bit get it?" ya tambaye shi fuskarshi a mugun daure dan ranshi yay tsananin baci, gyadamai kai Muji yayi ahankali dan ya shaku wlh, hakan yasa ya sake shi yana kai hanun hancin shi yana tsaki, da sauri Muji yay kanta ganin yanda take kuka
kaman zata mutu, dagota yay da karfi tareda saka hanunta daya ta bayan wuyan shi ya taimaka mata ta mike tsaye da kyar, fasa ihu tasake yi zata koma kasa. "Ya Muji bazan iya tashi ba, cikina, Wayyo Allah na jama'a, wayyo na shiga uku na lalace ku taimaken
i" ta rirrike shi, Muji dayake ji da bakin cikinta dan ita tajamai wanan muguwan shakan gakuma tausayin ganin yanda dukta rikice, ahankali yace "toyi tafiya ahankali muje waje mu shiga napep muje gida" girgiza mai kai tayi tafashe da kuka sosai tace "ni ka
dauke ni idan nai tafiya barkewa ciwon zaiyi ayanda nakejin yakemini" kwalalo ido Muji yay ya harareta yace "to ta ina zan iya daukan ki wai Balkisu, kinga wlh ko kiyi tafiya konabarki anan baruwa na narantse" kara maida hanun nata bayan wuyanshi yayi tana
kuka, ya jata da karfi dayaji kaman zasu fadi dan kin tafiya tayi sabida ciwon dake mata sosai, yafita da ita daga ginin ya sakata a keken yana hararan ta yace "ai Allah yakara uwar taimakon cikin ma yafashe banziya kawai" ya watsa mata mugun hararan jiya
ke kaman ya gwabje ta, ya shiga gaba azuciye
danhar yana buge kai, harya kunna keken yakasa hakura ganin yanda take kuka daga gani bakaramin buge ciwon tayiba gakuma wuyan shi daya rikemai dan har yanzu bai dena zafiba. Wlh bazan yarda ba" fita yay daga ke
ken yay hanyar ginin daidai shima mahaukacin yana fitowa sai wani kyankyani kyankyani yake yana kallon kuturun takalmin kafarshi injishi, ganin bolan wajen yasa yay turus ya tsaya yana tunanin yanda zaibi ya wuce, ganin Muji yadawo yasa ya zubamai mayun id
anunshi masu kama dana mage, dan komawa baya kadan Muji yayi dan yaune rana tafarko dayaji mahaukacin nan ya mugun cikamai ido, sanan ya kallai yace "wlh Allah ya isa bamu yafema ba dukan mu dakayi, kaga yarinyar chan daka tado mata da ciwo" ya nuna Bilki
su dake cikin keke ta cusa kanta a cinya tana kuka yace "da kana mahaukacin ka, duk uban dattin dakayi bata kyamace kaba ta kula dakai, ta gyara inda kake zama, tasaka ledar dakake kwana dinchan aciki wanda tundaga gida ta dauko, kullu yaumin saita debo ab
inci daga gida takawo ma kaci sabida dukan ka ake idan kasatoma yan shaguna buredi, tafasa asusun ta tasiyo ma wanan takalmin dake kafarka sabida yankewa dakayi akafa sabida rashin takalmi, tasaima wanan rigar jikin naka dan na jikin ka yagama yawo, sanan
ta karboma addu'a wajen Baban ta, tabaka kasha ka warke shine ka zanemu ko, to Allah ya isanmana wlh, da marinta da shakeni dakuma fama mata ciwon ta bamu yafeba" yana fadin haka yajuya da gudun bala'i ya shige keken dayariga ya kunna yabar wajen dan gani
yay kaman zai biyosu.
Wani irin dogon tsaki yaja kafin yakara kallon bolan yana rufe hanci yafi minti uku ahaka yana tunanin yanda zai tsallaka da kyar yabi bolan tareda runtse ido "jeez, i hate dis sh*t" saida ya tsallake sanan ya bude ido tareda s
auke ajiyar zuciya yana tofar ya yawu, kallon dogon layin yayi yana tunanin yanda zai iya tafiya akafa ya shanye layin, sanan ya kalli kayan jikinshi, sake runtse ido yayi tareda shafo kanshi da duka hannu biyu, abinda yatuna na karshe shine yana garden ya
nacin white rice da pepper soup. Ajiyar zuciya yakara saukewa mai sauti kafin yafara tafiya ahankali dan gabaki daya jinshi yake very very weak ko rabin layin bai shanye ba ya zauna akan wani dakali yana mayar da numfashi, cije lips dinshi yayi kafin ya du
nkule hannu yadaki iska. "f*uck wats all dis sh*t?" tunda yake baitaba dogon tafiya akasa hakaba, maganan yaran dayaji agabanshi yan kananu haka suna leken fuskar shi yasa yabude ido ya kallesu, sunata mai dariya suna waka "waye barawon buredi?" sauran su
na amshi "mahaukacin nan shine barawon buredin shagon malam liti mai shayi" saisuyi dariya suna mai gwalo, binsu yay da kallo kafin ahankali ya yunkura zai tashi aiko suka kwasa a guje suna ihu "wayyo mahaukacin yabiyomu Maman mu" bai sake kallon suba yaci
gaba da tafiya aiko yaran suka cigaba da binshi sunamai wakan mahaukata, ahaka haryakai bakin titi yarasa inda xaisa kanshi baimasan wani gari ne nanba saida garin bai mishi kama da kano ba, haka yadinga tafiya yana tare abin hawa babu wanda ya kulashi, ya
fi awa biyu dan harya fidda rai saiga wani dan xpress ya tsaya daga ganinshi kasan dan wiwi ne yace "kai yane mahaukaci lpy ka tsaya akan titi? Kosai wani ya kwashe ka ya aikaka lahira?" wani irin kallo yama dan Xpress din hakan yasa mai machine din yace "
wayihuhu kai wlh kafadama aljanun kanka nafi karfinsu dasuke min wanga kallo dama na tsaya ne nazaci ko wani abu kakeso dan naga tuntuni kake tsaye anan ashe duk cikin haukan ne" burga machine dinshi yayi zaitafi, ganin shine only hope dinshi yace "tsaya"
authoritatively yay maganan, kallonshi dan acaban yayi yace "kace mene kai mahaukaci?" dan shiru yay rasa maima
zaice, shi baisama roko ba, bai iya neman taimako ba, jin karan ya kunna machine zai wuce yasa yasake kallonshi yace "inane nan wurin?" "kaman
ya inane nan wurin, bakin titi mana?" dan lumshe ido yayi kafin yabude su ahankali yace "wani gari ne nan?" "zaria" dan acaban ya bashi amsa atakaice yana fito "ya muje ne" yanama wani singnal dake tsallake ko tafiya ne yaje sutafi, mayar da dubanshi yay k
anshi, kai tsaye yace "ban aran wayan ka?" karkato bakin glass daya saka a idonshi yayi ya kalleshi yace "wayyo ni iskokan kanshi na sona, kai mahaukaci ni wayata na wajen chaji aida nabaka naga uban me mahaukaci na iya da waya" runtse ido yayi jin maganga
nun shi gakuma zafin rana dake dafamai fata, gakuma gajiya, atsanake ya bude idon ya saukesu akan mai machine din yace "zaka kaini kano chan GRA?" yay maganan yana dafe kanshi sabida saramai dayayi, bin shi da kallo mai machine din yayi yace "ka warke newa
i? Naga kanata min magana ka
man mai hankali, nafa saba ganin ka dan liti nacin ubanka idan kasato mai buredi, yanzu kai to da baka da kosisi mezaka bani idan zan kaika Kanon?" tattaba aljihun shi yayi kafin ya shafa wuyanshi jin chain dinshi na nan yasa ya
ciro da sauri ya mikama mai machine din yace "24 karat gold chain ne, made in Austria
🇦🇹
, worth millions, gashi ka rike ka kaini kano yanzu" hanunshi mai machine din har rawa yake ya karba yana dubawa, gold ne har gold, ga chain din doguwa sosai irin ta
maza dinan yan iska, kasa rufe baki yayi ya kalleshi yace "hau, hau muje tasha inada aboki mai mota nasaka aciki mu kaika" kiri kiri yakasa hawa machine din dan baitaba hawa machine arayuwan shiba tunda aka haifeshi, ganin hakan yasa mai machine din yace "
dafani saika ware kafarka kahau" dafashin yayi kaman bayaso yana kallon rigar jikinshi da tsabagen datti tai annakiya sanan yay yanda yace saida yakusa fadin da machine din da kyar mai machine din yay controlling ya gyara zaman shi yace "kai kacika karfi"
sanan yatada machine din yawani jaa machine din tareda yin awizo ganin yana neman faduwa yasa ya dafa kafadar mai machine din yana yatsine fuska, wani gareje suka je suka sauka mai machine din yay parking machine din suka karasa wajen wani mota, cikin mint
i goma suka tada motar suka ce ya shigo ya shiga sai kano.
[7/15, 12:18 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
13 - 14
Daidai kofar gidansu Muji yay parking keken, lokacin duk daliban sun fita bara dan karfe goma dama ake tashi
n su, Baba da Isyaka ne duk a tsaye a kofar gidan sunje dogon bauchi makarantar su tsakanin jiya da yau yafi sau hudu nemanta, amma duk basu ganta ba, ganin keken Muji ya paka ga Bilkisun sai rusa uban kuka take yasa Baba yay azamar zuwa wajen daidai Muji
yafito daga keken, anatse Baba ya kallai yace "a ina ka ganta Mujittapa?" kame kame Muji yafara yama rasa wani karya zai shararo da sauri ya juya yafara kokarin fito da ita yace "chan hanyar gidan kawarsu na ganta awani lungu asume Baba" "subhanallah" yafa
da yana kokarin cirota daga keken da kyar suka fito da ita dan kasa tsayuwa tayi sabida cikin, da taimakon Baba da Muji sukai cikin gida da ita, Isyaka yabisu hankali atashe dan bazai iya daurewa ba ya shiga gidan ganin duka matayen tsaye a tsakar gidan ba
lullubi yasa yajuya da sauri yakoma zaure danba karamin kunyan su Mama yakeba.
"La'ilaha illallahu maiya sameta malam?" Baaba tai magana kafin ta kalli Mama dake gefenta tace "dauko tabarma Amina a shinfideta akai" daki Mama takoma ta fito da tabarma t
a shinfida anan bakin kofa sabida nanne da inuwa, nan Baba da Muji suka kwantar da ita, da kyar ta kwanta dan kafe musu tai a tsaye wai zafi, Baba zai juya yaje daki yadebo ruwan addu'an daya mata ta kamo hanunshi gam tarike. "Baba, Baba to ina zaka wlh az
aba yakemin yamafi na ranan nan, dan Allah ka tsaya kusa dani kaji Baba" tafara daddaga dayar hanunta saman tana neman ruko wani, dan haka take inhar tana rashin lpy to bata barin mutane tabuka komi duk kakkama su zatayi ta rike muku hannu hakan nasata jin
kaman ciwon ya ragu, hannun Baaba takamo ta rike gam cikin kuka tace "Baaba kene ko rikeni to, dan Allah kema karki tafi" tasake sakin wani ihun tareda damke hannayen nasu gam. "wayyo Allah na Mama, Mamaaa, Raiyana, na shiga uku Umma, Umma Umma zo kibude
min cikin yasha iska" jiki a sanyaye Umma ta tsugunna ta nannade mata rigar makarantar zuwa sama aikuwa wajen yadan kumburo kaman tahadiye karamin kwai a wurin, tagumi Mama tai ta zubama Baaba ido hakan yasa ahankali Baba ta juyo ta kalli Malam dake gefent
a ya tsugunna yana mata addu'a sanan ta kalli Muji dake kallon yanda Bilkisu ke kuka tace "wuce katafi nema zataji sauki kaji dan arziki" fita yay daga gidan jiki asake, Malam nagama tofa mata addu'an ya mike tsaye zai shiga daki hakan yasa Baaba tabi baya
nshi, sallama tai yabata izinin shiga, zama duk sukayi sanan tafara koromai zance anatse. "Malam wata yar magana nakeson nama dama, bawai inaja da Allah bane kokuma inaso nama shishigi ba, zancen ciwon Bilkisun ne dama, naga tun fa tana shekara sha bakwai
abinnan yafara fitomata dan karami kullum saidai aita mata addu'a aruwa tasha ya lapa, gashi har yanzu tana sha takwas amma ana kan abu daya saima kara girma yake, ni dama cha nayi ko za agwada na turawa ne mugani koya kagani malam?" shiru yayi yanadan dog
on tunani kafin yace "da yardan Allah haka za'ayi amma akwai wani maganin gargajiya dazan karbo mata wajen wani abokina anjima inhar tasha babu chanji to zamuje asibitin" murmushi jin dadi tayi ganin Allah ya dorata akanshi dan Maman Bilkisu tasha fama das
hi akai yarinyar asibiti yaki yarda hakan yasa tafito daga dakin rai fes ta sakan musu murmushi tareda kallon Bilkisun dake baccin wahala har wani irin nishi takeyi abaccin.
*************************
*Kano*
Agaban wani Mansion yasa sukai parking,
wanda girman gidan kadai yayi girman wani anguwa fita yay daga motar, su dan acaban sai kallon gidan suke hakadai suka kunna mota sukabar unguwar, tunkarar gate din yayi wanda securities sunfi biyar biyu agaban gate sauran kuma suna tsattsaye akowani bang
are na wajen duk shi suke kallo, hanyar gate yay zai shiga securities din suka tareshi da fuskokin su da babu alamun wasa sukace "wakake nema