Showing 69001 words to 72000 words out of 127150 words

Chapter 24 - SANGARTATTCE COMPLETE

01 Nov 2026

105

kudin baku amma kudau kome kukeso" wani irin finciko hanunta dayayi saida hanunta yay kara yajata tana tirjewa yafita da ita daga dakin sauran hudun suka rufa musu baya, ih

u take sosai. "na shiga uku Ya Ayaan, Wayyo Allah Babana" tutturjewa take yanajanta akasa hanunta yaja plate din dake kan center table din falon saman daidai sunkai wurin stairs zai sauka yana janta ta daddage ta mike ta kifamai kwanon akan hanun daya rike

ta dashi hakan yasa tai wuf zata koma daki daya daga cikin hudun da suke bayansu yasa kafa yawani irin tokareta aciki da baya tayi luuuuu tawani irin mugun faduwa a stairs wani irin wahalallen kara tayi kafin tafara tumble tumble tumble har takusa kai kasa

sai kuma kanta yay wani irin landing da buguwa a karfen stair case din, ko kara bude idonta batayi ba tasume warwas sai jini dakebin kanta yana zuba a stairs din.

Daidai lokacin ya shigo part din big Mum rike da abin auna Bp dan yadade yana nema baisa

n inda ya ijiye ba, wani irin faduwa gabanshi yayi da baisan lokacin daya saki abin auna BP hanunshi ba yafadi akasa, daura hanunshi yay akan kirjinshi yay shiru, Big Mummy tadan dago dakai ta

kalleshi kaman mara lafiyan gaske tai magana ahankali tace "Boy

lafiya zoka dubani man" sake danne zuciyar shi dake bugawa sosai sanan ya kalli Big Mum, abu yaji yana gangaro wa daga hancin shi ahankali ya kai hannu yataba yaga jini, da sauri big Mummy tace "ur nose is bleeding boy" kirjinshi yakara tabawa dake bugaw

a sosai yace "Big Mum she's not fine, i can sense it, my heart is telling me" da sauri ya juya yace "am coming" da saurin shi yafita daga dakin Big mum na kiranshi ya shiga mota yay horn yafita daga gidan dawani irin azababben gudu hancinshi na jini.



Dayan daya rikota ne tun farko ya fizgo wanda ya tokaretan sai a lokacin yay magana yace "dan uwarka ance mutaba tane?" tureshi yay da karfi ya sauka suna biye dashi abaya, daukarta yayi ya sabata akafada gatanan kaman mara rai kanta na diddiga da jini suk

a fita daga dakin ya wurgata acikin bakar van din dasuka shigo da ita compound din, daya daga cikin su yay gudu yaje yabude musu gate yana kallon mai gadin da har yanzu yake asume suna fita ya bisu ya shiga motar sukabar anguwan da mugun gudu gate din gida

n abude.

[7/25, 9:18 PM] 0mmer Farouk: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

61 - 62

Ko parking bai gama yi da kyau ba awaje yafito yana kallon gate din gidansu dako rufewa ba'ayi da kyau ba, runtse idonshi yay da mugun karfi kirjinshi na wani

irin bugawa kaman ba gobe, da kyar ya iya daga kafan shi daya mugun yimai nauyi ya shiga ciki, da mai gadi yafara cin karo azube kaman baya numfashi ga fuskarshi dukta kumbura sabida naushi, wani irin bugawa kirjinshi yayi ya karasa ya tsugunna ya sauri ya

na duba pulse dinshi ganin he's still alive suma ne kawai yasa yay reviving dinshi sanan da gudu yay cikin gida, jinin daya gani a stairs yasa heart dinshi ke wani irin mugun racing da mugun gudu, yay sama yana kallon plate dake kasa sanan ga dakunan su du

k abude, dakinta ya shiga da gudu babu kowa, wani irin mugun bugawa kirjinshi yayi kaman zai fashe da sauri yabude bayi ya shiga nan ma ba kowa, da gudu yasake fita kaman mahaukaci ya shiga dakin shi da bayin shi bakowa yasake fitowa da gudu ya shiga dayan

dakin bakowa, yafito yay kitchen ba kowa ya shiga store bakowa, yafita yay garden bakowa, dawowa falo yayi yana jujjuya wa yana kallon ko'ina amma bakowa, kanshi yawani irin rike da hannu biyu kafin da bude baki da karfin bala'i yace "Bilkisssssss" yawani

irin zube akasa ya rirrike jikinshi dake wani irin mugun rawa kaman mai farfadiya, da gudu yafita yay inda mai gadi yake arude ya dauko ruwa ya yayyafa mai hakan yasa yabude ido gabaki daya da sauri ya dagoshi da idanunshi dasukai jarababen ja muryan shi

har bata fita da kyau tsabagen bala'i yace "me..me..meya...meya faru?" Mai gadin da biyu biyu yake gani da kyar yace "wasu mutane su biyar sukazo amota sun rufe fuskokin su, suka dakeni sukai cikin gida daga nan bankara saning meya faruba daga nan ba" Gaba

ki daya jikinshi rawa yake kokarin ma saita yanda zuciyar shi ke bugawa yake sabida karya samu heart attack, da kyar ya mike tsaye yana dafe zuciyar shi yana runtse ido kanshi na juyawa da kyar ya iya ya lalubo waya bama yagani da kyau ya lalubo number Abb

a yakira ringing biyu Abba dake kan dadduma yagama shafa'i da wuturi ya dauka yace "Boy" da kyar ya iya bude baki yace "p...pops kazo" zumbur Abba yamike daga kan dadduma jin yanda

muryar shi ke fita da kyar tana breaking, Mami dake kwance ta bishi da kall

on mamaki, arude yace "Boy are u okay, menene, talk to me Boy, u don't sound like u, menene?" da kyar yace "Pops Bilkis, an, ban..ban ganta ba..an dauke..." tsabagen yanda jikinshi ke rawa ma wayar tazame tafadi akasa ta tarwatse, Abba yace "boy, boy" kall

on wayar yay yaga ta yanke, Mami tace "menene ba yanzu nan yabar nan ba bayan yay treating kafar hajiya baima tsaya ya auna BP taba fa haka Munari takece min" girgiza kai Abba yayi yace "sako hijabi ki sameni akasa, Boy doesn't sound gud something is wrong

" yana maganan yana fita Mami tadau babbar hijabin ta saka ta bishi abaya, Big Mum suka gani tana dingisawa tana zuwa sanye da hijabi hanunta rike da plate tana ganin Mami da Alhaji tace "ina zaku haka nida nazo na debi fruits a fridge nawa ya kare" Mami t

ace "ga Alhaji nan shinake bi wai Ayaan ba lpy" arude big mumy ta kalli Abba tace "meya sami Boy Alhaji? Mutafi mutafi mugano danmu" gaba Abba yayi suna biye dashi Big Mum ta kalli Mami tace "kedai wlh Allah wadaran halinki Ayaan baida lpy ne shine wai Ay

aan" direba Abba yakira ya shiga duk suka shiga aka jasu sai gidan Ayaan.

Yanayin parking motar Ayaan dasuka gani awajen yasa Abba yacema driver yay parking duk suka sassauko Abba ne yafara shiga tsakar gidan ko lura damai gadi ma baiyi ba sai Ayaan daya

hango a tsugunne jikinshi nawani irin rawa uncontrollably, da sauri Abba yay kanshi yana "Boy, Boy" dago shi Abba yay yay cupping fuskarshi, hanun Abba yakama gam gam yarike da kyar ya bude baki yace "Pops where is mah wife?" hanunshi Abba yakama ganin kam

an ma baya hayyacin shi yay cikin gida dashi yana binshi luuu su Mami suka bisu abaya hankali tashi, shikuma direba ya taimaka ma mai gadi ya shigar dashi dakinshi ya kwantar dashi yanamai sannu.

Zaunar dashi Abba yayi yana kallon jinin daya ga a stairs b

akinshi na furta "innalillahi wa innalillahi raji'un" Big Mum tafashe da kuka sosai ya kalli Mami datai shiru tana kallon Ayaan da jikinshi ke wani irin rawa hancinshi jini na zuba yace "ban ruwa Firdausi, mara sanyi" da sauri Mami tai kitchen ta dauko gor

an ever mara sanyi ta bude ta mikamai Abba ya karba da hannu daya dayan hanun nakan kafadar Ayaan yakai goran bakinshi yana tofamai addu'o'i, Kukan da big Mum keyi yasa Abba ya dakama ta tsawa akule yace "ke kokimana addu'a kokiyi shiru" yasama Ayaan gora

n abaki ya tsiyaya mai ruwan da kyar yasha sanan yadawo kusa dashi ya zauna ya kwanto dashi yadaura kanshi akan cinyarshi yana kara tofamai addu'an ko jikinshi zai dena rawan, kafin yaciro wayarshi daga aljihu number governor kano yakira gabaki daya, ring

ing biyu gwamna da kanshi da dauka, Abba yamai explaning abinda ke faruwa.

Within 15 good minutes karan motocin police kakeji suna shigowa anguwa, ansace matar da tilo ga Abdulrasheed Gwanaye ai dole gwamna dakanshi ya turo polisawan, tundaga waje CP y

afara saka team dinshi bincike wasu na interrogating mai gadi daya farfado kafin yazo da kanshi har bakin kofa yay sallama Mami tabashi izinin shigowa shida wasu manya police guda uku suka shigo ya tura biyu dake tareda shi sama bincike sanan ya zauna kusa

da Abba dake ma Ayaan dahar lokacin bai dawo daidaiba addu'a, saida Abba ya idar sanan ya nisa yace "Alhaji naga akwai CCTV camera a compound din" sai a lokacin ma Abba yatuna yace "harda ma falon nan akwai" IG yace "ina computer to zanzo mu kalla dan mus

an meya faru" da kyar ya mike tsaye Abba ya rike shi yace "Boy" gyada ma Abba kai yayi da kyar alamun zai iya, Abba yarike shi sukai sama IG nabiye dasu abaya, Mami da big Mummy ma suka bisu, wani daki sukaje nan suka tariyo computer har zuwa daidai inda g

oons din sukazo sukai horn mai gadi yafita waje dubawa sai gashi

daya daga cikin su sanye da mask ya shigo da mai gadi yana dukanshi kafin ya sumar dashi ya bude musu gate bakin van din ya shigo, pursing video IG yayi ya rubuta plate number motar down sana

n ya danna play suka cigaba da kallo gashi sun shigo sun fiffito daga motar sunyi cikin gidan sun bude kofa sun shiga falo sukai upstairs, dayake babu CCTV a sama basu ga maiya faru ba saidai ihunta dasuke ji da lokacin datake kiran Ya Ayaan, runtse idonsh

i yay da karfi wasu hawaye masu bala'in zafi suka zubomai da sauri ya share, saikuma inda daya daga cikin su yasa kafa yatokare mata ciki tafado ta fasa kai wani irin dunkule hannu yayi zai daki computer da sauri IG ya rike shi calmly yace "be strong Man,

i know how u feeling, zamu kamasu idan ma kidnappers ne dan basuyi kama da yan fashi ba, inda yan fashi ne da sata xasuyi, indai har kidnappers ne zasuyi contacting dinku, so u people should stay alert zasu iya kiranku kowani lokaci, yanzu dai one good thi

ng is zamu nemo motar nan tasu ta hanyar plate number nan koma ina motar take a fadin kanon nan, sanan Alhaji" ya kalli Abba yace "yakama ta yanzu akwai body guard dazasu dinga yawo da family ka most especially ur son, yanzu dai zan koma office zan zuba te

am dina akowani hanya da express way na barin garin kano zamu kamasu da izinin Allah, one last thing is i need hoton ta, dan nan CCTV footage fuskar ta is not clear sosai dan musa a media incase idan wani yagan ta" Da sauri Abba ya kalleshi yace "kanada ho

ton ta Boy kabamu?" saida yarike hanun Abba sanan ya iya magana da kyar yace "yafashe" Abba ya kalli Cp yace "wayarshi tafashe dazu amma zasu samo hoto bari yadawo daidai tukun" ajiyar zuciya cp ya sauke yace "shikenan we will use dis for now, please take

care of him he doesn't look good" yanuna ma Abba Ayaan sanan yawuce yafita daga dakin, da taimakon Abba suka fito sabida jirin dayake ji sosai suka zauna afalon sama ya daura kanshi akan kafadar Abba shi kadai yasan yanda yakeji, Abba sai addu'a yakemai j

in yanda zuciyar shi kewani irin rawa, tashi Big Mum tayi ta kalli Mami datai wani irin tagumi daurewa kawai take danji take kaman tai ihu tace "bare na shiga bayan gida" gyda mata kai kawai Mami ta iyayi tai shiru tana tunani abu kaman mafarki Bilkisu da

dazu dazun nan tana tare da ita, da dingishi Big Mummy ta shiga dakin dake kusa dana Bilkisu ta maida kofar ta rufe, bayi ta shiga ta rufe sanan tafito da wayarta daga zani wacce tuntuni ta maidata silent, message din Bala tagani da sauri tabude;

“hajiya

mun dauketan muna warehouse din saidai fa, Ahmad ya bugeta sabida gardaman dataso tamana kanta yafashe har yanzu bata farfado ba”

Da sauri big Mummy tamai reply

“Bala bakace min gobe zakaje Bauchi ba, inaso da daddaren nan kudau hanyar Bauchi kunemi wani

daji achan ku karasata kuyar, sabida yanzunan za'a baza police ako ina agarin nan, banason ko gawanta su tsinta agarin nan, ka tabbatar bata numfashin daga yanda nake ganin yaron ma dazaran ta mutun shima rayuwar tashi karewa zatayi, ka tabbatar kunbar ga

rin nan yanzu, yanzunan zakaji alert din kudi, kudin aikin ka kuma saina tabbatar kai komi da kyau sanan zan biyaka miliyan goma, kubar garin nan yanzu, i repeat yanzu! ". Tura mishi dubu dari tayi sanan ta kashe wayar gaba daya ta wanke fuskarta tafito da

ga bayin tadawo ta dayan gefen Ayaan ta zauna tana tofamai addu'a tana matse kwalla, ahankali Mami ta tashi ta dauro alwala ta shiga daya daga cikin dakunan tafara salla.

Bala na ganin text dinta ya kinkimeta yasata amota sauran ma suka shiga suka bar g

idan.

Shigowa dakinshi Abba yayi dauke da cup din coffee da Mami tahada mai, yana zaune ya jinginar da kanshi a bangon gado ya lumshe ido, lokaci daya wani irin hadadden zazzabi ya sauko mai, zama kusa dashi Abba yayi yana dafe kafadar shi tareda ijiy

e tea akan bedside drawer ahankali yace "Boy" fadawa yay jikin Abba murya chan Kass dake rawa sosai yace "Pops please bring her back, Pops dan Allah kace sudawo min da ita konawa suke so zanbasu or they should take me instead" ba karamin tashi hankalin Abb

a yayiba bayason abinda zai tabamai Ayaan, Ayaan nada mugun rauni akan abinda yakeso wanan tun yana karami yasan da haka, wlh koma su waye suka dauke Bilkisu sai yasa hukuma tamusu hukuncin daya dace dasu, daga kanta bazasu sake marmarin dauke wani arayuwa

r su ba. Ahankali yace "i promise u, Boy i promise you, ko ina ma suka kaita saimun nemota, even if it takes nai hiring private investigator, even if it means putting all i habe at stake saina nemo ma matarka, i promise u Son, don't worry wanan alkawarin b

aban kane" sake kankame Abba yayi sosai saiga hawaye shar sun zubo da kyar yace "Pops they hit her, she's hurt, kanta yafashe, Pops he dare hit mah wife wlh saina ka.." hawaye yahana shi karasawa, yafashe da kuka ahankali yana shesheka ajikin Abba, bakaram

in damuwa Abba yay ba rabon daya ga kukan Ayaan tun yana grade1, haka yadinga lallashin shi, ranan yanda sukaga rana haka sukaga dare dan wani irin ciwo ne da mugun zazzabi yarufe Ayaan sosai, koda gari yawaye baya gani da kyau tsabagen zafin zazzabin Mami

takira Dr.

Wuraren biyar na yamma suka shigo garin bauchi sundanyi tafiya mai nisa kafin suyi parking agaban wani daji, wani babban buhu daya daga cikin su ya dauko yazo inda take kwance kaman matatta dan sunma dauka ta mutu ne, ya bude bakin buhun d

a kyau biyu daga cikin su suka ciccibeta suka sakata aciki suka kulle bakin buhun sanan wanda ke tukin yafito yazo tabaya ya bude musu suka daukota da sauri sukai cikin dajin da ita da saurin bala'i. Jogging din daya sabayi kullum da yamma tunda yazo farm

house din Abban shi hutu yauma yafito yanayi, sanye yake da singlet din sport mai ruwan toka da dogon wando shima mai ruwan toka kafanshi sanye da bakin sport shoe sai kanshi acikin head phone yana jogging abinshi tunda idanunshi suka sauka akan bakin van

yaji baida natsuwa, barin ma lokacin dayaga sun fito dawani babban brown sack sunyi cikin dajin dashi hakan yasa yaji bai yarda dasuba, labewa yay abayan wani bishiya har suka fito duk yana kallon fuskar su kafin yaga sun shiga cikin van din sun tada sun t

afi, da sauri yay cikin dajin daidai ta inda yaga sun fito yasa hannu ya janye headphone din daga kanshi ya maida wuyanshi sanan ya cigaba da tafiya da sauri sauri yana shiga dajin yana kalle kalle amma baiga buhun ba har yay giving up yana shirin ya juyo

yaga buhun akan wani babban dutse da sauri yay wurin yana addu'a, ahankali yay bismillah ya daura hannunshi akan buhun yana tattabawa jin kaman mutum yasa yay maza ya kwance daurin bakin buhun da kafafun ta yafara cin karo, ahankali hanunshi na rawa yay bi

smillah ya daura akan feet dinta kafin yadan dago takan ya zare buhun gabaki daya daga jikinta, yabi jinun daya bata goshin ta da kallo, da sauri ya kamo hanunta yana checking pulse dinta ganin akwai yasa yagane da ranta, da sauri ya ciccibeta yana kallon

fuskar ta kaman yay kuka yafita daga dajin da mugun gudu baxai ma iya komawa farm house ya dauko car ba hakan yasa ya tare wani me machine din dake zuwa yahau kai yace kai ni town hospital. Yana zuwa hospital wani babban abokin shi mai suna Dr Ameenu ya ka

rbeta aka taru akanta.

*Kano*

Ayaan fa gashinan gashinan ne, kaman zararre kaman lafiyayye baida aiki se sumbatun kiran sunan Bilkisu kokuma yadau filo yarike yanama filo magana, Abba yay yay dashi sukoma gida yaki ya makale adakin Bilkisu anan yake

kwana yarike kayanta gam ya rungume yana fadin am sorry, am sorry, please come back. Big Mum dadi kaman zai kasheta har addu'a take Allah sa bakin cikin rashinta yasa yama mutu gabaki daya yanda dazaran Alhaji shima yamutu ta rike dukiyar gam gam.

Babu wa

nda yataba kawo tanada hand abacewar Bilkisu, anjira anjira yan kidnappers din sukira amma shiru.

Yau satin ta biyu a hospital din, kullum Guy din daya kawota yake zuwa dubata duk wani kudi da akai bukata na treatment dinta zai biya.

Yauma kaman kullu

m misalin karfe biyar yay parking motar shi a parking lot din asibitin ya fito yana sanye da farin lallausar yadi daya haska chocolate fatar shi, sai uban kamshi yake yay cikin asibitin yana taku daidai yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login