Showing 66001 words to 69000 words out of 127150 words
sukai cikin dakin itama tabishi ta daddage iya karfin ta ta saita tafiyar ta sabida kar agane, daidai wajen Mami yasaki hanunta ganin wani irin kallo datake mai da sauri ta tsugunna ta wajen kafan Mami dake
kan kujera tana gaida kowa kanta akasa.
Sun jima afalon suna hira itadai tana kusa da Mami kanta akasa shiko yana jikin Abba sai shagwaba yake zubawa, Abba na wani irin riritashi kaman kwai, akai akai yake satan kallonta. Big Mummy ne ta tashi bayan wayar
ta yay ringing ta kalli Mami tace "Munari ta iso bari naje" murmushi Mami tamata tace "tadan huta tukun anjima na shigo mu gaisa nima" to Big Mummy tace tafice daga dakin sai Mami ta kalli Bilkisu datai shiru ita kadai ganin mazan duk sun natsu kallon news
suke yasa Mami tace "tashi muje sama daughter" ahankali ta mike Mami ta kama hanunta da kanta dan tun shigowan su tagane komi sama sukayi yabisu da kallo asace.
Suna shiga dakin Mami tai kasa zata zauna hararan ta Mami tayi tace "kinga zamu batafa in kin
amin wanan kunyan niba maman ki bane?" gyada mata kai tayi tana dan murmushi gado Mami ta nuna mata tace "to tashi daga kasa ki zauna akan gado" ahankali ta tashi ta zauna Mami kuma tafita daga dakin tace "ina zuwa" Mama Jummai tabama kudi ta aikata wani w
uri cikin minti talatin saiga Mama Jummai tadawo da sakon karba Mami tayi takoma daki ta shiga bayi tahada mata ruwan zafi sosai dawasu magunguna aciki sanan tafito ta kalleta ahankali tace "daughter shiga bayi ki zauna a ruwan dana hada miki ina zuwa" Mam
i tafita daga dakin dan tabata sarari, kaman zata nutse da kunya haka takeji mikewa tsaye tayi da kyar ta shiga bayin kaman yanda Mami tace ta shiga ruwan bakaramin dadi tajiba ko, tadade aciki sanan tafito daure da alwala ganin ankira la'asar tana fitowa
tazo tayi, ta zauna akan gado daidai lokacin Mami ta shigo ta mika mata wayarta tace "ga Baaba" cike da farin ciki ta karbi wayan Mami tajuya tafita, sun dade suna magana da Baaba kafin Baaba ta mikama Raiyana dake kusa da ita dukta dameta, da sauri Raiyan
a ta karba tai uwar dakan Baaba tace "Anty Baby labari zan baki" dariya Bilkisu tayi sosai tace "ina jinki bani nasha" Raiyana cikin murna tace "Anty Baby kinayin aure nafara samari daban daban amma duk cikin su nafison copper dake koyarwa a school dinmu k
uma yazo wajen Baba yace zaima jirani har nagama ss3 kafin nan yagama service dinshi yasamu aiki, wlh Anty Baby ina sonshi" hanun mutum dataji akan cikinta yasa ta daga kai a tsorace wani irin kallo yake mata hakan yasa takasa magana ta sauke idonta kasa R
aiyana tace "hello Anty Baby" zama yayi kan gadon ya dauketa yasata ajikinshi tareda daura kanshi ta wajen wayan, Raiyana tace "hello Anty Baby kinji labarin kuwa" da kyar tace "eh" kafin ahankali tace "ke kinji
dadi ai kinsami wanda kikeso Baba kuma zai h
adaki dashi, niko saidai naji sabon zance ranan bikina" da sauri ta share hawayen daya zubo mata ahankali tace "ki gaidamin da Mama da Umma" ta katse wayar da sauri tana wasa da yatsun ta kama hanunta yayi yana kallon fuskar ta yace "ke" kin dago kai tayi
hakan yasa ya daura fuskar shi akan nata yana mata wani irin kallota yace "ke" bude kofar da akayi yasa yadago kai Mami ce ta shigo dakin dauke da tray ahanunta na abinci da sauri ta tashi daga kan jikinshi shima ya mike tsaye ya karbi tray yana kallon fus
kar ta ahankali yace "sannu da aiki Mami na" nunamai Bilkisu tai tace "abincin tane" sai a lokacin ma ya kalli plate din tuwo ne da miyan kuka dayasha namomi tabe fuska yayi ya ijiye mata agaban ta, tana ganin abincin batasan lokacin data saki murmushi ba
daya lobar da dimple dinta numfashin shi yakusa ya tsaya, ta kalli Mami data bude wardrobe kaman tana neman abu tace "nagode Mami na" yunkura wa tayi zata sakko kasa da sauri ya riketa dauke kai tayi ya saukar da ita kasan, zama tayi akasan ahankali ya dau
ko tray ya ijiye mata agabanta, shikuma ya kwanta akan gadon Mamin, wanke hanunta tayi da ruwan da Mami tasako mata atray din sanan tafara ci har wani lumshe ido sabida dadi gashi harda man shanu a kukan, juyowa Mami tayi ta kallesu kafin ta mayar da hanka
lin ta duka kan Ayaan dake kallonta kaman zai cinyeta itako bama tasan yanayi ba, dan gyaran murya Mami tayi tace "bakai da Abban ka zaku kai Baba Sulaiman airport bawai kazo ka kwanta anan?" dan sosa kai yayi yamike tsaye yace "na manta ma" fita yayi yada
n saci kallonta sai tuwonta takeci.
Bayan sallan isha suka dawo gidan shida Abba side din Big Mummy yayi shikuma Abba yawuce bangaren shi dan adakin Mami yake yau, yadade a side din big Mummy l yana hira da big Mummy da bakuwar ta Munari dataxo daga gia
da sanan yamusu sallama yafito yay part dinsu, tana kwance kan gadon Mami sanye da doguwar rigan da Mami ta bata daidai jikinta na atampa sai hira suke ita da Mami tuni ta saki jikinta tajita garau, da sallama ya shigo dakin yadan saci kallonta kafin ya za
una agefen Mami yana mata murmushi yace "Mami na nadawo" murmushi tamai tace "akawo ma abinci" girgiza kai yayi yace "naci a part din Big Mum" ya kalli Bilkisu datun shigowan shi tai shiru kaman ba ita ke surutu ba yace "tashi mutafi" wani kallo Mami tamai
tace "kutafi ina? Tana nan babu inda zata zatamin kwana biyu tukun" duk wani walwala da murmushin dake kan fuskarshi bacewa yayi kaman zaiyi kuka yace "Mamiii" gyada mai kai tayi tace "am serious fa" tashi yayi yafita daga dakin azuciye tundaga bakin kofa
yake kwalama Abba kira. "Pops, Popsy, Pops" arude Abba yafito daga dakinshi shigewa jikin Abba yayi Abba dukya rude ya dafashi jin yanda kirjinshi ke bugawa yace "menene Boy waya batama rai haka heart dinka ke beating fast?" kaman zaiyi kuka yace "Mami ne
wai bazan tafi da matata ba" "tace hakan?" Abba yay tambayan ranshi abace, gyadamai kai yayi, Abba yay kwafa yace "je mota ka jirata gatanan zuwa kutafi, ai kafin kai auren tafi kowa damun mutane yanzu kuma dakayi zata dauke ma mata, tafi mota abinka gata
nan zuwa" juyawa yayi ya sauka downstairs rai fess yay waje abinshi, Abba ya bude dakin Mami ya shiga ko Mami bai kalla ba ya kalli Bilkisu yace "yar arziki tashi kije mijinki na jiranki a mota kutafi gidan ku" dukar dakai tayi sabida yanda takejin nauyin
Abba ta sauko tadau hijabin ta da jakanta ta saka, Mami tace "Allah miki albarka zan kiranki gobe kinji" gyada ma Mami kai tayi tana kokarin hadiye hawayen dakeson zubowa wlh batason gidan, Abba dai juyawa yayi yafita da sauri tafada jikin Mami ta rungumet
a ahankali tace "Mami zakizo kiduba ni gobe?" dan dariya Mami tayi jin yarinyar take har ranta kaman yar da ta haifa, hakan yasa ta
gyada mata kai tace "eh oya tafi kinga goma saura" sakin Mami tayi tafita daga dakin ahankali har tsakar gida yana tsaye a p
arking lot jingine da motar shi hanunshi zube cikin aljihu tunda tafito yake kallonta harta karaso wurin motar batace mai komiba ta tazo zata wuce ta gabanshi ta zaga ta dayan side din ta zauna ya kamo hanunta, ahankali yajawo ta yasata ajikinshi ya rungum
eta wani irin siririn kuka tasaka mai, ajiyar zuciya yasauke sanan yadan duko dakai yakawo shi daidai saitin kunenta yace "kina son ki zauna da Mami?" gyada mai kai tayi hakan yasa yasake sassauta murya yace "ok next time dazamu zo saiki kwana, now stop cr
ying" cirota yay daga jikinshi hannunshi daya abayanta yarike kwankwason ta yasa dayan hanun yaciro handky daga aljihun shi mai taushi da kamshi ya daura akan kuncinta ya share mata hawayen dayabi ya bata mata fuska yana kallon idonta yanda tai kasa dasu t
aki bari su hada ido, maida handky yayi a aljihu sanan ya dawo da hannun ya daura akan kumatun ta kafin yadaura forehead dinshi yahada da nata har numfashin su nahadu wa murya chan ciki yace "ke look up" dago dara daran idanunta tayi ahankali ta sauke su a
kan nashi wani irin kasala da gajiya ne yaji ya sauka akanshi, ahankali yafito da tongue dinshi ya lashi lips dinta kafin yasake mannota ajikinshi sosai murya chan kasa yace "jekima big Mum sallama am waiting for u" sakinta yayi tareda karban jakan hanunta
yana kallon fuskar ta jiki asanyaye ta juya tai bangaren Mami shikuma ya bude kofar mota ya shiga ya zauna yana kokarin ciro wayarshi dake ringing.
Sallama tayi daga barander amma ba'a amsaba hakan yasa ta bude kofa ta shiga ciki babu kowa akatafaren f
alon, hakan yasa tai stairs tafara takala matattakala jin alamun magana amma kasa kasa, ahankali tai sallama agaban dakin big Mummy amma shiru hakan yasa ta tsaya tana waige waige corridor din toko tana part din Mami ne? A'a Mami ai tace tai bakuwa, tuna
bakuwa yasa ta mike corridor din dan zuwa guest room da tun kafin takai takejin muryoyin su na tashi kasa kasa suna hira harta daga hannu zatai knocking kofar saita tsaya sabida sunan Ayaan dataji Big Mummy tafada so kawai take takarajin halin mugun nan da
kyau saisa batai knocking ba tai shiru tareda kara kafa kunne ajikin kofan.
Big Mummy tace "saisa nakiraki kizo sabida na aiwatar da plan dina, abubuwa da dama sun faru bayan kin tafi nijar, kinsan ko lokacin nan da Alaji yatashi wai duka kamfanin shi
zai maida sunan Ayaan, manyan kamfani fa Munari, kina ganinshi haka yanada jirgin ruwan tsatso mai daga ruwa, idan aka tsatso man chan kampanin shi dake calaba ake kaiwa suna sarrafa man acire crude oil, acire kerosine, acire diesel, acire petrol, da saura
n abubuwa kinsan kudin Alhaji kuwa Munari? Mutumin dahar shugaban kasa yasan da zaman shi wanima shugaban kasa har aksashen waje ma fa, shine yatashi wai zai mayar da komi sunan Ayaan zai bashi duka dukiyar, hankalina yatashi nace wlh baza ai hakaba, idan
Alhaji yamutu fa yanzu Firdausi da danta Ayaan ne zasu kwashi kusan komi na gadon shi saidan kasona danni banda da, ai wlh bazai yuba, shine bayan kwana biyu nacemai inada biki a kaduna inaso naje, yabarni harda min kyauta banzame ko inaba sai gidan bokan
da kikamin kwatance nan nace mai inaso ahaukata yaron sanan bayan ya haukace akada shi yabar gidan bama gidan kadai ba yabar kano gabaki daya ta yanda kinga idan yaron yabace ai bazai maida dukiyar sunanshi ba, sanan dazaran Ayaan din ya haukacen zansan ya
nda zanyi da Alhaji kasheshi ba abu mai wuya bane, yariga ya tsufa dama, mutuwa yau ko gobe, amma kinsan abinda Alhaji yayi kuwa? Dudda yabace saida ya maida sunanshi hankalina yatashi sosai shikuma yaron bayan wata daya dayan
kwanaki sai gashi yadawo ya w
arke wanan yar iskan matar tashi damuka gani dazu damuka shiga shashin Firdausi ubanta ne yamai addu'a ya warke, banda hakama yanzu yamai na tsari kome namai baya kamashi wlh, amma yanzu na chanza plan gabaki daya saisa ma nace ki shiryo kizo" dan dariya M
unari tayi takara gyara zama akan katafaren kujeran datake kai, Big Mum tace "zan tura su Bala sumini kidnapping dinshi nariga nasa lawyer na yamini pepopin kuma na sato wasu documents din ownership of the company daga dakin Alaji, yanzu abinda nakeso su B
ala zansa sumin kidnapping dinshi jibi, kekuma zaki tafi chan gidan dazasu kaishi, abu daya kawai nake bukata daga wurin shi shine signature, inhar yamini to duka dukiyar ta dawo tawa daga nan zansa su Bala su kashe min shi shikuma Alaj..." kasa karashe ma
ganan tayi sabida karan fashewan abu dasuka ji arude duk suka mike tsyae big Mummy da gudu tabude kofa mace tagani da hijabi tana sauka daga stairs da gudu hakan yasa itama tabi bayanta, bigewa Bilkisu tayi da kujera hakan yasa tafadi da sauri ta mike sai
a lokacin big Mummy taga fuskarta tace "Bilkisu" kafin takarashe maganan Bilkisu tamike tafita daga dakin da gudun ta tana fita tai mota ta bude binta yay da kallo yana waya ganin yanda take nishi ta zazzaro ido, kunna mota yay da hannu daya yay horn aka b
ude musu suka fita atsorace ta rike hanunshi da kyar tace "Ya Ayaan" hannu yanuna mata alamun yana zuwa yacigaba da magana daga hospital ne wata patient tasami complications a surgery da ake mata shine yake fadinma Dr Ibrahim abinda zaiyi.
Da gudu Munar
i tafito ta tara da Big Mummy turus agaban kofa ta dafe kai tace "waye ya jimu?" cikeda bacin rai Big Mum tace "mayyar matar shice, ban wayana da sauri kafin ta batamin plan" da sauri Munari ta koma sama Big Mum kuma takoma cikin falon tasaka hannu tadau g
lass bowl din decoration dake kan center table ta buga shi akasa ya tarwatse, runtse ido tayi da karfi ta sanya kafar haggun ta akai ta taka wani karami aiko ya yanketa saiga jini da sauri ta zauna akan kujera tana runtse idon azaba, daidai lokacin Munari
ta sauko daga kan bene tana ganin jini tace "saratu kinada hankali kuwa" murmushi mai ciwo tamata tace "trust me i know wat am doing" karban wayan tayi tai dailing number Ayaan har lokacin busy yake yana driving yana magana da Dr Ibrahim sunma kusa gida, B
ilkisu dukta damu yagama wayar sai kallonshi take, saida suka shigo anguwan su sanan ya katse wayar ya ajiye akan cinyarshi yadan kalleta suka hada ido kafin ya maida hankalinshi kan hanya yay murmushin gefen baki yace "ke kallon fa" kaman zatai kuka tace
"dazu danaj..." wayarshi tai ringing big Mummy daya gani a screen yasa yace "1min" daukar wayar yayi daga tacan bangaren big Mummy tai wani irin murya tace "Boy kana ina?" dan murmushi yayi yace "gani nan a anguwan mu bama mukarasa gidaba, missing me alrea
dy" yanda yay maganan yasa ta gane bai riga yasan komiba wani irin nishi tayi da sauri yace "menene are u okay" Munari ta kanne ma ido hakan yasa Munari ta fizge Wayan cike da tashin hankali Munari tace "Ayaan hawan jininta yatashi jiri ya dibeta ta fadi a
falo yanzu hakama kafarta jini yake ta taka katoton kwalba, she's seriously bleeding, ka ajiye matarka agida kazo da wuri dan Allah" arude yace "okay okya, ki danne wajen try and stop d bleeding kafin nazo" katse wayar yayi daidai yakawo kofar gida yay ho
rn mai gadi ya bude ya shiga ciki adan rude ta kallai tace "ina zaka i want to talk to you" fuskarta ya kalla saikuma ya matso yama lips dinta kiss murya chan kasa yace "ina zuwa, sauka ki shiga gida big Mum bata da lpy" da sauri ta girgiza mai kai, tsayaw
a yayi yana kallonta ganin zatamai kuka yasa yace "ke" a tsorace ta sauka yatada motar yafita daga gidan, yana fita wayarshi takara ringing ya dauka
Munari tace "kataho kuwa yafaki tsayawa jinin" ahankali yace "nariga nataho inama hanya yanzu, idan akwai i
ce a fridge ki dauko kisa" da sauri ta katse wayar ta kalli Big Mummy tace "yariga yabar gida yafara zuwa" hannu Big Mummy tamika ta karbi wayar batare datama damu da kafarta da ke jini ba, wani number mai suna Bala naga tai dailing ringing daya ya dauka,
anatse tace "ka kwashi boys dinka yanzu yariga yabar gidan kuje ku dauko yarinyar koma tayaya ne ku kaimin ita warehouse, tariga tasan secret dina baniso ta tonamin asiri, idan kun daukotan karka kirani kamini text" shiru tayi tana sauraron meyake cewa kaf
in ta katse wayar.
Tafi minti goma a wurin kafin tai cikin gida ahankali tana goge hawayen idonta, yanzu dama big Mummy dake sonshi haka dama bason tsakani ga Allah bane, dama itace ta haukatar dashi lallai duniya abin tsoro, dama anacewa makashinka yana
tare dakai, kuma ma sabida dukiya take son kashe shi dukiyar banza, to yanzu idan tafadamai ma zai yarda da ita, da tunane tunanen nan takai dakinta ta shiga bayi tai wanka tafito ta shirya cikin rigan baccinta na doguwar riga mai kauri tai addu'an bacci t
a kwanta tanata tunane tunane toko tamai text? Tunanin hakan yasa ta tashi zaune tsaki taja tunawa da jakarta dake dauke da wayarta na cikin motar shi.
Da sauri ya shiga part din big Mummy rike da first aid box tana ganinshi tawani baje a kujera tana ni
shi ga kafarta na didduga da jini kadan kadan Munari na fifitata. "subhanallah sorry Big mum" kafarta ya dauka yay treating kafin ya mike tsaye yadan duko saitin kan big Mum din yace "ina zuwa bari naje side dina na dauko abin auna BP" yana fadin haka yafi
ta.
Har bacci yafara daukarta taji karan bude kofa sake shigewa tai cikin bargo tai lamo sosai kaman tana bacci dan karya mata komi ko yazo, taku dataji daban daban sanan anata bude kofofi yasa tadan bude ido dan wanan ba tafiyan mutum daya bane toko da
i dawani yazo ne, wani irin bugo kofar dakinta da akayi yasa takara bude ido atsorace, Maza ne guda biyar sanye da bakaken kaya da bakake mask sun rurrufe fuskar su. "hasbunallahu wa ni'imal wakil" kawai take maimaitawa ta runtse idonta da karfi dan gani t
ake kaman mafarki take yanda suka tsatsaya sun zagaye gadon suna kallonta da idanunsu tacikin mask, Babban cikinsu ne yawani irin fizgo hanunta hakan yasa ta fasa wani irin uban ihu wani irin mari ya sakin mata abaki batare dayace mata ko kala ba, aiko bak
i sai jini fashewa tayi da kuka tana tirjewa tace "dan Allah ku sakeni wlh ni banda