Showing 72001 words to 75000 words out of 127150 words

Chapter 25 - SANGARTATTCE COMPLETE

01 Nov 2026

117

kada key mota daya rike yay office din Dr Ameenu

kai tsaye, Dr Ameenu na ganinshi ya nunashi da yatsa yace "kaiko Aaman sai shegen gayu babu matan aure tuzurun banza kawai" tabe baki yayi tareda fizge cold bottle water dake hannu Dr ya zauna akan kujera saida yadan sha ruwa kadan sanan yaja tsaki yace "

sabida kadanyi aure last month ne zaka faramin iskanci, lallai muma Allah bamu masu sonmu" yay magana yana shafa dan gajeren gemunshi sanan yaja wata yar siriruwar tsaki agajiye yace "ya patient dina har yanzu bata tashi daga coma bawai" gyara zama Dr Amin

u yayi yace "i think rashin tashin ta has something to do with buguwan kanta, but once ta tashi we will conduct some special test akanta, but let's just wait till then" ahankali yace "okay" kafin ya mike tsaye dauke da ruwan goran a hanunshi yace "bari nad

uba ta" yafita daga office din dakin dayasa asata na mutum daya yaje ahankali ya bude kofan ya shiga yana kallonta har yanzu tana kwance as usual cikin kayan asibiti da nurses suka saka mata bambamcin kawai yau babu oxygen din da aka saba samata, kanta nan

nade da bandeji, kujera yaja ya zauna yadan kalleta nayan mintina kafin ya jingina goran ruwan daya dauko a jiki ya tura hanunshi acikin aljihu ya ciro wayarshi yana daddannawa. Motsin dayaga bargon da aka lullube dashi nayi yasa ya tsaya da danna wayar da

yake yi ya dago kai ya kalli fuskarta, motsin dayaga saman idonta nayi yasa yadan matso da kujeran shi kusa da gadon yana kallonta batare dayace komiba, motsin data fara sosai yasa yay magana cikin calm voice dinshi yace "Hey open ur eyes, u are safe now"

motsi tacigaba dayi kafin ahankali tabude idonta suna rawa harta bude duka ta saukesu akan fuskar wani mutum data gani yana kallonta ga cool murmushi akan fuskar shi, dakin tabi da kallo tana jujjuya kai tana wani irin fir fir da ido kafin idanunta su sauk

a akan goran ruwan data gani akan jikinshi da sauri ta yunkuru zata tashi da sauri ta dafe kanta tasaki wani irin kuka, da sauri yadan matso yace "careful" da karfin tsiya ta tashi zaune ta fizgo ruwan data gani ajikinshi tana dambe da ruwan tana kokarin b

udewa amma takasa hakan yasa ya tsaya yana kallonta, fashewa tasake yi sosai da kuka tana dafe kanta dake mata zafi, ahankali ya mika hannu ya karbi ruwan zata fizge ya girgiza mata kai ya bude marfin ya mika mata, karba tayi da sauri ta kafa abaki wani ir

in mugun kishi takeji, daidai lokacin aka bude kofar dakin afirgice ta saki ruwan hanunta tai wani irin ihu da yasa ya kalleta da sauri dan dama kofar ya kalla sanin either Dr ko nurse ne zasu shigo, tsalle tayi ta diro daga gadon ta labe abayan shi tafash

e da kuka tana

bobboye wa, da sauri Dr Aminu ya karaso da murmushi kan fuskarshi yace "wow alhamdulillah at long last yaushe ta farka Aaman?" matsawa yayi sabida Dr ya ganta da kyau tasake biyoshi ta labe abayan shi, ahankali ya juyo hanunshi daya cikin al

jihun shi ya nuna Dr Aminu yace "he's ur doctor zoki zauna" ya koma ta wurin gadon da sauri ta sake bishi ta tsaya a inda ya tsaya tana tana kallon fuskarshi hakan yasa yama Dr Aminu kallon irin wats wrong with her dinan, singnal da hannu Dr Aminu yamai ha

kan yasa yakara kwantar da murya ya nuna mata gado yace "sit" makemai kafada tayi, hakan yasa ya zauna abakin gadon da sauri itama ta zauna tana kallon fuskarshi, dan murmushi yay mata yace "sunana Barrister Aaman Muhammad, nina ganki lokacin wayansu sun s

higar dake daji acikin buhu sun yar, now i need you to tell me who you are sabida mu kira iyayen ki suzo su dauke ki, Ya sunanki?" tunda yake maganan ta kafeshi da ido ko motsi batayi, anatse yace "ya sunanki?" nuna kanta tayi akaro na farko tai magana cik

in siririyar muryarta tace "ni?" gyada mata kai yayi ahankali tace "nima bansani ba, ya sunana?" ta wurgamai tambayar itama tareda tsareshi da ido tana kallon fuskarshi, da sauri ya kalli Dr Aminu, dan matsowa Dr Aminu yayi hakan yasa ta matsa kusa da Aama

n da sauri hartana neman bigeshi da sauri ya matsa, ganin haka yasa Dr ya tsaya batare daya karaso ba ya kalleta yace "fadama na waye baban ki to" da sauri ta nuna Aaman, kallan kallo daga Aaman har Dr Aminu sukayi hakan yasa Dr yace "wanan bashine baban k

iba, waye Maman ki to?" sake nuna Aaman tayi, ahankali Dr ya kalli Aaman yace "muje office" yay gaba Aaman ya mike tsaye da sauri itama ta mike ya kalleta yace "jirani ina zuwa" makemai kafada tayi kaman yarinyar tafashe da kuka da sauri ya kalli Dr Aminu

daya tsaya ya kallesu yace "wai meke damunta ne?" ajiyar zuciya Dr Aminu ya sauke yace "inhar abinda nake tunani hakane inaga nin sanadiyar injury data samu akai yasa tasami shafewan kwakwalwa, ma'ana she lost her memory saisa kaga kaida tafara gani tasani

take yarda dashi, yanzu u are her everything kai zaka koya mata sabawa da yarda da mutane for now kafin mu dubata musan wani treatment zamu daurata akai".

♦♦

*SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

63 - 64

Dan juyo dakai yayi ya kalleta nayan

sakanni yana nazarin abinda Dr yafada, gashi tawani labe abayan shi tana wani zazzaro ido, yujawa yayi ya kalli Dr Aminu yace "Man come and examine her please" ya matsa gefe da sauri tasake binshi kaman zata shige jikinshi hakan yasa ya juyo da niyar mata

masifa ganin yanda take kallonshi yasa yakasa ya nuna mata bed yace "sit" make mai kafada tayi kaman zatai kuka tana shafa cikinta tana kallonshi da sauri ya dauke kai yace "menene?" da kyar tace "yunwa" juyo dakai yayi ya kalleta yace "sit lemme get food

for you" zama tayi ya juya zaiyi wajen Dr Aminu daketa kallonsu da gudu ta mike ta bishi hakan yasa ya tsaya chak tareda juyowa, shagwabe mai fuska tayi Dr Aminu yace "u know something, sata ta zauna na dubata tukun" baice mata komiba yay wurin gado ya zau

na abakin gadon da sauri itama tabiyo shi ta zauna abakin gadon tana haki, Dr Aminu yadau stethoscope daya ijiye akan fridge din dakin ya maida wuyan shi yana zuwa wurin su, ihu tayi ta koma kusa

dashi sosai ta rikemai riga da hannu daya tana nuna Dr da ha

nnu daya, ahankali yasa hannu ya fizge rigarshi data rike da kyar yace "hey calm down" ya mika hannu ya riko Dr Aminu yace "he's my friend, babu abinda zai miki, Dr kine so don't be afraid okay" gyadamai kai tayi tana kwalalo ido tana kara mamatso wa kusa

dashi, saida ta rike hanun rigarshi gam gam sanan tabari Dr Aminu ya dudduba tareda cire mata bandejin kanta ya chanza zuwa plasta yasa adaidai wurin ciwon sanan yay mata murmushi ganin yanda take yatsine fuska alamun zafi yace "wai Barrister zaka sha aiki

anan wlh" yadau byro yana rubuce rubuce sanan ya mikama Aaman, fizge hanunshi yayi ya mike tsaye da sauri itama ta mike ya karbi takardan, Dr Aminu yace "zaku iya tafiya da ita na sallame ku, memory loss dinne dai banda haka brain dinta yabugu dan haka za

kaga tana abubuwa sai ahankali, yanzu dai ran Wednesday zaku dawo ranan ne likitan brain din asibitin nan ke zuwa zai dubata nasan zai mata memory loss test sabida ya gane if long term memory loss ko short term ne, tasamu daganan saiya daurata akan medicat

ions in sha Allah she will be fine, but u need take extra care of her gaskiya" shiru Aaman yayi yana kallonshi ko motsin kirki yakasa, ahankali Dr Aminu ya dafashi turo baki tayi tasa hannu ta ture hanun Dr Ameenu daya daura akan kafadar shi dukansu atare

suka kalleta, turo baki tayi tana kallon Dr saikuma ta kalli Aaman ta washe mai hakora da sauri ya dauke kai ya kalli Dr, Dr Aminu yace "i know wat u are thinking amma karka damu duk mai taimako baya tabewa, dazaran ta warke saika kaita wajen iyayen ta kag

a yanzu idan ka barta wat if mutanen dasuka so kasheta sukazo suka karasa ta? Gwara ka tafi da ita chan farm house din for now inyaso ai zaka iya kiran gida chan Abuja Ummy tazo hutu, nasan kuma Abba zai barta tazo, in yaso saita tayaka kula da ita idan za

kaje site, u can go now buy this drugs for her kabata abinci taci kuma she need it" dan ajiyan zuciya ya sauke saikuma ya kalleta yanda dogayen kitso guda biyun da wata nurse tamata sabida ciwon dake kanta ke lilo tana kusa dashi takara washemai baki da sa

uri ya dauke kai ya kalli Dr yace "ina zamu samu hijabi" shiru Dr yayi kaman mai tunani sai chan yace "i think inada hijabin Maryam a office dina bari na dubo na kawo muku" da sauri yafita hakan yasa tawani irin juyar dakai ta harari kofar tana turo baki t

a gefen ido ya kalleta abinma mamaki ya bashi, zama yayi akan gadon yaciro wayarshi yana daddana wa, da sauri ta zauna tana kallon wayar, hannu tasa ta fizge wayar da sauri ya dago kai ya kalleta nunamai wayar tayi saita boye abaya tana makemai kafada, abi

nma dariya yadan so bashi hakan yasa yay mata murmushi 4 d first time, ware ido tayi saikuma ta ijiye wayan akan gado ta mike tsaye tana tafa hannu sosai tace "yeeeeee" dan girgiza kai yayi kawai yace "funny" yadau wayar ya maida aljihu, ana bude kofa ta d

awo kusa dashi ta zauna da gudu, Dr ne ya shigo dakin rike da maroon hijab ya mikama Aaman ganin yanda taketa murguda mai baki, karban hijabin yayi yace "thank u" ya mika mata hijabin da sauri ta karba tana jijjiga hijabin tana dariya kaman taga kayan wasa

, ganin batama san meba yasa ya fizge ya warware ya saka mata kallon kanta ta dingayi tana jajjjan hijabin tana kokarin cirewa hakan yasa ya girgiza mata kai yace "No karki cire" da sauri takara tambayar shi "karna cire?" gyada mata kai yayi itama da sauri

ta gyadamai kai, slippers yabata tasaka sanan yay hanyar fita Dr nagaba, da sauri tabishi suka fita a pharmacy ya tsaya ya saimata maganin duk tana kusa dashi tana kallon fuskarshi sanan suka wuce har wurin mota ya bude mata ya nuna mata ta shiga, ta shig

a ya rufe ya zagaya duk tana binshi da ido sanan ya ahigo ya tada motar sukabar asibitin.

Cikinta ta rike ta hijabi tana shafawa tana tabe baki kaman mai shirin kuka tana kallonshi, ganin hankalinshi nakan tuki yasa ta kece dawani irin shegen kuka da sa

uri ya juyo ya kalleta yace "menene?" wani sabon kukan takara kecewa dashi tace "yunwaaa" da sauri yace "okay okay dena kukan, zakici apple?" gyadamai kai tayi hakan yasa yay parking abakin hanya daidai wajen masu saida fruits yasai mata apples dayasa aka

wanke mata ya biya ya mika mata karban ledan duka tayi da sauri ta ciro daya tafara ci tana murmushi, kallonta yayi da sauri ta dago dara daran idanunta ta kallai washe mai baki tayi tasa hannu taciro katoton data balla yake cikin bakinta taciro ta mikamai

da sauri ya girgiza kai yace "no bazan ciba" wani irin ihu tayi, ta kece dawani irin kuka da sauri ya mika mata hannu yace "okay okay, sorry karki yi kuka bani to" sakamai tayi ahannu tana washe baki kaman ba ita take ihu da kuka yanzun nan ba, ya karba y

ana dan murmushi kafeshi tai da ido tana jiran yaci tareda shagwabe fuska ahankali tace "ci" kallon Apple din yayi yanda yay dama dama da miyau sanan ya kalleta yanda ta tsareshi da ido, dan murmushi dole yasake yimata yay yunkurin kulle hannun, wani irin

ihu datayi wlh saida ya firgitashi dan mutum ne shi marason hayaniya tawani irin fashe da kuka tace "ci" baisan lokacin daya hadiye apple dinma, tafashe da dariya tana kallonshi tacigaba dacin apple dinta shikuma ya kunna motar ya cigaba da tafiya har gida

n gona, bishiyoyi kala kala da shuka ne daban daban, ta gefe kuma wani flat ne kwara daya babba sosai, parking yayi yafito ya zagayo ya bude mata da sauri tafito tana waige waige rike da apple dinta ahannu, gaba yayi hakan yasa tabishi da sauri ya bude kof

a ya shiga, babban palour ne dayasha kujeru sai tv bango akan dogon kujera ya zauna hakan yasa itama ta zauna kusa dashi da sauri tana kallon fuskarshi, shima ita yake kallo saikuma yaciro wayarshi yay dailing number wani mai kula da kajinsu ahankali yace

"Umar dan Allah turomin Zainab" katse wayar yayi ya ijiye ya tashi, da sauri itama ta tashi dan juyowa yay ya kalleta saikuma yay Jim yacigaba da tafiya abinshi, kitchen ya shiga tana biye dashi tea yahada mata mai kauri a cup yadau slice bread ya shafa ma

ta butter ya daura mata akan plate ya dauko ya juyo ya kalleta ganin yanda take kallonshi tana kallon abincin yasa yace "zaki ci?" da sauri ta gyadamai kai yace "okay to muje kici" yajuya yafita daga kitchen din da gudu tabiyoshi falo suka shiga ya ijiye m

ata cup din tea da plate din akasa da sauri ta zauna tana kokarin cire hijabin takasa saita dago kai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta kwaye fuska tace "yaki fita" daidai lokacin wata yarinyar yar budurwa haka doguwa sanye da hijabin ta ta shigo bak

inta dauke da sallama tace "gani Uncle" murmushi yamata yace "yauwa Zainab dan tayani cire mata hijabin nan" murmushi tayi ta shigo dakin tace "Uncle bakuwa kayi" kwanciya yay akan kujera yace "yeah bamata da lpy ne" daidai lokacin zainab takaraso gabanta

da sauri takoma baya ta make ajikin kujeran dayake kai tanason tai kuka, ahankali yace "hijabin xata cire miki karki damu she's my sister" kallonshi tayi idanunta sun ciko da kwalla ya gyada mata kai tareda nuna idonta ahankali yace "don't cry, bari tacire

miki" ya kalli Zainab yamata alamun datazo, zuwa tayi da kyar ya samu tabari zainab tacire mata hijabin sanan ya dauko mata tea ta tacigaba da sha, saida tagama sha, nan ma bakaramin daru yasha da itaba kafin ta bari zainab ta kaita ciki dantai wanka da k

yar yasamu ta yarda suka shiga bedroom, suna shiga yadau key yafita dan zuwa yasiyo mata kaya sanan yayo take away danshi bai iya girki ba.

Ko minti talatin baiyi ba ya dawo ya paka motar shi a tsakar gidan, tun daga waje yakejin kukan ta girgiza kai ka

wai yayi ya bude bayan motan ya

dauko katoton babban leda daya siyo mata kayan sawa na mata, sai kuma ledan take away ya dauko yay hanyar cikin gida dashi da sallama ya bude kofan ya shigo falon da gudun ta tafito daga uwardakan tana sanye da doguwar riga

r atampa ja daga gani zainab ce ta bata kayanta, tazo da sauri tana kuka ganin shirin fadawa jikinshi take yasa ya juya da sauri yay facing kujera yana daura ledokin akan kujera hakan yasa ta tsaya abayanshi tana goge kwalla, ahankali ya juyo ya sauke idan

unshi akan fuskarta yanda hawaye ke gangarowa yanabin kuncinta, anatse yace "mesa kike kuka" hanyar uwardaka ta nunamai daidai lokacin Zainab tafito tana kokarin saka hijabi kayan jikinta duk sun jike, yace "ita ta jikaki haka zainab?" dariya zainab tayi t

azo wajen tace "ihu tadinga yi wai bazata yi wankan ba dana hada mata ruwa shine ta dinga zubamin da kyar dai tayi, Uncle wlh tanada kyau bakuwar nan naka ya sunanta?" da sauri itama Bilkisu ta kallai tanuna kanta tace "ya sunana uncle?" dauke kai yayi dan

idanunta namai wani irin ya zauna akan kujeran yadau leda daya na take away ya mikama zainab a kunyace ta karba tana godiya, da sauri ta zauna kusa dashi harda leka fuskarshi dago kai yayi ya kalleta hakan yasa ta washemai fararen hakoran ta, dan murmushi

yamata yana mamakin ta, tuntsirewa tayi da dariya takara matsowa kusa dashi tace "ya sunana?" Ahankali yace "kinaso na baki suna?" da sauri ta gyadamai kai tana washe baki lumshe ido yayi kafin ya budesu yakara daurasu akanta yace "okay dagayau sunanki Am

eerah" da gudu ta mike tsaye tana tsalle "yeeeee Ameerah, Ameerah" ta kalli Zainab data tsaya tana kallon ta tana yaba kyanta aranta ta murguda mata baki tare da hararan ta turo baki tace "sunana Ameerah ko Uncle" daga mata kai yayi Zainab tace "Uncle nata

fi" kudi yabata taki karba tafita da sauri.

Ahankali yabude dayan ledan dayan take away yaciro jellof rice ya kalleta inda take tsaye tanata kiran kanta da Ameerah tana juyi ahankali yace "Ameerah" da sauri ta dago kai ta kalleshi tareda washemai baki abi

ncin ya nuna mata hakan yasa tazo ta zauna kusa dashi yasa mata spoon yabata tafara ci saida taci kusan rabi ta ture tana yatsine fuska, maganin ta yabata da ruwa tasha da kyar tasha sanan tadau abincin tanaci tana wasa dashi shikuma chatting yake a watsap

p da Dr Ameenu, kanta dayaji ya kwanto akan kafadar shi yasa ya dago kai ya kalleta tai bacci ga takeaway akan cinyarta shinkafan dukya zuzzuba akan rigarta yakai kusan 5 minutes yana kallon fuskarta kafin ahankali ya janye kafadar shi ya gyara mata kwanci

ya akan kujeran tareda karbe take away ya kakkabe shinkafar jikinta acikin roban yawuce yakai kitchen sanan yadawo ya zauna kujeran nesa da ita yana kallon fuskar ta, addu'a kawai yake ko ina iyayen ta suke Allah ya bayyana su.

*kano*

Ahankali

Abba yay sallama ya turo kofar dakin Bilkisu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login