Showing 21001 words to 24000 words out of 127150 words
almajiran yak
e kaman baitaba ganiba, daure fuska yay yabi Abba suka shiga zaure ya nunama Abba allo yana wani yatsine fuska yace "wats dat Pops" gaba Abba yay abinshi ya barshi tsaye yanata kallon bangon da yaran daketa kallonshi suna washemai wani harda lashe majinan
daya fito daga hancin shi da sauri yajuya ya tabe baki kafin yabi bayan Abban nashi dayaga ya bude kofa suka shiga cikin gidan dake a gyare tsaf dashi, simintin sai kyalli yake, babu kowa a tsakar gidan sai kamshin turaren wuta mai dadin kamshi dake tashi,
iso Malam yamusu afaddadden falonshi dake gyare tsaf an shimfida babbar tabarma a tsakiya duk suka zazzauna sai bin dakin yake da kallo yanda yaga littatafai kala kala sun cika bangon dakin an jerasu kaman mesuim, Baba ya kalli Muji tareda ciro kudi a alj
ihu yace "jeka sawo ruwan gora" ganin yanayin su na yan gayu ne, da sauri Abba yace "ina ga randa nan ina gani kawani ce ruwan gora malam, ban yarda ba gaskiya" yay maganan yana nuna randar dakin yana dariya, tashi Muji yay yadebo ruwa ya cika babbar jug d
in malam mai tsafta yadaura akan tray dinshi sanan ya sanya kopuna biyun a kai yakawo musu Abba ya karba yana washe baki diba yay yasha Baba Sulaiman ma yasha ruwan dadi ga sanyi, tsiyayawa Abba yay ya mikama Ayaan dake gefenshi duk atakure, murmushin dole
yay yace "ina azumi kamanta ne Popsy" shanye ruwan Abba yay sanan ya ijiye cup din, Baba yay murmushi yace "Masha Allah sassannun ku da zuwa saidai ban ganekuba wlh" Muji ne yadawo kusa da Baba yace "Baba uhm dama" saikuma yakasa magana Baba yace "ina jin
ka" ahankali Muji yace "Baba dan Allah kayakuri daga ni har Bilkisu bamu fada muku komi akaiba, dama akwai wani.. ...." nan Muji yafadi ma Baba komi, Abba ya chabe da. "Malam babu abinda zamu iya ce muku sai ubangiji Allah ya saka da alheri yakuma biya buk
ata yakara daukaka ka, ai da Ayaan yafada mini shine muka shirya tundaga kano mukazo neman ku, munsha wuya kafin mu gano nan, Allah ubangiji ya biya muku bukatun ku duniya da lahira, yanda kuka taimaki dana kuka sani farin ciki ubangiji Allah yasaku ku far
in ciki ranan gobe kiyama, watana daya da kwana goma sha biyu banga Ayaan ba rana daya kawai yadawo ta sanadin ku, nagode nagode malam" murmushi Malam yay yace "Ameen Alaji mugode ma Allah, a'aa ikon Allah kaji magana fa, shine kuma yaran nan sukamin karya
, inda ace
Bilkisu tafadamin ai danasa ma har gida anje an dauko shi namai addu'a nabashi magun guna anan, to ubangiji Allah ya kara mana katanga da makiyan mu, ko lokacin dana bata addu'an nace mata inhar sihiri ne dazaran yasha zai karya ashe kam sihirin
ne" Abba ya girgiza kai cike da damuwa yace "bamusan waye ke neman shi da shairi hakaba, amma muna kan rokon Allah daya bayyana mana gaskiya" Baba yace "ai wanan ba matsala bace zan bashi addu'o'i dazai dingayi kullum safe da maraice in sha Allah babu abi
nda zasuyi dazai kara kamashi da izinin Allah kuwa dan kariya ce" Abba da kaman yazuba ruwa akasa yasha yace "mun gode, mun gode akaramakallahu, Allah ya biya bukata" sukadan yi shiru shidai Ayaan kanshi akasa Allah Allah kawai yake Pops yagama surutun shi
sutafi, gashi yakasa daddana waya hakanan yaji malam ya cikamai ido, maganan Abba ne yadawo dashi daga zancen zucin dayake yi. "Malam ina diyar naka Bilkisu zanzo mu ganta mu kara yimata godiya idan ba damuwa" murmushi Baba yay yace "tana makaranta chan d
ogon bauchi, dayake na rana takeyi sai biyar da rabi zata dawo" Abba yay shiru chan yace "inba damuwa zamu jirata tadawo Malam" Malam yace "babu komi ai tama kusa tunda gashi yanzu hudu saura" nan fa hira yakachame tsakanin Abba da Malam da Baba Suleman k
aman sunsan juna ataba nan ataba chan, suna yin la'asar Muji yamusu sallama yatafi nan Umma ta gabatar musu da abincin da aka dafa musu farar shinkafa da jar miya bayan ta gaisa dasu ta fita, abincin su Abba sukaci sosai abinsu dan wlh yay dadi.
Wura
ren biyar da rabi ta shigo gidan nasu da sallama a gajiye, tun awaje take mamakin babar motar data gani a pake akofar gidan su, gashi kuma gidansu nawani fitinannen bakon kamshi, abakin kofar su ta zaunar ta ijiye jakan makarantar ta agefe tana kokarin cir
e takalmi da safa dan bama ta lura da takalman dake gaban kofar dakin Baba ba, cikin yar siriyar muryan ta ta kwalama Maman su kira "Mama nadawo" safan tacire tarike su ahannu tana kallonsu ganin sunyi datti yasa ta taka farar kafarta datama jan lallin sal
atef jiya dayay kyau sosai zuwa wajen botikin dake gefen rijiya ta wurga zafan tajuya zata shiga daki taji muryan Baba daga dakinshi yana kiranta. "Bilkisu" "Na'am Baba" tajuya zata tafi da sauri Raiyana dake falo zaune tace "Baby bakine fa kizo ki chanza
kaya" turus tai a tsakar gidan tana kallon takalman da sauri tadawo daki hijabin makarantar kawai tacire sanan tadau pink hijab dinta data goge dake makale ajikin kusa tasaka, har kasa hijabin ya kaimata mai hula aiko bakaramin kyau yamata ba yafitar da ba
by face dinta sosai, ko silifas bata sakaba tai hanyar dakin Baba, abakin kofa tai sallama sanan ta shiga, gani tai kowa na dakin ita yake kallo banda mutum daya da kanshi ke kasa, murmushi tadan kakalo daya lobar da dimple dinta sanan ta shiga tsakar fal
on, dukawa tayi tafara gaida wanda bata ganin fuskarshi danya dukar dakai, sanan tadan matsa batare data jira amsar shiba ta gaida tsohon na tsakiyan su wanda tunda ta shigo yake kallonta yana washe baki ahankali tace "ina yini Abba" murmushi Abba yay yace
"andawo yan makaranta Bilkisu ya karatu?" a kunyace ta sunnar dakai tace "Alhamdulillah Abba" sanan tagaida Baba Sule da shima ya amsa mata cike da fara'a kafin ta koma gaban Baba ta tsugunna kusa dashi tace "gani Baba" Baba da tunda tashigo yake kallonta
yadan nisa yace "wajen ki akazo?" dan zaro ido tayi dan bataga wanda tasani cikin suba hakan yasa Baba ya gyara zaman shi ya fuskanceta da kyau yace "yaushe kika faramin karya Bilkisu? Maisa baki gayamin gaskiya ba ranan dakika zo kika karbi addu'an nan?
Eh? Inda nasan gaskiyar zancen aidana hadaki dasu Isyaka kun
kawoshi nadinga mai magani agida" rasa abinda zatace yasa tafashe da kuka mara sauti, jikinta ta har rawa yake tasa bayan hannu ta goge idanunta ahankali tace "Baba kayakuri, tsoro nakeji na dauk
a xakamin fadane" takarashe maganan cikin kuka, akaro nafarko kenan daya dago kai yadan saci kallonta da sauri ya kawad dakai kuma. Malam ya nisa yace "shikenan ya wuce haka Allah ya kaddara faruwan lamarin, gashin nan shida iyayen shi zunzo yimana godiya
tun dazu ke suke jira ki dawo daga makaranta, daga kano suke"Juyo dakai tai tadan saci kallon su daidai lokacin shima yasake dago kanshi suka hada ido da sauri ta janye nata kirjinta na bugawa, yanzu wanne ne dama mahaukacin nan kai anya kuwa. Maganan Baba
yadawo da ita daga duniyar tunani ya kalli su Abba yace "bari indan leka yaran nan Alaji" Abba yace "to Malam, saimun fito muma" fita Baba yayi Abba ya gyara zama ya kalleta yace "yar arziki Allah yamiki albarka y'ata, yabiya miki bukatun ki duniya da lah
ira, duk mai taimako baya tabewa ladanki na wajen Allah, Allah ubangiji ya baki duk abinda kikeso anan duniya da lahira banda abinda xan ce miki Bilkisu amma nagode, nagode, Ayaan yafadan mana abinda kika mai shine mukazo mu gode miki, Allah ya saka da alh
eri" wani irin kunya ne ya lullube ta mutumin da yamafi Baba tsufa ne yaketa gode mata haka lullube fuskar tai da hijabi kanta akasa hakan yasa Abba yay murmushi sosai ya kalli Baba Suleman yace "kaga yar albarkan kunyamu take ji, zomu basu waje sabida shi
ma yamata tasa godiyar" yay maganan yana hararan Ayaan dake kallonshi kaman zaiyi ihu, fita sukai daga dakin sukai zaure wajen Baba, hakan yasa dakin yay shiru tamaki dago kai sai wasa take da yatsunta dasuka sha jan lalle a kumba.
Daga chan tsakar gida
Raiyana ta kwala mata kira. "Anty Baby kizo wai" tashi tayi ahankali batare data kalleshi ba tafita daga dakin, Raiyana dake wurin zaure tace "Baba yace kikai mai charbin shi" tana fadin haka tafice daga gidan ahankali tajuya jiki asanyaye tai hanyar daki
n Baban idanunta ne suka sauka akan Layla dake labe a kitchen tana mata game da waya, "lalala wayata Layla jeki ijiye kafin kija arufemin sim" tai maganan tana tafiya, tana kaiwa bakin kofar Baba takara juyowa ta kalli kitchen din dan taga ko Layla ta ijiy
e wayar ganin bata ganta ba yasa tahau kan dakalin da zaka tsallake ka shiga dakin Baba, ta kama labulen ta rike gam kafin ta daga kafa tana leken kitchen din ta window ko ta labene awani wajen, daidai lokacin shikuma yazo zai fita yasa hannu yakama labule
n yaja zai bude, jan labulen dayayi yasa kafarta ta turgude tayo baya gabaki daya tafada jikinshi tabaya tareda sakin labulen yakoma jikin kofa, mugun firgitan datayi ne yasa takasa motsi saima sauke ajiyar zuciya datake yi jin kirjinta kaman zai fado waje
gashi takasa juyowa takuma kasa barin jikinshi, kafarta datasha jan lallin salataf yabi da kallo yana kallon gashi gashin ta daya leko ta hular hijabin ta zufan datayi yasa sun kwanta luplup, yafita tsawo sosai hakan yasa har kwakwalwanta yana gani, hannu
yasa ya juyo da ita atsorace ta kallai, daure fuska yay kaman baitaba dariya ba yace "banason rawan kai, ki natsu, karki sake barin irin haka yasake faruwa" yay maganan yana mata wani irin kallo sanan yawuce yafita daga dakin cike da izza duk takun dazaiy
i saitaji a kirjinta harta dena ganinshi, tafi minti biyu a tsaye a wurin sanan ta share yan guntun hawayen dasuka zubomata ta rufo kofar tafito tai dakinsu.
Sai bayan sallan magrib suka tafi Baba yamusu rakiya har wurin mota sanan yakoma ciki, ba'a dade
ba saiga amajirai sun kawoma malam manya manya ledoji da rapan kudi yan dubu daidai guda biyu malam baiyi niyar karbaba yafita waje da sauri dan ya maida musu amma harsun tafi haka
yadawo yabama su Isyaka leda daya su rarraba tunda kayan kwalama ne dayan l
edan kuma ya shiga gida dashi da kudin.
Abba ne zaune gefen Ayaan dayay bacci abinshi a dakinshi na hotel yay tagumi yana kallon fuskar Ayaan yayinda dayar hanunshi ke shafa kwantacen gashin shi, sosai ya zurfi a tunani hoton Balkisu yakasa barin ransh
i, for d first a duniyar nan yaji lokaci yayi da Ayaan zai ijiye mata ya ijiye iyali zaizo yaga jikokin shi kafin yabar duniyar nan, yana mugun kwadayin ma Ayaan Bilkisu, yarinya hafiza, ga ilimi natsuwa da kunya ai itace tafi dacewa da Ayaan sanadinta hal
a ya natsu. Sai wajajen karfe daya sanan yabar dakin Ayaan din yawuce nashi.
Misalin karfe biyar na yamma suka fito daga cikin school dan anatashi su biyar ne na yamma, suka jero ita Aisha shehu, Walawa, Fa'iza dakuma Fatima, itace a tsakiyar su cikin
dogon farin hijabin ta dayasha guga da wandonta purple kafarta sanye da farar safa tasaka brown takalmin makaranta mai igiya, babu komi a fuskar ta sai kwalli dakuma mai data shafa a lips dinta bayan sallan la'asar wanda yasa har yanzu pink lips dinta ke
shining sosai da black din abin sai yay kaman tasa jan baki, murmushi dukan su sukeyi dan Fa'iza ke basu labarin yanda sukai da saurayinta jiya dayazo tadi sunata murmushi, bayan Fa'iza tagama duk sukai dariya, takara yin wani irin murmushi daya lobar da d
imple dinta tana dan tunani tace "niko jiya da Isyaka yazo ko" sai kuma tai shiru tana fari da ido hakan yasa Walawa ta dafata tace "fada mana yar malam meya faru dayazo ke badai ya mammatse kiba" hararan ta tayi tace "Allah kyauta bama iskanci mu" murmush
i duk sukayi suna kallonta, sai kuma tasake yin fari da ido tace "anbiya shi kudin aikin hannu shaddan dayayi aiko ya siyomin ice cream jiya, muka sha nida su Raiyana" ihu suka hau yi suna tafi. "woh ke woh ke, ashe dai ustaxai sun iya soyewa su isyaku an
iya sawo ice-cream" dariya tai kafin ta dauke kai tace "an sa fa, nan da 2weeks da some days ne?" "mene!" dukan su suka tambayeta atare Aisha Shehu ce tace "amma kin cika yar iska Billyn Malam, keda kikace mana sai bayan kun gama exam?" kaman zatai kuka ta
ce "wlh bahaka bake fa, Babane yace ranan walimar shi kawai ahada da auren" duk shiru sukayi suna tafiya ahankali saikace ba gida zasu ba sai kallon su take tana murmushi, chan Walawa tace "inko hakane bazamu yarda ba wlh dole mutaba mu mulmula su kafin Is
yaka yataba" ihu sosai tayi da saida sauran daliban gabansu suka juyo ta arce da gudu sosai tana dariya saida ta musu nisa sosai dan har bata hangosu sosai sanan ta jingina dawani mota tana mayar da numfashi tana dariya tana kallon layin data kusa kurewa d
a gudu, kirjinta ta dafe tace "wayyo Allah na" jin yanda ya wani irin buga sanan tacigaba da nishi tareda lumshe ido tana kokarin saita numfashin ta, wani irin kamshin turaren kamshi daya daki hancin ta yasa ta bude ido ahankali ta saukesu akanshi ya tsaya
agaban ta yay folding hannu akirji yana sanye cikin wani black bodyhug daya kama
shi dan kana ganin layi layin six pack dinshi, da fadadden kirjinshi dake nan kaman ya rabe biyu, sanan hannun rigar yakama muscle
💪
dinshi jijiyoyin sun fito, kafara shi ci
kin wani original tomford sneakers, ya sanya wani dan iskan crazy jeans dayay tokin rigar aciki sanan yasaka belt mai bala'in kyau, kana iya hango sarka dake kyalli ta wuyarshi gawani sheken dan kunne na diamond wanda maza ke makalawa da gum, dan dan kunne
n da gum dinshi yake zuwa, idanunshi sanye cikin dark shade da bata iya tantance mema yake kallo, yanda ya tsaya a gabanta sosai yasa tama kasa janye jikinta daga motar dan go tafiya daya
kacal tayi zata iya gogan jikinshi ta lafe ajikin motar numfashin ta
nafita da sauri da sauri, hannu yasa a aljihun bayan wandon shi yazaro bandir din kudi yan dubu daidai ya rike kudin kafin ya kalleta, kanta akasa tana wasa da bakin hijabin ta, wurgamata kudin yay a fuska wanda har saida ya bugi bakinta kafin ya fadi aka
sa tsakakanin kafanta, yabi kudin da kallo sanan ya tabe baki yace "Pops ne yadaman nabiyo ki school dinku namiki kyauta, so here u go" yajuya yay inda ya paka mota zai shiga, bin kudin tai da kallo ranta ya mugun baci da sauri ta share hawayen dataji ya z
ubomata ta tsugunna ta dauki kudin ta mike ta kalli motar daya shiga ganin baibar wurinba yasa tai wurin motar, kai tsaye tabude daidai lokacin ya dauko bottle water ya bude zaikai baki, ajiye mai kudin tai akan cinya ahankali tace "nagode amma ni bana buk
atar wani abu daga wurin ka" tajuya zata tafi karaf taji yarike wutsiyar hanunta, da sauri ta juyo taga bama ita yake kallo ba saima kai bottle din dayay bakinshi yana shan ruwan shi a natse, duk iya karfinta takasa kwance hanun gashi duk yan makarantar su
dazasu wuce nata kallonsu duddu su Walawa basu riga sun karaso ba, zafin dataji hannun nayi yasa hawaye ya gangaro mata a kunci, saida yagama shan ruwan sanan ya ijiye bottle din ya juyo da kanshi ya kalleta tareda cire bakin glass din idonshi ya ijiye a
gefe ya kafeta da idanu da sauri ta janye nata ta cigaba da kokarin fizge hanunta, muryar ta har rawa yake tace "ka sakeni natafi gid..." "ke!" ya daka mata tsawan da batasan lokacin data fashe da kuka ba ta hadiye sauran maganan, wani irin mugun kallo ya
mata dayasa ta hadiye hawayen tarasa mesa take shakan shi haka, cikin wata irin kakkausar murya yace "kinsan wayeni kuwa?" dan murmushin gefen baki yayi dayawani irin karamai kyau kafin yasake damke fuska yace "Am Dr Ayaan, a doctor, double degree holder,
masters holder and PhD holder, am a surgeon and a pathologist, mace bata kawomin wargi, babu abinda bansani ba na mace, so ki kula! Ki natsu! I don't take shit! dan haka pick dis money and get out of my sight" yafada cikin tsawa tareda jawo hanunta daya da
mke tun dazu ya daura kan kudin yamata wani irin kallo dayasa ta bude hannun da sauri ta dauke kudin sanan ya turata dahar saida tafadi kasa yaja motar dawani irin gudu yabar wajen yana tsaki, baisan mesa Popsy kemai wanan abinba wlh me zaiwani sa yazo nan
, thank God yau zasu bar garin.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: [7/13, 10:15 PM]
Maman Abd Shakur
23 - 24
*For Sell! idan baka biyaba dont F*ck*ng read it in Ayaan voice. Aha*
Hawaye ta share tabi wut
siyar hanun nata da kallo yanda yay ja abunku da farar fata ahankali tace "kuma ban yafeba mugu kawai" ta tashi da gudu tana kuka tai bakin titi batare data waigi su Walawa dake kiranta ba, ta tare Bus ta shige tana share kwalla ahaka har gida. Tana zuwa g
ida kofar gidan su tai turus tana kallon baban trailer company Uniform, suna sauke katipu irin na boarding school dinan ankawo ma almajirai kowa daidai, aiko sai tsalle suke suna murna wajen ya kacame da hayaniyan su, karasawa tai wajen Baba dake tsaye yay
shiru yana kallon masu sauke katifar tace "Baba waya aiko da wayan nan katipun?" "mutanen dasuka zo