Showing 24001 words to 27000 words out of 137402 words

Chapter 9 - TURKEN GIDA BOOK1 COMPLETE

01 Oct 2026

375

tafi na ba ta 500 na ce ta hau abin hawa, tafiyarta ba dadewa su Jidda suka dawo daman na yi ma Salisu maganan zai kai su Alu Venue anguwan su Anty Maimuna sai ya ce mini bari ya je ya yi sallar jumma'a ya dawo kan nan sun shirya.

  Sai murna s

uke yi tunda na ce can za su yi Weekend,tunda akwai jikokin yarta na fari Mardiya suna wajen Anty Maimunan ne sa'anin Baby ne, sannan autan ta ma sa'ar Jidda ne Afiyatu.

  Ban yi musu girki ba, Coorfleck na ce su sha bayan sun sauya kaya sun yi sallah.

Kayan su suka saka iri

ɗ

aya shadda mai ruwan ƙasa da na

ɗ

inka musu da sallah da ta wuce da mayafansu, iri

ɗ

aya har takalminsu iri

ɗ

aya ne, na fa

ɗ

a ma Jidda su yi kitso a can saboda na san ba da wuri za su dawo ba. Ban san me ya sa Anty Maimuna ta ke kulafa

cin su Jidda ba, ko don Baby ita aka yi ma takwara? Ko kuma daman can ita mai son yara ce gaskiya.

Ɗ

aya da rabi na rana Salisu ya dawo ya

ɗ

auke su suka tafi. Suna tafiya nima na shirya na saka wata atamfata hollad mai ruwan ganye, sai na yi amfani da gr

een

ɗ

in mayafi jaka da takalmina kuma na saka baƙi, key

ɗ

in gidan da na

ɗ

auka sai da na tabbatar da na kashe komai na wuta sannan na fita na rufe get

ɗ

in da makulli, ban samu adai daita ba sai da na taka zuwa babban titi, anguwan shuru daman haka take to t

a masu ku

ɗ

i ce, kowa na gidajenshi shi ya sa ƙawa ko

ɗ

aya ban da

shi a rukunin nan sun shigomin lokacin da muka tare amman ni da ya ke halina sai ni sau

ɗ

aya na taba shiga gidan gefen mu gidan maman muhsana, da ta haihu na yi barka. Allah ya halliceni mace

mara sson shige ma mutane, ko yan gidanmu in ba wani abu ya faru ba, ba kasafai nake zuwa ba, gwara na yi zama na a gida in yi barci ya fiye minim

  Drop na

ɗ

auka zuwa Gwammaja. Muna tafe na ji wayata na ringing a jaka na

ɗ

aukota na duba sai na ga Zait

una ce Matar Yaya Abubakar. Na yi mamakin ganin kiranta domin ni dai ban wani yi da ita na fi yi da Anty Khaleesat

ɗ

in Yaya Hamza. Ita Zaituna akwai kwa

ɗ

ayi da surutu da an ce kace kace shi ya sa ban cika sakin mata ba, sannan daman ina jin haushin mijinta

shi ya sa na

ɗ

auka a dakune ban sakar mata fuska ba.

Bayan mun gaisa, sai na yi shuru ina jiran abin da za ta ce.

"Kina gida ne Sadiya?

  Yamutsa na yi kafin na ce"A'ah me ya faru?

Kai tsaye ta ce"Ayya daman ina kusa da anguwarku ne, mun zo suna

gidan wata ƴar'uwarmu ne, na ce bari in kira ki in kina gida, sai na biyo."

  Daga yanayin yadda take magana kamar a wahale, na fi tunanin ƙila sun je ne ma ba abinci za ta ce ina kusa bari ta kirani ta da

ɓ

o gayyar danginta su zo min gida, na ji da

ɗ

i d

a ba na gida saboda ita ma Zaituna ƴar ƙashin bayan Ma'u ce.

"Ai ko ba na gida, ina hanya za ni Gwammaja gidan su Yalla

ɓ

ai."

  Sai ta ce to shike nan, daman ta

ɗ

auka ina gida ne, daga nan muka yi sallama.

Na kashe wayata ina hararan wayar kamar ita

ce a ciki, na tuna ko fa

ɗ

an da muka yi da Ma'u a gidan Rahila, suna yan gaba gaban saka bakin cewa ni ce ba ni da gaskiya.

  Wayata na mayar jaka, ni ka

ɗ

ai ina ƙunƙuni ni fa su san halina duk wanda ya ci tuwo da ni wallahi miya ya sha, ga su ga Ma'un du

k za su ci ubansu.

  Mai adaidaita bai direni ko'ina ba sai ƙofar gidan Iyayen Mijina da ke Anguwan Gwamnaja. Na sauko daga adaidaitan ina miƙa mi shi ku

ɗ

in shi na ji an kira sunana.

"Anty Sadiya.."

  Ina juyawa sai na ga Adnan ne, sai da na salla

mi mai adaidaitan ya tafi sannan na nufe shi, ya na tsaye a ƙofar gidan shi da abokonsa guda biyu sun sha manya kaya ƙila daga masallacin jumma'a suke.

"Adnan manyan kasa, yaushe a gari?

Na fa

ɗ

a ina kallonsa yana dariya ya ce"Jiya na shigo garin. Ina s

u Jidda?

  Ina amsa masa da cewa sun tafi gidan Anty Maimuna, abokansa suka gaisheni na amsa, jakar hannuna ya kar

ɓ

a muka jera zuwa get

ɗ

in gidan.

  Gidan Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa babban gida ne, mai bene sama da ƙasa. Ko haraban gidan wargaje

je ne, duk da mai gidan ya fi shekara ashirin da rasuwa, gidan bai rankwafa ba, saboda ya hayyafa, kuma ƴa'ƴa sun tasa, in wannan bai kawo ba wannan zai kawo, shi ya sa ƙyallin gidan har gobe bai daina haskawa ba.

  Muna tafe ne zuwa cikin gida Adnan na

yi min hira makaranta. A ABU ZARIA ya ke karatunsa na Engniaring, a tsakar gidan muka ga Jawahir na shanyan ƙananun kayanta da ta wanke.

  Tana ganina ta washe baki ta na fa

ɗ

in" Anty Sadiya."

Na amsa ina fa

ɗ

in"Au kema kin zo hutun ne? Ko guduwa kika y

i?

Dariya ta saka tana fa

ɗ

in" Kai Anty Sadiya, da ne fa yanzu ai mun zama ƴan makaranta."

  Adnan ya ce"Tunda ba ki son bokon ki yi aure mana ko Anty Sadiya? Kai na gya

ɗ

a ban yi magana ba Jawahir ta balla ma Adnan harara lokaci

ɗ

aya ta na fa

ɗ

in" To ai

sai ka zo ka yi min auran ubana."

Yana ƴar dariya kafin ya ce"Ko ba ki fa

ɗ

a ni ubanki ne, domin zan iya

ɗ

aura miki aure."

  Suka kacame da gaddamansu na saƙo da saƙo ni kuma ina ta dariya. Jakata na kar

ɓ

a hannun Adnan ina fa

ɗ

in"Bari na karisa, su Hajiy

a Iya ba sa nan ne na ji gidan shuru?

  Jawahir ta ce" Maman Farko ba ta nan an yi musu rasuwa, Iya kuma ta kwanta ne Nene kuma ki haura sama ta na ciki."

  Wuce su na yi, na bar su suna musu, ya na cewa shi ubanta ne, ita kuma ta na cewa Allah ya ky

auta ya zama babanta.

  Shashen ƙasa Hajiya Iya ne da Mahaifiyar su Jawahir marigiyayiya Hajiya karima Allah ya jiƙanta, sama kuma Hajiya Nene da Maman Farko suke bangaren sama, amman a ƙasa akwai

ɗ

akunan baki daga can haraba kuma akwai

ɗ

akunan mazan gi

dan.

  Sama na haura, ƙofar shashen Nene ne a farko tun kafin na shiga na jiyo hayaniya, ina sallama bayan na cire takalmi na sannan na shiga babban falon na Nene. Hauwa na gani zaune a falon sai fama take yi da yara, Hauwa matar ƙanin Yusuf ne mai bi m

asa, Muttaƙa. Sai ƴaƴan Halima da su ban ga uwarsu ba, ina ga su ka

ɗ

ai aka kawo Nene ba ta falon ma gaba

ɗ

aya.

  Hauwa na ganina ta tare ni da mirmishi, karamar ƴarta, Sahla ta nufoni ta na min oyoyo na taro ta ina ƴar dariya saboda yarinyar ta gane ni,

duk in da ta gani ta riƙa gwarancin mgana kenan, suna zuwa gidana sosai nima ina zuwa saboda Hauwa tawa ce, duk cikin Facalolin gidan ba ni da kamar Hauwa.

  A bangaren Matan gidan ba ni ba ce Babba ba, akwai Matar Yaya Usman Zabba'u, sai ni sannan Muni

ran Yaya Nasir sai Hauwa da tsakanin auren mu da

na su shekara shidda ne. Amman ina son Hauwa saboda muna da kamaceceniyar hallaya, ba ruwanta tana da sanyin hali duk da yar uwa ce tun da ƴar rano ce a can Mutaƙƙa ya auro ta.

Gaisawa muka yi faram faram

kamar yadda muka saba in mun ha

ɗ

u.

"Ina Nene?

Sai ta ce mini ta shiga ciki ta kwanta.

Yaran Halima na kallah kafin na ce"Tare da Haliman suke? Na ga ban ganta ba?

Sai ta ce mini "A'a su ka

ɗ

ai baban ya kawo ya ce Haliman ba ta jin da

ɗ

i"

Sai na ce Al

lah ya sauwake, sai da na ji Hauwa na fa

ɗ

in ƙila ma Haihuwa ce.

Baki na saki domin ni har ga Allah ban san tana da ciki ba, har sai da na furta ma Hauwa. Ta na dariya ta ce" Kin da

ɗ

e baki ganta ba ne? Ni mun ha

ɗ

u a walimar sabon gidan Anty Suwaiba, a ca

n ne na ganta da cikin".

Kai na jinjina kafin na ce" Ni kin san ban samu zuwa ba."

Sai ta gya

ɗ

a min kai, hira muka cigaba yi, amman hankalin Hauwa na ga yara, ita yayanta hu

ɗ

u, sauran ta ce suna gida tare da babansu da Sahla kawai ta zo amman sai wahal

a take yi da yayan Halima da ba sa jin mgana.

Muna zaune muna hira Walid da wayonsa ya fi shekara biyar ya yi fitsari a cafet, mamaki ya isheni ganin Hauwa ta miƙe jikinta na rawa ta na masa fa

ɗ

an me ya sa ya yi fitsari a zaune bai zai yi magana ba?

 

Sai kawai yaron nan ya fasa kuka ya nufi bedroom

ɗ

in Nene, na saki baki galala ina kallon abin mamaki.

Ina kallo Hauwa ta je ta di

ɓ

o ruwa ta zo da towel tana tsane fitsarin ina zaune ko motsi ban yi ba, na yi wannan wahalar a baya amman ban yi wahalan ƴaƴ

an ƙannen miji da yayyensa ba, na yi dai na uwar mijina a baya amman a yanzu wallahi na daina, in ba a gode na baya ba a barshi.

  Falon duk sun yi kaca kaca dashi sai da ta share, sannan ta dawo ta zauna Walid dai tun da ya shiga bai fito ba, Salha da

Afra kuma Hauwa ta ce su sauka kasa su je wajen Anty Jawahir.

  Sai da suka bar falon sannan na kalleta kafin na ce"Wai sannu da aiki."

Mirmishi ta yi mini ba ta yi magana ba..ni kuma da ban iya shuru na ce"Ke wai har yanzu ba ki daina wannan wahalan b

a? Uwarsu na can gida tana hutawa, ke kin baro na ki yayan wajen ubansu, kuma kin zo nan kina hidiman na wasu."

  Dariya ta yi kafin ta ce"Kai Anty Sadiya ba ki da dama."

Daman haka ta kan kirani, kai na girgiza kafin na ce"Tab. Wallahi Hauwa ba ƙanwar

miji ko y'ar mijin da zan yi ma bauta, na yi ma mahaifiyarsa ita ce dole na, ko ita na yi a baya yanzun ma sai abin da ba a rasa ba."

  Cewa ta yi" Allah ko? Na

ɗ

aga mata gira sai muka yi dariya har da tafawa ƙasa ƙasa ta ce"Nene ce kafin ta shiga ta k

wanta tace mini na kula da su, gwara ke Sadiya ha

ɗ

uwan juction kuka yi da Yaya Tafida, ni fa yar uwa ce abu ka

ɗ

an zan yi a taso min shi ya sa."

  Ta

ɓ

e baki na yi kafin na ce"Kina da aiki. Ni fa sanin da na yi ko na yi ko ban yi ba sai an yi sururtu shi

ya sa da gangan na ke ƙin yin abin,tun da ko ka yi ba godewa suke yi ba su yi ta bin ka da ƙananun maganganu. Ballatana ni da na yi ƙaurin suna."

  Dariya muka saka har muna ƙara tafawa, bajewa muka yi a falon Nene muna ta hira kiran sallar la'asar ne y

a tashe mu, ni ce na leka

ɗ

akin Nene ta na barci ga Walid a gefenta sai na bubbuga gefen gado ba ta da nauyin barci ta bu

ɗ

e ido, sai ta ganni.

"Lokacin sallah ya yi Nene."

Kafafunta ta sauko ƙasa ta na fa

ɗ

in"Sadiya? Yaushe kika zo?

Rankwafa na yi ci

kin ladabi kafin na ce"Tun dazu, Hauwa ta ce kin kwanta."

Sai ta mike,

ɗ

ankwalinta ya zame kanta cike da furfura, ni na

ɗ

auko mata

ɗ

ankwalin na bata ta

ɗ

aura lokaci daya tana fadin"Ina su Hauwa'un na ki? Ko sun je gidan Maimunan ne yau?

Da e, na amsa mat

a sai ta jinjina kai kafin ta ce"Tafida ya je Rano ko? Ko ya dawo ne?

  "A'a Nene, sai ya dawo zai biyo ta nan mu koma gida."

A sanyaye ta ce Allah ya maido su lafiya.

Nene dattijuwa ce ce za ta haura 60 da hu

ɗ

u haka, jikinta ya yi tubus saboda hutu

da jin da

ɗ

i amman tana da hawan jini ga sugar, amman da ka ganta ka ga ƴa'ƴanta saboda da ita suke kama barin ma Mazan, matan ne su ka

ɗ

an

ɗ

auko kamanin mutanen Rano.

  Ni na riƙeta har Tiolet sai da ta shiga sannan na fito, a

ɗ

akin da muke sauka na fa

lon Nene muka shiga muka yi alwala ni da Hauwa, muka yi salla, muna zaune muna

ɗ

an taba hira haka sama sama ni da Hauwa.

*Janafty*

*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*

*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY

)*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su

da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu farga

ba.

*

🅿

️

05*

Ni da Hauwa muna Gwammaja gidansu Nene har bayan sallar isha'i. Maman Farko ba ta dawo ba, Nene ta ce daman ta ce sai an yi uku za ta dawo wani kawunta ne ya rasu, sauran ƴa'ƴan nata ma da surukanta suna can gidan gaisuwan tare da ita. Ha

jiya Iya kuma na shiga mun gaisa bayan ta tashi.

Akwai wata ƴar dattijuwa Dije mai yi musu aikace aikace da girki amman ba kwana take yi ba zuwa take yi ta tafi, ranar ma ko da na zo ba ta nan an kira ta a waya jikanta ba lafiya.

  Ni da Hauwa muka gya

ra shashen Nene muka yi girki, saboda yara ne sannan ga Nene ga su Jawahir da daman kamar a

ɗ

akin Nenen suke duk da ita Jawahir a bangarensu ta ke kwana in ta zo gida hutu a School of Nursing na ABU kongo take karatunta tana Aji biyu.

  Sai wajen tara n

a dare Yusuf suka shigo gidan tare da Muttaƙa, da Musabahu, ko kafin su shigo ina ta kiran Yusuf ban samu ba, dare ya yi sannan ni na gaji da zaman hankalina ya koma gida ga yaran Halima ba sa jin mgana Hauwa ce ke ta fama da su, ni dai ina zaune nima fama

na ke da kaina, girki dai na ta ya Hauwa muka yi saboda Nene.

   Gaisawa kawai muka yi da su Muttaƙa, na ce ma Yalla

ɓ

ai ya zo mu wuce gida sai ya ce bari ya shiga ciki su gaisa da Nene, saboda ita ta na ciki mu ka

ɗ

ai ne a falon muna bidiri, sai da mang

ariba ne ma Jawahir ta shigo nan muna tare da ita.

  Sai da muka ƙara

ɓ

ata lokaci sannan mu ka yi shirin tafiya, Hauwa Mijinta mashin gare shi, su suka fara ma tafiya mun rabu akan cewa zata shigo gidana sati na sama, bayan sun miƙa ma nima na shiga na

yi ma Nene sallama sannan muka tafi. Yaran Halima aka bar Jawahir da jage jagen su tunda uwar ta su ba lafiya.

  Musbahu ne ya rakomu har wajen mota ina yi masa tsiyan yaushe  rabon da ya zo gidana? Ya na dariya ya ce ayyuka ne suka yi yawa shi ya sa ba

ya samun zama. Da ya ke shi ya ke zama a gidan bulo

ɗ

in Yusuf, shima gidan bulo

ɗ

in  duk ya yi ƙasa ya fi aiki in har an samu babban kwangila na ginin makaranta haka ko kamfani. Kuma sannan yana zama a can ma office

ɗ

in Yalla

ɓ

ai in baya nan.

  Muna han

ya na kalli Yalla

ɓ

ai ina fa

ɗ

in" Ya Ranon? An dace?

Hankalinsa na kan tuƙi kafin ya ce" Alhamdulillah."

Ganin ya yi shuru bai yi magana ba ya sa na gyara zama ina fa

ɗ

in" Ka samu kwangilan ne?

Sai ya gya

ɗ

a kai kafin ya ce"Muna saka ran haka, wani gidan bu

redi za a gina shi ne ana neman enginear sai Abba ya yi musu magana. Na je na ga wajen yanzu dai har zanen ni zan yi sai in har an gama zanen sai mu ga in har kwangilan za ta fa

ɗ

a."

Kai na girgiza kafin na ce"To Allah ya tabbatar. Ya kuma ba da sa'a."

Ya amsa da Amin. Kafin ya ce" Su Jidda na gidan Anty Maimuna ko? Kin kira su?

Sai na girgiza kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login