Showing 1 words to 3000 words out of 79243 words
*GAMO DA KATAR*
(yar makahi)
*Na*
*yar mutan jibiya*
(AMMYN KHAIRAT)
(¯`*•.¸,¤°´
✿
.
。
.:*
ք
ʀ
օ
ʄɨ
ƈ
ɨɛ
ռ
ȶ
ա
ʀɨ
ȶ
ɛʀ
ֆ
*.:
。
.
✿
`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση
_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*"BISMILLAHI-RAHMANIR-RAHIM*"
*Page*
1
⃣
Garin Abuja sanyi ake na fitar hankali mai tattare da hazo da hunturu wanda mutum ko na gaban shi baya gani asanadiyyar hazon da ake fama dashi agarin.
Tafe suke ahanya tana ta mita tana cewa "gaskiya Inna nina gaji tun qarfe bakwai muka fi
to gashi yanzu har tara tayi,amma bamu samu komai ba ni yunwa ma nake ji gashi sanyi ya shaman kai hanci na sai zuba yake da majina gashi kin hana na tsaya gidan Alhaji na samu sadakar koko, su maryam na can yanzu sun samu koko sun gasa hanjinsu kin barni
nina nawa hanjin sun dunk'ule wuri d'aya".
"Allah Inna daga nan ban matsawa ko'ina".Tana rufe bakinta aikam ta saki sandar Inna qasa ta dafe ciki ta k'wala qara tana cewa "wayyo cikin uwar hanjina ta dunk'ule!".
Inna tace "haba Narim
tashi mu koma
gidan Alhajin ki samo sadakar kunu kinji Narim d'ita tashi mu koma ki samu kokon kinji".Inna ta k'arashe maganarta cikeda matuk'ar
tausayinta. Narim ta zumb'ura baki tace"ni wallahi ko munje ya riga ya qare nifa Inna ban ma iya tafiya uwar hanjina ta qull
e, kuma wallahi ko mun koma sai dai cikin kud'in barar jiya kibani na siyo shayi".Ta ida maganarta cikeda matuk'ar rakin yunwa.
Sannan ta sake fad'ar "dama Ammar d'an Alhaji shi keban shayi idan ban samu koko ba yanzu kuma yau ya tafi makaranta kuma s
ai da malam yace karmu tafi bara mu bari ya gama sak'a kabarsa ya saido yau mu zauna mu huta kikace sai munzo bara gashi yanzu sanyi ya laqumeni sai hancina ke zuba wayyo cikina! ".Inna tace" tashi ki kama sandar".Ta rik'e sandar tana riqe ciki haka da
i suka cigaba da tafiya suka kama hanyar zuwa gida....
_Tofa tirqash koya zata kaya atsakaninsu wannan labarin labari ne mai ban tausayi, al'ajabi tun tana yarinya take fama da mutanen b'oye gashi mahaifanta makafii_
_Ku biyo golden girl kuji
yanda zata kasance vote& comments shi zaisa inji k'arfin yi maku typingggg_
*GAMO DA KATAR*
(yar makahi)
*Na*
*Yar mutan jibiya*
(AMMYN KHAIRAT)
*Dedicated to my sarauniya beelat*
(¯`*•.¸,¤°´
✿
.
。
.:*
ք
ʀ
օ
ʄɨ
ƈ
ɨɛ
ռ
ȶ
ա
ʀɨ
ȶ
ɛʀ
ֆ
*.:
。
.
✿
`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com
/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*Page* 2
⃣
NARIM dafe da ciki take tafiya dan magana ta gaskiya tanajin yuwa bata da jimirin yunwa, sandar ma dak'yar take kamawa In
na ita.
Abinka da makaho sai mita Inna keyi tana cewa" da nasan haka zaki man NARIM yau da bamu fito bara ba! Daman nasan tunda Malam yace karmu je ba yau mu tsaya mu huta nasan haka zaki man,gashi yanzu mun sha sanyi abanza ko naira bamu samu bah!".
NARIM tace"ni wallahi Inna muyi sauri dan ninan bama jinki nake ki bari cikina ya d'auka sannan ki fad'i duk abinda zaki fad'a.. ".
Inna naji ta buga tsawa tace"ni rufe man baki acici kawai"
NARIM ta fashe da kuka tana diddire k'afafunta tsakar k'
asa wai dan me inna zata ce mata Acici?
Sai kuka take tana fad'in" wayyo Allah Inna kin sani bana son ana ce man acici ke kuma sai kita ce man acici ,
wa yaqi ci Inna kema yanzu muna tafiya inajin hanjinki na cewa k'uuuuuu".
"Ni wallahi ki daina
ce man acici kinga su Maryam har sun fara ce man acici suma, da ace man acici qara aita ce man 'yar makahi".
"Shima bawai so nake ba aman da ace man acici qara ace man 'yar makahi aida mani 'yar makahin ce".
Tunda ta fara tijararta Inna tai tsaye da
sanda tareda hangame baki tana jinta dan tasan tijarar NARIM in ta fara to sai ta dasa aya.
Zuwa can ta qara fasa qara sakamakon cikinta daya qara murd'awa tace" wayyo cikina Inna!Inna!!Inna!!! Wai yau so kike yunwa ta kasheni kinja kinyi tsaye?".
I
nna tayi
😄
dariya tace" NARIM 'yar Inna in banda abinki taya bazan tsaya ba tunda ni ba gani nake ba balle intafi kece 'yar jagora kuma kin tsaya kina abinda kika saba ".
"In kin gama sai mu tafi NARIM".Cewar Inna Narim taja dogon numfashi tace"Inna
kenan da baki ta qyaleni ba aida yanzu mun kai gida".
Duk wanda yazo wucewa sai ya kalle su inda sabo sun saba ganin kullam fad'a da Inna da 'yar jagora.
Ba ranar basu fad'a sai dai in basu fito ba wasu abin birge su yake yanda sukeyin abin sai kace
kwamedi.
Dan in kana kusa suke abin dole sai ka dara
😂
.
Wani d'an unguwar su ne yazo wucewa ya tarar NARIM na ta kuka tanawa Inna tijara yace " NARIM 'yar makahi yau kuma me ya faru keda Innar taki? "
NARIM tace"wallahi d'an masu ido Inna ce
tace man acici kuma tasan banason ana ce man acici ".
"Dan Allah yanzu qarfe nawa?". Sai yace" yanzu kusan goma da wani abu".Afirgice Narim tace"goma".
😳
NARIM ta zaro ido ta aza hannu akai tana fad'in" na shiga ukku Inna kin kasheni har qarfe goma
yau ban karya ba shi yasa uwar hanjina ke quuuui kauuuu quluuluulu".
Ta kalli fuskar saurayin tace"d'an masu idon yanzu kokon gidan Alhaji nasan ya qare shi daman nasan ban samun shi daka tafo wannan mai shayin yana nan?". Sai saurayin yace mata " eh ya
na nan na baroshi zai tashi".Ta k'yalla ihu tace"na bani yau ko sai nayi zawon yunwa". Taja sandar Inna k'erere suka tafi.
Shima yana dariya yayi gaba tare da karkad'a kai NARIM na birge shi gata yarinya qarama sai wayo shi kuma k'yau ba'a maganar shi.
k'yak'k'yawa ce sosai ina gata girma komai ya bayyana.
Inna sai cewa take" bini ahankali NARIM kinga ba gani nake ba sai jana kike yadda kika gadama dan Allah ki bini asannu kinji NARIM kar na fad'i".
Narim tace"yo kema dai Inna in na biye maki
yau saina yi zawon yunwa kuma kinga uwar hanjina in ba abu mai ruwa mai zafi nasa masa ba bata warwarewa".
Inna kam tace "wannan yunwa Allah ya rabamu da ita wannan yarinya Allah ka shirya man ita ."Amin" inji NARIM.
Wurin sauri Inna tai tuntub'e data
fad'i Inna sai cewa take" innalilahi NARIM so kike ki kadani wallahi inbaki bi hankali ba sai na kwad'a maki sandar nan".Tace" yi haquri " .Tebirin mai shayi suka yad'a zango yana ta had'a kayan shi zai tashi Narim tace "Aslm tsaya dan Allah ka taimakama
n karka had'a kayanka ".
Wajen sauri ta aza Inna kan benci ashe bata azata daidai ba gefen bencin ta azata Inna ji kake ragwab ta fad'i ta bige kai ga bango!.
NARIM tace" wai Inna kema ga wurinan na azaki kan benchi shine kika matsa kika fad'o".
Inn
a ta hasala sosai tace"na fad'o d'in gidanku ni gani nake baki azani dai dai ba yau dai so kike ki kasheni
dana bi maganar Malam da yace kar na fito baran nan da duk haka bata faru ba".
Mai shayi yace " Inna kiyi haquri inda sabo ai kun saba keda d'
iyar taki".Inna tace" hummm yaro nan ina ne ta kawoni?".Yace mata"wajen mai shayi".
Inna tace"kaine mai shayi ?".Yace" Eh mana nine".Inna ta k'ara cewa"to had'a mata na naira hamsin " .
NARIM tace"ni wallahi na hamsin bai isata kai had'aman na d'ari
da hamsin ka had'a man harda k'wai"." D'ari da hamsin?".Inji Inna". ni ina naga d'ari da hamsin yanzu".
NARIM tace"wallahi kinadasu kud'in baran jiya ba d'ari da hamsin bane kuma ba abinda kika siya dasu".
Inna tace "tafd'ijam kud'in baran jiya s
une zan baki kici k'wai da shayi dasu lallai NARIM ".
"wai Inna in kina bashi ki bashi ya had'a man wa kike nemarwa kud'in bani ba kuma ai naga nike kaiki kina samo kud'in".
Ta juya ta kalli Mai shayi tace"kai Mai shayi had'a man". Yace" to Inna yan
zu kud'in duka zaki canyesu cikin cikinki ki duba kiga jiya wahalar da muka sha da k'yar muka had'asu ai gara yau na mori abin mu ".
"ki dai mori abinki nida makanta keda cin kud'i"."Kaji Inna to ai harda ke za,aci dad'in ko baki ci?". Inna dai ko qala
bata qara cewa ba.
hahahaha Inna fa anaso a d'an lasa shiyasa akayi shiru. Mai shayi yana jinsu sai dariya yake bayan ya kammala sai yace"' yar makahi an had'a tace "to ".
Inna naji tasa hannunta cikin kwagiri ta fido mashi kud'inshî NARIM ta amsa ta
mik'a mashi" .Inna tace "yanzu ko na goro baki ragaman ba?"."Yi haquri Inna Allah ya bamu kafin muje gida sai ya sake bamu". Inna tace" hummm".
"NARIM tashi mutai gida na karya dan qamshin wainar k'wan nan ta cika man hanci baki na sai cika yake da y
awu".
Taja sandar Inna tana cema mai shayi zata maido mashi kofin shi yace" to zo ga sadakar hamsin a saima Inna goro". tace "yauwa mun gode kin gani ko Inna Allah ya sake bamu ".
Ahaka suka isa gida da sallama malam na zaune kan tabarmar kaba yana
saqa tabarma ta kaba da kuma tubar igiya yayi kusan guda ukku,ya d'ago kanshi ya dube su tareda amsa sallamar idanu shi fes dasu aman bai gani dasu aman in ya kalleka za kai tunani yana gani dasu.
NARIM tace" mun dawo malam".Ta zauna Inna ma ta zauna ka
n tabarmar da yake zaune nan suka zauna. NARIM ta fito da biredin ta da waina da man had'e suke waje guda tai bisimilla ta fara ci.
Malam yace" yau 'yar tawa shagali ake". Inna tace" humm 'yan kud'in baran jiya ne ta kashe yau ko kwabo ba mu samu ba".
Malam yace"ai sai da na ce maki kuyi zamanku yanzu bara da kike gani ba,a samun komai cikinta sai qasqantar da kai wani wurin yana maka wulaqanci shiyasa banason kina fita bara na fiso kuyi haquri na saida kabata na kawo maku kud'in ku sarrafa ". Inna t
ace" aiko malam yau bana yarda inyi tafiya da yarinya nan kaji yanda tai tai man tijara iri iri wai ita yunwa zata kasheta".
malam yace"NARIM kenan 'yar Inna da malam in tana jin yunwa kinsan ba lafiya ".
NARIM najin su qala ba tace masu ba duk kir
an yunwa da take ruwan shayin tafi sha sosai saboda ita tafi son tasha abu mai ruwa da safe kuma mai zafi.
Sai naga ta dauko biredin da shayi ta dawo gaban mahaifan nata ta zauna tace "Inna kiyi haquri kinji naga kamar ranki ya b'ace inda sabo ai munsab
a muyi fad'a muyi shirya ko inna ta".
Inna tace"ah ah wane irin fad'a, mu ba muyi fad'a ba bari ma fad'i kar ajimu" yauwa Inna ta".
Biredin ta ciro had'e da k'wai tai bisimilla tana basu a baki inta ba wannan ta ba wanna tare da had'a masu da ruwan
shayi duk da ba mai yawa bane haka sukaci kuma ya wadatar dasu suna ci suna sa mata albarka da adu'o'i gareta na Allah ya shirya masu ita ya kuma kare masu ita daga sharin masu sharrin.
Bayan sun cinye sai ta tashi tareda fad'in "Alhmdulillahi ala ku
lli halin".
D'aki naga ta nufa d'akunane k'ananan irin nada d'in nan qofar qarama ce sai ka duga ka shiga
wanin qamshin turare ne naji d'akin nayi mai dad'in gaskey tsaye naga tayi tare da ruqe qugu tana dube dube komai take duba oho d'akin tsaf da
shi 'yar katifa ce guda da zanen ta gefe guda kuma da lallausan bargo ne dai an aje gefe.
sai wasu akwatuna guda biyu saman su kuma ga darduma nan ta sallah,zuwa can sai naji tana magana ita kad'ai tana cewa "yau ma kunzo kenan nifa banason haka nan t
aya ba,a zowa sai na fita ko nayi barci shi wannan qamshi na meye kuke saman adaki?". Zuwa chan sai naji tsuwar wani abu na kuka d'akin kamar kukan tsuntsu wanda sai ka saurara kaji ba kukan tsun tsun bane!.
Ga binda yake fada cikin kukan nan shi w
anda haka muryar shi take" barka da zuwa NARIM ".Shine abinda yake fad'a .
sauran magangaanu kuma ban san miyake fad'a ba NARIM " ashe kana nan dan Allah ka fito in ganka ni banji abinda kake cewa ba sunana kad'ai na fara fahimtar mi kake cewa kafito i
n ganka ni kawai ban ganika sai dai inta jin motsinaka kuma ko na duba ban ganinka waye kai?". Zuwa can sai taji kamar
anyi tsoki bata qara jin komai ba sai tace" hummm kullum da nayi maganganuna ko tambaya sai ka yi tsaki kayi nima tsuuut
😉
".
"I
ndai tsaki ne shima ina gane shi karde a qara san yaman qamshi cikin daki ayyhee na dai fad'a maku ".
Tofa kuta yani gani da ji mizai wakana?
ku biyo
golden girl kuji...
Ina son ruwan comments in ban ganiba saina barshi.
~c
omments d'inku shine k'warin gwiwata~
_vote&share_
*GAMO DA KATAR*
(yar makahi)
*Na*
*yar mutan jibiya*
AMMYN KHAIRAT
*Dedicated to sarauniya Beelat*
(¯`*•.¸,¤°´
✿
.
。
.:*
ք
ʀ
օ
ʄɨ
ƈ
ɨɛ
ռ
ȶ
ա
ʀɨ
ȶ
ɛʀ
ֆ
*.:
。
.
✿
`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιт
ү
тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*Bismillahir-rahamanir-rahim*
Page 3
⃣
*Narim* bayan ta gama magana da mutanan b'oyenta kayan wanki ta fido na mahaifanta domin ta wanke masu bata bari su tara kayan daud'a,ko kala biyu ne suka
cire sai ta wanke su ita ke masu wanki yarinya ce mai tsabta,kujera naga ta d'auko tareda botikin wanki da roba.
Ta zauna ta fara wanki tareda waqarta sai naji inna nace mata" *Narim* ba dai wankin bane kike cikin sanyi nan ba?Gashi mura ta sha maki kai
dan Allah maida shi sai zuwa azahar rana ta fito"."Inna ai basu da yawa kala biyu ne na yau da kuka cire, sai nawa kala ukku kenan yanzu na wanke su".
"To *Narim* Allah yai maki Albarka wai dan saboda mura da kikeyi ne"." Karki damu Inna mura kuma ai t
a riga data kamani sai dai tai man sauqi."
"To Allah ya kawo maki sauqin". Amin Inna"."Yauwa gama kizo ki sayo maganin mura" ."To Inna kin san nifa ban shan magani ita mura kuma maganin tana man kai".
"Na man kai Inna mai dan romo romo". Tofa kee *
Narim* bakinki ya san makwantar dad'i"."Hahaha Inna kenan wayaqi dad'i sai in bai samu bah ko baba?". Babanta yace" haka ne *Narim* kowa ma yana son dad'i maza gama wanki mutai kasuwa naga tufkar igiyar nan da tabarmar sai mu saido sai mu biya ki sawo na
man kan". "Yauwa Baba yanzu kuwa zan ida yau zamu sha dad'i d'anye zamu sayo Baba ni zan dafa mana shi". Yace" to".
"Gama sai mutafi". Inna tace" yanzu malam biye mata za kai kuka so kud'in maimakon ayo cefane da siyo kayan abinci sai ka biye mata asiyo
nama gaskiya da zakaji shawarata kar asiyo naman nan"."Kaji Inna kuma in ansiyo sai kinfi kowa ci".
"Hummmm *Narim* kenan Malam kada ka biye mata dan Allah qara ayi malaiji kaga bara nan ko anje basa mowa ake ba balle muci in mun canye anjima mu koma
".
Malam yace"ba komai ni daman ban son kuna zuwa bara nan in dai kana sana,a ai komai mai sauqi ne tunda Allah ya bani baiwar yin abubuwa ko kana gida anzo asiya".
*Narim* tace "haka ne baba Allah ya bada sa,a muruqacin gumenmu kulum muna shan dadi
kama gidan su Amar".
Baba yace". Ameen 'yata". Bayan ta gama wanki tayi wanka duk kuwa bala,in sanyi da ake sau ukku take wanka kuma da ruwan sanyi da safe da zasu bara tayi yanzu kuma gashi tayi *Narim* kenan ba dai tsafta ba 'yar ga Inna da malam 'ya
r makahi inji mutane sunan da suke mata kenan itako tace" maka d'an masu ido"
Ta shirya tsaf da ita riga da suket ne tasa mu kyau da tsada ba wata kwalliya tayi bah mai ne ta shafa da hoda sai gazar sai hijab din ta dan garami dai dai kafad'arta .
Tayi kyau sosai duk da kasancewarta yarinya sai baza qamshi take na wani mayan turare
Baba na shirya to ta hada igiyoyen wuri guda ta daure tabarmi ma ta hadasu da igayar ta daure su duka waje guda" inna taso na kai ki d'aki nan rana ta yi yawa kafin
mu dawo kuma zata kawo maki".
*Narim* kenan kina shagwab'ani in banda abinki ko rana ta kawo ai zan iya ko mawa d'aki i naji ni dai tashi na mai daki tunda ina nan
Ta kama hunnu ta su kai d'aki tare da kai mata ruwa ga buta da roba mai fadi lokaci w
alaha