Showing 33001 words to 36000 words out of 135595 words
dai-dai ta parking muka fito daga motar maigadi yakaraso yana mana sannu batare da dukkanmu mun amsa ba Bappa yayi saurin cewa
"Wayaje y
a É—auko su Naseem a makaranta a cikin ku?."
maigadi yace "Gaskiya babu wan da yaje É—auko su dan tun da kuka fita ma babu wan da yafita, yau kam sunsha zama a makaranta Yakubu yayi hanzarin zuwa É—auko su."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un an ce anzo
an É—auke su kuma kace ba wan da yafi tun fitar mu an sace su kenan."
nayi maganar tare da fashewa da kukan da Bappa ketasa ni danneshi, nacigaba da faÉ—in
"Ina suke ina suka shiga waya É—auke su.".
maigadi ya walalo ido tare da faÉ—in
"Iye! ansace su
!."
Bappa yace "Ka tabbatar da babu wan da yafita."
yace "Wlh babu wan da yafita tun fitar ku ina bakin get É—in nan........!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:55 - Ummi Tandama😇: An buɗe murfin motar, baya na ɗan yi da sauri dan kaɗan ya ra
ge marfin ya bige ni, kasan cewar nazo daf da motar sosai. da sauri na É—ago dan ganin wan da ke cikin motar, ido na waro da É—inbin mamaki ganin mutumin da su Nasmah suke cewa Daddy ne, tsayuwa ta na gyara ganin yazuro kafar sa waje yafito daga cikin mota
r,baki na buÉ—e cikin masifa ganin yan da yayi kusan bige ni da murfin motar sa, "Malam ya haka baka ganine?."
nayi maganar ina yi masa kallon sama da kasa.
tsayuwar sa ya dai-dai tare da mai da murfin motar ya rufe, kana yashiga nuna min yatsa tare da k
aÉ—a yatsar yasoma magana.
"A kan wani dalili zaki rika birkita wa yara ƙwaƙwalwar su, kinyi yunkurin sauya musu School abaya, ba'a baki dama ba shine kika ajiye su a gida tsawon sati guda, sannan kika sauya musu Makarantar, ilimi kike so su samu ko kuw
a birkita musu ƙwaƙwalwa kike son yi, kada ki kuma yunkuri da tunanin sauya musu makaranta kan wani dalilin ki mara amfani, idan kuma ba haka ba."
sai yayi kwafa tare da kaÉ—a yatsar sa.
kamar daga sama nake jin maganar nasa mamakin sa da furucin sa su
ka sani gyara tsayuwa ta ina yi masa kallon kacika mai karfin hali.
"Dakata malam."
nafaÉ—a ina É—aga masa hannu, kana nacigaba da faÉ—in.
"A kan dalilan su Æ´aÆ´ana ina da ikon yin komai da su, dalilina mai amfani, kada ka kuma cewa dalilina bashi da
amfani tun da baka sanshi ba,
Æ´aÆ´a nawa ne nike da ikon yin komai kansu, malam kafita daga rayuwar Æ´aÆ´ana kana ta yau darar su da danganta su da kai, da suna mai kama da uba, Æ´aÆ´ana basu da uba kuma basa bukatar uba domin bazai yi musu amfanin komai
ba, rayuwar su a haka tafiye musu rayuwa da uba sau dubu dan bashi da wani amfani a gare su."
sassauta maganar da nake nayi tare da haÉ—e hannaye na biyu kana nacigaba da faÉ—in
"Dan Allah kafita daga rayuwar Æ´aÆ´ana kada ka yaudare su da wannan kalma
ta uba, dan basu da uba kuma basa bukatar uban, kuma ba shegu bane Æ´aÆ´ane tsaftatattu mafiya daraja."
Afusace yashiga matso ni, ganin yan da yanayin sa ya sauya gaba É—aya, sai na shiga ja da baya, shiko maso ni ya cigaba da yi tare da nuna ni da yats
a, yana huci kana yasoma magana cikin É—aga murya
"Idan kika sake cewa basu da uba sai ranki yayi mummunar ɓaci, idan kika kuma sako kallamr yaudara sakani na dasu!..."
sai yayi kwafa tare da kaÉ—a yatsar sa alamun gargaÉ—i,
mamakin ganin karfin halins
a muraran nake, wai ni da Æ´aÆ´ana ake nuna min iyakata a kansu,
bil hakki da gaskiya yake maganar dan kuwa fuskarsa ta nuna, niko
baya na kuma ja ganin yan da ya matso ni sosai yana maganar kamar zai kai min hannu,
wani irin kallon shekeke nabisa da s
hi sannan na ce
"Idan ba yaudara bace mene ne, kana cusawa yara abun da babu shi, cikin rayuwar su,
ina sanar maka da hakan ne sabo da matsaltawan ka kansu, na dai faÉ—a maka kafita daga tsafgar Æ´aÆ´ana idan kuma ba haka ba zan sa ayi maka gargaÉ—in da
zaka fi fahimta."
ina kai wa nan najuya.
Shan gaba na yayi a fusace cikin muryar da yake nuni da tsantsar gargaÉ—i ya ce
"Yazamo na karshe fitar kalmar nan daga bakin ki, idan kika sake kika sake furta kalmar durkuso cikin rayuwar su, bazan sa ayi mik
i hukunci ba ni zan yi miki hukunci da kai na! ki sake nanata kalmar basu da uba kigani!."
yayi maganar cikin
fusataccen amon sauti, a zaburi namatsa gefe dan maganar nashi ta shige ni rabon da ayi min ihu da tsawa irin haka har na mance, shiyasa abun y
azo min a sabo.
ba zato naji kafata ta ta dama ta wuce cikin abu kamar rami, da sauri na juyo sai kawai na tafi luuu gaba É—aya, idanuna na rumse da karfi ina jiran najini a kasa, sai jina nayi zundum cikin ruwa,
kara na ƙwalla wan na hakan yayi sana di
yyar wucewan ruwa cikin bakina,
fafutukan niman numfashi nashiga yi, da niman ceton kaina, duk buÉ—e bakin da zanyi sai ruwa ya wuce ciki, nayi-nayi na iya mike wa tsaye na kasa, duk da kuwa zurfin ruwan idan zan shiga da kafata iya kirji na yake zuwa min
.
Shiko Ahmad da sauri ya faÉ—a cikin swimming pool É—in ganin yan da ta ke bubbuga hannu da yin sama da shi
da alamun niman ceto.
hannu na ya ruko da karfi ya É—ago ni yamikar da ni tsaye.
ruwan da ke kunshe cikin bakina dana ki haÉ—iye shi dan cikar
da ciki na yayi, na furzar da shi tare da sauke tagwayen numfashi, ina damke cikina da ruwa yacika shi, a wahalce na na É—ago hannuna É—aya na share fuskata tare da tattaro gashi na daya rufe min fuska, na mai da shi baya,
ida nuna na sauke kansa, dai-d
ai lokacin daya kai
hannu ya share ruwan dake fuskar sa, sai a lokacin na lura ruwan dana furzar daga baki na a fuskar sa na fesa.
shima idanun sa a kai na tun daga gashin kaina yake bina da kallo har kasa, kasan cewar rana ya taso ya haske cikin ruwan
ana iya kallon abun da ke kasan ruwan.
dogon tsaki na ja dan nakasa magana tsabar haushi, bugu da kari yan da cikina ya cike tam da ruwa.
a hankali na soma tafiya cikin ruwan har na isa bakin gaɓar gun matattakalar shiga da kuma fita daga cikin swimmin
g pool É—in,
a sannu na soma hawa maganar sa na jiyo,
"Ki tsaya a taimaka miki kirage ruwan da kika sha."
cigaba da haurawa ta nayi batare da
waige ko tsayu ba,
ina karasa fita da sauri nayi hanyar part É—ina jin zuciya ta na tashi, cikin sauri na sh
ige cikin side É—in direct sama na haura,
ina shiga bedroom É—ina da sauri nashige bathroom, ai tun kan na karasa bakin toilet nafara sheka amai tsakiyar bayin, zallar ruwa narika aman sa.
da kan sa aman ya tsaya kamar yadda yazo bazato ba sammani, numfa
shi narika sauke wa ina tallafe da cikina da yanzu nake jin sa wayam, sai dai É—an murÉ—ar da yake min.
a daddafe na tsaftace bayin na tuɓe kayan jikina da suka jike gaba ɗaya na wurgasu cikin wishing machine, nafito doguwar riga mara nauyi na zura, ka
na na isa bakin gado na zauna ina mai cigaba da sauke numfashi,
tsaki narika ja a-kai-a-kai tsabar haushin da nake jin kaina ciki, har lokacin kasa iya furta komai nayi.
idan na tuna ruwan da na hambuÉ—a a cikina sai naji kamar nayi ihu, sauki na ma É—a
ya jiya-jiyan nan nasa aka fidda ruwan dake cikin swimming pool É—in, aka wanke cikin sa a ka kuma zuba wani, ban kuma yi amfani da shi ba.
wani dogon tsakin naja yayin da na kai bayana na kwanta kan gado.
mamakin karfin hali da takaicin mutumin nan suka
rika zuwar min,
wai ni yake yiwa gargaÉ—i kan Æ´aÆ´ana,
ya kuma yi sanadiyyar faÉ—uwa ta cikin ruwa, badun kwanana na gaba ba wata kila da yanzu ana kan shirin kai ni makwanci.
Dole nasa jami'an tsaro cikin lamarin dan ban amin ta da mutumin nan ba, aw
ani dalili zai rika shiga min cikin gida kai tsaye har yarika yimin barazana kan Æ´aÆ´ana.
Mikewa zaune nayi tare da É—aukar waya ta, number Mr Aliyu nakira wato P.A na, ko da ya É—aga bayan mun gaisa na É—aura da faÉ—in
"Mr Aliyu ina so a saka min jam
i'an tsaro a gidan nan."
da sauri ya ce "Madam meke faruwa akwai matsala ne?."
yayi maganar cikin nuna damuwa sosai kana yaci gaba da faÉ—in
"Ai Madam tun farko shiyasa nace azuba jami'an tsaro gida kamar wannan dole sai da manyan Security masu rike da
bindiga, kikace abar mai gadi
kaÉ—ai ma ya isa, ina kuwa zai isar wa gida kamar wannan, yanzu kuwa zan fita in sha Allahu anjima zamu zo da su."
na ce "To Allah ya kaimu."
nakashe wayar, ina katse kiran kiran Bappa na shigowa, na daga da sallama daga cik
in wayar Bappa ya ce
"HAMDAH ko kina bacci ne?." na ce
"A'a ba bacci nake ba Bappa." ya ce
"To kizo yanzu maza." da sauri na mike jin yana faÉ—in haka ya kashe wayar.
cikin hanzari na nufi side ɗin su Bappa da sauri na dan Bappa bai taɓa min irin wan
nan kiran ba nasan komai akayi akwai wata masalar, da ire-iren waÉ—an nan tunanin nashige cikin side É—in.
turus naja na tsaya yayin da jikina ya kama ɓari ganin Yakubu durkushe yana kuma rungume da uniform ɗin su Nasmah,
cikin tsanani tashin hankali n
a karaso cikin parlour'n gaban Yakubu natsaya cikin rawar murya da kuka keson kwace min na ce
"Ina yara na?!."
nayi maganar cikin rawar murya sosai tuni hawaye yacike ido na.
Bappa da ke zaune kan kujera ya dube ni tare da faÉ—in
"Zo zauna nan HAMDAH."
yanu na min kujerar da ke kusa da shi, ban iya bin umurnin Bappa ba dan kuwa hankali na yakai kololuwa wajen tashi, duba da yan da Yakubu yake ɓari yakuma rungume uniform ɗin gam-gam.
Inna Wuro ce ta mike tazo taruko faÉ—ata ta jamyo ni ta zaunar da ni
kan kujerar, tuni hawayen da suka cuko idona suka fara zuba. Bappa ya girgiza kai yana faÉ—in
"Muma mun shiga irin yanayin nan da kika shiga a yan da yashigo mana kamar an rakoshi a guje,
tam bayar da na fara mishi shine ina yaran suke ganin uniform É—
in su a hannun shi, da kyar ya iya ba mu amsar suna nan kuma suna makaranta, yaji tsoron ya tinkare ki kai tsaye shiyasa yazo nan."
kai Yakubu yashiga gyaÉ—a wa yana É—an rarrafowa da guiwar sa yana kuma faÉ—in
"Dan Allah dan Annabi Bappa Malam ka rokar
min afuwar ta wlh duk yan da naso na hana faruwan haka bai yuwu ba, wlh fin karfi aka nuna min muraran."
Bappa ya katse shi ta hanyar É—aga masa hannu ya ce
"Ya isa." kana Bappa ya juyo da kallon sa gare ni ya ce
"Lokacin da suka fita zai kai su makaran
ta a hanya suka haÉ—u da Ahmad Tijjani Sabil ya sai da su, yake tambayar su ina zasuje ganin ba hanyar makarantar su suka nufa ba, sannan kuma ga wata uniform É—in daban a jikin su, to shine shi Yakubun ya shai da masa in da zasu, shikuma Ahmad yace kada y
a kuskura ya kaisu wannan makarantar yawuce ya kaisu wan can makarantar su, to dai a takaice tare suka tafi da shi wancan makarantar da aka cire su yasa aka basu wani uniform, yakuma tuɓe musu najikin su shine yabashi wan da yacire musun yace ya mai do sh
i gida,
to shine ya dawo hankali tashe yakuma ji tsoron yaje ya tinkare ki da batun shine ya zo nan,
kafin na kira ki sai da na kira shi Ahmad ɗin sabo da ina da lambar sa dan ranar da yazo nan na karɓi lambar sa, ashe dai zatayi amfani gaba akuma ir
in wannan ranar,shine na kira sa dan ji dalilin sa na yin hakan,
ya bani tabbacin dalilin sa na yin haka, kuma na gamsu, yace yawai ta canza musu makaranta a karancin shekarun zai iya birkita musu ƙwaƙwalwa gara abar su idan suka gama can ɗin kan lokac
in sun daÉ—a wayo sai suyi gaba, kuma nima nayi nazari naga hakan yafi abarsu a can É—in, nayi masa
maganar dalilin ki na canza musu makarantar yace za'a kara tsaro sosai babu wata matsala."
Yakubu da tun da Bappa ya soma maganar yake ai kin gyaÉ—a ka
i da buga bayan hannun sa cikin É—aya tafin hannun sa, yayi kalar tausayi, Bappa na gama maganar shima ya É—aura da faÉ—in "Wlh tallahi Hajiya na rantse miki da Allah, ba laifi na bane, na dage wajan ganin ba'a kuma samin wata matsala ba kamar yadda nayi
miki alkawari, wlh Hajiya dana buÉ—e baki zanyi masa musu dawani yafito daga cikin motar sa, ya shake ni sai da naji kamshin kabari, shi ya hana mutumin da yanzu na sheka,
ki gafar ceni Hajiya ki tai maka kibar ni a bakin aiki na."
Numfashi na sauke j
in akasin abun da nake tunani yafaru a kansu, dan Ni nagama tunanin hatsari sukayi sun mutu shine yakawo kayan su gida.
duban Bappa nayi ina shere hawayen fuska ta nace
"Yan zu Bappa ka amin ce da abun da yafaÉ—a kenan?, to shi ina ruwan shi da su me ya
shafe shi da lamarin su da har zai rika shiga, har fa Daddy yake cewa surika ce mishi meye gamin sa da su."
murmushi Bappa yayi irin tasu na manya kana ya ce
"To in ban da abin ki HAMDAH ai wan da ya nuna yana son naka yagama yi maka komai a rayuwa, kuma
da kike cewa yana shiga lamarin su basu kaɗai ba lamarin koma waye yana shiga, idan baki mance ba na taɓa baki labarin sa nazu wa rugar mu da yayi, muma ba lamarin mu yashiga ba yakuma jiɓanci lamuran mu, yayi silar magance mana wutar fitinar da take t
a kunno mana,
ko jiyan nan da daddare munkalli labarai gidan TV wasu iyaye sun fito suna mika masa godiya kan gudumawar da ya bada kan Æ´aÆ´an su, su iyayen ma basu ma sani ba Æ´aÆ´an ne suka dawo gida suke faÉ—a musu alkhairin da yayi musu,
a makarantar
gwamnati suke karatu ya cire su ya mai dasu na kuÉ—i,
sannan kin ce meye gamin sa da su,
ke da kike taimakon bayin Allah meye gamin ki da su?,
ai shi tai mako basai wan da kasani kake taimaka masa ba, duk wan da Allah ya sa da rabon sa yafaÉ—o ta kansa
sai ka taimaka masa ladan ka na gurin Allah,
shiya sa Allah ya halittomu kala biyu mai kuÉ—i da kuma talaka hakan kuma jarabta ce, idan kai me kuÉ—i ne kayi kokarin cin jarabawar da yayi maka, wato kajikan na kasa da kai, ka kuma tsare dokokin Allah, to
da yardar Allah babu shakka zaka shiga aljanna ta sanadiyyar jaraftar ka da yayi da arziki,
idan kuma kai talaka ne, karike talaucin ka kabi dokoki Allah, kai ma zaka wuce aljanna da yar dar sa.
shi tai mako ba sai wan da kasani kake yi masa ba.
kiran s
a da sunan uba kuma da suke yi, ai duk É—a nagari shike daraja nagaba da shi yakira sa Yaya wan da ya haifesa kuma yakira sa da sunan uba, wan da yayi jika da shi yakirasa da Kaka, abun alfahari ne É—anka yazamo daga cikin irin waÉ—an nan Æ´aÆ´an, ba ai bu
bane dan sun kirasa da suna Daddy tun da yakai ya haife su, zaki so ace Æ´aÆ´an ki suna da rashin kunya ko basu da tarbiyya?."
Shiru nayi batare da nace komai ba.
murmushi Inna Wuro tayi,dan ta fahimci in da maganar tawa ta dosa, kana tace
"HAMDAH ke
nan ai laifin wani baya shafar wani."
kana ta kawar da zancen da faÉ—in
"Sai kiyi wa Yakubu hakuri ya dai na wannan tafa hannu da ɓarin jikin da yake."
da sauri Yakubu ya daÉ—a rarrafo wa gaban mu yace
"Whl Innar Gida kada kiga shakar da mutumin nan y
amin, tsaro biyu ne suke girgiza ni a jikina, tsoron kada Hajiya ta kore ni daga ai ki na, da kuma tsoron wannan basamuden mutumin da suke tare da Ahmad Sabil daya makuren makogaro."
yayi maganar yana É—aga wuyar sa da nuna mana in da ya shako san.
dariy
a duk sukayi ban da ni dana murmusa kawai.
na yar da da dukkanin maganar da Bappa yayi, sai dai inajin abune me wuya na iya jure wa dajin kalmar uba na fita daga bakin su Naseem.
Bappa yacewa Yakubu ya tashi ya tafi anjima yaje ya É—auko su a makarantar.
ya mike yana zuba godiya yayi waje.
Haka su Bappa sukayi ta jana da hira bani na bar side É—in ba sai wajen karfe 12, gani lokacin dawowar su Naseem yayi nayi musu sallama nakoma side É—ina.
komawa ta bada jimawa ba su Nasmah suka shigo a guje, kal
mar da suka fara furta min shine Daddy'n su ya ce gobe zai zo ya É—auke su a mota.
ban iya ce musu komai dan ko na faÉ—an ma abanza ne...
A ɓangaren Ahmad Tajjani Sabil, tun da yabar gidan tuki yake kamar mai koyon tukin, a haka ya iso bakin wani
katafaren get me girma da tsaruwan gaske, yayi hon batare da ɓata lokaci ba a ka wangale masa katafaren get ɗin,