Showing 99001 words to 102000 words out of 135595 words

Chapter 34 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

ne yayi ribas ya dawo da baya, kanta t

a nuna alamun ita yace Eh.

sai ta juyo ta nufi in da yake.

kansa ya leko ta window motar yace

"Hajiya kika ce meye sunan wan da kika zo neman ta?."

tace "HAMDAH." yace "Babu wani inkiyar ta HAMDAH É—in ne kaÉ—ai?."

shiru Ummi ta É—an yi tana son tuno

sunan da taji an kira ta da shi a TV da kuma wan da ta taɓa gani a wani gidan mai.

mutumin yace "Dama akwai wata ce me irin sunan nan sai dai tana da inkiya, mutane da dama basu san ta da ai nahin sunan taba sai inkiyar nata,sau ɗaya nataɓa jin ainihi

n sunan nata shine nake tuna nin ko ita É—in ce."

Ummi tace "Tabbas akwai sunan da ake kiran ta da shi amma naman ce."

yace "To wata kila ba ita bace ni wanda na sani idan kuma ban mance ba HAMDAH baji an faÉ—a amma sunan da aka fi sanin ta dashi shine w

an da take amfani da shi kan kamfanoni da gidajen mai asibitoti da sauran su, shine *HAM'NAS* ita kuma matar Ahmad Tijjani Sabil ne."

da sauri Ummi tace "Kwarai kuwa tabbas ita ce so nake na tuna "*HAM'NAS* É—in na mance, dan Allah bawan Allah kai ni gida

n nata."

yace "To a gaskiya dai ni ban san gidan ta ba gidan Ahmad Sabil É—in kaÉ—ai na sani kuma ance gidan ta da ban ne, sannan kuma gidan sa a gaskiya akwai matakan tsaro ko na kaiki ma ba lallai bane a barki kishiga in ba wai an san da zuwan ki bane."

É—an shiru yayi sai kuma yace "Amma dai shigo mu je tun da kin ce ita ce samun gidan ta bazai bada wuya ba sai muyi tambaya."

godiya Ummi tashiga yi masa da addu'ar samun nasara a rayuwar sa.

Tun daga gurin suka fara tambaya har suka sami wan da yayi

musu kwatance har unguwar da take da kuma lambar gidan.

suna isa dai-dai gida mai lambar da aka faɗa musu ya tsaya yace da ita sun iso, ta sauka tayi ta masa godiya kana ta baki 5k, ya karɓa shima yana yi mata godiya, kana yaja motar sa yayi gaba.

ido

ta zubawa katon gidan wan da tsaruwan sa ya kai ya kawo a ranta take faÉ—in.

anya kuwa gidan ne, anya ma kuwa HAMDAH suka gani a TV ko dai idanunsu ne ke yi musu gizo, ko dai wata ce me irin sunan ta suka gani suke tunaÉ—in É—iyar su ce?.

kai ta jinjina

yayin da jikin ta ya É—anyi sanyi da tunanin afili ta furta

"Sai na ga wannan É—in idan na tabbatar da ba ita ba bace sai na tafi na cigaba da niman ki HAMDAH."

a hankali ta karaso bakin get É—in ta kwankwasa har sau uku, kana mai gadi ya taso ya buÉ—e

karamar kofa ya leko kansa yace

"Wane ne?." tace "Nice." yace "Gurin wa kika zo?." tace "Gurin HAMDAH." É—an shiru yayi kana yace "Tasan da zuwan ki ne?."

Ummi tace "Bata san da zuwa ta ba."

yace "To ba a bamu masaniyar cewa wata zata zo ba ki nimi izin

in shiga kafin idan aka sanar mana sai ki shigo."

yana kokarin mai da kofar yarufe

tayi saurin cewa "Dan Allah kace mata Mamar ta ce ta zo."

yace "Maman ta haba Hajiya mun saba jin irin wannan."

ya mai da kofar zai rufe da sauri tamaso bakin kofar tana

faÉ—in

"Ganin ta kawai zan yi idan ba ita bace bama ni zan tafi." wani

security ne ya mike daga in da yake zaune ya zo bakin kofar yana faÉ—in "Mene ne wa tazo gurin sa?."

maigadi yace "Wai gurin Hajiya ta zo wai ita mamar Hajiya ce, nace mun saba jin

irin wannan masu neman taimako su rika fakewa da Æ´an uwan ta ne sai sun shiga kaji babu abin da ya haÉ—a su."

jami'in tsaron yace "Ita ta gayyaci ki ina katin shaidar."

Ummi tace "Bata san da zuwa ta ba kuce mata mahaifiyar ta ce tazo."

sauran securit

y suka mike daga in da suke tsaye cikin faÉ—a suka ce

su rufe kofar takira a sanar musu tukun abar ta ta shigo.

maigadi ya rufe kofar.

yana faÉ—in "Mutane babu godiyar Allah kaduba wannan matar kwata-kwata batayi kama da mabukata ba amma hali irin na mu

tum kabari a bawa na kasa da kai wai kai ma sai ka nimi kari."

Faty da ta fito daga side É—in su zata je gidan makotan su gurin kawarta, ta nufo bakin get tana hango yan da security suke magana da faÉ—a-faÉ—a da alama dai da wani wanda ya nimi shiga gidan

suke,

ta karaso bakin get É—in, mai gadi ya mike ya buÉ—e mata get tasa kai zata fita, sai ta hango Ummi a tsaye a gefe tayi jigum.

sai ta leko tace wa maigadi

"Wace ce wannan É—in?." mai gadi yace "Wai gurin Hajiya tazo kuma mu Hajiya bata bamu masani

ya kan cewa wata zata zo ba, wai cewa tayi ita mamar Hajiya ce."

Faty ta dube ta kana ta karasa fita waje."

kana mai gadi ya mai da kofa ya rufe.

har Faty tazo zata gota ta sai ta ce mata sannu.

Ummi ta amsa da yauwa, kana ta wuce.

Ummi kuwa gefe da g

et É—in ta nima guri ta zauna, a ranta take ayyana bazata tafi ba har sai taga wannan HAMDAH'N idan ba HAMDAH'N ta nane

sai ta tafi...

Har Faty ta gama zaman ta gurin kawar ta tafito lokacin yamma tayi sosai,

tayi mamakin gani matar nan har lokacin za

une a gurin.

har tazo bakin get zatayi knocking sai ta juyo ta dubi Ummi daÉ—an fuskantar tausayi ganin ta zauna shiru, tace "Wai wa Adda HAMDAH kika zo gurin ta."

da sairi Ummi ta juyo tare da gyaÉ—a mata kai, Faty tace "To ki kirata ki sanar mata kina

bakin get zata sa mai gadi ya barki ki shigo, in ba haka ba security baza su barki ki shigo ba."

Ummi tace "Bani da lambar ta, amma dan Allah kice mata mamar ta ce ta zo."

kai Faty ta gyaÉ—a da mamakin matar jin tace wai ita mamarta,ita kuma wannan kalar

nata salon kenan ko ba komai in ta faÉ—i haka ai za'a barta tashiga, gata kuma zubin ta baiyi kama da irin masu zuwa suna karyace-karyacen nan dan a barsu su shiga cikin gidan ba.

kai Faty ta jinjina.

sai tayi knocking maigadi ya buÉ—e ta shige ciki.

U

mmi ko zama ta kuma gyara wa.

ganin lokacin sallar magriba saura kaÉ—an ga unguwar shiru babu ko motsin mutane, tun da ta zauna ita dai bata ga wani mutum yazo ya wuce ba sai dai motoci É—ai-É—ai su zo su wuce, unguwar shiru kamar babu bil'adam, sai sauti

n kukan karnukan gadi.

a hankali Ummi ta mike tazo jikin get É—in ta kwankwasa.

mai gadi ya buÉ—e ido ya waro yace

"Har lau kece?."

a fusace security suka tambaye sa waye?

yace musu "Matar É—azun É—in nan ce." a fusace É—aya daga cikin su ya mike yaf

ito yace mata maza-maza ta bar bakin get É—in nan tayi nesa da gidan nan tun bai sa bindiga ya harbe ta ba, ya É—aga bindiga yana faÉ—in tayi sauri ta bar eriyan nan.

ai ko da sauri ta É—au jakar ta tasoma tafiya, cike da takaicin wai ita ce ake yiwa kora

r kare irin haka, amma babu komai zata jure koma mene ne har idan zata samo É—iyar ta...

Acikin gidan kuwa Faty na zaune a parlour ganin Bappa ya mike yana faÉ—in

"Lokacin salla ya kusa bari na shiga Masallaci."

da sauri ta mike tace

"La na mance wat

a mata tun É—azu ta zo tana bakin get security sun hanata shiga, wai cewa tayi ita mamar Adda HAMDAH ce, na mance naje na faÉ—a mata ko zata sa a barta ta shigo wata kila taimako ta ke nima."

tsayuwa Bappa yayi kana yaÉ—an yi shiru yace

"Tace ita maman t

a ce?." kai ta gyaÉ—a tana mike wa da faÉ—in

"Bari naje na faÉ—a mata Allah ta ban tausayi tun É—azu take zaune a waje."

Inna Wuro tace "To shine tun tuni baki je kin faÉ—a mata ba kika zauna shiriri ta, ace tunruni tana waje ai ko kuÉ—in mota aka bata z

ata ji daÉ—i."

waje Faty tayi tana faÉ—in "Yan zu zanje na faÉ—a mata ai wata kila har yanzu tana waje dan ko shigo wa ta ma a waje na barta."

Ina daga parlour'n sama najiyo muryar Faty a parlour'n kasa, Ahmad na zolayar ta budurwar Ustaz tana ce mas

a ita bata ma sanshi ba,

ta hayo saman tana dariya.

na sako kai na zan sauko ita kuma zata shigo parlour'n sama tace

"Yauwa Adda HAMDAH dama gurin ki zan je, tun É—azu wata mata tazo tana bakin get security sun hanata shiga tace wai ita mamar ki ce, su

kuma suka ce karya take so take abarta ta shigo kawai."

ido na waro tare da dafe kirji nace

"Wai ita mama tace?." kai Faty ta gyaÉ—a min. da sauri nace "Tana ina?." tace "Tana bakin get." da saur na wuce ta ina faÉ—in

"Ina so na ganta babu wan da ta taÉ

“a zuwa tayi karyar cewa ita mama na ne, sai dai suce su Æ´an uwa na ne, ina so na ganta."

nayi maganar ina karasa sauka daga step da sauri, gaba É—aya jikina ya É—au kyar ma,

cikin hanzari na nufi kofa da sauri haÉ—e da sassarfa nayi waje.

da sauri Ah

mad ya mike rungume da Ahmad karami yana tambayar Faty ta faÉ—a masa ko mene ne, bayan na yabi da sauri su Naseem suka biyo sa...

tun daga farfajiyar gidan naÉ—aga murya ina faÉ—in

"Mai gadi ina matar take."

har na karaso get É—in, da sauri msi gadi ya

mike yace "Hajiya an kore ta ta tafi."

murya a hargitse nace "Kuje ku kira ta yan zu ku dawo da ita ina so na ganta."

cikin hanzari biyu daga cikin security sukayi waje suka lelleka kana suka dawo suka ce, basu gan ta ba.

ganin yan da gaba É—aya lokaci

guda na ruÉ—e cikin tsawa Ahmad yace

"Kuje ku nemo ta yanzun nan kuzo da ita."

ai ko da sauri sukayi waje.

niko tsayuwa na gyara ina mai da numfashi kamar wacce tayi tsere.

Bappa ya karaso in da muke yana tambayar matar ta tafi ne?.

Ahmad ne ya iya ba

shi amsa nikam gaba É—aya na ruÉ—e sai kyarma nake haka kawai naji ina so na ganta.

munkai tsawon minti 15 tsaye a gurin kafin aka turo kofa,

ganin security ne yasa ni É—aga murya nace

"Ina take?." yace "Gata nan Madam sai da muka fita can farkon eriya

kafin muka iske ta."

yayi maganar ne yana shigo wa ciki, niko leken bayan sa nake ina alla-alla naga matar.

a sannu ta sako kafar ta cikin gidan da sallama yayin da É—ayan security ke biye da ita.

kamar almara kamar a mafarki nake binta da kallo yayin

da na wawwaro idanuna waje cikin matukar mamaki.

ido na kuma waro wa da karfi na furta

"Ummi Ummi na!!." da gudu nayi in da take na rungume ta ina faÉ—in

"Ummi dama kece Ummi kece."

sai kawai na fashe da kukan farin ciki ina daÉ—a rungume ta.

ita ma

rungume ni tayi tana bubbuga baya na yayin da hawaye ke zuba a idon ta tana faÉ—in

"Kiyi hakuri HAMDAH kiyi hakuri........!

8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 33

Bappa ya soma da addu'a bayan addu'a ya É—aura da faÉ—in

"Alhamdulillah mu

na godiya wa tabakara maÉ—aukaki mabuwayi mai izza, wan da ya nuna mana wannan rana, muna niman tsari da sharrin masu sharri Allah ya kaÉ—e mana fitina, muna godiya wa Allah da ya nuna mana wannan rana, Allah ya daÉ—a kaÉ—e mana fitina duniya da kiyama."

kowa ya amsa da amin amin,

Bappa ya gyara zama tare da ci gaba da faÉ—in

"Abubuwa sun faru da dama bama fatan hakan ta kuma faruwa Allah ya kaÉ—e fitina, ya iyar mana abun da baza mu iya ba, Allah yayi mana maganin makiya da masu hassada kamar yadda ya

nuna musu karshen sharrin su,

hakika addu'a makarin Mumini ne, a na son musulmi a duk in da yake a duk halin da yake ya kasan ce mai ruko da addu'a, domin addu'a takwabi ne mai kaifi ya kan tsare fitina da sharri da kaifin sa, hakika wannan abu da ya faru

ya nuna É—an dakacin addu'a kaÉ—an duk da Allah yayi taimako an farga da wuri, Allah ya da É—a tsare mu ya yi mana katangar karfe da azzalumai."

Abbu ya jinjina kai cike da gamsuwa yace "Amin ya rabbil izzati, hakika addu'a takwabi ne mai kaifi hakika la

marinnan ya jijjiga mu ba kaÉ—an ba duk da bakin mu baya iya

furta wa amma zuciyoyin mu tana kuna."

ya É—an sakai ta maganar tare da duba na kana yaci gaba da faÉ—in

"Kiyi hakuri HAMDAH duk da bamu kuma yunkurin niman ki ba amma zuciyoyin mu suna tare

da ke a ko da yaushe."

kai Bappa ya jinjina dan ya san cewa ai kin sihiri kenan shi yasa ake so a koda yaushe mutum ya zamana yana cikin sarki da addu'a idan aka jefe ka da shi bazai yi wani tasiri a tattare da kai ba...

Abbu yace "Muna mai ci gaba da b

aki hakuri hakika mun ai kata rashin kyautawa wa rayuwar ki, a matsayin mu na iyayen ki da kike da hakki a kanmu da muka gaza sauke shi na wasu shekaru mu na ruko da ki yafe mana."

da sauri na shiga girgiza kai yayin da hawaye ke zuba a ido na

kwalla na

share nace "Abbu bakuyi min komai ba, Abbu ka rokar min Abba ya yafe min dan naga kamar har yanzu bai yafe min ba amma wlh ni ban taɓa ai kata zina ba."

wani kuka ne ya tsuɓuce min na fashe da kukan, Aunty Rafee'at ta rungume ni itama ta fashe da kuka.

cikin matuƙar nadama Abba yake faɗin

"Ki gafarce ni HAMDAH tsananin kunyar ki ce ta hanani iya furta komai, tabbas nayi danasanin yanke hukunci cikin fushi, ki gafarce ni ki gafarce ni HAMDAH ina mai da na sanin yanke hukunci cikin fushi,

dana kore ki

HAMDAH ina kika shiga ina kika shiga HAMDAH nayi da na sani nayi na dama HAMDAH ina kika je wani rayuwa kika yi?."

Abba yayi maganar cikin nuna nadama sosai kamar zai zubda kwalla.

in da yake na rarrafo tare da rike hannunsa gam kana a hankali nashiga b

asu labarin abun da ya faru, tun ranar da na sa kafa na bar gida da

rayuwar da na fara fuskanta,

da rayuwar da mukayi cikin daji ni da su Naseem da,

irin gwagwarmayar da na sha a rayuwa har na kai matsayin da na ke a yanzu.

tun da na fara bada labari

n

gaba É—aya parlour'n ya kacame da koke-koke su Aunty Rafee'at har da jan shassheka, Ummi Mamie gaba É—ayan su kuka suke wei-wei kamar kananun yara,

Abba Abbu Bappa Ahmad duk kanin su sai sharar kwalla suke.

Abba yana sharan kwalla yana faÉ—in na yafe

masa,

kai na shiga girgiza wa

nace "Baka yi min komai ba Abba."

Mamie tana kuka ta rungume su Naseem da tun É—azu take jin wani yanayi a kansu a kasan ranta take faÉ—in a she dai jinin ta ne su shiyasa tun da ta sanya idanunta kan su take jin su a ciki

n jikin ta.

su Abbu suka shiga yiwa Bappa godiya da irin kokari da jajirce wa kan lamari na da yayi yake kuma kan yi shi da matar sa wato Inna Wuro.

Bappa yace ai yiwa kaine, da É—a da dukiya bana mutum É—aya bane kuma ba'a yi musu keta.

sun yaba kwar

ai da gaske da irin kokarin da Mama mai awara ta yi a kaina suka kuma É—au alkawarin niman ta suyi mata godiya.

Ahmad ma godiya suka yi ta masa suka kuma yi jinjina ga Rasheedat matar da ba kasafai ake samun irin su a duniyar mu ba....

A É—aya side É

—in da babu kowa ciki wan da yanzu su Talatu suke kwana ciki, nasa su Talatu suka fita suka koma side É—in su Inna Wuro suka shiga É—aya daga cikin É—akunan side É—in wan da ba kowa ciki,

wannan side É—in kuma nayi wa su Abbu da Abba Ya Masa'ud Fauzan mas

auki ciki.

É—aya daga cikin

É—akunan kasa kuma aka shigar wa Mamie kayan ta ciki, É—aya É—akin kuma Aunty Jaleela da Aunty Rafee'at da Nusaiba.

a ranar raba dare mukayi muna hirar bayan rabo da ahlina abu mafi soyuwa a rayuwa ta, Ahmad kuwa gidan sa ya

tafi yace ya barni na gana da Æ´an uwa na, bayan ya gama zolaya ta wai na share shi na nuna masa wariya...

kwanan su Abbu uku suka soma shirin komawa gida bayan na kaisu na nuna musu duk kanin kadarori na da suke cikin garinnan,

sauran na wasu gararruwan

kuma a computer na nuna musu..

ranar da suka cika kwana biyar suka juyo Bauchi, amma banda Ummi dan ta ce ita tana nan sai ta yimin zaman arba'in tukun.

Abba ko da wasa bai yi yunkurin hana ta ba, sai dai ma karfafawa zaman nata da yayi, yace ta zauna t

ayi min wankan arba'in kamar yadda ake yiwa mai haihuwar fari dan na cancanci haka, duk da na sami ingantaccen kulawa gun Mama mai awara a haihuwa ta ta farko wan da ya kamata ace uwata ce ta bani wannan kulawar,

to amma guri bai kure ba, ta zauna nakuma

kara samu agurin mahaifiya ta...

Ahmad yayi musu goma na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login