Showing 15001 words to 18000 words out of 135595 words
ki gaggansu gobe za'a fara tafiya shiyasa sukace kihuta yanzu."
k
ai na jinjina alamun gamsuwa, ikon Allah abun kamar a mafarki yake zuwar min.
knocking É—in da ake ne yasani mike wa nanufi kofar da nafi zaton tanan ake knocking É—in, na isa jikin kofar na buÉ—e,
wani nagani tsaye rike da basket har guda biyu a hannuns
a, É—an risinar da kai yayi alamun girmamawa kana ya É—ago yayi min barka da warhaka, na amsa kana yace min order ne daga hotel É—in su akace yakawo nan gidan, kai kawai na girgiza kana nabashi hanya yawuce ciki.
dinnig table ya isa ya aje kayan abincin k
ana yayi mana sallama yafita.
muna nan zaune a parlour sai wajen la'asar mukaje mukaci abincin, daga nan Bappa yakuma fita domin zuwa Masallaci shida Naseem.
Washegari da safe kamar yan da mutanennan suka ce zasu zo suka iso,
suna zaune a parlour niku
ma ina ciki domin kimsa su Naseem, ina gama kimsasu muka sauko nan muka É—unguma.
yau munsha yawo kaman kaman domin kuwa tundaga unguwar muka fara, wani gida mukaje sakanin sa daÉ—an rata da gidan da muke ciki, sannan muka wuce wasu unguwanni biyu duk ka
nin su da gidaje É—ai-É—ai, wan da an gama musu komai suna kulle,suka nunnuna min dakuma tabbacin nawa ne, nasha mamaki kwarai daganin manyan gidajen wai kuma a matsayin nawa.
daga nan wani tsalelen gidan mai muka je tun daga can nahango ( *HAM'NAS Co Pet
roleum Nigeria LIMITED* ) wan da aka rubuta da manyan harufa a saman gidan man, tunga nesa zaka iya hango shi ɓaro-ɓaro.
idanuna na lumshe tare dayiwa Ubangiji buwayi gagara misali tasbigi a kasan raina kana na buÉ—e,
Mun zaga gidan man na yaba da ts
arin sa kwarai yana rufe ne ba'a fara aiki da shi ba,
daganan kuma wasu gidajen man mukaje har guda uku duk masu É—auke da ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) daga nan muka kuma zuwa asibitoci suma masu É—auke da sunan ( *HAM'NAS International HOS
PITAL* )
suma asibitotin guda uku a gurare daban da ban manyan gaske, sai dai duk a kulle suke anzuba kayan aiki komai da komai acikin su sai dai ba'a fara ai ki da suba.
daganan kuma makarantu da kamfanoni muka nufa duk kanin su da tambarin *HAM'NAS* In
ternational School Of Science's And Technology, *HAM'NAS Store Complex's su ma duk ba'a fara ai ki da suba. sai kuna masallatai manya guda uku anzuba komai a ciki suma ba'a fara amfani da su ba.
Zuwa yanzu kam nidai komai ganin sa nake kamar almara naf
ara yarda kan cewa komai da gaske ne, sai yamma muka dawo gida, mun dawo a gajiye suke faÉ—a min cewa muhuta nan da kwana uku sai mu fara tafiya guraren kaddarorin dasuke garurruwa nesa da nan, nace to Allah ya kaimu..
Damin Bappa narikayi nace nidai ya
sa su Inna wuro da Fatu suzo kafin mutafi nan da kwanan ukun,
yace a'a abarsu tukun ba yanzu ba,
haka dai dole yasa direba yaje ya taho da su dan na tubure a la dole sai an kawo su, ko da direba zaije É—auko su nace yace musu kada suzo da komai, dan ciki
n side É—in dana matsawa Bappa sai ya zabi É—aya daga cikin side É—in gidan wan da zasu zauna ciki, akwai kaya komai na bukata sai suzo suyi amfani dashi abun da babu sai a karo musu kamar kayan sawa shi da babu a sauran side É—in.
hakan kuwa a kayi ranar
da su Inna wuro sukazo murna kamar nayi yaya, suma agefen su ba'a magana, na rungume Fatu inata murna, tarika É—aukar su Naseem cikin tsananin farincikin kuma ganin su.
a ranar ma Uncle Mahmoud yazo har da matarsa da yaran su, dan su anan Abuja suke gun
ai kin sa.
nan muka wuni da su wunin ranar yayi min daɗi matuka, sai narika jin su tamkar wani ɓari ga ahalina,
ganin su yaÉ—an rage min kewa da begen family na.
Yau asabar hakan yayi dai-dai da kwanaki ukun da zamuyi tafiyar, da sassafe muka É—auki
hanyar suwa Kano, motoci biyu muka tafi dasu motar mu ni da Naseem da Nasmah dakuma Bappa,sai É—aya daga cikin jagororin ke zaune a gefen direba, É—aya motar kuma mutane huÉ—u ne a cikin ta suna gaba muna biye da su.
mun isa cikin garin Kano da misalin Æ
™arfe 12:30pm sai da muka tsaya mukayi sallah kafin muka nufi inda zamu,
gidajen mai muka fara ziyarta kafin asibitoti dakuma kamfanoni.
bamufi awa biyu a cikin Kano ba muka É—au hanyar Kaduna a kaduna muka kwana, washegari muka nausa Katsina.
Sati bi
yu muka ɗauka muna yawon zuwa garuruwa ganin in da aka zuba ayyuka, masha Allah duk garin da mukaje daga gwamnatin su muke samun tarba da karɓa mai muhimmanci, daga karshe muka biyo garin Bauchi,
lokacin da motar mu tashiga cikin Bauchi state, tashin
hankalin da nashiga bazai misaltuba, wani irin tashin tsikar jiki da sanyi mai matukar shiga jiki su suka ziyarce ni, wani irin ɓari da kakkarwa nasomayi lokaci guda har hakorana suna garuwa da juna, sai kuma wani masifaffen zufa yashiga keto min, hankali
n Bappa yayi musifar tashi ganin halin dana shiga lokaci guda,
cikin tsananin tashin hankali jin bakon yanayin daya ziyarce ni lokaci guda tamkar ƙwaƙwalwa ta zata fashe jin wani irin abu mai matukar nauyi da kara ya dankare min a kai, kunnuwa na tamkar
ana busa wani irin busa mai matukar kara da firgitar wa, da karfi nakai hannuna na toshe kunnuwana cikin matukar jin azabar dake kokarin tarwasa min rayuwa nashiga faÉ—in
"Bappa mu tafi Bappa kace musu kada mu tsaya Bappa mutafi wayyo Allah na".
kaina
nashiga juyawa da karfi jin yan da zabar da nakeji na karuwa nan take nanimi tunani na na rasa.
cikin É—aga murya ganin numfashi nakokarin barin jikina Bappa yace
"Direba yi hanzari mufita a cikin garin nan yi maza da sauri!".
gudu direba ya kara bai t
saya ba sai da muka fita a garin, gabaki É—aya, hankalin kowa yayi masifar tashi ganin halin da nake ciki,
Bappa ko karatun Kur'ani yasoma yanayi yana tofa min, hankali na bai dawo jikina ba har sai da mukabar eriya'n Bauchi gaba É—aya.
A hankali narikaj
in abun da nake jin na sassauta har ya washe.
numfashi Bappa ya sauke tare da saida karatun da yake, kai ya girgiza tare da faÉ—in
"Kai mutum abin tsoro ne Allah kashiga sakanin nagari da mugu akwai hisabi ranan gobe kiyama".
yadubeni da kula yace
"S
annu ko HAMDAH".
kai na girgiza yace "Me kike ji yanzu?". nuna masa kaina nayi da hannu dan shi ke yimin ciwo sosai.
"Zai bari insha Allahu".
yayi maganar tare da buÉ—e tafukan hannunsa yasoma karanto Suratul (Khafi) aya goma na farkon surar haÉ—e da a
yatul Qursi'yu ya tofa kana yashafamin a kan. cikin yar da da buwayar Allah naji ciwon kan na sauka.
Ko da muka shiga jahar plateau state, farkon shiga garin Jos NARKUTA. wasu zafafan kwalla ne suka gangaro kan fuskata tuno da Mama mai awara, da sauri
nayi yinkurin yin magana a tsaya amma abun mamaki sai naji harshe na yayi min mugun nauyi gaba É—aya jikina ya sake babu alamar karfi tattare da ni, abun da na fahimta tun lokacin da nayiwa Bappa maga shigar mu Bauchi zan kuma wata maganar naji na kasa, ha
r kuma yanzu ina jin yanayin...
da daddare muka shiga Abuja, da kyar da taimakon Bappa na iya sauka cikin mota muka shiga ciki.
Inna wuro ta firgita da ganin yanayi na, ko da Bappa yayi mata bayanin abun da ya faru, hankalin ta yayi masifar tashi, yace t
a taimaka min naje na kwanta, shikuma yafita can ya dawo da ɗan karamin ƙwarya da magani a ciki yabawa Inna wuro yace
"Kibata tasha babu komai insha Allah zata ware garin ne kwatakwata basa so tashiga sai dai tayi nesa da shi sun mance cewa Allah baya b
acci".
Inna wuro tace "Ikon Allah wannan irin shiga sakani sai sakayyar Ubangiji".
ko da Inna wuro ta bani maganin inasha bada jimawaba bacci yaÉ—auke ni, ranar a kaina ta kwana, Fatu kuma tana tare da su Naseem a É—aya É—akin dake kusa da nawa.
washeg
ari kuwa cikin yarda da buwayar Allah namike garau...
muna tare a parlour ni Inna wuro Fatu dan har lokacin basu koma side É—in suba, labarin garuruwan da mukajejje narika basu ina washe baki da faÉ—in
"Allah Inna wuro bakuga abubuwan yan da sukayi kyau
ba kai har da garin da ban taɓa zuwa ba".
nayi maganar ina washe baki, dariya suka rika min, nan
Bappa yashigo ganin jikina shima yazauna mukayi ta hira....
bayan kwana biyu
Mutane biyu daga cikin jagororin nan suka zo su da wasu mata guda biyar
sukace na zama a cikin su wan da zasu rika yi min ai ki,
mata ne irin wan da suke karkashin paundation, irin waɗan da mazajensu suka sake su dakuma wan da mazajensu suka rasu, akan ɗauke su ai ki irin gidajen masu kuɗi ɗin nan, a cikin su na zaɓi gud
a uku dasukafi kwanciya min a rai, kana nace zan gwada ai ki da su.
É—aya na É—auke ta a matsayin mai kula da su Nasmah dakuma kula da tsaftar side É—in,
na biyun kuma mai girka abibci, sai kuma É—ayar na turawasu Inna wuro ita zata rika kula da tsaftar
side É—in su dakuma girkin su.
nan suka kuma gabatar min da masu maza wan da nazo nasame su a cikin gidan, direba sai mai baiwa fulawa ruwa shi zai rika wanke mota, sai mai gadi dakuma mai kula da tsaftar farfajiyar gidan gaba É—aya.
mun zauna da su na É
—an wani lokaci na fahimci mutane ne masu kirki da rukon amana.
Haka rayuwa tacigaba da tafi, tuni akayi bikin buÉ—e masana'antu da masallatan nan manyan shuwagabannin Nigeria sun halacci torurrukan sun kuma bada gudummawar su kwarai da gaske wajen gani
n an É—ibi ma'aikata masu inganci.
Bayan wani lokaci
Tuni aka damkamin ragamar duk wasu kaddarori na ni nake bada umurnin ayi da kuma kar ayi, har kuma yanzu muna tare da jagororin nan su suke sanya ido kan ganin komai yatafi dai-dai.
tuni nasa aka
baiwa Fatu uniform a É—aya daga cikin makarantu na, dan dama acan rugar ma tana karatun ta tacigaba a nan.
Zaune nake a parlour ina dudduba jerin sunayen mata da matasan da nasa a É—iba, a karkashin paudasion É—ina domin basu tallafin wasu kuÉ—aÉ—en da
zai jamusu jari domin dogaro da kai na tura da kuÉ—aÉ—en tallafin izuwa asusun *HAM'NAS* paudasion.
a hankali na mike tsaye tare da yin mika haÉ—e da salati, wayoyina na tattara haÉ—e da sabuwar system É—ina, na haura sama,
kan bedside na ajiye su kana
na haye gado dan bacci nake ji, ina so nayi baccin kafin su Naseem su shigo dan suna can side É—in su Bappa.
har na kwanta na tuna da akwai maganar da nake so muyi da Bappa kan wani Company na murza karfe da ake gina shi a Lagos,
mikewa nayi na fita dan
ina so muje ziyarar gani da ido acikin satin nan.
da gudu Nasmah ta shigo tana faÉ—in
"Mommy kin ga Naseem ko jai camin jiji".
Naseem shima dagudun yashigo yana binta da abun yana dariya, Fatu na biye da su tana dariya da faÉ—in "Naseem kabari kar ka sa
mata".
da sauri nakarasa sauka kan step na rungumo Nasmah dake falfala gudu kamar zata kife kasa nace "K.......!�
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:54 - Ummi Tandama😇: HMD
WASA FARIN GIRKI!!!âœğŸ?
_(Book 3)_
🅿�4
Asannu a ka wangale tamfatsetsen get É—in gidan, motar gaban mu yakusa ciki, a hankali direban dake jan mu ya danna hancin motar cikin gidan, a tsakiyar farfajiyar gidan duk suka faka motocin, a sannu na zuro kafafuna waje, "Ya ilahi ya litta
hi".
abun da na furta kenan lokacin da na dai-dai ta tsayuwa ta a cikin gidan, bin gidan nashiga yi da ido har ina wai ga gefe da gefe na.
gaba É—aya gidan da tsaruwar sa yatafi da ni, tsaruwan gidan yawuci misali komai an tsarashi a inda ya kamata yana
ajiye a in da ya dace,gida ne babba mai É—auke da part har huÉ—u, daga gefe can gabar da gidan side ne guda É—aya sai kuma gefe ta hannun dama shima side ne guda sai kuma gefen hagu shima side É—aya, sai dai Æ´an madaidaita ne ba wasu manya ba.
daga tsak
iyar gidan kuwa wani side ne na musamman wan da yazamo sauran side É—in sun sashi a tsakiya shi kam gini ne mai hawa É—aya babbane ya tsaru iya tsaruwa, daga saman side É—in har kasan sa yaji ado da gilasai masu ban mamaki an kawata shi tamkar a turai,d
aga kasa kuma an zagaye shi da wasu flaw's masu matukar kyau da É—aukar ido,
gaban side É—in wani shinfiÉ—aÉ—É—iyar swimming pool ne wan da aka kawatashi da rubber grass malaye har bakin kofar shiga side É—in.
gefe can kuma parking space ne É—auke da la
fiyayyun motoci da suka kai guda uhu a cikin sa,
daga farin shiga gidan kuma gefe da É—akin mai gadi masallaci ne shin fiÉ—aÉ—e agun,
sai kuma É—akuna guda É—ai-É—ai a jere guda uku a gefe da masallacin ta can.
Maganar Bappa naji yana faÉ—in
"Muje ci
ki ko HAMDAH." da sauri nadawo daga duniyar kallon gidan dana tafi, da murmushi kan fuskarsa dan ganin yan da na tafi gaba É—aya na shagalta da kallon gidan.
na ce "To Bappa". a hankali nabi bayan su side É—in da ke gefe ta hannun dama muka nufa a hanka
li nake taka kafata ina cigaba da baza ido cikin gidan har muka isa cikin side É—in.
masha Allah É—an madaidaicin side É—in ya tsaru matuka.
side ne mai É—auke da 3 bedroom ko wanne da banÉ—aki a cikin sa, É—an madaidaicin parlour haÉ—e da dinning
da k
itchen da komai da komai, an tsara komai yan da yakamata duk wani abun bukata an tanadar babu abun da babu.
É—akunan cikin parlour'n muka rika shiga wan da komai akwai hatta gadon É—akunan duk da shinfiÉ—ar su, sunsha lafiyayyun bedsheets.
bayan mungama
zagaye cikin side É—in gaba É—aya, muka fita É—ayan side É—in dake gefen hagu muka shiga, shima kamar wancan side É—in yaji komai. kowa sai faÉ—in masha Allah yake, nidai kasa magana nayi sai binsu nake inata baiwa idona abinci sabo da gaba É—aya yanayin t
sarin gidan yatafi dani.
daga nan É—aya side É—in dake can gabar da gidan muka nufa, shima tsaruwan sa da tsarin sa kamar sauran part biyun nan,
koda muka fito daga cikin part É—in baki na washe nadubi Bappa dake ta faÉ—in
"Kai komai yayi masha Allah ko
mai fa yayi yadda yakamata". baki nakuma washewa ina faÉ—in "Kai wlh Bappa gidan nan Allah yayi kyau kaga fa nan irin wancan can ma irin wancan kai tsarin gidan yayi kyau komai iri É—aya, sai dai kawai kalolin kayan cikin sune daban-daban".
dariya Bappa y
ayi kana yace "Da gaske gidan yayi kyau ko?."
"Wlh kuwa Bappa." nafaÉ—a da sauri ina cigaba da washe baki, shima dariyar ya kuma yana girgiza kai kana muka rufawa mutanen baya in da suka nufi wannan kayatacce rantsatstsen babban side É—in nan dake a tsaki
yar gidan wan da yazamana da sauran side É—in sun sashi a tsakiya.
a hankali muka isa bakin kofar da sauri É—aya daga cikin mutanen ya isa bakin kofar side É—in wan da yake na glass ya É—aura hannunsa gefe kan wasu madannai ya daddanna sai ga glass É—in y
afara bada sauti É—an baya yaja kana ya dubeni yace
"Bismillah Madam É—an zo ki tsaya a nan."
ya nuna min kan step É—in da yasauka akai wan da saika haura kansu kafin ka isa bakin kofar,step ne guda uku, nuna kai na nayi alamar ni?. yace "Eh." a hankali
na matso na haura kan step É—in, daga in da yake yamika hannunsa yakuma danna wasu lambobin kana yace na É—aura hannuna kan nan yanuna min wani É—an zagaye da hoton yatsu, a sannu nakai hannuna na dai-dai ta yatsuna kan zanen yastun, nan yafara bada sauri
É—it-É—it sai kuma yakuma danna wata lambar data fito mai alamar Okay. nan take kofar tazuge gefe ai ko da sauri na É—aga hannuna.
ya juyo yana duba na kana yace
"Madam wannan kofar special ne mai amfani da zanen yatsune mutum É—aya ke amfani da shi, sai
kuma wancan". yanuna wata kofar dake gefe ya isa gurin muma mukabi bayan sa,ni dai cikin rashin fahimta nake jin sa, yace
"Shi wannan common door ne kamar yanda aka sani kowa zai iya amfani da shi."
ya murÉ—a handle É—in kofar yabuÉ—e muka shiga ciki.
sai gamu mun bayyana cikin wata katafaren parlour ya ilahi ya lilahi, har bansan san da na furta "Kai! amma wannan duk yafisu kyau!".
nayi maganar cikin hakikance gaskiyar abun da ke cikin zuciya ta wan da maganar fitowa kawai tayi,
Bappa ko karamar dari
ya yayi tare da jijjiga kai.
suma sauran dariya suka bini da shi, nan muka fara kusawa cikin katafaren parlour'n, baki da hanci gaba É—aya na buÉ—e wajen kallon katafare kayataccen parlour'n, faÉ—an tsaruwar sa da misalta tsarin parlour'n ma ba zai mis
altuba, yaji kayan alatu da more rayuwar duniya tsaruwan sa ya zarce sauran side É—in da muka shiga babu haÉ—i ko kaÉ—an.
bedroom É—in dake cikin parlour'n muka rika shiga É—aya bayan É—aya, bedroom ne zafafa har guda huÉ—u masu É—auke da tsalatsalan bath
room,
daga gefe da parlour'n kuwa katon dinning area ne sai kitchen babba a gefe.
sama muka hauwa wan da shi kanshi step É—in haurawan sama abun kallo ne domin kuwa shima