Showing 45001 words to 48000 words out of 135595 words
kannan nata sai ya iya motsa mata, muje zamu same su a gida ma y
an zu,
yaron arziki mai son taimakon al'umma."
da sauri na ce
"Waya ce masa bukatar taimako muke." nayi maganar ina waigin hanyar da suka fita tare da murguÉ—a baki kamar yana gani na.
murmushi Bappa yayi kana ya ce
"Babu wan da ya ce masa ana bukatar
taimako halinsa ne hakan."
juyawa nayi na shige cikin mota ba tare da na kuma cewa komai.
Koda muka isa gida ganin babu motar sa yasa nayi tunanin ko har ya ajiye ta ya wuce ne, da sauri nashiga ciki.
Naseem da ke tare da su Zulai ya rungume ni yana
yi min oyoyo.
su Talatu sunayi min sannu da dawowa ya mai jiki, ban iya basu amsa ba sai tambayar su nayi "Ina Nasmah?."
"Hajiya ba tana asibiti ba."
cewar Zulai. kaina girgiza tare da faÉ—in
"An dawo da ita gida." Talatu tace "A'a Hajiya ba'a dawo da
ita ba."
da sauri na juya nafita waje a sakar gida na tadda su Bappa suna kokarin wucewa part É—in su na ce
"Bappa bai fa dawo da ita ba."
murmushi yayi tare da faÉ—in
"Zai dawo da ita je ki huta."
juyawa kawai nayi badun naso ba sai dun bana so nayi
masa musu.
Nakai tsawon awa guda zaune cikin parlour zaman jiran dawowar ta,
ganin guri ya fara rufawa magriba ta kusa sai na mike na haura sama, sai da nayi wanka na gabatar da sallar magriba kafin na sauko.
nasa Zulai ta kawo min te
a sai a lokacin na sa wani abu a ciki na.
zuwa yanzu kam ina ji bazan iya cigaba da hakuri da sa sammanin dawo da ita ba, yunkurin mike wa nayi dan zuwa gurin Bappa, ya faÉ—a min gidan sa naje na É—auko Æ´ata.
da sauri na waigo kofa jin an turo kofar
parlour'n........!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:55 - Ummi Tandama😇: Tun da yatafi masallaci bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha, dan tun san da aka idar da sallar zai koma ciki, yayi ba'i dan haka yasa akayi musu masauki a parlour'n ba'i,
basu kuma bar gidan ba sai daf magriba, dan haka masallaci ya zarce sai yanzu bayan sallar isha ya shigo.
ko da yashigo parlour'n babu kowa, sai sanyi me fidda daddaÉ—an kamshi ke tashi cikin parlour'n.
direct bedroom É—in sa ya wuce, hular kansa ya ci
re ya É—aura saman bedside, kana yatafi a hankali zuwa bakin gado ya zauna, a hankali yakai
bayan sa ga katifa ya kwanta rigingine, yayi pillow da hannayen sa kafar sa na kasa yana É—an lilo da shi.
shiru yayi yayin da ya kurawa pop'n É—akin ido, kamar ma
i karantar wani abu a jiki.
a hankali ta turo kofar ta shigo da sallama, ido ta kura masa na Æ´an dakikai kana a sannu ta taka zuwa bakin gadon,
sai ta faÉ—a jikin sa gaba É—aya ta sake nauyin ta a kansa,
ido ya waro tare da faÉ—in
"Wash zata karya ni,
Kawa kin kara nauyi fa."
cikin muryar dariya ta ce
"Allah Aboki babu wani nauyin dana ƙara in da nake da haka nake yanzu ma."
"Tap waya faÉ—a miki ke baki ganki kwana biyu sai daÉ—a zama duma-duma kike ba, niko sai tatse ni kike."
kwanciyar ta tadaÉ
—a gyara wa a kansa cike da shauki tace
"Kai Aboki kai ma fa baka ganka bane kayi kiba kwana biyun nan."
dariya yayi yana dai-dai ta fuskar su a hankali ya manna mata kiss kan laɓɓanta.
yan da suke yiwa junan su idan ka gani zaka fagimci santsar kauna
soyayya shakuwa yarda a saka nin su.
cike da shauki ya mirgino ta yadawo da ita kasa shi ya haye kanta,
nauyin sa shima ya sake mata, yana faÉ—in
"A hakan kike cewa nayi kiba jini fa babu ko nauyi kamar pepa kullum kina tsotse ni, kullum sai na tsame w
ani abu daga jikina na zuba shi jikin ki, taya bazaki daÉ—a kara zama wata duma-duma ba."
Æ´ar karamar kara ta sake tana faÉ—in
"Allah Aboki kayi nauyi wash Aboki na tuba É—aga ni."
Æ´ar dariya yayi tare da shafa sumar kanta yana nan a kanta.
Æ´an was
an ni suka cigaba da yi sakanin su me cike da zallar shauki da kauna,
zallar soyayya da É—in bin kauna kake hangowa tsagwaran ta a tattare da su.
Cikin yanayin da suke ta dube shi tana faÉ—in
"Aboki ka rama É—aga ni na tashi, idan ka kara yafi haka ni
ma sai na rama."
tayi maganar tana ture shi.
Æ´ar dariya yayi mata tare da mirginawa ya koma gefe yakwanta rigingine tare da yin pillow da hannayen sa biyu, ta mirgina tayi pillow da damtsen hannun sa, sai kuma ta É—ago tasaka hannun ta a kumatun ta, yaz
amana da guiwar hannun nata najikin katafi, in da da kyau take iya kallon fuskar sa, duban sa tayi da kyau naÆ´an sakanni kana a hankali taso ma magana
"Meke da mun ka aboki?." tayi maganar idanunta cikin nashi. idanun sa ya lumshe tare da buÉ—e wa yaÉ—a
n ja numfashi kana yace.
"Tambayar É—azu kuma har lau, to me kika gani yanzu bacci nake ji."
murmushi tayi kana ta shafa gefen fuskar sa sannan ta ce
"Bacci kuma him Aboki kenan,
adalilin yin baccin ka na rana zaka kuma yin wani baccin ne da misalin k
arfe 12 na dare, yanzu karfe 8:30 saura akwa uku da rabi lokacin baccin ka yayi, sam karya baya yi maka kyau sabo da rashin iya shi da bakayi ba shi yasa ko kayi ake saurin gane ka."
kokarin kawar da maganar yayi ta hanyar janyo ta jikin sa, kana ya shig
a wasa da wasu sassan jikin ta,
a hankali ya furta
"Kawa ke baki ga in da idona sukayi ba bacci ne a cikin su, da alama dai baccin da É—azu kika sani bai ishe ni ba."
ta ce "Him wai ni yau ake ɓoyin wani abun, Aboki yaushe ka fara ɓoye min damuwa
r ka, yaushe ka fara sanya hijabi sakanin sirri na da naka, duk faɗin da kake ni da kai abu guda ne ashe ba haka bane??, shin da ma ashe akwai wata ranar da zaka ɓoye min damuwar ka, ni ce fa wacce muke tauna matsalolin mu mu magance sa batare da wani ya
sani ba, ashe dama faɗin mu tsirrin junan mu ne da kake abun ba haka yake ba, ban taɓa tunanin zuwan wannan ranar ba."
É—an sakai ta maganar nata tayi tare da mike wa zaune ta tankwashe kafafun ta takuma duban sa da kyau, nan take sai ga hawaye yacika
idon ta, hannun sa ta ruko ta kankame shi cikin nata, ta ce
"Tabbas akwai abun da yake damun ka
da ma ai ni na sani akwai ranar da zatazo irin haka."
hannun sa ta daÉ—a kankamewa cikin nata, taci gaba da faÉ—in
"Kayi hakuri amma ka sani nafika jin damu
wa fiye da kai, ni na riga da nasa ni, dama kana hana ni damuwar ne kai kana yi,
idan da a ce mutum shi yake ba kan sa abu da karfin dukiya WALLAHI dana sadaukar da dukiya, WALLAHI idan dana san in da zanje na sami maganin da zansha yazamo silar haihuwa
dana tafi ko da bangon duniya ce,domin samin farin cikin ka, nagaza baka É—a kayi hakuri kayi hakuri kayi hakuri!!."
takuma nanata kalmar hakuri yayin da tuni hawayen idon ta suka fara zuba.
Da sauri yamike zaune tare da janyo ta jikin sa yana faÉ—in
"Ke meya kawo wannan maganar?, banace kada nasake jin wannan maganar a bakin ki ba?,meye na yin ta meya kawo ta yanzu kuma?,
Okay so kike ki kawar da farin cikin da ke nan ko?,
hauhuwa dama ashe mutum shi yake bawa kansa haihuwa?, okay kin mance cewa All
ah shi yake bai wa bayin sa haihuwa?, so kike kiyi tsaɓo to kiyi gaggawan tuba, maza yanzu."
yayi maganar yana share mata hawaye.
kana yaci gaba da faÉ—in "Dai na kunan kada na sake jin wannan maganar a bakin ki, kada na sake ji idan kuma so kike ki ko
yi yan da zaki rika ɓata min rai to ki kara yin ta,
na ce miki ina son haihuwa Allah bai nufa na samu bane, idan yaso sai ya bamu bare ma muna da su Æ´aÆ´an da muke yi musu hidima kama daga gidan marayu makarantu da dai sauran su suÉ—in ba namu bane,
suma Æ´aÆ´an mu ne, mai da hawayen kinji Fara Æ´ar duma-duma ta." "
kai ta shiga girgiza wa tana faÉ—in
"Nayi shiru bazan sake ba ka yafe min."
kai ya jinjina kana ya koma yajin gina bayan sa da jikin gado, ita ko zaman ta tagyara suna fuskantar juna
ya ce
"Ko ke fa fara Æ´ar duma-duma ta to na yafe."
dariya tayi kana taɗan langwaɓar da kanta cikin muryar shagwaɓa a hankali ta ce
"Na yar da ba abun da na faÉ—a yanzu ke damin ka ba amma na tabbata akwai wani abun, zuciya ta baza ta sami sukuni b
a har idan ban za mo silar kawar da damuwar ka ba, amma babu damuwa tun da ka nuna baka so na sani, yau rana ta farko daka taɓa ɓoye min damuwar ka, ban taɓa tunanin akwai ranar da zata zo ka ɓoye min damuwar ka ba, damuwar ka tawa ce kamar yan da yake
tawa takace,
ai ban san cewa haka yanzu ka É—auke ni ba shike nan babu damuwa."
tayi maganar tana kokarin sauka a gadon.
dakatar da ita yayi ta hanyar rike hannun ta kana yaÉ—an ja numfashi sannan ya ce
"Abar shi kawai faÉ—ar shi ma bashi da wani amf
ani."
ido ta kura masa sannan tace
"Haka kace abar shi yaci gaba da damun ka da cin ka a rai ko?, kada ka mance nafi kowa sanin ko kai waye tun sati biyu da suka wuce na fara fahimtar akwai wani abun da ke damun ka, ban daÉ—a gaskata hakan ba sai yau da
ka shigo gida, rungumar ka da nayi jikin ka da zuciyar ka suka tabbatar min da haka, dakuma tabbacin damuwar naka yakaru a yau,
tanbayar ka danayi É—azu da zaka tafi masallaci yakuma bani amsar abun da nake zargi, babu halin da zaka shiga koda dai-dai na
second 1 ne ban gane shiba."
Ganin yan da ta hakikan ce tanuna damuwar ta matuka a kanshi takuma nuna ɓacin ranta nakin faɗa mata da yayi wan da ada ba haka asakanin su.
sai ya janyo ta jikin sa ya rungume,
tabbas ita wata sashi ce a rayuwar sa da
bazai iya ɓoye mata komai na rayuwar sa ba, kamar yan da tun fari suka gina rayuwar su ta hanyar faɗawa junan su sirrukan su,
bata ɓoye masa komai kamar yan da shima baya ɓoye mata, ko a yanzu dayake ta kokarin barin abun cikin zuciyarsa shi kaɗai ya
na ta shan fama da É—awai niya da zuciyar sa dan bai saba ba sam.
numfashi ya ja kana a hankali yasoma magana
"Akwai wani abun da ke damu na amma sam banso na fitar ba naso nayi jarumtar iya barin sa a raina dan faÉ—ar sa sam bashi da amfani."
wani numf
ashi yakuma saukewa kana a hankali ya cigaba da magana
"Kiyi hakuri da abun da naketa ɓoye shi a zuciya ta ni kaɗai, wan da nagaza iya dan neshi sabo da ban saba da irin saba, yabani wuya sosai a zuciya ta, kiyi hakuri yanzu da zakiji shi a kan laɓɓan
a, tabbas da gaske bazan iya ɓoye miki sirri na ba kokarin yin haka dana yi kuwa dan cigaba da ganin kwanciyar hankalin ki yabani wuya sosai a zuciya,
nayi ta kokarin danni shi cikin zuciya ta hakan ya garara gashi bugun farko kin gano da akwai abun da y
ake dami na."
hannun ta ya damke cikin nasa kana yaja numfashi ya sauke sannan yaci gaba da faÉ—in
"Wata ranar da Company na ya tura kayan bukata izuwa wata makarantar yara, kamar da yan da kika sani a ka saba,
lokacin da motar Company ya isa aka shai d
a min da isar sa, sai na tashi da kai na naje makarantar domin ganewa ido na kalar farin cikin da yara zasuyi kan kayan da aka kai musu wan da yawan ci kayakin wasa ne irin na yara,sai sabbin kujeru, dan nima naji daÉ—i, duk da kuwa makarantar bana Gwamnat
i bane, makaranta ne ma irin na Æ´aÆ´an masu kuÉ—i,
lokacin da na shiga makarantar nayi arba da wasu yara guda biyu, sunata wasanni da kayakin wasan da aka kai musu, duk da yara dayawa agurin amma nafi ganin farin cikin waÉ—an nan yara guda biyun sosai c
ikin matukar farin ciki da kuma jin daÉ—i suke ta wasa da kayan da motar Company na ta sauke,
naji daÉ—i matuka ganin farin ciki a fuska da zukatan É—aliban, amma sai dai hankali na yafi karkata kan farin cikin da ke baiyana ga waÉ—an nan yara guda biyu,
kasan cewar lokacin tashi yayi nan É—alibai suka fara watsewa, wasu diraibobin su suka zo suka kwashe su wasu kuma motar makaranta ta kaisu, haka yara sukayi ta watsewa.
ina nan a cikin makarantar muna magana da shugaban makarantar bayan mun gama maganar
na fito, lokacin tuni students sun watse, a bakin get na tadda waÉ—an nan yara guda biyun, da lokacin da na shigo makarantar su na fara ganin su da É—in bin farin ciki kan fuskokinsu, tare da mai gadin makarantar suna zaune a bakin get.
ko da na iso guri
n su kan su na shafa tare da duban mai ganin na ce,
yaya su ba'a zo É—aukar su bane kokuma motar makaranta zasu bi kuma naga É—alibai duk sun watse.
mai gadin ya ce
Ba motar makaranta zasubi ba direban su ne zai zo ya É—auke su ko mai akayi dai yanzu ya
na hanya, yau an É—an makara ne wajen zuwa É—au kar su.
kan su na daÉ—a shafawa sai nayi waje cike da jin sha'awar yaran, ina fita kuwa sai suka biyo ni a baya, sai na tsaya naruko hannun su ina tanbayar su yaya sunan su,
kai yaya sunan ka nafara tambaya
r na mijin sai yace min sunan sa Naseem, ita kuma macen tace min sunan ta Nasmah,
nafahimci wayo sosai tattare da yaran duk da kuwa ƙarancin shekarun su, dan bazasu wuce shekaru uku zuwa uku da rabi ba,
bayan nayi musu tambayar sai suma suka mai da min
tambayar.
to kai ma yaya sunan ka, wayon yaran ya burge ni sosai jin yan da suma suka iya mai da min tambayar,
Sai nace musu sunana Daddy, kin san wani irin yanayi nagani a tare da su lokacin da nace musu suna na Daddy?."
Dan sakai ta maganar yayi tar
e da daÉ—a matse hannun ta cikin nasa kana yaci gaba da faÉ—in
"Ihun murna suka sake haÉ—e da tsalle suka rungume ni suna faÉ—in laa kai Daddy ne irin Daddy'n su Aeeman,É—in class É—in mu, to kai Daddy'n su waye ne?, maganar yaran yasa Ni shiga wani yanay
i, sai dai farin cikin danake hango wa tare da su da kuma fahimtar da nayi kalmar sunan Daddy dana furta musu yazo mu su a sabon abu ko makamancin haka,
Sai na ce musu Daddy'n ku.
kin san me yaran sukayi?."
nan ma hannun ta yakuma damke wa cikin nashi k
ana yaci gaba da faÉ—in.
"Da É—a rungume ni sukayi suna ta tsallen murna da nanata kalmar sunan Daddy,
wani irin abu naji acikin jiki na da zuciya ta, a duk san da suka furta kalmar Daddy a gare ni, sai naji wani irin farin ciki da jin daÉ—i mara misalt
uwa a gare ni, cikin kan kanin lokaci naji yaran sun shige cikin zuciya ta,
har nake ji tamkar Æ´aÆ´an da na haifa ne a gaba na suke kira na da wannan suna,
abun da na daÉ—a lura da yaran a lokacin sosai na ke hango jin daÉ—i irin na samun sabon abu a ta
re da mutum, sai suka ce min
Daddy kai ma zaka bamu chocolate irin wan da Daddy'n Aeeman yake bashi. na ce musu kwarai kuwa, to lokacin akwai ragowar Chocolate a mota wan da nake baiwa yara a gidan marayu idan naje,
sai na ruko hannun su nace muje na ba
su chocolate yana mota ma kuwa.
lokacin da muka nufi gun mota, a dai-dai lokacin wata yarin ya ta iso gurin a cikin mota."
Sai kuma yayi shiru batare da yaci gaba da Maganar ba.
ita ko zaman ta tagyara sosai wannan karon ita ta mai da tafin hannun sa
cikin nata tasar kafe yatsun su guri guda, kana ta sanya idanun ta cikin nashi, cikin daÉ—a karfafa shi da bashi kwarin guiwar gama fidda damuwar da take ganin tamkar ta yaye masa, tagyaÉ—a masa kai cike da bashi kwarin guiwar yaci gaba da da fidda damuwa
r da take yi masa kallon cuta ce barin sa a ransa.
A hankali kuwa yaci gaba da maganar yayin da ya daÉ—a sarkafe hannun nasu sosai,
ya ce "Kawa kin san me naji?, wani abun mamaki naji wan da ban san mene ne shi ba,
bayan da yarin yar ta É—auke su ta
tafi da su,
sai na tsinci kai na cikin wani irin yanayi mai ka ma da da muwa,
mai kama da son in sake ganin su, amma nafi alakanta son in sake ganin yaran ne,
bayan kwana biyu sai naji tunanin nawa yanata rikiÉ—a, madadin tunanin yaran su biyu