Showing 21001 words to 24000 words out of 135595 words

Chapter 8 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

na kwanta na tuna da akwai maganar da nake so muyi da Bappa kan wani Company na murza karfe da ake gina shi a Lag

os,

mikewa nayi na fita dan ina so muje ziyarar gani da ido acikin satin nan.

da gudu Nasmah ta shigo tana faÉ—in

"Mommy kin ga Naseem ko jai camin jiji".

Naseem shima dagudun yashigo yana binta da abun yana dariya, Fatu na biye da su tana dariya da fa

É—in "Naseem kabari kar ka sa mata".

da sauri nakarasa sauka kan step na rungumo Nasmah dake falfala gudu kamar zata kife kasa nace "K.......!�

Mommyn Twins ce

8/19/22, 10:54 - Ummi Tandama😇: "Kai Naseem me zaka sa mata kai ka bari za

ta faÉ—i fa kabari."

nayi maganar ina É—ago Nasmah cak na rungume ta a jikina, shiko dariyar yake yana matsowa in da muke ya É—aga hannun sa sama tare da yin É—agelgel da kafa, yana washe baki,

na ce "Idan ka zo nan sai na mare ka, zo kagani zo ka samata

kagani,

dariya sosai yarika yana faÉ—in

"Mommy dan tamata ne dan ta mata wannan."

"To ka samata kagani sai na maka bulala."

kiran Talatu mai kula dasu nashiga yi ina faÉ—in

"Talatu zo ki kaishi wa É—awisu ta cakwaÉ—e shi tun da dai shima sa mata jiji

zaiyi."

Talatu ta iso da sauri tana faÉ—in

"Ayi hakuri Hajiya kar a kaishi wa É—awisu zata cake shi, zo nan Naseem kada kasa mata ko, so kake a kaika wa É—awisu ta cake ka,zo ko É—an lele na mene ne zaka sawa Nasmah É—in?."

É—an karamin tafin hannunsa

da ya dunkule ya buÉ—e kaÉ—an ya nuna mata kana ya kuma dun kulewa yana cigaba da dariya, "Lalala shine zaka sa mata?."

cewar Talatu tayi maganar haÉ—e da dariya, kai ya gyaÉ—a yana washe baki, duban Fatu nayi ina faÉ—in

"Wato Fatu keda Naseem kuke sawa

Nasmah ta abin tsoro ko? to bazata sake wasa da ku ba."

dariya Fatu tayi tare da faÉ—in

"Allah Adda HAMDAH kin ga bansan in da yasamo ba kawai ganin sa nayi ya shigo da shi a hannunsa,malam buÉ—e takarda ne fa."

"Au malam buÉ—e takarda ne ya É—auko sh

ine yake so ya sa mata to bari yagani sai an kaishi wa ɗawisu shima, shine baki karɓa ba ko Fatu kika tayashi tsoratar da ita."

"Allah Adda HAMDAH binshi nake na karɓa shine yagudu."

Talatu ta É—auke shi tabuÉ—e hannunsa taciro abun tana faÉ—in

"Kaw

o shi nan a yasar da shi kada ka saka mata kaga tana jin tsoro, kaima kada ka sake É—auka a hannun ka."

tana rike da hannunsa tafita waje ta yasar da shi kana suka dawo ciki.

karaso wa cikin parlour nayi na zauna kan kujera tare da zaunar da Nasmah kan c

inya ta, na dubi Fatu nace

"Fatu Bappa na ciki ne?."

tace "A'a yafita". sai kuma ta turo baki gaba tare da faÉ—in

"Adda HAMDAH nifa wannan sunan Fatun nace ki dai na faÉ—in shi, Fatun nan fa a can Ruga ne fa ake kiran Fatun nan tun da yanzu mutum yazo b

irni har yanzu ayi ta ce mishi wani Fatu, gaskiya Adda HAMDAH ni wlh na canza suna Fatu ai duk su Inna wuro ne suka wani lankwasa min suna yaya Mahmoud dake shi a birni yake ai Fatima yake cemin,haka jiya wata Æ´ar ajin mu tana ta min dariya wai ni Fatu,

aradun Allah na canza suna ko a ajin mu ma na faÉ—a na canza suna".

dariya muka tuntsire da shi, Talatu tace

"To Fatu man yan gari me kike so ace miki kenan?".

"Ai sunana da yawa masu daÉ—i ma, Nana, Fatima, FaÉ—imatu, Faty Zarah duka gasunan masu daÉ

—i sai a rika cewa mutum wani Fatu kamar rugo".

nace "To lallai kam kamar kin sani da ma kam wannan sunan bai dace da ke ba yanzu dai kawai Faty za'a rika ce miki."

tace "Yauwaaa Adda HAMDAH Faty wlh yama fi amma kuna ta cemin wani Fatu kamar rogo".

"Hh

hhh Faty kenan Allah bakida dama".

tace "Yauwa Adda HAMDAH gashi kin iya faÉ—in sunan dai-dai mai daÉ—i".

kai kawai na girgiza ina dariyar ta.

tace "Zo muje muyi wasan mu o Nasmah."

nace "O'o kuje bazata biku ba kuje kusata kuka bazata biku ba kam kuta

fi ku."

"Allah bazan barshi yasa mata ba". fuskata na kawo dai-dai fuskar Nasmah nace

"Zaki bisu?". kai ta gyaÉ—a "To muje daga gun na duba ko Bappa ya dawo".

nafaÉ—a ina mikewa na direta kasa tare da ruko hannunta muka nufi side É—in su Inna wuro.

a

parlour muka tadda Inna wuro Bappa bai dawo ba sai na zauna muna ɗan taɓa hira da ita.

muna nan zaune har Bappa ya shigo yazauna muka cigaba da hirar da shi, acikin hirar nake yi masa maganar yace kwarai kuwa ya dace kam aje domin a ganewa ido, in yaso

satin sama sai a je, duk da akwai idanu da yawa akan lamarin. nace "Toh Allah yakai mu."

muna zaune sai ganin Naseem mukayi ya kin kimo school bag É—in Faty, a tsakiyar parlour'n ya zauna ya tuttuÉ—e littatafan cikin jakar kasa ya É—auki littafi guda ya b

uɗe yana ta gwalaɓe wai shi yana karatu.

dariya duka muka saka, Faty ko da gudu ta mike taje ta tattari litattafan ta tana ta faÉ—in

"Kai kasan meye a ciki ka iya karatu ne".

Inna woro tace "To ai karatun yake baki gani ba".

cikin muryar dariya nace

"Um karatu yake ko gwalaɓe har da wani mike kafa kamar mai karatun gaskiya."

"Ah to gaskiya za'a saku a makaran ta tun da har ka iya É—auko littafi kazauna ka buÉ—e kana karatu".

cewar Bappa yana yi masa dariya.

"Wlh Bappa nima dama ina so a turasu ma

karanta amma a sona sai sun cika shekara uku da rabi, amma gashi nan bakin su ya buÉ—e kawai sutafi yanzu."

Bappa ya jinjina kai kana yace

"Kwarai kuwa ya kama ta kam tun yanzu, tun da ga bakin su nata kan buÉ—e wa a kai su makaranta yakarasa buÉ—ewar a

can"....

A cikin satin akayi musu komai da komai nashiga makaranta, sai dai wata makarantar daban badaga cikin nawa ba, dan *HAM'NAS* International School Of Science Of Technology. suna da nisa saka nin mu, duk da dai shima makarantar da aka sasun yan

a da É—an nisa sai dai baikai su nisa ba,

Islamiyar da a kasasu kuma anan unguwar tamu yake.

ranar da zasu fara zuwa kuwa zo kaga murna wajen su, da misalin karfe 7 na safiya Talatu taga ma shirya su tsaf, Zulai kuma ta shirya musu lafiyayyen breakfast É

—in su.

ina rike da hannun su muka fito in da Talatu ke biye da mu rike da school bag É—in su da baske, parking lot muka nufa, tun kan mukaraso Yakubu direba dake goge mota yayi hanzarin buÉ—e marfin motar, cike da ladabi yaÉ—an duka yana faÉ—in

"Barka d

a safiya Hajiya."

"Yauwa barka." nafaÉ—a cikin É—an jin nauyin yan da suke yimin idan zasu gaida ni, duk kanin ma'aikatan gidan sun girme min nesa ba kusa ba wasu ma sun haife ni sun juya,nakan ji nauyi a duk san da sukayi min irin wannan gaisuwar.

Nasma

h naÉ—aga nasaka ta cikin motar, Naseem kam cemin yayi shi da kan sa zai shi, Talatu tayi dariya tana saka musu school bag É—in cikin mota tace

"Naseem iyayen rigima kai bazaka bari a saka ka ba da kan ka zaka shi ka girma ashe".

kai ya gyaÉ—a yana gyara

zama tare da faÉ—in

"Eh nagima da kaina naciga."

tace "To babban zance ke kuma Nasmah yaushe zaki girma?". Nasmah ta cuno É—an karamin bakin ta gaba tace "Gobe dan gima ai".

murmushi nayi tare da shafa gefen suskar ta nace

"Au ke sai gobe zakiyi girma

n naki?". kai ta gyaÉ—a tana murmushi, kansu na shafa dukansu nace

"To sai an dawo ayi karatu sosai kunji".

sukace to. direba yaja mota ina É—aga musu hannu suma suna daga min

mai gadi yawangale get suka fita..

Kwana uku kullum cikin É—oki suke zuwa

makarantar ranar na huɗu kuwa ɗoki tafara kare wa, ina kwance sai ga Nasmah ta shigo da gudu ɗaure da ɗan karamin towel ɗin wankan su tahaye gado ta ɓoye a baya na tana faɗin

"Ni bajan je school in ba."

zanyi magana sai ga Naseem shima da wandon

uniform ajikin sa babu riga, sai muryar Talatu daga bakin kofa tana faÉ—in

"Kai Naseem kazo nakarasa saka maka kayan".

mikewa nayi zaune ina faÉ—in

"A'a yaya ne tsaya mana". ai kan kace me shima ya É—ale gadon

cikin cuno baki gaba Nasmah ta daÉ—a laÉ

“ewa jikina tana faÉ—in

"Ni Mommy bajan je School in ba".

ido na waro ina duban Naseem shima da yake faÉ—in

"Nima bayan jeba".

kai na langwaɓar gefe nace

"Oh yanzu wa School É—in kuke gudu ne, bazaku je ba kuma, yaushe ne kuka fara zuwan da har zaku

fara fashin sa?, kuna ji ko kuzo ku je makaranta".

kafaÉ—a suka make alamar o'o, rungumo su nayi dukan su ajikina ina murmushi kana nace

"Ina kallon da mukayi jiyan naaan na sojojin naaan, to waye meson zama irin su a cikin ku?".

da sauri Naseem ya mik

e a jikina yana washe baki tare da nuna kanshi yana faÉ—in

"Nine-nine". "Yau wa to har in kana son kazama soja to ko sai kaje makaranta, kaje makaranta kayi karatu sosai daga nan zaka zamo soja, in kuma baka so to kazauna kawai a gida ina baka so kazama s

ojan zauna abin ka kada kaje School".

kai yashiga girgizawa da sauri yace "A'a a'a Mommy ina so to danje School in nine toja".

"Yauwa to kada ka sake cewa bazakaje School ba dan soja baya fashin School, Nasmah ta kefa? baki son zama sojan ne?."

da sauri

tace "Ina to." nace "To ke bama soja zaki zama ba Dr Nasmah ce a nan, ina kina so kizamo likita kirika yiwa mutane allura."

ta gyada kanta da sauri, nace "Yauwa kinga in kikaje makaranta kikayi karatu da yawa to zaki rika yiwa mutane allura".

kuma gyaÉ—

a min kai tayi da sauri tun kan in karasa maganar, murmushi nayi ina shafa kansu.

kallon kofa nayi tare da É—aga murya nace

"Talatu kawo musu uniform É—in su saka".

daga can bakin kofar in da take tsaye ta waje ta amsa da to kana taturo kofar tare da s

allam, nakarɓi uniform ɗin nafara sakawa Naseem rigar sa wan da shi dama ta saka masa wandon shine yagudu,gyara masa zamar rigar nake ina faɗin

"Um kaga soja wannan yaro zai iya rike bindiga in ya girma ya zama soja".

baki yarika washewa yana É—aÉ—É—

aga kafaÉ—a da faÉ—in "Nine toja ai nine toja". "Ai kam ga sojan gasken gaske".

a haka nagama kimsashi

kana nasakawa Nasmah ita ma inata faÉ—in mata itace Dr zata rika yiwa mutane allura.

nariko hannun su muka fito parlour nan muka iske Zulai da kayan

break É—in su, Talatu kuma ta É—auko musu School bag É—in su, muka nufi parking space, da murna suka shige cikin motar Naseem sai faÉ—i yake

nine toja, Nasmah kuwa ta dube ni tace "Mommy ni meye?". kumatun ta naja nace "Kece Dr me yiwa mutane allura".

sa

i washe baki suke cike da murna direba yaja motar suka tafi.

Wani sati na gewayo wa muka fara shirin tafiya ziyarar gani da ido nan muka É—auki hanyar zuwa Lagos,

sai dai wannan karon bantafi da su Nasmah ba saboda School, ni da Bappa da wasu jagorori

biyu muka tafi, mun isa Lagos lafiya awani kayataccen hotel akayi mana masauki, mun isa yau washegari muka nufi Company da ake ta kan ginashi tamfatsetsen Company wan da girman sa ya kai ya kawo, an kai ni gurare da dama acikin sa an nunnuna min, masha All

ah komai yayi saura kaÉ—an a kammala.

a gajiye muka koma masaukin mu kansan cewar da kafa akayi ta yawo damu acikin Company'n.

kayan jikina na tuɓe nashiga baya na watsa ruwa kana nafito na sauya kaya na haye gado dan na ɗan huta, waya ta na ɗauka na

laluɓo lambar Talatu bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga, da sallama bayan mun gaisa nace

"Ina mutanen naki?". tace "Gamu nan muna tare da su a parlour muna kallo, ungo Naseem karɓa ga Mommy tana magana."

tasaka masa wayar a kunne,

"Mommy da mu biki kijo

jike da mu".

murmushi nayi jin muryar Naseem nace "To zan zo naje da ku, kuna karato sosai ko?".

kai ya gaÉ—a, Talatu tace "Ka amsa da baki ai bata ganin ka". yace "Eh." "To a dage sosai, bawa Nasmah wayar." ya mika mata Nasmah tace

"Mommy kina ina, dam

u biki kije da mu".

nace "Nasmah to zan dawo nazo naje da ku kinji."

"Mommy yaushe zaki jo?."

"Gobe zan dawo naje da ku kinji". to tace, haka sukayi ta zuba min surutu da gwalaɓen su ni ma ina biye misu kun kai minti 30 a haka daga bisani na kashe waya

r.

na gyara kwanciya ta dan bacci nake ji.

kwanan mu uku a Lagos muka juya Abuja.

Yau asabar ba makaranta muna tare da Æ´aÆ´ana a parlour munata sharholiyar mu cikin farin ciki da jin daÉ—e, duban daular da nake ciki a rayuwa da nake yin ta yan zu nay

i, Allah yabani duniya ya ɗaga ni ya ɗaukaka min daraja ta, a lokacin da duniyar ke kokarin suɓuce min a lokacin da rayuwa ta tazomo tamkar kwai a cikin tray, wan da yazamo baki-baki saura kiris ya suɓuce kasa ya tarwatse.

numfashi na sauke lokacin d

a tunanin Inna ta ya zomin, wasu zafafan kwalla ne suka zubo min,

Allah sarki Inna ta tabbas na yarda wani hanin ga Allah baiwa ce, ya É—auke ta a lokacin da nake tsananin bukatar ta arayuwa ta, lokacin da duniya ta juya min baya lokacin da narasa madafar

dafawa lokacin da na gwammaci mutuwa ta da rayuwa ta.

ya É—aukaka darajata abayan bata nan ya azirtani da arziki mai tarin yawa, wa zai iyayin duk wannan in banda *RABBUSSAMAWATI WAL'ARDI*.

Allah sarki Inna ta Allah yakai haske kabarin ki ya sa mutuwa y

azame miki hutu.

wasu kwallan nakuma sharewa lokacin da na kuma tunawa da wata uwar wato Mama mai awara, Allah sarki rayuwa

ta cito ni lokacin da duniya tafara wasan kwallo da ni, matar data jajirce wajen ganin an ceto rayuwa ta gun haihuwa, da awancan l

okacin bata samo kuÉ—in da za'a min cs ba wata kila da yanzu na mutu da ni da su

duka aciki, tarike ni tamkar ɗiyar da ta haifa a cikin ta. lokacin da tayi nisa wajen ceto rayuwa ta sai ta tsuɓuce min.

sai gashi yau Bappa yamaye gurbin su, yazame min ub

a kuma uwa, ya jajirce yatsaya kan lamari na yazamo silar isata matakin danake yanzu, matar sa ta zame min uwa Æ´aÆ´an sa suka zame min yan'uwa.

Rungume su Naseem nayi a jikina ina jin wani irin kuna, rumtse idanuna nayi da karfi jin kaina yana wani irin

tsara min, lokacin da tunanin abun da yayi silan rabani da ahalina yashiga yimin yawo a kwakwalwa da zuciya ta. zunbur na mike nashige bedroom É—ina, sam bana son narika tunawa da hakan duk ranar da na tuna nakan kwana cikin kunci da bakin ciki da matsana

ncin ciwon kai, dan ranar zan kwana ina kuka.

Zubewa nayi kan kado nakife fukata jikin pillow, kai na rika juyawa ina ta fafutukar son na mance da tunanin, amma ina sai daÉ—e tahomin yake, da karfi cikin karaji narika faÉ—in

"Wlh Allah Abba ban taɓa a

i kata zina ba, Ya SALEEM ba wani ɗa na mijin daya taɓa sani na mace bayan kai, duk da karancin shekaru na Inna ta ta tsoratar dani haɗe da kyamatar dani illan dake cikin zina, Ya SALEEM kai ka sanar dani mene ne aure, a lokacin da kuma nasan mene ne au

ren akayi min kagen zina aka kuma sheganta min ƴaƴa, bazan taɓa aikata zina ko da ace bani da aure bare ina da shi ɗin."

wani irin kuka ne ya tsuɓuce min, na kankame jikin pillow'n ina cigaba da kuka mai tsanini.

nakai tsawon awa guda ina kukan kana

da kyar na sai-saita zuciya ta na baiwa kai na da kai na hakuri, kana nagyara kwanciya ta wan da ba bacci nayi ba, sai tulin tunani daban-daban.

har yamma ina nan kwance, ganin tunani yana kokarin kassara ni sai na mike nanufi side É—in su Bappa,

a can

na iske su Naseem, har dare muna can sai wajen bayan sallar isha kafin muka koma side din mu.

zuwa lokacin kam naji saukin damuwa ta kwarai dan su Inna wuro sun yaye min shi da hirarsu mai É—ebe kewa.

Washegari Lahadi ma ban yarda na zauna a side É—i n

a ba da sassafe na wuce part É—in su Inna wuro acan mukayi breakfast, a nan nawuni muna hirar mu cikin jin daÉ—i.

Yau Monday da misalin karfe 7 narako su Nasmah har sai da naga tashin su kafin na koma ciki, ina gama abun da zanyi nawuce side É—in su Bap

pa, ina shiga bayan mun gaisa Bappa yake cemin

"Dama yanzu nake da shirin niman ki, kan ai kin masallacin nan ne harfa an rigada an gama shi, wan da aka bashi kwangilar jiya yake sanar min da cewa an gama."

da murmushi sosai kan fuskata nace

"Kai masha

Allah kai amma dai ai kin yamin sauri wlh."

Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in

"In dai da kuÉ—i a kasa komai cikin sauki yake zuwa, in dai da kuÉ—i ai komai mai sauki ne Allah dai yaba da ikon cin jarabawar da yayi dan shi kanshi arziki babban jarabawa n

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login