Showing 78001 words to 81000 words out of 135595 words
dai ace kin É—au ki hakkin su ki hukuntasu kan laifin da basa
da masaniya a kan sa."
baki na turo gaba nace
"Sai kuma ka gansu haka da lafiyar su, ban yaye su ba sai da suka kai na yaye."
murmushi yayi yayin da hannunsa yake kan ababen kirji na yana ta faman matse su a hankali yaÉ—an mike ya rankwafo kaina ya kawo
bakin sa saitin nono na yazuro harshen sa, ya lashe kan Brest É—in,
wani irin shock ne ya shige ni har sai da na É—an mike tare da gantsare wa, shiko É—an É—ago kansa yayi ya kalle ni tare da É—aga min gira sannan yace
"Naga basu yi kama da waÉ—an da ak
a sha bane."
baki na kuma turo, tare da matse idanuna jin yan da sakon sa ya shige ni, a kasan raina nace
"Sai aka ce kuma komai sai ka sani ne."
"Idan a kan ki ne ba."
ido na É—an waro da mamakin fitar maganar tawa.
saukar bakin sa kan ababen kirji n
a
naji, yarika tsaotsar su da shafani tun ina É—an tutture shi har na dawo bana ko iya É—aga hannuna sai da ya kashe min jiki gaba É—aya kafin ya É—an É—ago ya zame towel É—in gaba É—aya.
ya haye kai na jikin sa na ɓari yashige ni,
ban iya yun kurin d
akatar da shi ba dan gaba É—aya ya saukar min da muguwar kasala,
yayi ta sarrafa ni yana sakin sambatu, yajima sosai yana abu guda ganin kamar bashi da niyyar kyaleni, sai na fashe masa da kuka ina faÉ—in
"Ni na gaji."
tamkar kukan nawa kai mi yake da
É—a kara masa,
dun dole yayi release, yasulale kai na yana mai da numfashi..
ya zare jikin sa ya kwanta gefe na,
duk kanin mu numfashi muke sauke wa, a sannu ya sauka a gadon ya ruko hannuna ya mikar da ni muka shige bathroom a tare mukayi wanka muka f
ito...
yana saka kaya yafita yace zai je yayi wa su Naseem addu'a dan sai da yasa sukayi bacci kafin ya zo nan, bai kuma yi musu addu'a ba.
ni ko ina saka kaya gado na haye dan nagaji ga kuma baccin da nake ji.
zuwa can yashigo ya haye gadon ya kwanta a
gefe na. fuska ta ya leko
yace
"Kyakkyawa ta akwai kari ne?."
yayi maganar cikin zolaya,
baki na turo ina kokarin juya fuska ta taÉ—aya gefen.
yayi saurin ta ro ni ya matse ni a jikin sa, yayi ta zolaya ta da jana da wasa, har sai da ya sani fashewa
da dariya.
sai ya tsaya ya kuramin ido yana kallon yan da nake darawa,
yaja kumatu na yace
"Gaskiya ina da sa'a a rayuwa ta."
sai ya daÉ—a rungume ni, ya manna bakin sa kan nawa yayi kissing É—in sa kana ya É—ago, yana yi min kallon cikin ido, kasa jur
ewa kallon nasa nayi sai na lumshe idanuna....
Washegari da safe haka yaki kyale ni sai da ya sami abin da yake so,
wunin ranar kuwa bai leka ko nan da can ba muna tare, sai yammma yaje gidan sa, bai jima ba kuwa ya dawo.
akwanaki biyun da Ahmad y
ayi a gidan nan ya nuna min tsantsar so da kaunar da yake yi min.
bayan kwanaki biyun kuwa daya koma yakuma dawo wa,
a lokacin yasa zuciya ta yafara yin sabo da shi.
ko da ya gama yin kwanakin zai tafi har nake jin bada É—i....
Bayan wani lokaci tu
ni zuwa wannan lokaci sai da Ahmad ya tabbatar daya dasa wani abu mai muhimmanci a zuciya ta,
sai dai sam naki yarda kan cewa so ne, nafi yar da kan sabo ne kawai.
a yanzu nakan zauna muyi hira da shi sosai,
yanzu har na koya idan ya zolaye ni nima nayi
masa,
akuma duk san da ya bukace ni nakan amin ce batare da tirjiya ba....
Yau yakama Ahmad zai dawo gida na,
tun da yamma na shiga kitchen domin na shirya masa abinci da kaina, dan aduk san da nayi masa abinci da kaina yarka santi da nuna yabawa sa
i ya daÉ—e yana yaba min.
sai daf magriba na gama nashiga wanka, ina fita na na saka kaya na haye kan sallaya,
kasan cewar nayi al'wala.
bayan na idar da sallah mikewa nayi na je na ɗau waya ta, na laluɓo number sa, ganin har magriba tayi bai iso ba,
iwar haka ai ya daÉ—e da zuwa gidan.
har na dannawa number sa kira sai na koma na she, na aje wayar na cigaba da wani da muwa.
har aka kira sallar isha nagabatar, har wajen misalin karfe koma saura kwata bai iso ba.
sai naji duk babu daÉ—i nakuma ji ina
son sanin dalilin daya tsayar da shi har wannan lokacin.
a sannu na turawa number sa kira,
wayar tayi ta ring ba'a É—aga ba har ta yanke.
a hankali nakuma mai da kiran, shima har na fidda ran daga kiran sai na ga an É—aga, shiru na yi banyi magana ba,
daga can cikin wayar najiyo muryar Rasheedat tana yin sallama.
na amsa sallamar tare da faÉ—in
"Ina yini Aunty Rasheedat ya gida."
murya É—auke da murmushi tace
"Lafiya lau HAMDAH ya yarana suna lafiya, kifaÉ—a musu ranar weekend zan zo na É—auke su."
nace To.
dariya ta yi tace
"Kingan shi shiru bai iso ba ko, kinyi tunanin na rike miki shi ne? to babu ruwa na, in yazo ki titsiye shi ya faÉ—a miki in da yaje yakai dare dan nima yanzu na ganshi, ya dai shiga wanka yanzu, zaki ganshi yanzu insha Allah
dan nasan wannan ɓarin jikin da yake alla-alla yake ya isa gare ki."
murmushi nayi cike da jin kunya nace
"A'a wlh nafi zaton yana wajen ne ma."
cike da zolaya tace "A'a faÉ—i gaskiya dai."
da sauri nace da ita "Sai da safe Aunty Rasheedat."
dariya
tayi tace "To Allah ya kai mu..........!
25
Muna zaune a parlour muna kallo, har su Nasmah sukayi bacci na kwashe su na kaisu É—aki,
sannan na dawo parlour'n na zauna.
tun daga step's najiyo takun sa haÉ—e da kamshin sa, da s
auri na waigo, karaf muka haÉ—a ido muka sakar wa junan mu murmushi.
yakaraso ya zauna kusa da ni tare da sumbatar kumatu na yace
"Bakiyi bacci ba."
kai na gyaÉ—a sai kuma na turo baki nace
"Ina ka je kayi dare?, Aunty Rasheedat tace min ita ma yanzu t
a ganka."
yace "Zan ce naje gurin wata budurwa ta shine ta rike ni nayi dare."
kaina na kawar tare da É—aga hanci sama.
yace "In faÉ—a miki tarika miyin daÉ—aÉ—an kalamai shiya sa nayi dare a gurin ta."
"Ya isa."
na faÉ—a ina mike wa tsaye na sa kafa
zan bar gurin, da sauri ya ruko ni ya janyo ni nafaÉ—o jikin sa, sai ya rungume ni.
dariya sosai yayi, fizge jikina nashiga yi ina faÉ—in
"Ni ka kyale ni ka tashi ka koma gurin ta kaje can kaci gaba da jin zantuka masu daÉ—in."
dariya ya kuma yi yace
"
A'a ina kuma zakije tun bangama baki labarin yadda hirar tamu ta kasan ce ba."
kunnuwa na na toshe da hannaye na nace
"Bana bukata ka tashi ka tafi kaje kai da kake bukata kaje ka kara ji."
da kyau ya daÉ—a rungumo ni cikin muryar dariya yace
"Sha kur
umin ki Ahmad naki ne ke da Rasheedat kun maye zuciyar babu É—an É—igon gurbin da wata zata samu ta tsugunna, babu wacce naje gurin ta zance babu ita ba kuma za'a yi ta ba,
ma'aikatan kamfanunnukan Alhaji na ne muka yi zama da su shiyasa na makara har dar
e ayi min afwa, ba zance naji ba."
baki na taɓe nace
"Ni ina ruwa na ma idan gurin watan kaje, meye damuwa ta."
saida dariyar da yake yayi yazuba min ido kana hankali yace
"Akwai ruwan ki da kuma damuwar ki sabo da kina sona, ga kuma kishi na nan ciki
n idanuwan ki."
hannunsa na bige daya kai shi karkashin ido na nace
"Babu wani abu a tare da ni kada ma kaga na tambaye ka in da ka tsaya kayi tunanin wani abun ne."
yace "Haka ko?, to kalli cikin ido na kice bakya sona, ki kalli cikin kwayar ido na kic
e bakya sona, oya kalla ki faÉ—a yanzun nan."
kawar da kaina nayi na turo baki gaba nace
"Ni ka kyale ni."
dariya yayi sosai har yana buga kafa ya manna min kiss a kumatu ya É—ago tare da faÉ—in
"Aha yarin ya kina wasa, ni É—in fa bana wasa bane jarum
i ne ni nan da kike gani."
baki na taɓe nace
"Jarumtar me?." yace "Na iya sace zuciya mana, Allah mai girma yaji tausayin bawan sa mai wahala da dakon so a zuciya da ilahirin jikin sa, ya amshi addu'a ta ya sa miki sona a zuciyar ki, kai gaskiya ni mai
sa'a ne."
"Waya faÉ—a maka kadai na yaudarar kanka dan na tambaye ka in da ka tsaya,
ka laune maganar ta koma wani abu daban, kyale ni natafi na kwanta."
nayi maganar ina kokarin zame wa a jikin sa.
daÉ—a rungumo ni yayi yashiga zolaya ta,har sai da ya
sani nayi dariya kana ya É—ago ni cak yayi cikin bedroom da ni.....
Washegari yau natashi da kewar ahalina, har da Mama mai awara,
ga ba É—aya bani da walwala yau, Ahmad yana cikin É—aki nafito parlour na zauna nayi jugum,
tabbas yau ina cikin kewar s
u sosai, Allah sarki Mama mai awara
"Ko tana ina?." nayi wa kaina tambayar, hawaye ne suka ciko ido na Allah sarki wata uwa Mama mai awara, tabbas bazan taɓa mancewa da ke a rayuwa ta ba, ke tamkar uwa ce gare ni.
ji nayi an dafa ni a hankali na É—ago n
a zuba masa ido, a sannu ya zauna a gefe na yaroko hannuna yace
"Me ke damin ki kyakkyawa ta?."
ido na lumshe tare da kuma buÉ—e wa sai na kuma rike hannunsa gam nace
"Family na ina jin kewar su, har da Mama mai awara matar data rike ni tamkar Æ´ar data
haifa, tayi min gata irin wacce uwa take yiwa É—iyar ta, badun ita ba awancan lokacin da na rasa raina nida abin da suke cikina, ta saida makwancin ta da duk wani abun da ta mallaka tabiya kuÉ—i akayi min CS."
hawaye ne suka zubo min sai na yi shiru da m
aganar dan nasan zan iya fashewa da kuwa.
a hankali ya janyo ni jikin sa ya rungume, yashiga share min kwalla yace
"Kiyi hakuri babu abin da yake tabbata har idan ya zamo fararre, bagashi yanzu kina bada labari ba, yazama tarihi komai mai wuce wa ne har
idan yazamana yana da mafari,
kishir ya gobe mukai mata ziyara."
da sauri na É—ago da murmushi yayin da hawaye ke ci gaba da sauka a idona nace
"Da gaske?." kai ya gyaÉ—a min shima yana murmushi,daci gaba da share min hawaye...
bai gushe ba har saida y
aga ya sanya ni dariya...
Washegari kamar yanda yafaÉ—a motar mu ta hau hanyar Jos, bayan munyi wa su Bappa sallama, kwarai Bappa yaji daÉ—in jin cewa gurin Mama mai awara zamu je, yayi ta zuba mana addu'a da fatan isa lafiya, yaku ce mu gaishe ta sosai
da sosai.
ni da shi muna gaba Naseem da Nasmah suna baya, dan yaki direba ya biyo mu yace tafiyar family ne dan haka direba yayi zaman sa.
da misalin karfe 2 na rana muka iso cikin garin Jos,
daga nan nafara yi masa kwatance har muka iso Narkuta,
wani
numfashi na sauke a bayyane lokacin dana ganni dai-dai kan kwalbatin shigan layin gidan Mama mai awara,
nan take tunanin rayuwa ta ta baya tashiga zuwar min, bazan mance ranar dana zo garinnan ba akan wannan kwalbet É—in na zauna har dare, har wasu mutan
e suka zo amota suna yimin tayin shiga na biyo su,
idanuna na rumtse da karfi ina kokarin mai da hawayen da ya ciko min ido.
muryar sa najiyo a hankali
"Kibar tunanin nan sam bashi da amfani tuna irin haka sai dai ya sanya maka damuwa da ɓacin rai, ina
zamu bi?."
a hankali na buÉ—e idanuna da tuni hawaye ya gangaro min, nayi masa nuni da hannu nace
"Mu mike nan."
a hankali ya sa kai cikin layin, sai É—an kalle-kalle nake, garin ya canza anyi sabbin gine-gine,
nayi ta masa nuni da hannu har muka iso
kofar gidan Malam Musa, dakyar shima na iya gane wa dan an yiwa gidan fenti ga kuma sabbin gine-ginen daya zagaye su.
kallon sa nayi nace "Ina zuwa bari na shiga na tambayi Zainabu gidan da Mama ta koma sai ta nuna mana muje."
kai ya gyaÉ—a, na buÉ—e mar
fin motar na fita.
da sallama nashiga gidan, ga mamaki na wasu mata na gani zaune a cikin gidan suka amsan sallama na karaso ciki, ina ta É—an raba ido ko zan ga Zainabu,
na gaida matan suka amsa suna faÉ—in Sannu da zuwa, nace "Yauwa dan Allah Zainabu t
ana ciki ne?."
É—aya daga cikin matan tace
"Wata Zainabu?."
nace "Matar Malam Musa." sukace "Au wai ai sun jima da tashi a gidanan na sun koma wata unguwar daban."
da sauri nace "Innalillahi dan Allah wata unguwar suka koma? ko za'a nuna mana ko ayi ma
na kwatance."
sukace wlh sam basu sani ba, suma haya suke ana gobe zasu tare a gidan su kuma suka bar gidan, sam basu san wata unguwa suka koma ba.
cikin sanyin jiki na juya nayi musu sallama na fita,
jiki ba kwari na shige cikin motar na zauna
duba na
yayi yace
"Ya dai tayi miki kwatancen gidan ne?."
kai na girgiza a hankali nace
"Bata nan wasu ne a cikin gidan,kuma wai basu san in da suka koma ba."
wasu hawaye ne masu É—umi suka zubo min sai nayi saurin sunkuyar da kaina.
a hankali ya dafa kafaÉ—
a ta yace
"Kiyi hakuri idan da rai da rabo wata rana zaku haÉ—u."
kai kawai na girgiza, a hankali ya share min hawayen yace
"Ya isa haka na roke ki kada ki sake zubda su ina jin zafin su har cikin dai na, Please na roke ki."
ya haÉ—e hannayen sa biyu.
kai na girgiza masa a hankali na karasa share hawayen.
a sannu yaja motar muka bar gurin.
muna fita bakin layin unguwar,na juya da kallo na ta gabar wato hanyar Bauchi, ya lura da hakan sai ya saka hannu ya juyo da fuska ta a hankali cikin tausasshen l
afazi da son sama min karfin guiwa yace
"Zamuje shima idan Abba ya daÉ—a huce wa."
yafaÉ—i hakan ne kawai dan sama min nutsuwa da kwanciyar hankali,
a can kasan zuciyarsa sa kuwa bayan Bappa ne sukayi masa ca,
"Lallai mutum abin tsoro ne, ka haÉ—a tsih
iri da mutuwar ka sabo da kasan duk mai halin irin naka Allah yana musu talala ta hanyar barin su a duniya su shafe shekaru masu yawa,
tabbas akwai hisabi ranar gobe kiyama."
duban sa nayi jin yaja kwafa afili nace
"Ya dai?." kai ya girgiza min da sauri
yace "Ba komai ina tunanin tafiyar dake gaban mu ne mukwana a cikin gari kawai, mu huta gobe da safe sai mu juya."
nace "A'a kawai mu tafi."
ya juya ya dubi su Naseem da tuni suka bingire da bacci yace "Sun gaji kiga baccin su nawa, kema kuma nasan kin
gaji."
nace "Ni dai mutafi gida kawai."
yace "To shi kenan."
ya haura hanya muka É—au hanyar Abuja...
kasan cewar da abincin mu muke tafe bamu sha wani wahalar yunwa ba,
ana kiran sallar magriba muna isa ciki Abuja,
yanayin gosulo da muka tarar bamu
shiga gida ba sai bayan sallar isha.
koda ya gyara parking na buÉ—e marfin motar na fito,
ina saka kafata kasa naji wani jiri ya fisge ni, da sauri na dafa jikin motar, har yafita ya zaga yaÉ—au ki Naseem da Nasmah ina dafe da jikin motar,
yazo in da h
ake yana gyara rukon su yace
"Muje ko?."
a hankali na mike tsawo na yayi gaba nabi bayan sa a hankali ina jin yan da jirin yake ta cigaba da fizgata, a haka muka shiga ciki direct sama ya haura, niko a parlour'n kasa na zube kan kuje ra, tare da kife fus
kata jikin pillow'n kujera, na rumtse idanuna da karfi jin juwan nadaÉ—a fisga ta.
ya kai su É—akin su ya kwantar da su kana ya sauko kasa yazo in da nake ya zauna kusa da ni.
yasa hannunsa ya É—ago ni yana faÉ—in
"Shi yasa nace mukwana a cikib Jos sabo
da nasan zaki wahala, kika ce sai dai mu juyo, kin ga irin ta ko."
murmushin karfin hali nayi dan yanayin da nake jin yana son wuce tunani nace
"To baga shi mun dawo ba, ai mun huta basai goben mun yi ta tunanin kuma hawa hanya ba"
Yaruko lips É—ina
yace "Wannan baki da duk abin da aka faÉ—a sai yakawo hujja".
dariya nayi nace "To ai rainon ka ne."
shima dariyar yayi yace
"Au haka zaki ce."
gira na É—aga ina murmushi. gefen fuska ta ya shafa kana ya ruko hannuna yace
"Taso na taimaka miki mu haur
a ki wasa ruwa zaki ji karfin jikin ki."
a hankali naÉ—an yunkura ya É—ago ni ya mikar da ni, idanuna na É—an rumtse kana a hankali nashiga É—aga kafata, yana tallafe da ni har muka haura sama.
a bakin gado ya zaunar da ni kana ya shiga taimaka min na ra
ge kayan jikina,
ya kuma ruko hannuna muka muka shiga bayi wankan ma sai da ya taimaka min gaba É—aya jikina ba kwari ga jirin nan yaki bari na, ga masifaffen ciwon kai.
muna fita daga bayin doguwar