Showing 96001 words to 99000 words out of 135595 words
mai firgitar wa,cike da fargaba Raliya ta dubi Na'ima tace
"Ko kinji abin da nake ji?."
cikin bushewar zuciya
Na'ima tace "Naji yanzu haka wani gagarumin ai ki yake muje a shigar da namu gaba É—aya ayi akashe ta na huta."
suna haurawa
saman tudun babu shiri suka ja wani wawan burki, gaba ɗayan su jikin su ya ɗau ɓari.
bakon suka hango kwarkwasa sun maye jikin sa tun daga saman sa har kasa ko fuskar sa ba'a iya ganin, sun cike ko ina a jikin sa, kunne ido baki hanci ta ko ta ina sun
baibaye sun rufu a jikin yam-yam.
shiko sai wani irin kara da gurnani yake, sai ya yanki jiki ya faÉ—i akasa ya goga fuskar sa a kan duwatsun da suke gurin yayi ta goga wa jini yana fita, yakuma mike wa yakuma faÉ—uwa kamar wan da ake É—aga shi ana buga s
hi da fuska, kwarkwasar nan kuma suna nan a jikin sa.
da mugun gudu suka juya ganin wasu kwarkwasa suna gangaro wa in da suke, nan take bokan nan yakuma yin sama kamar wan da aka É—aga shi sai gashi cikin wutar da yake hurawa domin yin wani asirin sa ko s
han É—umi.
yayi ta birgima yana bige-bige da kara haÉ—a da gurnani mai firgitar wa cikin wutar.
Raliya da Na'ima har suna rige-rigen shiga motar har gindin motar kwarkwasar na suka biyo su Na'ima ta ja motar a guje suna waigen bayan su da duba kasan kafa
r su ko kwarkwasan sun biyo su..
sai da sukayi nisa sosai kafin Na'ima ta dubi Raliya tana haki tace
"Raliya boka ya mutu yanzu meye mafita?."
Raliya tace "Gurin wani bokan zamu je ai basu kare ba."
daga nan suka nufi gurin wani bokan
da Raliya ta faÉ
—a mata ita ma wata kawar tace ta nuna masa gurin sa.
suna zuwa bayan sun gama zayyane abun da ya kawo su, bokan yace
ta ajiye miliyan 10 wan da za'a fara ai ki da shi, dan ai kin nata babba ne.
babu wani dogon nazari ko tunani ta ajiye masa check É—in
miliyan 10.
yace suje nan da kwanaki biyu su dawo...
A ɓangaren su Ummi kuwa kowa ya tsurawa TV ido in da ake kan cigaba da gudanar da biki,
yayin da su Ummi Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Ya Masa'ud Fauzan Nusai ba, duk kanin su hawayen farin
ciki ne ke zuba kan fuskokin su.
Abba da Abbu kuwa ido suka zubawa TV kawai, har kuma lokacin suna tsaye da ƙafafun su,
duk kanin su kuma sun kasa iya furta komai sai zuciyoyin su dake ta ambaton sunan Allah dayi masa godiya.
a hankali suka rika jin zu
ciyoyin su tana washewa tamkar ana É—aga musu wani nannauyar dutse data danne musu zuciya.
Abba Abbu Mamie a tare suka dafe kirjin su da suka ji kamar an fincike wannan abu mai nauyi an cire sa gaba É—aya,
a tare suka sauke nannauyar numfashi...
a ɓang
aren SALEEM da tun fitar sa daga parlour'n É—akin Masa'ud ya shiga ya kwanta kan gadon sa, dafe da kirjin sa har kuma lokacin yana dafe da kirjin nasa, wacce take yi masa wani irin mugun zafi, a take shima yaji kamar an fige masa wani abu mai nauyi cikin z
uciyarsa, sai dai zafi da zugin da zuciyar tasa take masa...
Acan cikin parlour'n kuwa Mamie ne tayi wani irin mike wa tare da furta "Wlh HAMDAH ce tabbas ita ce, Alhaji baka ganta ba?."
tayi maganar tana duban Abbu.
Abbu yashiga gyaÉ—a kai yana nu
na TV da yatsa tare da faÉ—in
"Tabbas ba shakka ita ce."
wani hawayen farin ciki ne yakuma zubowa kan fuskar Ummi, ganin yan da sukayi firgigit tamkar waÉ—an da suka farka daga bacci, tasan dole watarana gaskiya zatayi halin ta.
Abba kuwa cikin matuka
r nadama yake kallon É—iyar tasa daga cikin TV.....
Abuja
Har wajen magriba ana ta kan gudanar da shagalin bikin, salla ce kaÉ—ai take É—aga wasu agun.
da misalin karfe 11 na dare aka rufe taron bayan an cike waÉ—an da suka zo bikin da kayan da Ah
mad yasa a tanada domin duk wan da ya ziyarci bikin,
duk wan da yazo bikin idan mamace turamen manyan zani guda biyu da kuÉ—in É—iki naira dubu goma acikin jaka mai É—auke da katon hoton Ahmad karami a jiki.
idan kuma na miji ne tsadadden shadda ne shima
guda biyu haÉ—e da kuÉ—in É—in kin sa a cikin jakar.
a gajiye muka fito daga cikin hall É—in mota ta kwashe mu.
ga mamaki na sai na ganmu a airport,
da fuskar mamaki na dubi Ahmad nace
"Rakiya muka zo ne?." da murmushi kan fuskarsa sa yace "Mu aka zo
raka mu."
nace "Ina?." nayi maganar ina waro ido.
kuma tuna yaja kana yace "Lagos zamu, gobe za'ayi bikin buÉ—e Company ki na can, wan da É—ana ya hanaki samun sukunin buÉ—e shi."
baki na buÉ—e zanyi magana sai aka buÉ—e marfin motar,gefen sa da fege
n
a, sai nayi shiru na fito kawai.
direct cikin jirge muka shige anan na tadda wasu daga cikin mutanen da suka halar ci bikin mu waɗan da suka zo daga wasu ƙasashe har da wasu ɗaiɗai ku ƴan nan kasar mu,
a can kujerar gaba na hango Bappa yana zaune, a
cikin jirgin nake faÉ—a wa Ukhtee in da zamu je, na tausaya mata ganin yana yin ta na san tafaji sosai.
a jere suka zauna da Aunty Rasheedat da Naseem da Nasmah, in da muka zauna ni da Ahmad a kujerar bayan su, yana rungume da Ahmad karami...
muna isa mo
toci suka kwashe mu suka kai mu masauki, ni da Ukhtee É—akin mu É—aya Naseem da Nasmah kam ma ban ga idanunsu ba.
a gaye muka shiga rage kayan kijin mu,
ganin Ahmad karami ya nata mita nasan cewa wan ka yake bukata, na tuɓe sa nayi nashiga dashi bayi na
yi masa wanka cikin bathtub dan dole sai dai nan É—in tun da ba bu wabon da zan masa a ciki, na naÉ—o sa a towel É—in sa na sauya masa wani kaya, dan gani kawai nayi an biyo mu da akwatin mu.
sai da yayi bacci kafin na shimfida shi, lokacin Ukhtee tafito
daga wanka, nima na shiga nayi wan ka, yau kam babu wani hira muna kwanciya dukan mu sai bacci..
washegari ban farka ba sai wajen karfe 9.
ko da na farka na tadda Ukhtee har tayi wanka, ina dire a gadon Ahmad na buÉ—e ido, sai da na fara yi masa wanka ka
fin nima nayi. kayan
breakfast É—in da aka shigo da shi tun ina bacci, bayan na shirya na zauna muka yi breakfast É—in, sai tan nan naje na É—au wayata da na kashe ta tun jiya isowar mu na kunna.
ai ko ina kunnawa sai ga kiran Ahmad ya shigo, yace
"Kyak
kyawa ta an tashi lafiya ya gajiyan jiya."
nace "Gajiya ya washe."
yace "Alhmdllh Nagode wa Allah, ina Ahmad ya tashi kuwa ga su Naseem har yanzu basu farka ba." nace
"Shikam ina tashi shima ya farka gashi nan yana ta rarraba idanu."
dariya yayi yace "
Sa masa wayar kusa da shi naji numfashin sa."
wayar na kawo kusa da shi nace "Daddy na magana." murmushi yayi mai sauti yace "Shafa min kansa." nace To.
yace "Anjima karfe 12 za'a tafi gurin nan, karfe 2 za'a gama yau zamu koma gida."
nace "To Allah ya
kaimu."
yace su Naseem su tashi bari ya yi musu wanka zasu shigo nace to...
Da misalin karfe 12 da kwata gaba É—ayan mu muka hallara a farfajiyar hotel É—in.
nan motoshi suka rika kwasan mutane suna tafiya da su.
kamar yan da muka tafi wancan filin
taron jiya motar mu É—aya da shi yau ma haka,
tun daga wajen kamfanin har cikin sa an zagaye shi da adon fulawa, a katafare filin da ke cikin kamfanin aka gudanar da taron, wan da mai girma Gwamnan Lagos shine babban bako a gurin taron da sauran mukarraba
n sa.
an guda nar da taron cikin lumana da kwanciyar hankali in da ake nuna taron kai tsaye a kafafen sadar wa.
anan gurin aka tantance ma'aikatan da suka nimi yin ai ki a kamfanin, aka kara akan wan da dama can aka tantace su kwararru masana ai kin...
karfe 2:30Pm aka watse a taron kowa ya kama gaban sa, a ranar wasu suka koma kasashen da suka fito wasu kuma sai zuwa gobe.
da misalin karfe uku jirgin mu ta É—aga zuwa Abuja.
muna isa yau washegari Ukhtee tace zata koma, Ahmad yayi mata cuku-cukun koma
wa sai dai ba'a sami jirgin da zai tafi Saudi kai tsaye ba dole na dubai daga can sai ta shiga jirgin Saudi.
har airport muka yi mata rakiya Ahmad na ta yi mata godiya, bayan cike ta da yayi da goma na arziki.
lokacin da ake sanar wa kan fasinjoji su shi
go cikin jirgi sai muka rungume juna muka fashe da kuka, da kyar Ahmad ya ɓanɓare ni a jikin ta jin ana ta cigaba da sanar wan, ta wuce cikin jirgi muna ɗagawa juna hannu...
a mota yayi ta lallaɓe na har sai da yaga nayi dariya, ya dube ni fuska ɗau
ke da sihirtaccen murmushi mai bayyana zallar so da kauna yace "Ina son ki kyakkyawa ta."
idanuna na lumshe kana a hankali na kwanto da kai na jikin kafaÉ—ar sa a hankali cikin yin kasa da murya nace
"Nima ina son ka My."
wani irin wawan burji ya ja,
da sauri na buÉ—a idanuna na É—ago kaina da sauri cikin hanzar na dafe gefen kujerar moton jin yan da nayi gaba kamar zan garo da gaban motar.
a gefen titi yayi parking, ya wani irin jan yo ni ya rungume tamkar zai cusa ni cikin jikin sa, yace
"Nagode ky
akkyawa ta Nagode da jin fitar wannan kalma daga bakin ki, ako da yaushe zaman jiran sa nake naji yafito daga bakin ki,
ina son ki! ina son ki!! ina son ki!!!, ako da yaushe kamar daÉ—a kara min son ki ake."
sai ya shiga sumbatar fuskata ta ta ta ina yar
ika manna masa kiss,
ya ruÉ—e yagama zauce wa, sai kokarin daÉ—a nuna min yanda yake so na da kuma kauna ta yake.
sai da na janye jikina da karfi nace Ahmad na gida zai iya yiwa Inna Wuro kuka.
kafin ya ja motar muka bar gurin,
yana tukin sai ya juyo y
a sumbaci kuma tu na, aha muka isa gida.
ranar bai matsa ko nan da can ba a yana like da ni, karshe Inna Wuro fita tayi ta bar mana side É—in gaba É—aya sai dare ta dawo....
Bauchi
Ranar da aka gudanar da toron buÉ—e Company HAMDAH duk ka fami
ly'n su suna gindin TV, Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela suna daga gida jen su suna waya a gida, cike da murna suna tambayar suma suna kan kallo ko.
Ummi farin cikin ta har ya gaza ɓuya duk tarin kawai cin ta.
washegari da sassafe Ummi ta tashi da shiri
, Abba ya shigo ya same ta tana ta shiri, da É—an mamaki ya dube ta yace "Shirin me kike ta yi haka?."
tace "Gurin É—iya ta HAMDAH zani."
ta faÉ—a a takai ce ta cigaba da shirin ta.
Abba yaÉ—an yi gyaran murya kana yace
"Yan zu muka gama magana da Yaya
Idris ya kama ta ki bari mu shir ya tafiyar duka."
da sauri Ummi ta É—ago ta dobe shi tace
"Babu abun da zai hanani tafiya yau sai ikon Allah, idan kana tunanin cewa ma zaka kuma dakatar da ni ne, kamar lokacin da kayi ahakan a lokacin da take bukatar t
aimako da mafaka, na amin ta nayi maka biyayya to ka sani a yanzu bazan taɓa hanuwa ba, zan fita naje na nimo ƴata tun da har Allah ya nuna min tana nan da ranta, sai dai daga nan kakuma cewa kada na dawo maka gida,
ko ban same ta ba na tabbata banyi as
ara ba."
shiru Abba yayi yana kallon ta yayin da jikin sa gaba É—aya yayi sanyi,
tabbas yasan Ummi mata ce mai hakuri da kawai ci, duk da shi ya kori HAMDAH da kansa ko dai-dai da rana ɗaya bata taɓa nuna masa ɓacin rai ba, kuma bata gushe kan biyayta
r da take masa ba.
yana tsaye tagama shirin ta ta É—au mayafin ta, taÉ—au jakar ta tayi waje.
ya biyo yana faÉ—in
"To ki tsaya direba ya kai ki." bata ko saurare shi ba.
a sakar gida suka haÉ—u da Abbu ya tambaya ina zata, Abba ya faÉ—a masa, Abbu ya j
injina kai cike da yabawa da hakuri da kawai ci irin na Ummi yacewa Abba kada ya dakatar da ita da tafiyar, tafiyar nata shine zai samar mata da mutuwar data rasa shekarun baya da suka wuce tun barin HAMDAH gida, wan da ta rika dauriya da juriyar iya danne
shi ta barwa ranta...
Ummi na fita a dai-dai ta ta tsara ya kaita tasha daga nan ta shiga motar Abuja, idan bata man ce ba anan taga taron bikin farko da su HAMDAH sukayi, kuma taji Æ´an jaridun suna faÉ—in daga Abuja,
taÉ—au haryan Abuja da tunanin
idan ta neme ta bata same ta ba zata wuce Lagos in da taga an gudanar da taron buÉ—e kamfanin ta.........!
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 31
Koda Ummi suka iso Abuja ta sauka a tasha, tunanin ta in da zata fara ta shiga yi.
mene ne abin
yi tayi tambaya a babban gari irin wannan tana ganin kamar babu mafita a yin hakan,
to amma ai HAMDAH ta sanu a yanzu wata kila baza ta sha wuya wajen samo ta ba.
a da ire-iren irin waÉ—an nan tunanin ta tsare mai abun hawa, ko da mai taxe ya tsaya ya l
oko ta yana faÉ—in
"Hajiya ina zuwa?." tace "Malam ko kasan gidan wata da ake cewa HAMDAH?."
É—an shiru yayi alamun tunani kana yace
"Gaskiya ban sani ba wace unguwar take?."
tace "Ban san unguwar da take ba." yace "To in banda abin ki Hajiya zaki tsa
ri mai abin hawa baki san in da zaki ba, a gari irin wannan zaki tambayi wata batare da sanin adireshin ta ba ai ba lallai ki iya samin ta ba ko a kauye ba'a haka bare a birnin tarayya."
yaja taxes É—in sa yayi gaba. Ummi tace
"In sha Allah zan same ta k
o batare da adireshi ba."
wani ta kuma tsare wa shima irin tambayar da tayiwa wancan shi tayi masa,kusan irin amsar da wancan ya bata irin shi shima wannan ya bata.
ta tsari masu taxe da suka gai kusan guda goma duk kusan amsa iri É—aya suke bata idan ta
yi musu tambaya kan sun san gida wata da ake cewa HAMDAH...
har yamma tana tsaye a bakin titi, wani mai taxe É—on taxe yazo zai wuce da ido kawai ta bishi dan har ta gaji da tsare masu abun hawa, ta fara tunani ta sami masauki ta huta dan ma Allah ya taim
ake ta tayi salla cikin tashan lokacin da suka sauka.
har ya É—an gota ta sai ya dawo da baya yace
"Ina zuwa Hajiya?. a É—an gajiye ta dube shi tace "Masauki mafi kusa da nan."
yace "Hotel kenan?." tace "Eh." yace "To shigo muje." taÉ—au jakar ta tashig
e cikin motar da bismilla.
har sun fara tafiya sai me taxe É—in ya É—an waigo kana ya mai da idanunsa ga titi yace
"Babban hotel kike so a kai ki ko me É—an dama-dama?." tace "Me É—an saukin kuÉ—i dai wanda bazan kashe yafi dubu hamsin ba."
kai ya jinji
na kana suka cigaba da tafi,
sun iso daf da hotel É—in me taxe yace "Yau wa gamu mun iso bari na karasa da ke can basai kin tsallaka ba sai ki shiga."
tace to. baki ya washe "Amma Hajiya a garin nan fa komi dare ana samin mota duk garin da kike son zuwa
zaki sami mota, ai da zai fi miki akan ki kashe kuÉ—i mai yawa gara ki shiga mota ki wuce gaba É—aya,
ko da shike manya basu fiye son zaman mota da yawa ba wai shima wahala ce agurin su, kai talaka kam gara ka wuce É—in ka adana kuÉ—in da zaka nimi masauk
i kayi wata bukatar da shi."
yakara sa maganar yana cigaba da washe baki.
Ummi tace "Allah ya rufa mana asiri duniya da kiyama, amma ba wani gari zanje ba iya ka ta nan garin idan ban dace ba kuma sai na wuce Lagos,
ni gidan wata nake nima tun É—azu na
iso garin nan gashi har yamma tayi, ina ta tambaya ban dace ba."
yace "Tambayar gidan wata a cikin garin nan, gaskiya zai yi wuyar samu in ba wai kasan adireshin gidan bane, to ke baki da lambar ta ne ki kirata tayi miki kwatance?."
Ummi tace "Bani da la
mbar ta."
yace "To gaskiya zaki sha wuya ne kawai wajen neman ta, manya ne waÉ—an da aka sansu akasar sune idan kashigo niman su cikin garinnan bazaka sha wuya wajen samun su ba, tun da sun sanu yawanci zakiga an san su, gaskiya zaifi ki koma gida ko kuma
ki kira aturo miki lambar ta sai ki neme ta, amma ya sunan ta ko sunan take kusa da su wata kila manya ne tanan zaki iya dace wa?."
tace "HAMDAH sunan ta." yace "Wai to Allah yasa ki dace."
tace "Amin ngd." dai-dai nan yagyara fakin ta sauka ta biya sa
kuÉ—in sa, taÉ—au jakar ta ta gangara hanyar da zai sada ta da cikin hotel É—in.
har ta kai bakin get É—in hotel É—in taji ana faÉ—in
"Hajiya Hajiya Hajiya." ta juyo dan gani ko da ita ake sai taga mai taxe É—in nan