Showing 39001 words to 42000 words out of 135595 words
/>
Naseem yace "Daddy dakajo anjima?."
kai yagyaÉ—a yana
mai cigaba da wannan murmishi wan da kamar da shi aka gina fuskar sa yace
"Sosai ma zan zo mana."
Cikin hatsala haɗe da ɓacin ran ganin yau ma kamar na ranar da na same su tare da shi a kofar makarantar su, ina nayi musu magana sukayi kamar basu sa
n ni ba,
sai shi da suke ta biye masa suna bashi amsar duk abun da yace musu,
bugu da karin bacin raina kiransa da sunan dana hane su a gabana.
cikin tsawa nace
"Kai Naseem me nace maka waye Daddy'n ka wato bakaji ba ko, ban ce muku kada ku kuma cewa w
ani Daddy ba, wato duk maganar da nake muku aban za bakwa ji ko, idan naji kasake cewa wani Daddy sai na fasa maka baki,wuce mutafi nace!."
ko da nake masifar harlau idanunsa a kai na, sai ya saki wani murmushin gefen baki yayin da gefen kumatun sa na dam
a ya lotsa, har kuma lokacin yana rike da kafaÉ—ar su.
a sannu yaÉ—an sun kuyo yadubi Naseem kana yakuma dubi Nasmah kana yakuma sakin wani murmushin sannan yace
"Naseem Nasmah mene ne ma suna na?."
suka haÉ—a baki wajen cewa "Daddy Daddy tunan ka."
y
ace "Kai yaran nan to Allah yayi muku albar ka, to maza ku tafi ciki ayi muku wanka kuci abinci maza kuje."
ya faÉ—a yana tura keyar su.
ai ko da gudu suka yi ciki suna dariya, ganin rainin wayon nasu da yawa yake wato umurnin sa ma zasubi ba nawa ba. na
dube shi tare da rike kugu nace
"Kai malam kana ji ko, kada ka sake zuwa in da yara na suke kada ka sake kasake zuwa in da suke, kada ka sake cusa musu ra'ayin cewa wai kai Daddy'n su ne, kai ba Daddy'n su bane basuma san ka ba, ni ban gayyaci wani acikin
lamarin Æ´aÆ´ana ba,karabu da harkar yara na idan kuma ba haka ba wlh zan É—auki tsatstsauran mataki a kanka, kada ka kuskura ka
sake zuwa in da yara na suke, kada ka sake yi musu karya kan abun da ba haka bane, bana kara kan haka dan Æ´aÆ´ana nice kaÉ—ai
uwan su kuma uban su,
dan Allah malam kada ka sake cusawa Æ´aÆ´ana wannan gurguwar ra'ayin, ka gane ko?!."
na karashe maganar da nuna masa yatsa haÉ—e da murguÉ—a masa baki, na juya a hatsale ganin duk maganar da nake madadin ya shiga taitayin sa sai m
a daÉ—a sakin wannan murmushin nashi yake.
tafiya na soma cikin fushi dan nalashi takwabin yau sai na zane yaran nan tun da har ni zasu gwadan wani yafi ni muhimmanci agurin su har zasu ji maganar sa akan nawa.
sai jin maganar sa nayi daf dani
"Kece uw
an su kuma uban su to ya akayi kenan hakan ta faru, ke kika ba kan ki cikin kenan,faÉ—a min da ma a she mace tana bawa kanta ciki da kanta, dama a she uwa tana bawa kanta ciki ita kaÉ—ai batare da uba ba??."
wani irin juyi nayi jin sautin sa kusa dani bat
are da zato ko sammani ba, maganar yashige ni tamkar shigar shoc cikin jini na, wani irin mugun kallo na watsa masa tare da jan dogon tsaki, najuya na nufi kofar side É—ina da sauri...
shiko bayana yabi da wannan murmushin kana ya juya yashige motar sa ya
ja yabar gidan.
Koda na shiga banbi takan su Naseem ba dan nasan koda na yi musu hukuncin danayi niyyar ma bashi zai sa su dai na abun da na hanasun ba,
sai kawai nashige É—aki nazube bakin gado, kamar an zabure ni kuma na mike na isa gaban mirror in d
a wayoyi na suke ajiye, number Yakubu na kira, nafara zazzage masa masifa
"Wato Yakubu dana ce kaje ka É—auko su shine bakaje ba kabar wannan É—an rainin wayon mutumin wai Ahmad yake ko wa yaje ya É—au ko su ko?,
idan ka gaji ne kafaÉ—a sai a sallame ka.
"
da sauri yatari numfashi na da faÉ—in
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri wlh yanzu haka ina hanyar dadowa ne ina ma kokarin kiran ki kenan sanar miki sai ga kiran ki, naje makarantar aka ce min yazo ya É—auke su, ai Hajiya baki sani bama É—azu da zamu kai s
u sabon makarantar yazo ya mai da su cikin makarantar yace mutafi mu barsu anan."
ido na waro da ɗinbin mamaki mai haɗe da mugun ɓacin rai,
ban san san da na dakawa Yakubu tsawa ba nace
"Dalla malam ya isa ni da kai na nace ayi abu kan Æ´aÆ´ana sanna
n wani can daban yazo yace ba hakaba kai kuma ka yarda, umurnin sa kabi kenan? ok to ka wuce gidan sa daga nan kaje can yacigaba da baka umurnin!."
nakashe wayar rai ɓace,
"Lallai ma wato ashe ma ba'a kai su makarantar ba shike nan ya hana ko me?."
A
fusace na danna number shugaban makarantar yana É—agawa nace
"Malama ya zan ce ga abun da nake so sannan kuma wani yazo ya hana kuma ku amin ce, to gaskiya daga yau bazama su sake zuwa makarantar ba ma sun fita kenan."
da sauri yace
"Ranki shidaÉ—e mah
aifin su ne yazo yace kada a canza musu makarantar bawai yin kan mu bane."
kashe wayar nayi jin raina yadaɗa ɓaci.
dogon tsaki naja tare da yin kwafa nama kasa cewa komai saboda sabar bakin ciki,sai dai naci alwashin daga yau baza su sake zuwa makarant
ar ba,
zan mai da su *HAM'NAS* International School Of Science And Technology.
After 1 week
Tsawon sati guda agida suka yishi ranar Lahadi nasa aka kawo musu uniform na *HAM'NAS* International School Of Science And Technology.
washegari Monday da
misalin karfe 7 aka gama kimsa su tsaf,
muna tsaye a parking space, daga can na É—agawa Faty hannu da fito war ta kenan daga side É—in su, nayi mata alama da tayi sauri, ta Kara so da sauri, tace
"Ina kwana Adda HAMDAH." murmushi nayi tare da faÉ—in "L
afiya lau antashi lafiya."
"Lafiya lau." tafaÉ—a tare da
duban su Nasmah tace
"Yau yara sun koma School É—in mu."
hannun ta Nasmah tarike taÉ—ago kanta tana duban ta tace
"Aunty Faty School inku akwai lilo?."
Faty tace "Eh har da abun zame-zame da
mota mai lilo da doki mai lilo."
tsalle Naseem ya tuma yana faÉ—in
"Yeee nine zan shiga moto in tuka ku."
dariya duk mukayi, na dubi Yakubu dake ta faman goge mota, nace
"Dan Allah kabar goge motar nan haka in ba halitta zaka sake masa ba, kutafi haka
kada kasa su makara,kuma dai kaji abin da na faÉ—a maka wlh aka kuma samin wata matsalar duk wani hakuri da magiyar ka bazai maka amfani ba."
nayi maganar ne cikin jin haushin sa na rannan dan da kyar na hakura da hakurin da yayi ta bani.
da sauri ya bar
goge motar yabuÉ—e marfin motar yana faÉ—in
"Zo ku shiga Naseem, wlh hajiya in sha Allahu baza a sake samin wata matsala ba, wancan rabar ma tsautsayi ne, dakuma ganin shi babban mutum ne a kasar nan shiyasa ban masa musu ba, dan gudun kada yasa a kwashe
ni akai ni gidan maza,
dan musu da babban mutu awannan zamanin haÉ—ari ne."
tsaki naja tare da faÉ—in
"Kabari zai kai ka karshen É—auri kenan."
najuya naso ma tafiya ina É—agawa su Nasmah hannu da cigaba da faÉ—in
"Kadai ji abun da na faÉ—a maka."
y
ace "Kwarai Hajiya, ai daga yau bazaki sake jin wata masala ba."
ban kuma bi ta kan sa ba nawuce part É—in su Inna Wuro."
A parlour na tadda su Bappa suna breakfast na zauna nima bayan mun gaisa Inna Wuro tazubo min kayan breakfast ta turo min gabana,
nan nashiga ci muna ɗan taɓa hira.
Bappa yace
"Mutanen sun tafi makaranta ko?."
nace "Eh sun tafi." Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in "Yanzu kam an bar kuka idan za'a tafi."
"Dama ai rashin sabo ne yanzu kam an saba."
cewar Inna wuro. Bappa yace "
Hakane kam wai me yasa ne aka sauya musu makarantar ko yayi musu nisa ne? ko da yake *HAM'NAS* International School yafi shi nisa, me ya sane?."
"Babu tsaro yan da yakama ta a makarantar shi yasa."
nafaÉ—a a takaice.
Inna wuro tace "Hakkum gaskiya sabo
da Allah kam ya kamata su kara sa ido kan É—aliban su, susan duk wani wan da zai kawo É—alibai yakuma zo É—aukar su, duk da dai ranar Malam yace min mutumin kirkin nan ne Ahmad Tijjani Sabil yaje ya É—auko su ake tunanin ko masu garkuwa da mutane ne, amma
dai ya dace sosai su sa ido kan É—aliban su."
kai kawai na jinjina batare da nace komai ba,akasan raina kuwa faÉ—i nake
"To waya sani ma ko mai satar mutanen ne dole zan sa jami'an tsaro cikin gidan nan tun da har ya fara shiga cikin gidan nan yana leken
asiri."
maganar Bappa dana ji shi ya kashe min zancen zucin danake
"HAMDAH har yanzu banji kin ce komai ba kan maganar mu ta rannan,
Yakamata yanzu kam kiyi aure ki fidda miji na gari kiyi aure, domin darajar ki yadaÉ—a ninkuwa, kwanakin can munyi ma
ganar nan bakice komai ba,
daraja da kimar hace baya ɓata cika cif har sai tana tare da abokin rayuwa wato mijin aure."
tea ɗin da na kurɓa ne nahaɗiye shi da kyar, sam bana son jin wannan kalmar gaba ɗaya naji nakoshi da abincin a hankali na mai da
cup É—in na aje kana a hankali nasoma magana.
Bappa aure kuma, ai ni bazan yi aure ba rayuwa ta a haka tafi min."
yace "A kul ɗin ki kada na sake jin wannan maganar, a wannan shekarun naki zaki ce baza kiyi aure ba, nutsuwa bata taɓa cika sai da aboki
n rayuwa, kiyi na zari sosai ga abokan kasuwancin ki da suke zuwa gidan nan, ko wannan Alhj Muttari nan ai mutumin kirki ne ko ranar yaso yimin zan cen sai dai bai fito muraran yayi maganar ba,
in yaso sai ku dai-dai ta kiyi auren ki kamalar ki ta daÉ—a
cika."
Inna Wuro tace
"In ban da HAMDAH ma ai mutane basu taru sun zama ɗaya ba, dan wani abu yafaru da rayuwar auren ki na fari bashi zai sa nan gaba yakuma faruwa ba,ai Allah baya taɓa jarabtar bawan sa da abun da bazai iya ba, duk kuma musulmi an s
anshi da karɓar kaddara me kyau ko mara kyau,
ki gode masa ta hanyar kuma kara yin wa ni auren."
"Hmm." kawai nace dan bana jin kamar abun da suke faÉ—an zai kasan ce, har can kasan kololuwar raina bana jin zan kuma aure, babu abun da natsana a yanzu ka
mar aure.
meye acikin auren ban da tashin hankali da musifa, in dai har aure nutsuwa ce kamar yan da suka faÉ—a to gara na tabbata ni bani da wannan nutsuwar.
Duk wani nasiha da jan hankalin da su Bappa suke jin su kawai nake,dan a yanzu babu abun da n
afi tsana ma kamar aure!.
sai da na bari suka gama yi min nasihar kafin na mike nace dasu zanje na É—an kwanta kafin su Naseem su dawo, abin cin da ban karasa ci ba kenan nafito.
ina fita daga side É—in wata mota na shigo wa cikin gidan, a hankali na ke
tafiya har na iso in da motar tayi parking kasan cewar dole sai nabi ta hanyar kafin na wuce side É—ina,
ina isa dai-dai in da motar take sai ji nayi an.......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:55 - Ummi Tandama😇: Da sauri cikin matukar t
ashin hankali tun kan ya karasa abun da zai faÉ—a na ce "Tamutu tamutu ko?!!."
nayi maganar hankali a mugun tashe dan nagama tsinkewa da yan da naji yake maganar.
ya ce "A'a Madam ba mutuwa tayi ba, dama bata da lafiya ne?,
tun zuwan su School É—in Aun
ty'n su tace taga yanayin ta kamar batajin daÉ—i, shine ta tambaye ta sai tace mata wai kan ta keyi mata zafi, to tafita taje ta É—auko magani a office kenan ta dawo ta samu tana rike da kanta tana kuka tana faÉ—in kanta zafi, kan tayi aune ma ta faÉ—i kas
a a sume, tun É—azu muna asibiti ban so kira na sanar ba sai ta farfaÉ—o amma har yanzu likitoci sun kasa shawo kan ta."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un wlh lafiyar ta lau ta bar gida."
na furta da karfi yayin da jikina ke cirawa cikin azama na duro a
gadon wayar na kare a kunnena ina tambayar sa wani asibiti ne, yana faÉ—a min nakashe wayar batare da na tsaya sauraran abun da yake cigaba da faÉ—a ba.
wardrobe na buɗe na janyo mayafi na takalmi mara tudu na saka da sauri nafita na nufi ƙasa, bibbiyu
nake haÉ—a steps,ina sauka na nufi kofa har ina haÉ—awa da sassarfa.
su Talatu suna zaune cukin parlour'n da sauri suka mike ganin yanda na sauko a firgice, tambaya ta me ke faruwa suka shiga yi suna biyo ni a baya,
tuni nayi waje ban tsaya basu amsa ba
, har parking lot suka bini, suna tambayar abun da ya faru. sai a lokacin na ce da su "Nasmah ce ke asibiti asume."
salati suka shiga yi suna tambayar garin yaya.
wan nan karon ban tsaya basu amsa ba dan ji nake tsayuwa basu amsa ma ɓata lokaci ne.
kan
kace me sabbin Security É—in da aka zuba cikin gidan sun iso in da muke, ganin yan da su Talatu suketa rafka salati, suma duk tambayar da suke ban tsaya basu amsa ba, su Talatu ne suka sanar musu abun da ke faruwa.
Yakubu nashiga kwaÉ—awa kira,
da sa
uri haÉ—e da gudu yafito daga cikin É—akin su, da sauri na shige cikin mota, yana ganin haka ya koma É—akin da sauri ya fito rike da makullin motar cikin hanzarin yashige motar.
cikin matukar da muwa da rawar murya nace
"Yakubu kayi sauri ko ka bani key
É—in motar ni naja."
key yayi wa motar tare da figar ta aguje, da gudu mai gadi ya buÉ—e get muka fita a gidan, sai da muka haura titi kafin yake tambaya ta in da zamu nafaÉ—a masa sunan asibitin.
duk gudun da Yakubu yake gani nake kamar bayayi asibitin
tayi min nisa.
Number da aka kira ni da shi aka sanar min da tana asibitin na kuma kira wayar tayi ta ring ba'a É—aga ba,
kuka ne naji ya zo min nayi saurin toshe baki na a raina nake faÉ—in
"Shike nan ta mutu."
kokarin mai da kiran nake dai-dai nan n
ajiyo muryar Yakubu yana faÉ—in
"Hajiya mun iso."
da sauri na É—ago dan ban san har mun iso ba.
da sauri na buÉ—e motar na fito batare da na jira faÉ—in da yake bari ya zo ya buÉ—e min motar ba.
da sauri haÉ—e da sassarfa nayi cikin asibitin, a kofar s
higa cikin parlour'n asibitin na haÉ—u da Aunty'n su Nasmah tana kokarin fitowa cikin sauri take tafiya da ka ganta gaba É—aya hankalin ta a tashe yake.
tana gani na ta juya da sauri tana faÉ—in
"Madam ta farfaÉ—o amma tana ta kuka."
da sauri nabi bayan
ta ina faÉ—in "Ina take."
tun da ga cikin parlour'n nake jiyo kukan ta, da gudu nanufi kofar room É—in da nake jiyo kukan ta ciki,
wasu daga cikin ma'aikata asibitin sukayi yunkurin dakatar da ni, ban ko saurare su ba
na tura kofar na sa kai ciki.
ina
ji Yakubu daya biyo ni yana sanar musu da ko ni waye.
Likitoci har guda uku a tsaye a kan ta suna rirrike da ita sai ihu take tana bige-bige, da gudu na isa in da take na kusa sakanin su na rungume ta,sai kawai nima na fashe da kuka ina faÉ—in
"Nasma
h me ya same ki, me ya same ki Nasmah?!!."
kuka sosai na ke ina rungume da ita, itama kukan take tana ta fisge-fisgen nan kamar wacce bata cikin gayyacin ta.
Turo kofar aka yi da karfi yana gaba wani na biye da shi.
in da muke suka karaso da sauri, wa
n da ke biye da shi É—in ya dubi likitocin da ke cikin É—akin yana faÉ—in
"Wai har yanzu bakuyi wani abu a kai ba?."
cike da girmamawa sukace "Sir muna kai kenan yanzu ta farfaÉ—o so taki tsayuwa Muna kan kokari ke nan mu shawo kan matsalar, ruwa za'a s
aka mata sai dai taki tsayuwa sau uku ana samun jijiya sai ta gauce ya ɓata, zamu nima ta kafan ta ko kai ne a saka mata, na hannayen ta kam duka mun rasa su."
cikin faÉ—a Dr da suka shigo tare da Ahmad da alama shine babban su ya ce "Shirmen banza sai
kace ba ai kin ku ba."
sai kuma ya dubi Ahmad ya ce
"Sorry Sir ko mai zai dai-dai ta insha Allah."
kai kawai Ahmad ya jinjina ya É—an maso in da nake rungume da ita ya ce
"To meye amfanin kukan, kin rungume ta kina kuka ita tanayi, to da wanne zata ji
da ciwon da ke damin ta ko da wannan kukan naki?."
hannu ya mika ya ɓamɓare ta a jikina, sake masa ita nayi dan na rasa abun yi guda ɗaya ganin yanayin nata yakuma jefani cikin kiɗi ma, da firgici da tashin hankali, ya ɗago ta ya saka ta a kafaɗar s
a ya na faÉ—in
"Kun ɓula ta da yawa dubi yan da hannayen ta suka fara kumbura."
"Sorry Sir ta ki tsayuwa ne."
É—aya daga cikin likitocin yafa É—a. tsaki yaja kana ya ce
"Me yasa tun kan ta farfaɗo baku ni mi jijiyar ba, sai da ta farka zakuyi ta ɓul
a