Showing 120001 words to 123000 words out of 135595 words
nauyi ya É—auke su, wan da basu farka ba kuma sai yanzu.
É—aya daga cikin security ya bada
tabbacin cewa
shi bai sha lemun da wuri ba ya aje nashi sai daga baya yasha, lokacin da bacci ya fara fizgarsa bai kai ga É—aukar sa ba yaga mai gadin yaje in da karnuka suke yana fesa musu wani abu, sai dai baccin da ya zo mishi babu zato ya hanashi tas
hi ya bincike mai gadin kan abun da yake yiwa karnukan...
har gari yayi haske sosai sojoji na zagaye da gidan, tuni gidajen TV dana rediyo suka fara sakin labarai kan rahoton da suka samu.....
A parlour mukayi salla dukan mu har da su Bappa, dan Ba
ppa yaki matsawa ko nan da can daga in da nake.
ganin gari yayi haske kuma har zuwa lokacin security basu zo da Ahmad kamar yadda Bappa ya faÉ—a ba.
gashi duk kiran wayar sa da nake baya É—agawa,
na saka musu kuka nace ni sam zan tafi zanje da kaina gid
an.
wayar Bappa ce tayi kara, ya É—aga tare da yin sallama.
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un."
abun da Bappa ya furta kenan, zumbur na mike tsaye ina kallon Bappa, Bappa ya kawar da kansa tare da sauke wayar a kunnen sa, yayin da laɓɓan sa ke motsa
wa alamun salati yake.
ɓari jikina ya soma murya na rawa nace
"Bappa mene ne wa yayi maka waya?."
kai ya girgiza yayin da idanunsa suka kawo kwalla, sai ya kawar da kansa daga kallo na yace
"Babu komai je ji sa babban mayafi ki zo sai muje gidan Ahma
d É—in kawai tun da har yanzu basu zo ba."
ya dubi Inna Wuro yace
"Je ki rakata tasa mayafin."
sai ya sauya harshen sa izuwa fulatanci yayi mata magana cukin harshen fulatanci,
Inna Wuro ta saki salati tana dafe kirji, sai kuma tayi saurin sauke hannun
ta a kirjin sabo da maganar da Bappa ya kuma mata da fulatan ci, ta ruko hannuna yayin da hannunta ke ɓari ta janyo ni muka haura sama.
muna shiga muka tadda su Naseem duk sun farka, tace na cire hijabi da kayan baccin da ke jiki na na sa wani kayan.
ji
ki a sanyaye yayin da hawaye ke bin fuskata nayi kamar yanda tace, nasaka babban hijabi, kana ta ruko hannun su Nasmah ni kuma na É—au Ahmad karami muka sauko kasa.
tun kan mu karaso parlour'n kasa su Mama suna ganin mu kowa ya shiga sun kuyar da kai suna
share hawayen su cikin dabara sai kowa ya mike da sauri akayi waje gaba É—aya.
da sauri na É—aga murya nace
"Kukan me kuke yi?."
da sauri Bappa yace
"Kuka kuma sam ba wan da yayi kuka a cikin mu."
cikin rawar murya da kuka ke son kwace min nace
"Na
ganku da idona na, ganku kuna kuka ku faÉ—a min kukan me kuke yi?."
Mama tayi murmushi wan da yafi kuka ciwo tace
"A ina kuma HAMDAH mu sam bamuyi kuka ba muje direba yana jiran mu."
ta ruko hannuna muka karasa fita waje...
koda muka iso parking lot Ba
ppa yace su Zulai su zauna da su Naseem a gida.
a tsakiya suka sani Mama da Inna Wuro, Ahmad karami na rike a hannu na, Bappa kuma ya zauna a gefen mai zaman banza, direba yaja muka fita.
ina zaune shiru hawaye na zuba a idona na, ido na kurawa titi gani
n mun É—au wata hanyar daban ba hanyar gidan Ahmad ba.
a bakin wani katon asibiti direba yayi hon, aka buÉ—e masa ya sakai ciki ya faka motar muka fito, asibitin zagaye yake da sojoji da Æ´an sanda, can na hango Abba Bashir yana sunkuye da alamar kuka yak
e, wasu mutane na tsaye a kansa. Inna Wuro ta karɓi Ahmad karami dake hannuna, Mama kuma ta ruko hannuna gam ta janyo ni muka nufi cikin asibitin.
da kyar nake iya É—aga kafafu na da sukayi min mugun nauyi,
maganar Mama na jiyo tana faÉ—in
"Ba a ja da
ikon Allah duk abun da kaga ya sami bawa da sanin ubangiji, Allah kuma baya barin wani dan wani yakan kuma jarabci mutum ta ko wace hanya domin ya gwada imanin sa,
yana da kyau mu kasan ce masu karɓar kaddara mai kyau ko mara kyau aduk san da tazo mana,
Allah yafi mu son bayin sa duk son da muke musu, hakuri kuma shine magani nasan ki da hakuri da iya karɓar kaddara ina fata yau ma ki kasan ce a haka, kice Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kici gaba da nanata shi cikin ranki."
"Innalillahi wa'inna'ila
ihirraji'un³."
nafaɗa da karfi har sau uku dai-dai lokacin da muke sakai cikin parlour'n asibitin, Mama ta daɗa rike hannuna gam jin yan da ilahirin jikina yaɗau ki ɓari tace
"A hankali zaki faÉ—a ko a cikin ranki ki nusu HAMDAH."
muna shiga jami'a
n tsaro suka dakatar da mu suka ce mu tsaya anan, wani soja ne ya fito daga cikin wani room yakaraso in da muke yace "Zata iya shiga yanzu."
Bappa ya dube ni cikin rauni yace
"Kullu nafsin za'ikatulmaut duk mai rai mamuci ni, muma bamu da tabbacin zamu i
ya kaiwa nan da dakika É—aya, Allah yayi wa Ahmad rasuwa ki daure kiyi masa addu'a."
wani irin dimm haka naji kunnuwa na sunyi min mugun nauyi jiri haÉ—e da bakin duhuwa ya gilma min,
kallon bakin Bappa nake domin tabbatar da abun da yake faÉ—a dan ni da
i a yanayin da nake jin kaina ciki da yan da maganar tazo min a sama sai ji da gani nake kamar ba gaskiya bane, bakina kuma yayi min mugun nauyi na kasa iya furta komai.
sojan yace
"Madam bismilla sai hakuri fa."
yayi maganar yana nuna min hanya Inna Wu
ro ta mika min Ahmad karami, kana sojan yayi gaba na bisa a baya ina jan kafata da kyar.
muna isa jikin kofar room É—in ya murÉ—a handle É—in ya shiga, kana yaÉ—an ja gefe ya bani hanya na sako kai na ciki.
kana ya mai da kofar ya rufe, sojoji ne tsaitsa
ye cikin room É—in haÉ—e da likitoci,
ido na kurawa kan gadon da nake hango mutum kwance an lulluɓe shi daga sama har kasa, jikin a bun da aka lulluɓe sa da shi da ɗigo ɗigon jini tagurin kirjin sa da gefe da gefen cikin sa.
wani dake tsaye ta gurin
kansa ga dukkan alama babbane dan da zaran yayi magana sai sauran jami'an tsaron su sara masa.
ya É—aga hannu tare da yi min alama dana karaso, a hankali naja kafafu na zuwa bakin gadon, ya dube ni tare da faÉ—in
"Allah ya baki hakuri mun kira ki ne abis
a cika masa burin sa na karshe, kiyi hakuri bamusan rai zaiyi halinsa ba tun a daren jiya yanemi da a kira ki sai dai ganin halin da yake ciki yasa muka kasa iya ai watar da hakan burin mu kawai likitoci su samu nasarar kuɓutar da shi daga halin da yake,g
a wannan a hannunsa muka samu bayan cikawar sa, ko da muka duba sai muka ga a kanki yake maganar shine muka neme ki kafin mu É—aga shi a nan mu damka miki sakon sa a hannun ki."
ya mika min takarda wan da gefe da gefen takar dan duk da É—igon jini,
hannu
na na ɓari na karɓi takardan na dunkule shi cikin hannuna.
mutumin ya dubi nakusa da shi yace
"Ku buÉ—e mata shi ta gansa." ya yaye abun da aka rufe shi da shi daga kansa zuwa wuyan sa.
da gaske Ahmad ne a kwance wan da tun É—azu ban gaskata abun da
suke faÉ—a min ba sai gani nake kamar ba gaskiya bane.
wani irin tsalle zuciya ta yayi tamkar zai faso kirji na yafito,yayin da ilahirin jiki na ya ɗauki ɓari.
a hankali nashiga jan kafata ina daÉ—a matsowa bakin gadon yayin da idanuna ke kan fuskarsa
, yana kwance idanunsa a rufe yayin da fuskarsa ke bayyane da kayataccen murmushin sa, tam kar akirasa ya amsa.
kai na shiga girgizawa nashiga kokarin motsa laɓɓa na, na mika hannu izuwa jikin sa, nashiga girgiza shi tare da sakin kuka mai taɓa zuciya
cikin muryar kuka sosai tamkar numfashi na zai fita nashiga faÉ—in
"My bana son irin wannan wasan!, My kafarka dan Allah kadai da min irin wannan wasan,ka tashi mana nice fa gimbiyar ka kyakkyawar ka, ka tashi ka gani gani ga Ahmad É—an ka É—an da ka far
a samu a duniya, shin ka mance alkawarin da ka min da bakin ka kace min bazaka taɓa bari nakara yin kuka ba, kar kayi min haka kar ka tafi ka barmu dan Allah My dan Allah ka tashi so kake Ahmad ya zamo maraya, ka buɗe idanun ka ka faɗa min kalmar da kak
e faÉ—a min kullum kana sona nima ina son ka My ina sonka ina sonka My, My ka tashiiiiiiiii kar ka mutu dan Allahhhhhhhhh!!!."
kuka yaci karfi na sai kawai na kife kansa tare da É—aura Ahmad karami a kansa na saka fuskata kan nashi nashiga goga fuskata ci
kin nashi ina wani irin kukan danake jin ina ma ace yanzu nima na mutu na bishi, Ahmad karami ya saki kuka yana cakumar sa...
mutumin da ya sa aka buÉ—e min shi ya girgiza kai tare da share kwalla, kana yace
"I'm so sorry Madam hakika muma munji É—acin r
asa gwarzon jami'in sirri kamar Ahmad, sai dai abun farin ciki duk da bulet har uku da suka same sa a gurare daban-daban wan da ko da ace harbi ɗaya ne bazai iya taɓuka komai ba, amma da bulet ɗin a jikin sa ya kashe mutane biyar yayi wa biyu mummunar
raunin da bazasu iya morar raruwar su ba, hakika wannan abun alfahari ne, Allah ya baki hakuri."
sukace na tashi a É—aga shi fir naki sai ma daÉ—a kankame shi da nayi.
da kyar babban sun ya iya janye ni a jikin sa,ina mike wa a jikin sa sai ji nayi tamka
r an fisgo ni sai kawai na yanki jiki na zube a gurin nan take hankali na yabar jiki na ban kuma sanin abun da ake ciki ba....
After 5 hr.
Sai a lokacin na farka daga doguwar sumar dana tafi,
a hankali nashiga buÉ—e idananuna dasuka yi min
mugun nauyi, maganar Ummi na najiyo a kusa da ni, da sauri na yunkura zan mike, Ummi tayi saurin rike ni tana faÉ—in
"Yi a hankali HAMDAH."
nace "Ummi ni tashi zanyi." Mamie dake zaune a gefe da waya a kunnen ta tana faÉ—in
"Mun iso sai dai har yanzu
bata farfaÉ—o ba."
sai kuma tayi saurin kashe wayar ta mike tazo ta rike ni tana faÉ—in "Zaki iya tashi?."
kai na gyaÉ—a, tace "To tashi." suka taimaka min na mike zaune,
kokarin durowa a gadon nake Ummi tace
"Da kata HAMDAH ina zaki ko fisari kike ji?
."
kuka na fashe da shi nace
"Ni gun Ahmad zan je." hawaye Ummi ta share Mamie tace "Kiyi hakuri HAMDAH, ki tsaya ki daÉ—a samin sauki tukun."
kai na shiga girgiza wa ina faÉ—in "A'a ni gurin sa zanje ni dai zanje."
duk yan da suka kai da lallaɓi na f
ir naji nace nidai gurin sa zani, haka suka hakura suka kyale ni.
na sauko a gadon da gudu nafita a room É—in, nashiga waige-waige room É—in da aka kwantar da Ahmad na nufa a guje na tura kofar na shiga, turus nayi cikin É—akin ganin babu kowa ciki. sai k
uma na juya a guje tare da kuka sakin kuka nayi,
su Ummi da suka biyo baya na suka ruko ni.
Mamie ta rike ni gam tana faÉ—in
"Ki nutsu HAMDAH." nace "Ni gida zan tafi an mai da Ahmad gida nidai gida zanje."
Su Mama Inna Wuro Ummi Mamie duk kanin su ha
waye suke cike da matukar tausaya min, Ahmad karami na goye a bayan Mama yana bacci sai sauke ajiyar zuciya yake.
Mamie tace "To muje gidan...
ko da muka iso gida direba na dai-dai ta parking na fito da gudu nayo cikin side É—i na,tun daga parlour'n kasa
nake faÉ—in
"My kana ina My kadawo gida ko."
har na haura sama ban fasa kiran sa ba, na shige bedroom ina ta waige-waige.
Ummi data biyo baya na da sauri ta ruko ni tana faÉ—in
"HAMDAH kidawo cikin hayyacin ki, ki nutsu kiji ni, Ahmad ya rasu mutuwa k
uma ba karya bace, yanzu addu'a kaÉ—ai yake bukata shi da ma yayi kyakkyawar tafiya ki nutsu ki sawa zuciyar ki salama ki fauwalawa Allah komai, hakika akwai ciwo amma ki daure, ki daure jin Æ´ata Æ´ar albarka Allah ya baki ikon cin jarabawar ki."
"Ummi y
anzu shima ya tafi kenan bazan sake ganin sa ba kenan Kamar Inna."
kwai Ummi ta shiga girgiza wa tana kwalla.
rungume Ummi nayi tare da sakin wani irin kuka, bata hanani yin kukan ba sai bubbuga bayana da take itama tana kwalla.
su Mama suka janye ni a
jikin ta suka zaunar dani bakin gado na zube a gadon ina mai ci gaba da rusar kukan..
Basu hanani kukan ba sai da nayi sosai kafin suka fara rarrashi na, da ban baki har nayi shiru,sukayi ta bani baki haÉ—e da nasihohi nidai ina nan zaune amma hankali
na baya gurin, nan Ummi suke shaida min tare suka zo da su Abbu suna gidan Ahmad can in da ake zaman makoki...
Bayan kwana uku..........!
Mommyn Twin ce
8/19/22, 11:01 - Ummi Tandama😇: 37
Haka zan rungume Ahmad karami na
ta kuka cike da tausayin sa da kuma tausayin kaina,sai Mamie ko Ummi sun karɓe sa, tun ranar da Ahmad ya rasu Ahmad karami yaki shan nono,
Ummi tace a É—aga shi kawai a nonon tun da ya makai na yaye...
A ko da yaushe su Ummi suna tare da ni basa taɓa b
arina na zauna ni kaÉ—ai,yau su Aunty Rafee'ta suka zo ita da Aunty Jaleela da Ya Masa'ud da Goggo Hauwa,
da yamma suka É—unguma suka je gidan Ahmad domin yi wa Æ´an uwan sa da Aunty Rasheedat ta'aziyya har da su Mamie.
kamar yadda suma Æ´an uwan nasa su
ke zuwa har dama Æ´an uwan Aunty Rasheedat domin yimin ta'aziyya.
Abba Bashir da mahaifiyar Aunty Rasheedat su tun ranar rasuwar ma suka zo nan..
tare da su Abbu su Ummi suka dawo dan yau an gama zaman makoki...
ranar bakwai da safe Alhaji Bashir da mah
aifiyar Aunty Rasheedat da ita Aunty Rasheedat É—in da wasu daga cijin dangin su, da shaidu da kuma laiyoyi, da manyan malamai suka zo.
duk kanin mu muka hallara a parlour'n kasa.
Aunty Rasheedat na rungume da Ahmad karami a jikin ta, ta kura masa ido sa
i kawai ta fashe da kuka, ni ma kukan na fashe da shi dan nasan abun da nake ji a raina itama shi take ji.
rarrashin mu akatayi tare da yi mana nasiha har sai da zuciyoyin mu suka sami salama, kana a ka soma gudanar da abin da ya taramu wato rabon gado.
duk kanin dukiyar Ahmad da kaddarorin sa na nan gida Nigeria da kuma na kasashen waje da wan da aka kashe shi domin sa wan da ya damkawa manajan banki, duk aka haÉ—o kansu.
batare da ɓata lokaci ba malamai suka fara gudanar da rabon gado kamar yadda sha
riya ya shar'anta, duk kannnin mu uku a ka dan kawa kowa abin da ya gada ni Aunty Rasheedat da kuma Ahmad karami, nayi mamakin tulin dukiya da kandarorin da Ahmad karami ya gada,
daga mahaifinsa nakuma yi mamakin tulin taren dukiya irin na Ahmad.
Washe
gari su Abba Abbu Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Ya Masa'ud suka koma Bauchi, yarage saura Ummi na,
Ummi tana iya bakin kokarin ta wajen ganin ta gusar min da damuwa ta dan ko nan da can bata matsawa koda yaushe tana tare da ni.
yanzu Mama ma ta dawo
side É—ina ita ma muna tare..
lokacin da mukayi arba'in Ummi tace zata koma gida,
washegari bayan ta gama shiri ta je sashin su Bappa bayan sun gaisa take sanar masa yau insha Allah zata koma sannan ta É—aura da faÉ—in
"Bappa ina so na tafi da HAMDAH t
adanje tayi kwana biyu."
Bappa yace
"Kwarai kuwa kinyi tunani me kyau tafiya da ita É—in shiyafi saboda acan zata zauna cikin yan'uwanta da iyayenta tunaninta zai ragu akan zamanta anan É—in, Allah yatsare yakiyaye hanya."
Ummi ta amsa da Amin...
ina
zaune dasu Naseem da Nasmah suna gefena sai rikici suke min kaman kullum Naseem daya ware baki zaiyi kuka yace "
Mommy ina Daddy kince zai dawo."
kwalla nashare nace "Naseem nace muku daddy zai dawo daddy yayi tafiya zai dawo." Nasmah tace "Mommy nikam
kikaini gun Daddy kinji Mommy."
kaina girgiza yayin da hawaye yake zuba a idona inajin yadda yaran suke bori Naseem yasaya yana fadin nikam ki kiramin Daddy, yami kamin wayata, yana ci gaba da faÉ—in na kira masa Daddy.
kuka nafashe dashi na rungume y
aran ajikina ina mai matuqar missing na Ahmad.
Ummi ce tashigo ganin ina kuka tayi saurin isowa tana faÉ—in
"HAMDAH lafiya?." kaina girgiza ina fadin "Ummi Ahmad yatafi bazan iya qiranshi a waya ba Ahmad yatafi kenan bazai dawo ba, bazan sake ganin sa
ba, suma so suke su gansa."
kuka sosai nafashe dashi Ummi ta rungume ni tana rarrashi na, kana tace na tashi nahaÉ—a kayana zamu tafi Bauchi tare, baza ta iya tafiya ta barni cikin halin da nake cikin nan ba.
babu musu namiqe danni ma nasan tafiyar
zai fi min bazan iya jure Ummi tatafi tabarni Anan ba.
ita ta tai makamin mukashirya kayanmu tasa su Talatu suka fita dasu,
gabadaya yan