Showing 81001 words to 84000 words out of 135595 words

Chapter 28 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

rigar bacci kawai na zura na haye gado.

bakin gadon y

a zo ya shafo gefen fuskata a hankali na buÉ—e idona na zuba masa yace

"Kyakkyawa ta tashi kiÉ—an ci wani abu mana zaki daÉ—a jin karfin jikin ki."

kai na girgiza a hankali na mai da idanuna na rufe, ya hayo gadon ya kwanta tare da janyo ni kijin sa, a

hankali bacci ya É—auke ni...

can cikin dare jikina yahaɗa zafi rau sai ɓari nake,ina daɗa shigewa cikin jinin sa,

da sauri yabuÉ—e idanunsa ya daÉ—a rungumo ni jin yan da jikina ya É—au zafi yamike da sauri yana faÉ—in

"Subhanalla kyakkyawa ta zazza

ɓi ne haka Innalillahi."

gaba É—aya ya ruÉ—e yarika rungume ni yana yimin sannu, ya É—ago ni yana faÉ—in

"Taso muje asibiti jikin ki yayi zafi sosai."

kaina na kwantar a kirjin sa na rirrike sa a hankali nace

"A'a dare yayi sosai kada muje zai sauka z

uwa safiya."

a ruÉ—e yace "A'a kyakkyawa ta kijin ki yayi zafi sosai muje kawai."

duk yan da yaso mu tafi naki fir.

yana zaune ina rungumo a jikin sa a haka gari ya waye.

da asuba ya kaini bayi da kansa yayi min wanka a daddafe nayi al'wala shima yayi,

bai barni na taka da kaina ba ya É—auko ni ya fito da ni,

ya shinfiÉ—a mana sallaya a zaune nayi sallar in da shi kuma ya ja mana sallar.

muna idar wa na sulale kan sallayar.

shiko da sauri ya mike yaje ya É—au wayar sa yakira family Dr su, yace yazo y

anzu yayi masa kwatancen gidan.

kana yazo ya É—aga ni a kasa ya mai dani kan gado.

batare da ɓata lokaci ba Dr ya iso, ya bada umurnin a barsa ya shigo,

har cikin parlour'n sama ya bashi umurnin shigo wa,

kana ya shigo ya saka min hijabi kan rigar bac

cin da yake jikina, ya É—ago ni ya tallafo ni jikin sa muka fito parlour, ya zaunar dani kan kujera kana shima ya zauna kusa da ni,

a hankali na kwantar da kaina jikin hannun kujera, ina jin Dr yana tambayar me ya sa me ni,

yace masa tafiya mukayi jiya m

un wuni a kan hanya,muna dawo wa shine zazzaɓi ya rufe ta.

Dr ya É—anyi rubuce-rubuce kana yaÉ—a go yace "Baza a bata magani ba sai anyi mata test." Ahmad

yace "To." kana ya dube ni yace

"Bari a ja jinin ki ayi test dan asan maganin daya dace da kisha

ki warke da wuri ko kyakkyawa ta."

yayi maganar yana É—an jan hijabin jikina ya É—an tattaro shi yaciro hannuna ya ruko hannuna.

Dr ya taso yaja jinina kana ya tafi.

in da aka ja jinin yarika mulmula min a hankali,

shiru nayi ina kwance cikin kirjin s

a, a haka bacci ya fara fizgata,

ganin haka sai ya gyara zaman sa da kyau ya gyara min kwanciya ta cikin jikin sa.

nan da nan bacci ya É—au ni...

Acikin baccin narika jin magana, a hankali na buÉ—e idanuna, maganar Dr ne ya doki kunne na

"Congratul

ations ranka shidaÉ—i an sami karuwa Madam tana É—auke da juna biyu."

wani irin waro idanuna nayi na mike zaune.

Ahmad kuwa mike wa tsaye yayi zumbur yana bin likitar da wani irin kallo mai cike da É—in bin mamaki cikin rawar murya yace

"What! mekace!?,

kasan me kake faÉ—a kuwa?."

sai kuma ya girgiza kansa sannan yace

"Kodai kunnuwa na sun jiye min ba dai-dai bane."

murmushi Dr yayi tare da mike wa tsaye takar dar dake rike a hannunsa ya mika masa yace

"Wannan shine sakamakon test É—in da mukayi, kum

a ya nuna tana É—auke da ciki, amma idan ana kokonto za'a iya zuwa wani asibiti ayi gwaji ta hanyar yin scanning domin tabbatar wa."

takardar da ya mika masa yashiga dubawa har hannunsa na ɓari, wani uban kabbara ya sake, ya juya ya dubi gabar yasulale k

asa yayi sujjada............!

Kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu kanwa ta ce tayi ɓari so dole nice na zauna a kanta na tsawon kwana ɗaya da wuni ɗaya ban sami damar hawa online ɗin bama bare na shaida muku.

Mommy

n Twins ce

8/19/22, 10:57 - Ummi Tandama😇: 26

Ya É—ago tare da É—aga hannunsa sama yace

"Ya Allah ya Ubangijin rama Allah nagode maka Nagode maka Allah, ya buwayi gagara misali ya Hayyu ya Kayyum, bana da tsumi bana da dabara maikowa mai k

omai duk kai kaÉ—ai kake da su,

haki Ubangiji na mai girma ka azirtani da abin da bana da wayo da wayo da ikon iya bawa kai na,

duk arziki na bazan iya baiwa kaina ba kai kaÉ—ai kake da ikon iya bani, Allah Nagode maka Allah na gode maka Allah Nagode ma

ka."

yakuma mai da kansa yayi sujjada,

yana mai cigaba da kwararo addu'a da kirari wa Allah.

kana ya É—ago da sauri yamike yazo ya rungume ni tsam yana faÉ—in

"Hakika HAMDAH ke alkhairi ce a gate ni, ke fitala ce mai haske duhun dayayi shekara da sheka

ru, na gode wa Allah daya mallaka min ke amatsayin mata kuma fitila ga rayuwa ta,

HAMDAH ke ta daban ce ina sonki ina sonki HAMDAH inayi miki son dayafi wanda nakewa kaina!!."

yadaÉ—a kankame ni a jikin sa.

Dr da yake tsaye yana bin mu da kallo da mur

mushin taya murya,

yayi mana sallama yace zai tafi,

ai da sauri Ahmad ya sake ni yace

ya bashi account number É—in shi, nan take yayi masa transfer É—in 3 Miliyan.

yace tukuicin sa na sanar da kyakkyawan zance mafi girma, wan da tun da yake ba'a taɓa

yi masa albishir da kamar saba.

likitar yarika murna dayi masa fatan isowar baby lafiya ya bar gidan bakin sa har kunne, bayan ya aje mana maganin da yazo da shi.

Ahmad daya kasa zaune ya kasa tsaye yara inda zai sa kansa dan farin ciki, yadube ni yana

faÉ—in

"Me kike so kyakkyawa ta me kike so a duniyar nan? kifaÉ—a min ko mene ne shi ashirye nake nayi miki shi koda zai zamo gurfaniwar dukiyar dana mallaka da dukkanin kadarori na, me kike so nayi miki tukuici

da shi? motoci gidaje kamfanoni acikin ka

sar mu ko a kasashen waje, faÉ—a min duk abin da kike bukata zanyi miki shi koma mene ne, faÉ—a min yanzu kyakkyawa ta."

kai na rausayar gefe jin kai na nadaɗa sara min a hankali cikin yanayin jin zazzaɓi nace

"Ni bana son komai wayyo kaina."

na dafe

kaina dake cigaba da sara min.

da sauri ya mike yace

"Bari na É—auko ruwa kisha magani zai dai na in sha Allah."

da sauri yaje ya É—auko gorar ruwa cikin fridge yadawo in da nake, ya tsiyaye ruwan cikin cup É—in da ya haÉ—o da shi,

kana yaÉ—au laidar

maganin ya curo su daga cikin laida, kamar yadda yagani a rubuce haka ya cicciro su.

kana ya tallafo kaina yace

"BuÉ—e bakin ki na saka miki."

da sauri na kawar da kaina yayin da naji zuciya ta ta hautsune jin warin maganin nace

"A'a zanyi amai."

yac

e "Ya ilahi bazakiyi ba, buÉ—e baki kisha ga ruwa nan kusa."

cikin zubda kwalla na girgiza masa kai da faÉ—in

"Zan yi mana kabar shi kawai zan warke a haka basai na sha magani ba."

ido ya waro da karfi ya furta

"Wane ni wlh ban isa ba, kin san kuwa za

fin zazzaɓi yana iya zubda ciki, ki tai make ni dan Allah ki ceci rayuwa ta kisha maganin nan ki samu ki warke kada ya janyo min babban asara,

na roke ki dan Allah ki sha, ki taimaka min ni kaÉ—ai iyaye na suka haifa ki tai make ni abin cikin nan yafito

lafiya, naji a raina inada jinina aduniya."

ya juyo da fuskata yace

"Sha in Allah ya yarda bazakiyi amai ba."

idona na rumtse da karfi na É—auke numfashi tare da buÉ—e baki ya zuba min maganin kana ya bisu da ruwa.

da kyar sai da nayi kamar ina yi kaf

in suka wuce.

ido na ware da karfi jin zuciya ta na wani irin tashi cikin hanzari na tallafe kansa tare da manna bakina da nashi nashiga tsotsar bakin sa.

a hankali a hankali nashiga sauke numfashi, yayin da aman yake kwanciya a hankali.

sai na lumshe i

danuna a hankali ina mai cigaba da tsotsar bakin sa,

a hankali kasan tuwar mu da Ya SALEEM a irin wannan lokacin yafara zuwar min, sai na buÉ—e idanuna da sauri a sannu na zare baki na daga nashi.

shiko ido yakura min da yanayin mamaki sai kuma ya tallaf

o kaina yana kokarin kuma haÉ—e bakin mu.

da sauri na kwace kai na na turo baki gaba,nace

"Bana ce maka zanyi amai ba."

murmushi yayi yace

"To baga shi kin mai da aman ba, zo in kara kwantar miki da shi."

kafada na make ina mai cigaba da turo baki gab

a.

da sauri ya mike cikin rawar jiki yace

"Ina zuwa bari naje na sanar wa su Bappa wannan dadda É—an albishir É—in."

ido na waro nace "A'a kada kaje."

kafin na rufe baki ma yayi gaba.

A kofar side É—in su Bappa ya haÉ—u da shi yana kokarin fita.

ganin yan da yake ta washe ba yasa Bappa faÉ—in Ahmad "Wannan farin ciki haka me ya faru."

cikin matsananciyar farin cikin daya ke jin kansa ciki yace

"Bappa Malam HAMDAH tana da ciki, yanzu likita ya tabbatar min da haka."

Bappa ya faÉ—aÉ—a fuskarsa d

a annuri yana faÉ—in

"Masha Allah Allah abin godiya alhmdllh Allah mun gode maka, kai lallai wannan abin farin ciki ne, Allah ya É—aiyiba yaraba lafiya."

Inna Wuro dake ta ciki tana jiyo duk abin da suke ciki,

tayi murmushi mai bayyana farin ciki, ta gi

rgiza kai tare da faÉ—in

"Yaran zamani kenan wai shi ya É—auki kafa yazo faÉ—ar matar sa na da ciki."

takuma yin murmushi tana faÉ—in

"Dole kayi murna Ahmad lallai wannan abin farin ciki ne."

Anan kofa kuwa Bappa yayi ta zuba musu addu'a da fatan i

sowar abin dake cikin duniya lafiya, yajuya cike da É—in bin farin ciki, shiko Bappa ya koma ciki, yana shaida wa Inna Wuro.

tayi dariya tace "Ai duk ina jin ku murna ya hana shi sukuni."

Bappa yace

"Ai dole yayi murna abune sabo a gare sa wan da ya jim

a yana sumayar sa sai gashi kwasam Allah ya ai ko masa da shi, kin ga kuwa dole farin cikin sa yagaza ɓuya."

tace "Haka ne kam lallai muma munyi farin ciki kwarai aure yayi albarka."

Bappa yace "Haka ne kuwa kwarai da gaske."

haka sukayi ta nuna farin

cikin su

da sam barka da fatan isowar baby duniya cikin koshin lafiya...

Ahmad kuwa yana juyawa daga gurin Bappa Rasheedat ya kira a waya ciki farin ciki yasanar mata,

ihun murna Rasheedat ta sake tace "Ina HAMDAH haÉ—a ni da ita dan Allah."

yace "To

bari na kai mata."

ai bata jira ya karasa maganar ba ta kashe wayar da sauri ta zari matafin ta da makullin mota tayi waje.

Ahmad yana tafiya yana daddanna wayar sa nan da nan yashiga posting wa Æ´an uwa da abokan arziki, yana faÉ—in a taya shi murna..

Ina kwance a kan kuje ra in da ya barni yadawo ya same ni,

ya karaso in da nake da sauri ya sunkuyo ya sumbaci goshi.

ido na lumshe tare da buÉ—e su a kan a hankali nace

"Yanzu kaje ka faÉ—a musun ne?."

baki ya washe yace

"Eh mana ai dole duk wani

wan da ya sanni yasan wannan labarin."

ya zauna ta gurin kafafu na kana ya É—ago kafafun nawa ya É—aura su kan cinyar sa, a hankali yashiga matse su.

yana faÉ—in

"Sannu kinji kyakkyawa ta baki dai kin ciwon ciki ko?, iya ciwon kanne kaÉ—ai?."

ban tank

a shiba sai lumshe idanuna danayi..

kira yayi ta shigo wa wayar sa yana É—agawa yana faÉ—in yagode yagode, gaba É—aya bakinsa yaki rufuwa...

Acikin Æ´an mintina Rasheedat ta iso gidan tana haurowa parlour'n sama ta taho da gudu ta rungume ni daga kwanc

en da nake, cikin sananin farin ciki tace

"HAMDAH kai sannun ki da kokari ashe dai zamuga jinin mu Allah ya fito mana da shi lafiya."

ta mike ta sauri ta rungume ta Ahmad tana fadin

"Aboki wayyo Allah narasa yadda zan sa kaina dan farin ciki,

tabbas

yau ya daÉ—a yarda Allah bai mance da mu ba."

dariya yayi yana daÉ—a rungume ta a jikin sa yace

"Kwarai kuwa Kawa Allah baya bacci."

Haka suka yi ta nuna farin cikin su kamar zasu saka ni cikin jikin su.

suka rika tambaya ta me nake so, Aunty Rashee

dat tace me nake jin kwaÉ—a yin sa ta dafa min. nace ba komai.

kan kace me labari ya karaÉ—e yan uwa da abokan arziki.

ranar wuni Aunty Rasheedat tayi a gidan sai dare ta koma.

washegari

washegari da sassafe Ahmad yaje gidan su,

yau Æ´an gidan sun sha

mamakin ganin yan da yashigo da farara hatta Sakeenat yau sai da ya amsa gaisuwar ta.

É—akin Hajiya Karima ya shige, tana ganin sa ta faÉ—a fuskar ta da murumshi.

ya nimi guri ya zauna bayan sun gaisa ya dube ta fuska É—auke da masananciyar farin ciki

yace "Hajiya wani albishir nazo miki da shi."

zama Hajiya Karima ta gyara ta washe baki tana faÉ—in

"To Ahmadu ɗan Sabil na bada goron kar ɓar albashir fari soll."

yace "Hajiya HAMDAH nada ciki Hajiya ashe nima zan haihu?."

wani irin zabura Hajiya Ka

rima tayi, sai da ta zamo bakin kujera ta buga kirji ta waro ido tare da faÉ—in

"Me ne ciki!!?." wani irin murmushu yayi mai kunshe da ma'anoni daban-daban kana yace Hajiya kema kin ji abin a bazata ko? ai nima haka naji abin kamar almara."

dariyar yake

tayi sai kuma ta kama kame-kame tashiga faÉ—in

"La..laa..ikon..Ikon.. Allah...to ciki..

ciki, kai masha Allah lallai kuwa wannan shine bazata bayan fidda rai ga samu sai ga samun kuma, kai amma nayi farin ciki naji daÉ—i sosai, ashe zanga jika na, kai A

llah yayi albarka yaraba lafiya, Eh Allah ya raba lafiya."

"Amin amin." yafaÉ—a yana mike wa tsaye yace

"To Hajiya ni zan koma."

tace "To a gaida gida a gai da min me cikin."

yace to kana ya sa kai ya fita..

yana fita Hajiya Karima ta saki wani uban a

jiyar zuciya tabigi kirji tace

"Tabɗijam ciki!? kenan hakan na nufi Ahmad zai haihu yasami magajin dukiyar sa, wato wannan shigiyar yarin yar tana kokarin zuguza min shiri shine har da yin ciki, bayan ban taɓa kawo hakan cikin lissafi na ba, nasawa rain

a bazai haihuwa ba shine zata zo ta yi kokarin haihuwa masa, ina bazai yiwu ba da sakel wlh!...."

Acan cikin garin Bauchi



Abba ne da Ummi tafe cikin mota a hanyar su na komawa gida bayan dawo war su daga asibiti dubiyar wata Æ´ar uwar Ummi da ba

lafiya,

suka biya ta gidan mai domin su sha mai,

tun daga farkon shiga gidan man layi ne har cikin gidan man,

Abba da yake kokarin sako kan motar sa cikin gidan man yaÉ—an yi jim yana bin layin da ido.

Ummi tace "Abba'n Fauzan wannan layin idan muka s

higa ai sai mukai kisan dare ma layin bai iso kan mu ba, duba fa gamasu garaku da suke acikin motoci sannan ga su motocin kansu, yaushe za'a basu har a bamu."

Abba yace

"Gaskiya kam bari mu koma gida kawai nasa direba yafito ya sha man ko ba a nan ba, t

un safe ake layin nan motoci sai daɗa zuwa suke zamu ɓata lokaci kam muje gida kawai."

Ummi tace "To in ban da mutane ma ga wasu gidajen mai da yawa waÉ—an da naga babu ko layi wasu bai fi mota biyu zuwa uku ba, baza su je can susha man ba sai suzo nan

suyi tayin layi haka."

Abba yace "To ai sauki ake so shiyasa ake wa gidan man layi, ai ba nan kaÉ—ai ba idan da zaki zaga garin nan kiga gidan mai me irin sunan wannan gidan man zakiga layi kamar haka koma fin haka,

man su na da sauki sosai kuma litar su

na da kyau,

an ce wai mai gida jen man ne tace a rika sai da shi a farashin da yanzu suke sai dawar shiyasa duk gidajen man ta zakiga irin wannan layin."

kai Ummi ta jinjina ta É—aga kan ta tana duban sunan gidan man. tace

"*HAM'NAS CO PETROLEUM NIGER

IA LIMITED* wato mace ce mai gidan man?".

Abba daya juya akalar tafiyar tasu izuwa gida yace "Eh mace ce."

tace "Lallai tayi kokari Allah yasaka mata."

Abba ya amsa da amin amin.

suna isa gida motar SALEEM na shigo wa, w kusan tare sukayi parkin suka f

ito,

ya tako ya zo in da suke ya shiga gaida su,

suka amsa cike da kuwala Ummi taÉ—an zuba masa ido nan da nan ta hango Æ´ar karamar ramar da yayi, ta dube shi da kyau sannan tace

"SALEEM baka da lafiya ne kam?."

kai ya girgiza batare da yayi magana ba

.

tace "Ai ho nazaci baka da lafiya ne dan naga kaÉ—an faÉ—a kaÉ—an."

Abba yace

"Wata kila hidimar office ce ta sashi a gaba kin san shima yana sa haka idan ka rasa nitsuwar ka."

Ummi tace "Haka ne Allah yasa mu dace."

suna nan tsaye motar Abbu yashi

gidan, koda ya gyara parking yafito duk kanin su gaishe sa sukayi ya amsa, in da ya amsa gaisuwar SALEEM a sama-sama kana yayi gaba Abba ya bi bayan sa.

SALEEM kuwa motar sa ya shige yabar idan, Ummi kuma ta wuce side É—in ta.

Parlour'n da su Abbu suk

e zama suÉ—an tattauna nan suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login