Showing 54001 words to 57000 words out of 135595 words

Chapter 19 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

guda biyar suka shigo gidan masu É—auke da tambarin sunan Company'n Ahmad Sabil.

duk kanin su shake suke ta

m-tam da kaya.

shigar su ke da wuya kira ta shigo wayata, koda na duba mai kiran ganin bakuwar lamba ce, kamar bazan daga ba sai da kiran takusa yanke wa kafin na É—aga da sallama, daga cikin wayar numfashi naji an sauke kana daga bisani a ka soma magana

"Kyakkyawa ta barka da safiya inad fata kina cikin koshin lafiya ke da yarana gaba É—aya."

Shiru nayi batare da na amsa shiba sai murguÉ—a bakin da nayi kamar yana kallo na. yacigaba da faÉ—in

"Ga ba'i a waje suna niman izinin shiga."

kashe wayar nayi

ina kunkuni kasa-kasa "To ina ruwa da an hana ba'in shiga ne ko kuma wani sabon sai da hali ne."

Aunty Nusaiba dake kusa da ni tafube ni tana faÉ—in

"Wasu ba'i kuma?." baki na turo gaba nace "Wai wannan Ahmad É—in ne wai wani wai ga ba'i a waje ko da an

hana su shiga ne da zai wani kira yana faÉ—a wa mitane."

tace "A'a kodai motocin da yanzu naji shigar sun nan ne naga mutane tsaye a jikin motar wata kila sune ba'in to ace su shigo mana."

Faty tashiga kwallawa kira Faty dake É—akin su Naseem tafito par

lour da sauri tace

"Yi sauri kije kicewa mutanen da suke wajen nan su shigo sai ki sauke su a parlour'n kasa."

tace To,

jim kaÉ—an ta dawo tace sun shigo suna parlour, Aunty Nusaiba ta sauka taje ta same su.

bajimawa ta dawo tace min

"Masu ai ki ne w

ai Ahmad Sabil ne ya turo su wai zasu fita da kayan cikin side É—in nan su shigo da wasu."

kafin nace wani abu Hajiya Rahama tace

"To bismilla su fara mana, sai su fara daga kasan idan suka gama sai a koma kasan a basu guri su gyara nan É—in."

tace "To

haka ko za'ayi." ta juya ta koma domin sanar musu.

a raina nake faÉ—in

"Kamar wani an sashi ni shishshigi ne bana so."

Batare da ɓata lokaci ba ma'aikatan da suka kai wajen rai goma dukan su maza ne suka fara gudanar da ai kin su,

kan kace me sun

gama kwashe kayan cikin parlour'n kasa, kama daga kujerun cikin parlour'n, bed and bedside drow dressing mirror wardrobe dake cikin bedrooms É—in parlour'n, zuwa kayan kitchen and dinning.

kaf sukayi waje dasu suka jibge su cikin É—aya side É—in cikin gi

dan da bakowa ciki.

nan suka rinka shiga da kayan da suka zo dasu a mota suna shirya komai yan da ya kamata.

zuwa karfe 1 sun kammala komai sun shirya komai a inda ya kamata.

nan suka bukaci haurawa sama domin cigaba da aikinsu, muka dawo kasan muka bas

u guri.

lokacin dana sauko kasa sai nazamo Æ´ar kallo tamkar ba parlour na dana sani ba abun ba'a cewa komai tsaruwar sa ya wuci misali, kowa sai tabawa da sam barka yake....

Sai wajen yamma suka gama kammala komai sukayi mana sallama suka tafi.

abi

n kamar karya nake ganin shi sai daÉ—a zamowa gaske yake,ana gobe É—aura aure Ahmad yaki rani lokacin ana yimin lalle, naki É—agawa sai da yayi min missed call biyar kafin na É—aga, yace

"Madam gani na shigo fito muje asibiti a bincika miki lafiya ta."

"Meye damuwa ta da lafiyar ka."

nafaÉ—a tare da kashe wayar.

ina kallon wani kiran nasa na kuma shiga haka naki É—agawa, ga haushin lallen da aka bi aka dame ni da shi nifa in da anbi tanawa da duk waÉ—an nan fidda ficen da an barsu.

tsaki naja jin wan

i kiran ya kuma shigowa a fusace na É—ago wayar niyyata na gaya masa magana idan bai dai na dami na ba,

sai naga number Bappa ne ya bayyana kan Screen É—in wayar, da sauri naÉ—aga wayar tare da yin sallama Bappa yace

"HAMDAH fito kuje asibiti ga Ahmad na

jiran ki, kinsan yanzu ba ayin aure sai da gwajin lafiya kuje ku gwada lafiyar ku sabo da sai da shi

yanzu ake yin aure, kafin a É—aura aure gobe dole sai an bukaci takardar shaidar ingancin lafiyar ku wan da yafito daga hannun likita."

nace "Bappa lall

e ake min kuma yanzu akayi bai bushe ba."

yace "To bari ace yatafi in yaso anjima sai ya dawo."

To na amsa da shi a takaice...

Sai bayan sallar la'asar kafin lallen yabushe aka wanke, duk nabi na gaji, a gabiye na faÉ—a cikin bedroom É—ina, nashige

cikin bayi domin yin wanka nakuma gyara jiki na, dan naji alamar zuwan al'ada ta. shi yasa nace wa Hajiya Lubabatu zanje É—aki na na É—an watsa ruwa acan na huta dan nagaji da yawa,

ina gama kimsa jikina nafito, gaban mirror na zauna nasoma shafa haÉ—in m

ayuka masu daÉ—in kamshi data haÉ—a min.

waya ta ce tashiga ruri ganin mai kiran yasa nayi banza, yayi ta kira yafi a kirga ban É—aga ba.

knocking akayi tare da yin

sallama daga bakin kofa, jin muryar Faty ce yasa nace tashigo.

tace "Adda HAMDAH wai k

izo inji Yaya Ahmad."

fuska na ɓata nace "Kice bazan zo ba."

har takai bakin kofa nace "Bappa na gida ne?." tace "Eh." nace "Kice masa ina zuwa."

ta amsa da to tayi waje.

tsaki naja a fili nace

"Wlh badun kada Bappa yace naraina sa ba Allah da ba abi

n da zaisa naje."

sai da nagama iya yanga ta kafin nasaka kaya nafito ina gyara mayafin kaina, su Nasmah na ganina suka biyo ni da gudu suna faÉ—in "Mommy damu biki." Aunty Nasiba dake parlour'n kasa tana tare da masu aiki suna ta shirya abinci, nace mata

zamuje asibiti tace "A dawo lafiya Allah ya tsare."

nace "Amin." nayi waje su Naseem suka biyo ni suna cigaba da faÉ—in zasu bini..

Yana zaune a mota yana ganin mu tun kan mukaro ya fito acikin motar.

ihun murna yaran suka sake sukayi gurin sa a guj

e suna faÉ—in

"Laa Daddy yazo oyoyo Daddy." ya buÉ—e hannun sa suka faÉ—o jikin sa ya rungume su yana dariya tare da bin ko wannen su da sumbata.

na karaso gurin fuska ta É—aure tamau, yasake yaran yana faÉ—in

"Kuzo mu buÉ—e wa Madam mota kada ta gaji

da tsayu." yazaga É—aya barin ya buÉ—e yadube ni dakyau sannan yace

"Kyakkyawa ta bismilla taho ki shiga." yayi maganar tare da nuna min hanya da hannu yayin da É—aya hannun sa ke rike da marfin motar.

fuska na yamutsa namatso jikin marfin motar, ganin y

ana tsaye daf da in da zanbi nashiga cikin motar, sai na ja natsaya tare da naÉ—e hannaye na a kirji.

murmushi ya yi kana yaɗan ja da baya kaɗan tare da faɗin "Bismillah Madam." baki na taɓe nashige cikin motar da bismilla. yamai da marfin ya rufe.

t

uni su Naseem sun shige gidan baya sai tsalle-tsalle suke. yazaga gefen direba ya shiga ya ja motar a hankali yayi hon mai gadi ya buÉ—e get yasa kai yafita a hankali.

A hankali yake tukin kamar mai tautsayin kasa, yayin da su Nasmah keta zuba masa suru

tu yana biye musu, lokaci zuwa sai ya juyo ya kalle ni, niko na ɓata rai nayi kamar bana cikin motar.

sai da naji ya gyara parking kafin na É—ago, *HAM'NAS* International Hospital na ganmu ciki.

maganar sa najiyo yana faÉ—in

"Mushiga kyakkyawa ta ko na

sauko na buÉ—e miki ne?."

tun kan yarufe baki nayi saurin ɓalle marfin motar nafita ina jan karamar tsaki........!

Mommyn Twins ce

8/19/22, 10:56 - Ummi Tandama😇: *HMDH*

*WASA FARIN GIRKI*

*NA*

*RASHEEDAT S DIRECTOR

17

Yace "Hajiya za'a É—auko ta amma ba yauba sai bayan É—an wani lokaci."

Hajiyar takarkata baki tana faÉ—in

"Aure jibge kayi ne? yo in ba haka ba ace duk girman gidan nan ba rashin É—aki ba ba komai ba, kayi aure kabar matar ka wani waje bazaka haÉ—a

kan iyalen ka guri guda ba, ko gimbiyar taka ta hanaka kawota gidan ne?."

yace "Hajiya ita kuma meye nata a ciki, ai in da wan da yake son auren nan ma to bayan ta ne, wani É—an karamin dalili ne kawai yasa yau baza a É—auko ta ba."

tace "Eh ai dama ita

bata laifi badai ta yi sake an yi auren ba ai wayon ta ya kare."

Murmushi Rasheedat data sako kanta cikin É—akin ta sake dan duk abin da suke a kan kunnen ta,ba farau bane hakan gun Hajiya da dangin ta, a koda yaushe gani suke ta mallake shi sai abin da t

ace zaiyi, ko wannan auren ma dasuka jishi lokaci guda sunyi matukar murna acewar su yanzu ne zai auri mata ita kam itace mijin shine matar,duk da dai bahaka suka so ba sai dai babu in da suka iya haushi da sanar Rasheedat shi yasa su yin murnar auren nasa

. gani suke ta gama mallake sa sai abin da ta ce tahana wasu shigowa suci arziki, ita ba haihuwa ba, Hajiya Karima itace Uwar gidan Alhaji Tijjani Sabil wato mahaifin Ahmad, wacce yanzu yake kallon ta a matsayin uwa,

tun kafin ya auri Rasheedat Hajiya Kar

ima taso haÉ—a shi da É—iyar kanin ta wacce take hannun ta suna tare duka da Rasheedat É—in a gidan mai suna Sakeenat, yaki amin cewa yace sai Æ´ar uwar sa ta jini,

duk yan da Hajiya Karima takai ga shiga da fitan ta haka Ahmad yaki sam yake kuma Allah ba

i bata ikon juya shi ba.

karshe dai haka ta hakura badun taso ba, a ɓangaren Sakeenat ma kuwa tana son Ahmad kamar tayi yaya har kuma gobe tana son sa, sabo da shi taki zaman auren da aka mata ko yanzu da take zawarci tana fata da burin mallakar Ahmad, s

ai dai abune mai wuya dan ko gaisuwar ta baya amsawa...

Rasheedat

ta karaso cikin É—akin ta dire babban tray da aka shirya musu abincin su ciki, kana tayi musu barka da warhaka, a yatsine hajiya Karima ta amsa bai dame ta ba tana dago wa suka haÉ—a ido d

a Ahmad suka sakarwa junan su murmushi.

kana tayi waje.

wayar sa ce tayi kara ya É—aga kiran sannan ya mike yafita.

Da sauri ya bi bayan Rasheedat dake kokarin shiga corridor dazai sadata da side É—in ta, ya ruko hannun ta ya janyo ta sukayi gefen s

a suka shige cikin bedroom É—in sa, suna shiga É—akin ya janyo ta jikin sa ya rungume tare da marairaice murya ya ce

"Wash Kawa nagaji." gemun sa ta ja tace "To yau dai bazan ce ma sannu ba dan yau rana ce ta musamman gajiya dole."

fuska ya marairaice ya

ce "Haka zakice?." tace "Haka na faÉ—a, muje na tayaka wanka kanwata nazaman jiran ka, dan kasan dai kai zakaje ba dai ita tazo ba."

murmushi yayi tare da shafo gefen fuskanta yace

"Hukuncin da aka yanke min kenan?."

tace "Har ya zartu ma kuwa."

a tar

e suka saki dariya, nan tashiga taimaka masa yarage kayan jikin sa kana suka faÉ—a bayi, ta taimaka masa yayi wanka kana suka fito, nan ma ta tayashi sa kaya sannan ta bisa da turaruka masu daÉ—in kamshi.

gaban wardrobe ta isa ta buÉ—e ta ciro jaka mai É—

an girma sannan ta rufe ta buÉ—e É—aya gefen tashiga ciro kaya tana zubawa cikin jakar,

ido ya zuba mata ganin yan da take aikin zuba kaya cikin jakar yace

"Kawa ina za'a kai kayan kuma?."

bata bashi amsa ba har sai da ta cika jakar tam da kaya kafin ta

juyo ta dube shi tace

"Ina zuwa." ta fita jim kaÉ—an ta dawo da mayafi a kanta

ta ruko hannun sa tare da faÉ—in

"Taso muje na raka ka duba kagani har karfe 11 saura."

yace "Kawa ina kuma?." tace "Ina kuwa in ba gidan HAMDAH ba ko kasan cewa lokacin ta

kake shiga, yanzu haka tana can tana zaman jiran ka."

ido yaÉ—an waro yace "Shine da wannan katuwar jakar kamar wan da ake kori na."

tace "Eh ayau kam kusan haka din ne."

Ta janyo hannun sa tare da É—aukar jakar sukabi ta kofar baya,É—aya daga ciki

n motacin sa suka shiga ya jasu a hankali suka fita.

a hanya ta sashi ya tsaya ya siya gasassun kaji kafin suka wuce.

suna isa bakin get din gidan yayi hon masu gadi suka buÉ—e masa, yakusa hancin motar ciki yana dai-dai ta parking suka fito a tare, tan

a rike da jakarsa inda shi ke rike da laidar gasassun kajin da suka tsiya, suka nufi side É—in.

Sauko wata kenan daga sama yunwa ta dame ni dan wunin ranar yau bansa komai a ciki na ba,

na shige kitchen nashiga bude buÉ—e ko zan ga abin da zan sawa cikin

a,

wani kula na buÉ—e mai É—auke da tuwon farar shinkafa mai É—ume, na É—au plt na saka laida É—aya, kana na buÉ—e É—aya kular dana gani a kusa dashi, miyar agushi ne daya ji busashshen kifi da hanta na zuba akai kana nafito parlour na zauna nasoma ciki.

knocking É—in kofa akayi har sau uku akai-akai, ido naÉ—a zubawa kofar da tunanin mai buka kofar da daddaren nan, nai tunanin ko su Talatu ne, na mike a sannu na isa jikin kofar na murza key É—in tare da buÉ—o kofar.

da É—an mamaki na kalli waÉ—an da ke

bakin kofar, Rasheedat ta saki murmushi da faÉ—in

"Kada ace bacci kike muka taso ki?."

murmushin yake namayar mata ganin yanda take ta yimin magana cikin fara'a.

shiko na tsaye bai yi magana ba amma idanunsa a kaina, ganin yan da ya kafe ni da mayatattu

n idanun nan nasa sai na saki kofar najuya na koma ciki.

suka biyo bayana, zama sukayi kan kujera in da nikuma na zauna kan hannun kujerar da ke can karshe ina zaman jiran jin abin da ya kawo su da daddaren nan.

Rasheedat ta dube ni fuska É—auke da annur

i tace

"Narako sa ne da kaina na baki hakurin rashin zuwan sa da wuri wlh ba'i ne sukayi yawa sai a hankali, gashi nan na kawo miki shi da fatan za'a kula da shi yanda ya kamata,

to ni bari naje dare yana daÉ—e yi sai da safen ku Allah ya tashe mu lafiya

."

ta mike tare da duban Ahmad tace

"Aboki bani makullin motar na koma."

ido ya waro yace "A daren nan zaki fita ke kaÉ—ai? bazai yuwu ba bari nasa a maida ki."

murmushi tayi tana karɓar key ɗin a hannun sa tace "Babu abin da zai faru da yardar Allah

Allah zai tsare, ka mai da ni karamar yarin yace nifa yanzu na girma."

ta kashe masa ido tana kokarin juyawa ta tafi.

nayi saurin mikewa tare da dakatar da ita ta hanyar faÉ—in

"Da kin tsaya kin koma da shi da zai fi muku."

ina kaiwa nan na juya na ha

ye sama...

Rasheedat tayi murmushi tare da dafa kafaÉ—an sa tace "Aboki katashi ka bita ka shawo kanta, kasan amarya sai da lallami."

kai ya jinjina yaruko hannayen ta duka biyu yayi kiss É—in su, kana ya lumshe idanun sa tare da buÉ—e su a lokaci guda

,

ya mike tsaye yace

"Muje a maida ki gida hankali na zaifi kwanciya."

koda suka fita É—aya daga cikin security gidan ya umurce sa daya mai da ita gida, yana tsaye saida yaga fitar su kafin ya koma ciki.

yana shiga ya rufe kofar side É—in kana ya haur

a sama. yana kusa kansa cikin parlour'n sama,

idanunsa ya lumshe tare da jan numfashi ya shaki daddaÉ—an kamshi mai sanyi da rasa zuciya, a hankali ya buÉ—e idon nasa cikin kayataccen parlour'n a fili ya furta "Masha Allah."

a sannu yafara taka kafafun s

a cikin parlour'n yayin da yake rarraba idanunsa ga kofofin bedroom's É—in da ke cikin parlour'n,

a sannu ya nufi wasu kofafin bedroom's

guda biyu wan da suke a jere, yasaka hannun sa jikin É—aya kofar ya murÉ—a a hankali ya tura kofar, ya kusa kansa cik

i.

can ya hangi su Naseem kan gado suna baccin su cikin kwanciyar hankali,

murmushi ya sake a hankali ya karasa shiga cikin É—akin a bakin gado ya zauna yashafi gefen fuskar ko wannen su yana binsu da murmushi kamar waÉ—an da idanun su biya, kana ya mike

ya daÉ—a jan bargo ya rufe musu jiki, yafita ya ja musu kofar.

numfashi ya sauke lokacin da yamaso jikin É—aya kofar da ke kusa da bedroom É—in su ya tura kofar ya leko kansa ciki,

babu kowa cikin É—akin sai dai a gyare yake tsaf-tsaf gadon cikin É—akin

yasha shinfi É—akin sai kamshi yake tashi, shakar kamshin yayi yana mai jin daÉ—in kalar kamshin da side É—in gaba É—aya yakeyi, kuma ko wani bedroom da kalar kamshin da yake tashi.

mai da kofar yayi ya rufe ya juyo ya zuba wa É—aya kofar dake can gefe i

ta kaÉ—ai ido.

a sannu ya taka izuwa jikin kofar, sai kuma ya ja ya tsaya na Æ´an dakiku kana a hankali ya kai hannun sa jikin handle É—in kofar a hankali ya murÉ—a ya tura kofar a sannu ya kusa kansa ciki.

wani irin dogon numfashi yaja yana mai shakar

daddaÉ—an kamshin daya bigi hancin sa...

firgit na mike zaune jin an turo kofa, cike da mamaki nake kallon sa yana tsaye idanun sa a lumshe a sannu yaware idanun nasa a kaina.

A hankali ya soma takowa cikin É—akin, ina ganin haka na yi saurin zamowa ba

kin gadon ina binsa da kallon tuhuma, gani ya dumfaroni gadan-gadan yasani mikewa da sauri nace

"Meya kawo ka cikin É—aki na?, ka ketare tun daga kasa ka hauro sama kashigo min har cikin É—aki?."

sai da ya matso daf dani kafin yasoma magana

"Hurimi iko

mallaki, duk na haÉ—a yau, babu wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login