Showing 93001 words to 96000 words out of 135595 words

Chapter 32 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

taro ta, muka rungume juna muna ihun murna.

ranar kusan kwana muka yi muna hira...

Washegari tun sassafe Hajiya Rahama tazo da me makeup dan jiya mun yi waya da ita, bayan nayi wanka na zauna a ka shiga tsantsara min kwal

liya,

ana gamawa nasa Ukhtee ta zaɓo min ɗaya saga cin kayan da jiya Ahmad ya kawo min, na saka na zauna me kwalliyar tashiga naɗe min ɗankwalin kayan a kai tana gama ɗaurin, aka miko min takalli da ɗan madaidaicin pos wan da suma acikin akwatin aka

ciro su, nasaka takalmin narike pos É—in a hannu sai É—an karamin gyale wan da aka rataya min shi a hannu,

karfe 11 da minti goma a ka gama yimin komai, kowa ya tsaya kallo na kamar basu taɓa ganina ba, sai faɗi suke Masha Allah. Aunty Nasiba da Faty

da Ukhtee sai hotuna suke ta yimin.

hannu na wacce tayi min makeup É—in ta ruko muka tako gaban mirror mirror'n tayi min nuni da shi tare da faÉ—in

"Bismilla." ina sauke idanuna kan mirror sai da naÉ—an girgiza, sosai na kure kaina da kallo ta cikin mirr

or.

sai nake gani kamar ba ni bace, "Masha Allah." nafaÉ—a a kasan raina, ni kai na nasan nayi kyau ba na wasa ba.

kiran Ahmad ne ya shigo waya ta na É—aga yace

"Ki fito gani a waje time yayi fa har yaÉ—an go mun bar mutane acan."

nace to, nayi wa Ukht

ee magana da larabci kan ta karɓi Ahmad karami dake nannun Hajiya Rahama wan da shima aka shirya sa cikin kayan alfarma wan da ɗazu Aunty Rasheedat ta aiko dashi tace a sa masa.

muka fito gaba É—ayan mu, tsayuwa nayi ina kallon kayan dake tare cikin par

lour Inna Wuro da wasu ba'ki suna zaune suna kallon kayan, nan Inna Wuro take faÉ—a min dangin Ahmad ne suka kawo.

nace mata zamu tafi gurin taron ne ko zata je, tace min a'a ita kam tana gida.

wasu daga cikin mutanen cikin parlour'n suka mike suka ce su

ma zasu.

a parlour'n kasa na iske mutane tam wasu ma ban san su ba.

nan muka É—unguma mukayi waje.

motoci ne ajere a tsakar gidan da suka kai guda goma,

motar sakiya an bita da wani kalliyan furanni ta sama da gefe-gefen ta, kuma kaf cikin su rafi kowa

ni mota kyau.

da sauri wani soja dake tsaye jikin motar ya buÉ—e marfin gidan baya, can na hango Ahmad yana leko ni.

a hankali na karaso jikin motar, da sauri sojan yayi baya ya daÉ—a buÉ—e marfin motar, a sannu na shiga nayi wa Ukhtee magana nace ta shi

gaba.

sojan ya mai da marfin ya rufe.

kana ya buÉ—e mata itama ta shiga,

acikin motar na tadda su Naseem sun sha wanka na alfarma kayan su iri É—aya Nasmah har da makeup a fuskar ta, sun yi kyau sosai.

shima Ahmad É—in wani kaya ne a jikin sa na alfar

ma agogo da takalmin kafar sa sai sheki suke.

ido Ahmad ya kura min babu ko kiftawa yabuÉ—e baki da hanci gaba É—aya yana kallo na.

iska na hura masa a fuska nace

"Ya dai?." firgigit yayi sai yapl damko hannuna yace

"Kyakkyawa ta kin gan ki kuwa kin ga

yan da kika daÉ—a kara kyau."

murmushi nayi nace "To ai kai ma kayi kyau."

baki su Naseem suka shiga washe wa suna faÉ—in

"Mommy tayi kyau." nace "Kuma kun yi kyau."

Ahmad suka gaisa da Ukhtee yana yi mata ya gajiyar hanya.

jama'a kowa ya shishiga mo

ta a ka ja motocin a jere aka É—au hanyar hall É—in.

tun daga farkon shiga layin da zai sadaka da hall É—in jami'an tsaro ne ke tsaitsaye har bakin get É—in,

baka jin komai sai tashin sautin kiÉ—a,

a hankali aka wangale get É—in motoci suka kusa ciki,

cikin katon farfajiyar gurin cike yake da motoci, a haka aka rika faka motoci layi-layi.

sauran motocin da muka zo da su duk mutanen ciki suka fita suka nufi cikin hall É—in, muna zaune cikin motar har waÉ—an da suka zo daga bayan mu suka shige ciki.

zuw

a can Rasheedat ta fito daga cikin hall É—in, cikin shigar ta na burge wa irin shigar manyan mata matan manyan mutane.

ta karaso jikin motar in da wasu sojoji guda huÉ—u suka mara mata baya,

ta buÉ—e gefen da nake fuska É—auke da murmushi tace

"Ku sauko

ku ake jira."

a hankali na zuro kafafu na waje na mike tsaye,

É—aya daga cikin sojojin ya zaga da sauri ya buÉ—e gefen da Ahmad yake, shima ya fito, sannan a ka buÉ—e wa Ukhtee tafito rungume da Ahmad karami.

Naseem da Nasmah ma suka fito.

cikin hars

hen turanci Rasheedat tace wa Ukhtee ta bata É—an bayan sun gaisa tayi mata maraba da zuwa kasar mu...

Naseem da Nasmah suna gaba ni da Ahmad muna biye da su, in da Rasheedat da Ukhtee ke bayan mu, Rasheedat nata gefen Ahmad Ukhtee kuma tana ta gefe na.

haka Rasheedat ta tsara yan da zamu tafi a jere,

takuma bawa Naseem da Nasmah wasu fulawa masu kyan gaske suka rike a hannun su.

a hankali muka fata takawa a sannu har muka isa bakin kofar da zai sada mu da ai nahin cikin hall É—in.

a sannu muka kusa

ciki, wani irin wal-wal haka hasken camara ke haska mu, a take aka saiya kiÉ—a aka saki wani zazzakar waka mai kwankwasa zuciyar masoya, ga mamaki na sai naji sunan mu ake ambata cikin wakar,

gaba É—aya cikin hall É—in yaÉ—au ki tafi raf-raf-raf, yayin

da MC yashiga zuba kirari.

"Gafa taurarin sun danno farin wata sha kallo an gai da ango da amarya."

sai ya shiga bin wakar da ke tashin yana faÉ—in

"Ga HAMDAH sarauniya mata ga Ahmad sabil uwa ga Ahmad kaga mai farar aniya."

a hankali nake É—aga kafata

da naji tana yi min nauyi dan jama'ar da na gani cike a gun.

yayin da aka cigaba da haska mu da camara.

har muka isa mazaunin da aka tanadar mana,

kuje rune guda huÉ—u a jere sai wasu biyu Æ´an madaidai ta a ta kasa da namu wato step É—in dake kasa da

mu.

a biyun tsakiya muka zauna ni da Ahmad Rasheedat ta zauna a gefen sa in da Ukhtee kuma ta zauna a gefe na,

Naseem da Nasmah kuma a biyun da ke kasan mu.

muna zama kuwa camara suka cigaba da haska mu,

Æ´an jaridu ma aikatan gidajen TV ne ta ko ta i

na a gurin sai É—auka suke.

nan da nan akafara gudanar da biki, yayin sa Æ´an wasan hausa da mawaka kowa ya fito yana nuna bajin tar sa.

taro yayi taro anyi ɓarin kuɗi,

ma'aikatan hotel da akayi odar su hotel daban-daban da suka girka kalolin abinci

kala-kala. sai zubawa ake ana kaiwa tebur-tebur.

MC yace ana bukatar ango da amar ya su fito,

Rasheedat ta É—an karkato in da yake tayi masa maga, sai ya riko hannuna ya mike kana ya mikar da ni, a hankali muka sauka muka shigo cikin filin.

wani kiÉ—an

aka kuma sakewa shima da sunan mu cikin wakar.

yana rike da hannuna dukan mu muna tsaye, kai na na sunkuye,

yaÉ—an sunkuyo da kansa dai-dai fuskata yace

"Bazaki yi rawa ba."

kafaÉ—a na make cike da jin kunya nace

"Ban iya ba." yanayin yan da muke maga

nar da shi hakan yabada wani irin kala, ai ko hall É—in ya kaure da ihu da tafe.

cike da jin kunya na kife kaina jikin kafaÉ—ar sa.

hannu ya zura cikin aljuhu yaciro É—aurin kuÉ—i Æ´an 1-1k sababbi katakar yashiga lika min, yana murmushi ban É—ago ba kai

na najikin kafaÉ—ar sa,

sai da naji maganar Rasheedat daf da ni tana faÉ—in,

"Ba zakuyi rawa ba." sai na É—ago tare da girgiza mata kai ina murmushi.

liki tashiga yi mana tarika ciro kuÉ—i cikin jakarta tana wasa mana, ta dage tarika tika rawa.

nan m

anya manyan mutanen dasuka taho daga kasashe daban-daban suka rika shigowa filin suna lika mana kuÉ—i, wasu kuÉ—in kasar mu wasu kuma na kasashen da suke...

kai tsaye ake nuna shagalin bikin dan daga can jikin bangon hall É—in katuwar majiki ne ke haska d

uk abin da ke faruwa..

biki yayi biki

naira tayi kuka agurin....

A can cikin garin Bauchi Masa'ud ne kwance cikin É—akin sa da waya rike a hannunsa, yana kalle-kalle a yana gizo,

ido ya kurawa wani bikin da yaga ake gudanar wa,gani har ya shari

kusan minti 5 bai ga shigowar ango da amarya ba sai ya wuce.

yana yin gaba kuwa yakuma cin karo da wannan bikin da ake hasko sa kai tsaye.

da mamaki yakurawa amaryar ido tare da maimaita sunan da yaji MC yana kira "HAMDAH!."

yafurta da karfi, yayin da

hannunsa yashiga ɓari idanunsa a kan fuskarta, duk da ta kara girma da kuma kwalliyar dake fuskarta tabbas bazai taɓa iya mance fuskar nan ba.

da sauri ya mike yayi waje har yana cin karo.

tun daga bakin kofar side É—in Mamie yashiga kwaÉ—a mata kira

"Mamie Mamie Mamie."

kasan cewar yau weekend ne su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleeta sun zo gida dukan su da Æ´aÆ´an su,

Na'ima ma tazo da nata É—an, duk suna hallare a sashin Mamie har da Ummi.

da sauri Mamie ta É—ago jin irin kiran da yake kwaza mata s

ai kuma gashi ya faÉ—o cikin parlour'n kamar an jefo sa, ko gaban sa baya gani.

tace

"Kai Masa'ud wani irin hauka ne haka, bazaka shigo ba tun daga waje kake lafta min kira irin haka kamar wani sabon makaho."

da sauri ya karaso in da take kamar zai faÉ—

i a kan ta hannunsa na ɓari yace

"Mamie kigani Mamie HAMDAH HAMDAH ce."

sai kuma ya sake wa Mamie wayar da sauri ya juya ya fizge rimut É—in da ke hannun Nusaiba ya daddan na sai gashi ya kamo É—aya daga cikin tashoshin da ake haska bikin kai tsaye...

...........!

Mommyn Twins ce

8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 30

Masa'ud da gaba ki É—aya ya jikin sa ya kama suma kamar zai tashi sama yace

"Mamie kun ganta wlh itace HAMDAH ce ga ta nan itace wannan."

yakai hannu ya

na taɓa jikin TV dai-dai fuskar ta.

gaba É—aya cikin parlour'n suka mai da hankalin su kan TV. Aunty Rafee'at ta mike da sauri tazo jikin TV tana karewa wanda Masa'ud ke nunawa kallo, da karfi ta furta

"Wlh ita ce wlh HAMDAH ce wannan, masa musu su gan

i Masa'ud masa su ganta."

tayi maganar tana ture shi gefe.

Ummi da tayi mutuwar zaune tana kallon abin mamaki, sai ga hawayen farin ciki yana fitowa daga idon ta.

yayin da bakin ta ke ta furta kalmar

"Alhamdulillah³."

Mamie kuwa abun kamar a mafarki

take ganin sa yayin da zuciyar ta ke ta son tunano mata abubuwan da suka faru abaya, yayin da wani abu ya taso yake ta son danni hakan.

kokawa tashiga yi sakanin zuciyar da wannan abun da ke ta faman son danne hakan, lallai ba shakka wannan HAMDAH ce, du

k da girma da cika da sauyin da ke tattare da ita, koda shekaru É—ari tayi basa tare bazasu kasa gane jinin su ba.

wasu zafafan kwalla ne masu É—umi suka zubo mata, takasa iya furta komai kamar yadda ta kasa janye idanunta daga kan TV.

hannunta na rawa t

a shiga nuna TV da yatsa yayin da bakin ta yakasa iya furta komai, sai zafafan hawayen da suka cigaba da wanke mata fuska.

Da gudu Aunty Jaleela taje ta rungume Aunty Rafee'at tana faÉ—in

"Wlh ita ce HAMDAH ce Aunty Rafee'at da gaske ita ce."

Nusaiba

da Fauzan ma suka mike suka rungume suna faÉ—in

"Aunty HAMDAH ce wlh ita ce."

parlour'n ya kaure da hayaniya da ihun murnar da su Aunty Rafee'at suke..

A ɓangaren Na'ima kuwa tun san da ta sanya idanunta kan HAMDAH dake cikin TV, tayi wani irin daska

rewa

a zaune a gurin, wani irin bugawa kirjin ta yayi da mugun karfi har sai da takai hannu ta dafe kirjin nata.

su Abbu da suke zaune cikin parlour'n da suke zama shi da Abba, jin hayaniyar dake fita daga cikin side É—in Mamie yayi yawa sai suka mike d

a sauri suka fito.

dai-dai lokacin motar SALEEM yashigo gidan, daga cikin mota ya hangi yan da su Abbu suke sauri suka nufi side É—in Mamie.

cikin hanzari ya faka motar yafito yarufa musu baya.

a kusan tare suka shiga parlour'n Mamie Abbu ya buÉ—i baki

da zumbar tambayar abin da kefaru idanunsa ya sauka kan TV dai-dai lokacin da aka hasko katon hoton HAMDAH wan da ya maimaye fuskar TV gaba É—aya,

inda É—an jarida yake faÉ—in

"HAMDAH kenan shahararriyar Æ´ar kasuwan nan wacce aka fi sani da *HAM'NAS CO

PETROLEUM NIGERIA LIMITED*

ayau ne ake gudanar da shagalin bikin su da kuma murnar samun karuwan É—a da sukayi, ita da mijinta shahararren attajin nan shahararren É—an kasuwan nan wacce duniya ta sanshi wato *AHMAD TIJJANI SABIL* ."

sai a ka É—auke hoto

n ta kana aka kuma sakin wani katon hoto, tana tsaye rike da jariri Ahmad na tsaye a gefen ta ta dama yaÉ—an leko fuskar ta suna yi wa juna murmushi, in da Rasheedat ke tsaye gefen ta na hagu, Naseem da Nasmah suna tsaye a gaban su suna dariya,

É—an jarid

ar yaci gaba da faÉ—in

"Kai tsaye ake gudanar da shagalin bikin, gamu nan a filin taron, biki yayi biki jigajigan shararrun Æ´an kasun nan kuma ma'aurata Ahmad Tijjani Sabil da amaryar sa HAMDAH wacce akafi sani da *HAM'NAS* Co petroleum Nigeria limited,s

una cike da murna da farin cikin kuma samin karuwa da farin cikin karuwan family'n su, muna nan zamu cigaba da kawo muku yan da bikin take kasan cewa a filin taron kai tsaye kucigaba da biyo mu."

shagalin bikin aka cigaba da nunawa...

Kamar a mafarki k

amar abun almara haka dukkanin su suke kallon.

yanayin da Mamie ta shiga shi Abbu ya shiga, sai nuna TV yake da yatsa, Abba kam baya yayi ya jingina da jikin garu yayin da idanunsa shima ke kan TV.

a ɓangaren SALEEM kuwa wani irin wawan burki yaja yatsa

ya cak daga bakin kofa, yayin da zuciyar sa tayi wani irin tsalle tamkar zata faso kirjin sa ta fito,

wani irin rumtse idanunsa yayi da mugun karfi yakuma ware sa a kan TV,

dai-dai lokacin da Ahmad ya rungumo ta ita da baby'n su suna dariya, yayin da wan

i bature yake yi musu liki.

da karfi ya kai hannunsa ya dafe kahon zuciyar sa,da yake wani irin tafarfasa, wani tari ne ya suɓuce masa yashiga yin sa babu ko kakkautawa yana mai cigaba da damke kirjin sa,

baya yashiga yi hannunsa na dafe a kirjin sa.

M

asa'ud ne yalura da halin da yake ciki da sauri ya isa in da yake, ya yana faÉ—in

"Ya SALEEM sannu ka shake ne bari na kawo maka ruwa."

hannu ya É—aga masa kana yayi waje dafe da kirjin sa yana mai cigaba da tarin...

zumbur Na'ima da zufa yashiga keto

mata ta mike tsaye ta tsaɓe ɗan ta tayi waje da sauri, mai adaidaita ta tsare yakai ta gida, tana shiga gida hankali tashe takira kawar ta Raliya a waya tana ɗagawa tace

"Raliya kina ina." jin yan da tayi maganar hankali tashe yasa Raliya faÉ—in

"Amin

iya me ya faru? ina gida yanzu dai nake shirin fita."

tace "Kizo gida yanzu-yanzu akwai matsala."

Raliya tace "Wacce irin matsala kin tsinkar min da gaba."

cikin tsananin tashin hankalin da take ciki tace

"Ashe yarinyar nan bata mutu ba tana nan a raye

, ashe ita ce mai kamfanin *HAM'NAS* mai *HAM'NAS* Co Petroleum Nigeria Limited."

Raliya tace

"Wai wa kike magana ne kam ban gane ba."

tace "HAMDAH HAMDAH nake faÉ—a."

da karfi Raliya tace "Wacce HAMDAH ke bari gani nan zuwa."

tana kashe wayar ta zari

makullin mota tayi waje,

tarika kai wa da kawowa a parking space har Raliya ta iso. Raliya

tace "Wai me kike faÉ—a min ne kina nufin kice min HAMDAH bata mutu ba tana raye kuma anan kusa?."

da sauri Na'ima tashiga mota tana faÉ—in "Shiga shiga zakiji k

omai a hanya kada mu ɓata lokaci."

Raliya na shiga ta figi motar da mugun gudu suna fita a gidan Na'ima

ta dubi Raliya hankali a mugun tashe tace "Aminiya HAMDAH na da rai ko kin san ita ce me kamfanin *HAM'NAS* sai gata É—azu ana nuna ta a TV ita da wa

nnan mai kuÉ—in Ahmad Tijjani Sabil amatsayin miji da mata, Raliya ina cikin muguwar tashin hankali gurin boka zamu je yanzun nan, shi da yace baza a sake jin É—uriyar ta ba kwasam sai na ganta cikin daula, dole na sake sabon shiri ya daÉ—a jefa ta can da

nisa taya ne ma ta kasan ce haka ina wlh da sake wai HAMDAH ce tazamo mai kuÉ—i kuma wai har ta auri hamshakin attajiri, wani bokan ne yabata sa a haka."

kirji Raliya ta buga tace

"Wai da gaske HAMDAH ce mai kamfanin *HAM'NAS* amma taya akayi haka? kai a

mma ni ina da kokon to kan lamarin."

Na'ima tace "Ga abu a fili a TV naganta da idanuna ba faɗa min akayi ba mu gurin boka bamuyi haka da shi ba maza-maza yakashe ta kawai idan ba mutuwa tayi ba bazan taɓa samin sukuni ba."

gudu Na'ima take shararawa h

ar suka iso dajin da bokan yake,

a gindin bishiyar da suke faka motar su a duk san da suka zo gurin bokan a nan suka faka motar suka fito.

da sauri nufi in da bukkan bokan yake, tun kan su haura kan tudun da zai sada su da bukkan suka rika jiyo gurnani d

a wani irin kala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login