Showing 3001 words to 6000 words out of 135595 words
ka É—aukar wa ka
nka wahala shi ba mai uba ba wahalarka a banza, uban titi da bazai kalleka cikin halin labour yace ma sannu ba, tuni ban wanke shi na zubar ba in ma yasami shiga kenan mttss".
taja wani dogon tsaki tare da faÉ—in
"Kara mar Æ´ar iska bata san yan da zatay
i iskancin bama."
Dr Mukhtar da Na'ima kasan cewar suna kusa ne suna juyo duk abun da take fata akasin su da suke tsaye a sakiyar office É—in.
Dr Mukhtar yayi murmushi tare da faÉ—in
"Ko zaki sata a hanya ne idan ta sauke kayan dake jikin ta".
harara
ta dalla masa tare da kuma jan wani gajeren tsaki.
Dr Mukhtar ya mai da duban sa kan yaran sannan yace
"To a gaskiya bazamu karɓi haihuwar ba, na ɗaya babu kuɗin karɓar haihuwa sannan babu wani babba a tare da ku, bazamu karmi haihuwar ba saboda gud
un matsala, bugu da kari kuma É—an bashi da uba,
muzo mu karɓi haihuwa wani abu ya faru azo a dakatar min da asibiti gaskiya yanzu na daina irin wannan kasadar gaskiya kuje kawai kuje wani asibitin."
Da sauri Na'ima da Raliya suka juyo a tare tare da
yiwa junan su
kallon-kallo, sai kuma da sauri Na'ima ta juyo gun Dr tace
"Dr a taima musu a karɓi haihuwar ni zan biya kuɗin duk wani ɗawai niyar da za'ayi ni zan biya, zan kuma tsaya wajen ganin ba'a sami wata matsala ba, aje a kaita labour room."
kai Dr Mukhtar ya jinjina kana yace
"Okay." yadubi nurse É—in yace
"Akai ta labour room.
tace "Okay sir." tajuya da sauri tana faÉ—in "Kubiyo ni."
suka fita dukan su mai labour'n da kawar tata.
suna fita da sauri Raliya ta dubi Na'ima zatayi magana N
a'ima tayi saurin soma yiwa Dr mukhtar magana.
"Dr irin su ne idan suka haihu suke kashe É—an, har idan akabar ta ta tafi bazataje wani asibitin ba wani gun zataje ta haihu ta kashe É—an, ko kuma ta jefar da shi to ni ina son abun da zata hai fa har idan
na miji ne."
Dr mukhtar yayi wani dariya tare da faÉ—in
"Ai tun É—azu na fahimci hakan ai tun da naga kuna wannan kallon-kallon Na'ima Raliya bakuda kyau sai an haÉ—a da wanka, ai na san hali tun a makaranta har idan kukayi wannan kallon-kallon to wat
a tsiyar za'a kulla."
dariya suka sheke da shi suka tafa kana shima ya miko hannu suka tafa da shi dukan su.
zaman sa zagyar da kyau sannan yace
"To meye kaso na a ciki?."
Na'ima tace "Kana da kaso mai tsoka yanzu dai kaje ka bata kulawa ta haihu kuma
kayi fatan namiji zata haifa, yau nima zan haihu."
yace "kwarai kuwa har an shiga dake labour room".
dariya suka saka dukan su.
Nan sukayi ta wasu magan ganun su sakanin su batare da ni naji ko fahimtar me suke nufi ba..
Bayan awa uku, kukan jariri
ne ya soma tashi daga cikin labour room, Na'ima da Raliya da har yanzu suna zaune a office É—in Dr Mukhtar suka wani saki murmushi, lokacin da sakon Dr Mukhtar yashigo wayar Raliya wato tex message yana sanar musu da abun da aka haifa,
ciki murmushin ma
i kunshe da ma'anoni da dama Raliya tace
"Kai sannu Na'ima kin sauka lafiya kai gaskiya haihuwa akwai wuya kinsha fama yau."
itama wani dariya ta sake cikin kware wa a zunzurutun makirci da hatsabiban ci tace
"Na haihu yau ni Na'ima gaskiya haihuwa a kw
ai wuya".
darika suka kuma shekewa sukatafa.
Dr Mukhtar da yanzu shigowar sa office É—in bayan ya amshi haihuwar, zama yayi kan kujerar sa yana faÉ—in
"Gaskiya yau ba sauki oga SALEEM ya haihu um wayaga oga SALEEM da É—a abun ba sauki hhhhh".
"Shima ya
zama baba ni kuma mama".
Na'ima ta faÉ—a tana wani faÉ—i.
nurse ce tayi knocking tashigo taÉ—an dukar da kai tana faÉ—in
"Sir an gama kimsa komai sai dai har yanzu tana bledin, munyi iya kokarin mu bai tsaya ba ko zaka zo ka duba ta."
kai ya girgiza ka
na nurse É—in ta fita da sauri,
a tare Na'ima da Raliya suka mike ganin Dr shima ya mike sukabi bayan sa.
dukan su suka shiga É—akin da aka tanada domin haihuwa.
nan da nan yasoma baiwa yarin yar taimakon gaggawa ganin yan da jini ke fita a jikin ta,
b
atare da ɓata lokaci ba tadawo cikin hayyacin ta ,jinin kuma ya tsaya.
jaririn da nurse's suka gyara shi suka kunshi cikin É—ankwalin mahaifiyar sa sai musu-musu da kuka yake ga dukkan alama niman abinci yake,
nurse ta É—ago shi ta maso gaban gadon da m
amarsa take, wan da a Æ´an min tunan da ta sami kanta bayan Dr yabata taimakon da ya kamata har ta iya mikewa tazaune.
tamika mata shi tana faÉ—in
"Ga abun da kika haifa nan kuma da alama niman abinci yake gashi bakuzo da flas ba, bare a bashi ruwan zaf
i ya sha."
kin karbar sa tayi sai kukan da ta fashe da shi.
kawar ta da suka zo tare ita ta karɓi ɗan tashiga jijjiga shi, wayar ta dake cikin aljuhun wandon makarantar jikin ta yasoma kara alamar shigowar kira,da sauri takai hannunta guda ta cusa cik
in aljuhun wan donta,
É—aya hannun kuma ta gyara rukon jaririn da kyau ta zaro wayar.
ido ta waro kan screen É—in wayar murya cike da tsoro tace
"Mama." sai kuma da sauri taÉ—aga kiran takai wayar kunnen ta tare da yin sallama.
É—an shiru tayi sai k
uma tace
"Mama gani nan dawowa an tashi ne bansami abun hawa ba shine yasa na tsaya".
tana sauke wayar da sauri tadubi kawar tata tace
"Mama ce takira ni taga lokacin tashi yayi har yanzu ban koma gidaba, bayan ko makarantar ma banje ba,ni sai yanzu ma
na ga agogo tun É—azu lokacin tashi yayi, tofa zantafi gida yanzu yaya zamuyi ina tsoro kada Baba yadawo yasamu ban dawo ba,
kema zaki tafi gida ba kawai tun da yanzu kin haihu? muje na rakaki gidan ku nima sai na wuce gida,
karfa Mama tasa yayu na su bi
yo ni kin san fa in nakai wannan lokacin sawa take aje a nimo ni".
tana maganar ne cikin tsaro sosai.
itako mai jego kuka kawai take takasa cewa komai.
Dr yace "A'a taya za'ayi ta tafi yanzu bayan yanzu ta dawo hayyacin ta,sai mun daÉ—a ganin yanayin
jikin nata kafin mu sallame ta, yanzu kam ma allurar da akai mata zai fara ai ki in tayi bacci ta farka mukaga yanayin karfin jikin ta sai mu sallame ta, yanzu dai ke kije tun da ke a na kiran ki."
to tace da sauri ta mika mata É—an,
yanzu ma kin karɓar
É—an tayi.
Raliya ce ta karɓi ɗan a hannunta tace
"To kije kawai."
ai ko tafita da sauri.
bayan fitar ta Dr Mukhtar ya dubi yarinyar yace
ta kwanta ta sami bacci, a hankali ta gyara kwanciyar ta,su kuma suka fita suka koma, office É—in sa.
suna za
ma Na'ima tace
"Bani É—an na ganshi."
Raliya ta mika mata kyakkyawa fari kuwa da shi, sai dai yaron bashida girma É—an kankani ne hakan kuwa bazai rasa nasaba da rashin samun kulawa da ya kamata tun aciki ba.
takafe shi da ido tana wani irin murmushi t
ana É—an jijjiga yaron.
after 4 hr.
hakan kuwa yayi dai-dai da farkawar yarinyar da ta haihun a bacci, alhmdllh taji karfin jikin ta kwarai.
nan tanimi tafiya gida nurse tazo ta sanar wa Dr yace taje ta kira ta.
tare nurse É—in suka shigo da yarin ya
r,ya nuna mata kujera ta zauna kana yacewa nurse É—in taÉ—an basu guri, nan ta fita tajawo musu kofa.
duban yarinyar yayi kana ya ce
"Inane gidan ku".
cikin kame-kame tashiga faÉ—in
"Um..um..gidan mu gidan mu."
sai kuma tayi shiru.
da kyau yakuma du
ban ta sannan ya ce
"Bana son wani ɓoye-ɓoye nasan wannan ɗan bashi da uba cikin shege ne dan haka kawai tan bayar ki nake ki bani amsa inane gidan ku?."
kwalla ta matse tare da mutsutstsike yatsun ta kana ta soma magana,
"Gidan mu yana..yana Unguwar
Bakaro".
kai ya jinjina yace
"A Bakaro kike?."
ta gyaÉ—a kai, Raliya ta jinjina kai kana ta ce
"Ah to shikuma uban É—an a ina yake shima a Bakaron yake?".
tace Eh.
"To yan zun ina zakije keda É—an idan kika fita daga nan?".
Raliya tayi mata tambaya
r tana dubam ta, shiru tayi tare da musutssuke yatsun hannunta.
Dr Mukhtar yaÉ—an tsura mata ido kana yace
"Yanzu ina zaki kai É—an idan aka baki shi?."
kuka tafashe da shi tana faÉ—in
"Wlh idan na tafi da shi gida yan kani za'ayi wlh iyayena sun ce s
ai sun yanka ni yanzu ma in na koma gida nasan suka na za'ayi idan na tafi da shi zasu yanka ni".
kuka take sosai tana faÉ—in zasu yanka ta,
Na'ima kuwa carap tayi tace "To ni zan rike miki É—an ni ina son shi nasan idan kika fita yaddashi zakiyi ko b
a haka ba?".
tafaÉ—a tana duban ta.
da sauri yarin yar ta gyaÉ—a kai tace
"Wlh in natafi da shi gida ne za'a yanka ni in naje dashi gida ne."
Na'ima ta ce "To ya isa, in kika je da shi gida ne za'a yanka ki idan kika fita da shi daga nan kuma yaddashi
zakiyi to ni ina son shi zan rike shi".
hannu ta saka ta buÉ—e jaka ta ciro kuÉ—i masu yawa gudan dubu-duba ne a É—aÉ—É—aure É—auri uku,wacce a kalla ko wani É—auri guda yakai 100k ta mika wa yarin yar tana faÉ—in
"Karɓa in kinje kya nima abun da zaki r
ika ci wan da yakamata masu jego suci, ba sai kin jira iyayen ki sun yi miki ba tun da nasan cewa bayimiki zasuyi ba, da ma ace É—an da uba ne tun da bashi da shi kuwa ba mai saurarar ki, gashi sai kije kiyi jego shikuma É—an ina son shi zan rike shi, dan
bazan iya zuba ido ina gani azalinci É—an da baiji ba baigani ba ku mutane kurika jin tsoron Allah, É—an da bai san komai ba aje a jefar da shi ko a kashe shi."
da sauri yarin yar ta mika hannu ta karɓi kuɗin har hanunta na rawa ganin yawan kuɗin, kana
ta yimusu godiya ta mike da sauri ta fita,
har takai bakin kofa Na'ima tace
"Idan kikaje gida aka tanbaye ki ina abun da kika haifa sai kice yana ina?."
"Ya mutu tun a ciki!."
tayi maganar cike da karfafawa tana daÉ—a dunkule makudan kuÉ—in da ta bat
a.
murmushi Na'ima tayi tare da faÉ—in "Da kyau." da sauri yarin yar tayi waje ta haye abun hawa ta wuce gidan su cikin zillumi da tsoro..
bayan fitar yarinyar Raliya da Dr Mukhtar suka tuntsire da dariya, cikin muryar dariya Dr Mukhtar yace
"Kin ji Na'
ima har da É—an guntun wa'azin ta wai ku mutane kurika jin tsoron Allah tun da kin samu a sama ai dole kijefo wa'azi ciki hhhhh."
"In da kuÉ—i meye bazan samu ba kai bakaji takashe É—an nata tun a ciki ba, wannan kuma ni na haifa."
tayi maganar tana leko
fuskar yaron da yake baccin sa.
Dr mukhtar ya gyara zama tare da sauke numfashi sannan ya ce
"To yan zu ya za'ayi ne?."
tace "Dr ni da na haihu kuma me yazaunar da ni a nan a kaini labour room mana."
dariya ya sheke dashi Raliya ma dariyar tayi tana f
aÉ—in
"Ai kuwa mai jego a gado yakamata a same ta a kwance ba'a zaune a office É—in likita ba."
nan suka mike suka nufi labour room bayan sun gama shirya duk yan da abun zai tafi.
suna shiga ta haura gado ta kwanta, tayi shame-shame kamar wacce ta haihu
da gaske.
Waya Na'ima ta mikawa Raliya tace
"Kirashi a waya".
Raliya ta amsa ta danna number SALEEM......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:50 - Ummi Tandama😇: 🌺 *HAMDAH* 🌺
*WASA FARIN GIRKI!!*âœğŸ?
*NA*
*RA
SHEEDA S DIRECTOR*
_(Book 3)_
Littafin na siyar wa ne ki biya ki karan ta.
domin biyan kuɗin littafin sai ka-ki tuntuɓi wannan number 08034690723
🅿�2
Wayar tayi ta ringing har ya yanke bai É—aga ba, ta dubi Na'ima tace
"Bai É—aga bafa. "
ta ce "Sake kiran shi kin san shi ai murÉ—aÉ—É—en mutum ne idan baiyi ra'ayi ba bazai É—aga ba yanzu haka wayar tana kusa da shi É—agawar ne dai baiga dama ba."
kuma kiran nasa tayi namma har ya yanke bai É—aga ba, sai da ta kirashi
har sau uku a na huÉ—u ne ya É—aga.
ganin ya É—aga kiran takai wayar kunnen ta tare da faÉ—in
"Asslamu'alaikum SALEEMA Raliya ce muna asibiti da Na'ima tahaihu."
SALEEM dake zaune a office yana ta tarkasa Æ´an kayakin sa dan locin tashin sa yayi har ya
wuce ma, Æ´an wasu aiyuka ne suka tsaida shi. yamike zumbur yana faÉ—in.
"Haihuwa kuma? yaushe cikin nata yakai na haihuwa cikin ya fita kenan?."
yajero tanbayar da alamun hankalin sa a É—an tashe yake.
ta ce "Eh haihuwa ce ba fita cikin yayi ba sai da
i bakwaini ta haifa É—a na miji."
numfashi yasauke jin akasin abun da yake zato,shi gaba É—aya jin lamarin na bazata ya mantar da shi zata iya haifar cikin tun da yakai wata bakwai, ya ce
"Ina jaririn yake yanzu yana cikin wani hali yana dai lafiya ko?."
"Eh gashi can a cikin kwalba."
katse wayar yayi batare da yace komai ba, Na'ima da take jin duk abun da yake faÉ—a kasan cewar tasa wayar a amsa kuwa ne ta ce
"Lallai ma wannan wato shi ta jaririn yake bazai fa taɓa sauyawa duka ba."
dariya Raliya ta
yi tare da faÉ—in
"SALEEMA kenan miskili kafi mahaukaci ban haushi bafa zai sauya ba dan kuwa a jinin sa yake."
SALEEM na kashe wayar, wayar Mamie ya kira, zaune Mamie take da su Aunty Rafee'at Aunty Jaleela da su Ummi kiran sa ya shigo.
bayan sun ga
isa yake faÉ—a mata Na'ima ta haihu.
"Haihuwa." Mamie tafada da karfi
kana ta ce "Wani irin haihuwa ciki wata bakwai." ya fuskanci yanayin da yashi ga lokacin da Raliya ta sanar masa da haihuwar shi Mamie ta shiga yanzu.
yace "Eh ta haihu bakwaini ta h
aifa tana asibiti ma yanzu."
"To Allah ya raya." Mamie ta faÉ—a a takaice tare da kashe wayarta.
gaba daya hankalin Æ´an cikin parlour'n yakoma kan Mamie, Ummi ce da sauri tace
"Wa ta haihu Na'ima ce?".
Mamie tace
"Wai haka, wai ta haihu". Mamie ta
faɗa tana taɓe baki.
Ummi ko baki ta washe tana fadin
"Ikon Allah, kaji ikon Allah ko to Allah dai yasa abun da aka haifa nacikin koshin lafiya".
baki Mamie takuma taɓewa tare da faɗin
"Ina kuwa zai zama cikin koshin lafiya ciki wata bakwai sai dai
yabada wahala dai".
a ɓangaren Aunty Jaleela ma fuska ta yamutsa tana faɗin
"Gayyan wahala dai ciki wata bakwai ai ba arziki."
"Ina kuwa arziki duk uban iyayi da cikin ashe dai rabin halitta za'a haifo ba arziki."
Aunty Rafee'at ta faÉ—a, tana tura
É—ankwali gaban goshi.
duk kanin su in ka gansu babu wani mai farin ciki da jin daÉ—in haihuwar, akasin Ummi da fuskarta ke É—auke da annuri bakin ta ya kasa rufuwa sai faÉ—i take
"Kai masha Allah Allah dai ya raya mana."
mikewa Ummi tayi tana cigaba
da faÉ—in
"Kai masha Allah zamu wuce asibitin ba yakamata mu tafi asibitin yanzu".
Mamie ta kawar da kai gefe tare da faÉ—in
"Ummi'n Fauzan ni gaskiya ba yanzu zanje asibitin nan ba gaskiya inaga kamar ina da abun yi, ai dare yayi yanzu ga magriba yaka
wo kai."
Ummi ta girgiza kai tana faÉ—in
"Kai Mamie'n Nusaiba yakama ta dai muje yanzu ace babu wani nashi a can gaskiya baiyi ba."
fuska Aunty Rafee'at takuma yamutsawa tana faÉ—in "Um ni kamma kucire ni a tafiyar dan yanzu Abba'n Adeel zaizo ya É—auk
e mu."
dakuwa Ummi tayi mata tare da faÉ—in
"Maza tashi kushirya ke Jaleela tashi maza muje".
Aunty Jaleela da tazo har wuya ta kwaɓe fuska kana tace
"Ni wlh ina ji ma kamar kar inje dan nima Daddy'n Fadeel nasan zai zo yanzu."
haɓa Ummi ta rike tan
a sallallami da kyar dai ta tirsasa musu ta samu suka fita, suka nufi asibitin bayan sun sanar wa su Abbu.
A asibitin suka tadda SALEEM shima isowarsa kenan a tare suka shiga cikin asibitin.
direct É—akin hutu suka nufa in da nurse tayi musu jagora zuw
a ciki,take sanar musu da cewa an mai da Na'ima can domin ta huta.
nan suka tadda Na'ima kwance tana ta sauke numfarfashi Raliya na tsaye a kanta tana ta yi mata sannu.
da sauri Ummi ta matso in da take tana faÉ—in
"Sannu sannu kinji Na'ima, kin sami ka
nki kalau?".
dakyar ta buÉ—e baki cikin yanayin mutum yasha wuya murya can kasan makoshi tace
"Lafiya lau."
Mamie ko kallo É—aya tayi mata kana tace mata Sannu.
namma da kai ta amsa.
Aunty Rafee'at kam ko kallo bata ishe taba, Aunty Jaleela ce ma a sa
ma tace mata sannu ita ma.
Ya SALEEM da ya naÉ—e hannu a baya yana tsaye tagurin kafafun ta yadan dubeta kana yace
"Ina yaron yake?". Raliya tace "Yana can ansashi a kwalba.
kai ya jinjina cikin yanayin nan nasa, ya maida duban sa kan nurse É—in da ta y
imisu jagora yace
"Muje a nuna mana in da yake, ina Dr yake?".
ta ce "Yana office".
fita sukayi duka har da Raliya,
Raliya tayi saurin shigan office É—in Dr tare suka