Showing 12001 words to 15000 words out of 135595 words
2 akayi knocking na mike naje na buÉ—e, É—aya daga cikin mutanen da mukazo tare nagani tsaye yace
"Madam kun kammala zamu iya tafiya
?".
kai na gyaÉ—a masa, juyawa nayi dan kiran su Naseem sai ganin su nayi a bayana suna kokarin fita daga É—akin,
mutumin ya ruko hannunsu nikuma na koma na É—au mayafi na nabi bayan sa muka fita..
tun daga bakin get É—in da muka iso na fahimci banki mu
ka zo dan gashi a rubuce (First bank) buÉ—e baki nayi a raina nake faÉ—in "To me mukazo yi a banki." bakin na rufe jin yana faÉ—in
"Bismillah fito muje ko." sai lokacin na lura ashe ma har sun fita har ya buɗe marfin ɓarin da nake ban sani ba, a hankal
i na zuro kafafuna waje na fito.
direct cikin bankin muka shige batare datsaida mu ko bincike ba, akasin jama'ar da nagani tsaye bakin bankin an tsaida su an hana su shiga.
tun da nashiga cikin bankin aka bani gurin zama ban motsa ba, duk wani cike-cike
da kai kawo wasu suke tayi su da wan da mukazo da su, sai dai abun da yakamata ni nayi da kaina shine nake tashi naje nayi, awa 1 da zuwan mu aka kammala komai aka bani ATM,
muna fita daga bankin zato na masauki za'a maida mu sai ganin mu nayi a get É—in
wani banki, shima kusan mintunan da mukayi a bankin da muka baro mukayi a nan É—in kafin muka kammala, nan ma da ATM É—in bankin muka fita. ina mai jin mamakin kuma zuwan mu wannan bankin.
mamaki na bai karu ba sai da nakuma sin tar kaina cikin wata banki
, wunin ranar muka kare ta a bin bankuna dan sai da muka je banki biyar kuma duk wan da mukaje da ATM É—in sa muke fita..
sai yamma liss muka dawo masaukin mu, a gajiye na zube bakin gado in da É—aya daga cikin mutanen da muka tafi da su yashigo da su Nas
mah, wata laidar dake rike a hannunsa ya mika min yana faÉ—in
"Gashi ance na baki."
bin laidar nayi da kallo kana namika hannu na amsa shiku yafita,
zamata na gyara tare da zuba ATM É—in da suke hannuna kan table É—in gabana.
a sannu nashiga buÉ—e laid
ar dan ganin abun da ke ciki,
kwalayen wayoyi ne har guda biyu nagani ciki a sannu na ciro su ina jujjuyasu, rabon da narike waya haka a hannuna a matsayin nawa har na mance, sai kuma cikin hanzari nashiga buÉ—esu dan tun ban ciro su ba wayoyin suka tafi
da ni, da sauri na ciro cazar wayoyin duka namike cikin hanzari naje na saka su a cj, ina saka wa kuwa suka nuna min acike suke, da sauri na dawo in da na tashi na kunna wayoyin, ai ko ina kunna wa sai ji kake É—uÉ—ut-É—uÉ—ut alamun shigowar message alert
akai-akai.
ido na kurawa musu ganin alat ne na kuÉ—i suke ta shigowa, na bankunan da muka buÉ—e É—azu, ido na zubawa sarautar Allah ganin kuÉ—aÉ—en da suke ta shigowa ni bama zan iya kiyaste adadin su ba.
sai da naji wayoyin sunbar kara kafin nashiga lat
sa su, contacts nashiga da sauri sai gani nayi babu number ko É—aya, jiki a sanyaye nake kallon wayar, abu na farko da ya fara zuwar min shine lokacin da Abbu ya siya min waya yasaka min number family na aciki,haka narika bin lambobin Æ´an'uwa na ina kiran
su.
hawayen da yagangaro kan fuskata na share ina mai jin kewar ahalina, a sannu na mike na isa in da jakata yake na buÉ—e naciro number Ukhtee da ke rubuce a takarda, na saka cikin wayat kana na dannan mata kira,
tana É—aga wa dajin nice mai kiran ata
re muka saki ihun murna.
hira mukayi tayi da ita har magriba kafin na mukayi sallama...
Kasan cewar ina fashin sallah gado na haye nayi kwanciya ta cike da kewar ahalina daya baibaye ni lokaci guda...
washe gari da rana Bappa ya iso Abuja, nayi murna
matuka da ganin sa har nake jin wani ɓari na kewar ahalina dana kwana dashi ya yaye da ganin sa.
isowar sa ba da jimawa ba muka bar cikin hotel É—in har da kayan mu.
wani katafaren gida mai matukar kyau da tsaruwa gida ne babba wan da girmansa yakai ya
kawo tsarin sa gwanin burgewa, a bakin ramɓasheshen get ɗin gidan motar gaban mu ya tsaya, wan da mutanen da suka ɗauko mu a airport da wan da muka haɗu dasu a banki jiya dakuma wasu karin mutun biyu da yau nafara ganin su, sune acikin motar, motar da
muke ciki ke biye da su, sukayi hon, abakin get ɗin ramɓasheshiyar gidan........�
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:51 - Ummi Tandama😇: HMD
WASA FARIN GIRKI!!!âœğŸ?
_(Book 3)_
🅿�4
Asannu a ka wan
gale tamfatsetsen get É—in gidan, motar gaban mu yakusa ciki, a hankali direban dake jan mu ya danna hancin motar cikin gidan, a tsakiyar farfajiyar gidan duk suka faka motocin, a sannu na zuro kafafuna waje, "Ya ilahi ya littahi".
abun da na furta kenan
lokacin da na dai-dai ta tsayuwa ta a cikin gidan, bin gidan nashiga yi da ido har ina wai ga gefe da gefe na.
gaba É—aya gidan da tsaruwar sa yatafi da ni, tsaruwan gidan yawuci misali komai an tsarashi a inda ya kamata yana ajiye a in da ya dace,gida n
e babba mai É—auke da part har huÉ—u, daga gefe can gabar da gidan side ne guda É—aya sai kuma gefe ta hannun dama shima side ne guda sai kuma gefen hagu shima side É—aya, sai dai Æ´an madaidaita ne ba wasu manya ba.
daga tsakiyar gidan kuwa wani side ne
na musamman wan da yazamo sauran side É—in sun sashi a tsakiya shi kam gini ne mai hawa É—aya babbane ya tsaru iya tsaruwa, daga saman side É—in har kasan sa yaji ado da gilasai masu ban mamaki an kawata shi tamkar a turai,daga kasa kuma an zagaye shi d
a wasu flaw's masu matukar kyau da É—aukar ido,
gaban side É—in wani shinfiÉ—aÉ—É—iyar swimming pool ne wan da aka kawatashi da rubber grass malaye har bakin kofar shiga side É—in.
gefe can kuma parking space ne É—auke da lafiyayyun motoci da suka kai g
uda uhu a cikin sa,
daga farin shiga gidan kuma gefe da É—akin mai gadi masallaci ne shin fiÉ—aÉ—e agun,
sai kuma É—akuna guda É—ai-É—ai a jere guda uku a gefe da masallacin ta can.
Maganar Bappa naji yana faÉ—in
"Muje ciki ko HAMDAH." da sauri nadaw
o daga duniyar kallon gidan dana tafi, da murmushi kan fuskarsa dan ganin yan da na tafi gaba É—aya na shagalta da kallon gidan.
na ce "To Bappa". a hankali nabi bayan su side É—in da ke gefe ta hannun dama muka nufa a hankali nake taka kafata ina cigab
a da baza ido cikin gidan har muka isa cikin side É—in.
masha Allah É—an madaidaicin side É—in ya tsaru matuka.
side ne mai É—auke da 3 bedroom ko wanne da banÉ—aki a cikin sa, É—an madaidaicin parlour haÉ—e da dinning
da kitchen da komai da komai, an
tsara komai yan da yakamata duk wani abun bukata an tanadar babu abun da babu.
É—akunan cikin parlour'n muka rika shiga wan da komai akwai hatta gadon É—akunan duk da shinfiÉ—ar su, sunsha lafiyayyun bedsheets.
bayan mungama zagaye cikin side É—in gaba É
—aya, muka fita É—ayan side É—in dake gefen hagu muka shiga, shima kamar wancan side É—in yaji komai. kowa sai faÉ—in masha Allah yake, nidai kasa magana nayi sai binsu nake inata baiwa idona abinci sabo da gaba É—aya yanayin tsarin gidan yatafi dani.
dag
a nan É—aya side É—in dake can gabar da gidan muka nufa, shima tsaruwan sa da tsarin sa kamar sauran part biyun nan,
koda muka fito daga cikin part É—in baki na washe nadubi Bappa dake ta faÉ—in
"Kai komai yayi masha Allah komai fa yayi yadda yakamata".
baki nakuma washewa ina faÉ—in "Kai wlh Bappa gidan nan Allah yayi kyau kaga fa nan irin wancan can ma irin wancan kai tsarin gidan yayi kyau komai iri É—aya, sai dai kawai kalolin kayan cikin sune daban-daban".
dariya Bappa yayi kana yace "Da gaske gidan
yayi kyau ko?."
"Wlh kuwa Bappa." nafaÉ—a da sauri ina cigaba da washe baki, shima dariyar ya kuma yana girgiza kai kana muka rufawa mutanen baya in da suka nufi wannan kayatacce rantsatstsen babban side É—in nan dake a tsakiyar gidan wan da yazamana da
sauran side É—in sun sashi a tsakiya.
a hankali muka isa bakin kofar da sauri É—aya daga cikin mutanen ya isa bakin kofar side É—in wan da yake na glass ya É—aura hannunsa gefe kan wasu madannai ya daddanna sai ga glass É—in yafara bada sauti É—an baya ya
ja kana ya dubeni yace
"Bismillah Madam É—an zo ki tsaya a nan."
ya nuna min kan step É—in da yasauka akai wan da saika haura kansu kafin ka isa bakin kofar,step ne guda uku, nuna kai na nayi alamar ni?. yace "Eh." a hankali na matso na haura kan step É—
in, daga in da yake yamika hannunsa yakuma danna wasu lambobin kana yace na É—aura hannuna kan nan yanuna min wani É—an zagaye da hoton yatsu, a sannu nakai hannuna na dai-dai ta yatsuna kan zanen yastun, nan yafara bada sauri É—it-É—it sai kuma yakuma dan
na wata lambar data fito mai alamar Okay. nan take kofar tazuge gefe ai ko da sauri na É—aga hannuna.
ya juyo yana duba na kana yace
"Madam wannan kofar special ne mai amfani da zanen yatsune mutum É—aya ke amfani da shi, sai kuma wancan". yanuna wata ko
far dake gefe ya isa gurin muma mukabi bayan sa,ni dai cikin rashin fahimta nake jin sa, yace
"Shi wannan common door ne kamar yanda aka sani kowa zai iya amfani da shi."
ya murÉ—a handle É—in kofar yabuÉ—e muka shiga ciki.
sai gamu mun bayyana cikin wa
ta katafaren parlour ya ilahi ya lilahi, har bansan san da na furta "Kai! amma wannan duk yafisu kyau!".
nayi maganar cikin hakikance gaskiyar abun da ke cikin zuciya ta wan da maganar fitowa kawai tayi,
Bappa ko karamar dariya yayi tare da jijjiga kai.
suma sauran dariya suka bini da shi, nan muka fara kusawa cikin katafaren parlour'n, baki da hanci gaba É—aya na buÉ—e wajen kallon katafare kayataccen parlour'n, faÉ—an tsaruwar sa da misalta tsarin parlour'n ma ba zai misaltuba, yaji kayan alatu da m
ore rayuwar duniya tsaruwan sa ya zarce sauran side É—in da muka shiga babu haÉ—i ko kaÉ—an.
bedroom É—in dake cikin parlour'n muka rika shiga É—aya bayan É—aya, bedroom ne zafafa har guda huÉ—u masu É—auke da tsalatsalan bathroom,
daga gefe da parlour'n
kuwa katon dinning area ne sai kitchen babba a gefe.
sama muka hauwa wan da shi kanshi step É—in haurawan sama abun kallo ne domin kuwa shima an kawatashi na musamman.
wow masha Allah shima tsarin saman kamar kasan sai dai banbancin kalolin kayan dake c
ikin su, kalar kujeru da labulayen bedroom and parlour kasan white and ash da É—an ratsin lemon-green. saman shima 4 bedroom ne a cikin sa kalan kayan bedroom and parlour'n kuma white and sky-blu.
Antsara komai yadda yakamata sai tashi da sassanyan kamshi
mai haÉ—e da kamshin sababbin kaya yake.
kai gidan ya haÉ—u fa nidai bakina yakasa rufuwa wajen kallon tsaruwan gidan, bayan mun gama zaga lungu da sako na saman muka gangaro kasa anan muka yada zangon mu cikin parlour'n kasa.
Kowa sai yaba kyau da ts
aruwar gidan yake, É—aya daga cikin mutanen yadube ni kana yayi gyaran murya sannan ya ce
"Madam komai yayi ko? komai ya miki wannan gidan yayi miki? kokuma mu isa wani gidan?."
kallon sa nayi cikin rashin faminta sai kuma na maida dubana ga Bappa danaji
yana faÉ—in
"Duk da dai bataga sauran ba amma ga yanda take ta washe bakin nan ai ba a magana."
da sauri nace "Bappa gidan..". bai bari na karasa ba yace "Gidan ki wannan gidan duk girman ta nakine akwai kuma ire-iren su suna nan".
ido na waro kamar a
mafarki nakejin zancen, "Wannan ya miki?". mutumin yakuma jefo min tambayar, kai nashiga gyaÉ—awa da sauri sai kuma naruko hannun Bappa ina faÉ—in
"Eh wlh yayi-yayi Allah Bappa gidan yamin kyau sosaiiiii".
Dariya Bappa yayi yace "To sake min hannu kad
a ki ɓala".
ai ko sauran mutanen ma suka rika dariyar ganin yan da nake washe baki ina jijjiga hannun Bappa, Naseem da Nasmah dariya suka rikayi suna tsalle jikin Bappa kamar wan da sun san abun da ake.
Mutumin yacigaba da faÉ—in
"To masha Allah wan
nan side É—in shine naki a yanda aka tsara ginin gidan, sauran kuma ke kikasan yan da zakiyi da su, yanzu mu zamu koma mubarki ki huta zamu dawo zuwa gobe, domin sauran baya nai."
Sukayi mana sallama suka fita, suna fita, na dubi Bappa ina waro ido nace
"Bappa wai da gaske wannan gidana?". Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in "DaÉ—ina da ke akwai shirme." hannu nashiga tafawa ina faÉ—in "Kai wlh gidan nan yayi min mugun kyau." ya ce "To sai ki goyashi kuta yawo tun da dai naki ne." ido na waro tare da sa
dariya nace
"Bappa gidan zan goya?." kanshi ya jinjina yana murmushi.
rungume Naseem da Nasmah nayi cikin tsananin farin ciki, sai kuma na sake su.
da sauri nace "Bappa ina su Inna wuro da Fatu?."
yace "Suna can ruga". nace "Bappa shine bakazo da su ba
kace su dawo nan suzo mu zauna da su a nan, kaji Bappa."
nafaÉ—a ina jijjiga hannun sa, "Kaji Bappa kace su zo". nakuma faÉ—a ganin yayi shiru bai ce komai ba,
yace "A'a HAMDAH su zauna acan zan koma ai nima".
ido nakuma warowa da karfi nace "Bappa ni
kaÉ—ai za'a barni a wannan gari gudan, da ni kaÉ—ai zan zauna a gidannan ai dani daku zamu zauna."
nayi maganar ina nuna cikin parlour'n "Tap Allah bazan iya zama ba dan Allah Bappa kace su dawo nan, wannan gidan ai tsoro zai rika bani ni kaÉ—ai a cikin
sa, kaji Bappa?."
nafaÉ—a ina bubbuga kafafuna a kasa. "To babu damuwa zasu zo amma ba yanzu ba."
na ce "Bappa sai yaushe." ya ce "Bari dai mana a gama Hajiya HAMDAH."
dariya yake bani in naji ance Hajiya HAMDAH, ai ko na washe baki,
yace "To meyasa b
akisa hakorin hajji ba acan?."
"Kai Bappa,hhhh to zan sa in na kuma komawa."
"Allah ya kai mu ai kamar yanzu ne shekara zata kuma zagowa Allah ya nuna mana cikin masu rai da lafiya."
yayi maganar yana mikewa tare da cigaba da faÉ—in
"To ni bazanje mas
allaci gashi ana ta kan kiran sallah, mutumin zo muje muyi sallah".
da sauri Naseem ya mike ya roko hannunsa suka fita.
Da sauri na mike inata daÉ—a waigen cikin parlour'n inshiga wan É—akin in fita inshiga wancan haka narikayi, daga nan kuma naja ha
nnun Nasmah muka haura sama ina faÉ—in
"Bari naje na zaɓi bedroom ɗin da yafi min."
koda muka haura ɗakunan duka na shiga kana nazaɓi ɗaki ɗaya, nan cikin bedroom ɗin nabuɗe bathroom ɗin sa na shiga mai girma da tsaruwa kamar ɗakin kwana.
kay
an jikina na tuɓe duk da ban jima da yin wanka ba nacika ruwa cikin basin nashige ciki, lumshe idanuna nayi ina jin daɗin ruwan na ratsani, najima sosai a ciki kana na wanke jikina da sabulu mai sanyin kamshi da nagani cikin bathroom ɗin, sannan nafito.
Na sami Nasmah gaban mirror ta É—auki janbaki sai murkawa take a bakin ta.
dariya nayi ina faÉ—in
"Oh wannan yarin ya ke kam akwai ki da son janbaki".
itama baki ta washe tana cigaba da kwaɓula janbakin a bakin ta.
da sauri na sauka kasa akwatin ka
yan mu na janyo nadawo É—akin, a sannu na isa gaban wardrobe dan na shirya kayan ciki, ina buÉ—e wa ido na ware cikin wardrobe É—in ganin kaya ashake a ciki, kama daga kan leshi atamfa material shadda dogayen riguna iri-iri, sai dai ba a É—inke suke ba,a h
ankali na zaro É—aya daga cikin dogayen riguna wan da suke jere gefe guda masu kyan gaske, na dawo gefen Nasmah na zauna, kana na sauya kayana da dogon rigar nan...
Tsabar farincikin da nake jin kaina ciki yau bazai misaltuba, muna zaune har su Bappa su
ka dawo muka sauko parlour'n kasa muna ɗan taɓa hira dakuma kallon tv.
duban Bappa nayi sai kuma kamar an zabure ni na mike ina faÉ—in
"Bappa ina zuwa."
sama na haura in da na aje karamar jakata ta hannu na É—auko na buÉ—e jakar naciro wayoyin da jiya
aka bani wan da tun da na kunna su nakuma kashewa najefa cikin jakar, dakuma ATM É—in da jiya aka bani su a banki, nadawo in da Bappa suke da sauri nace
"Kagani Bappa jiya mutanen nan suka É—auke ni sukayi ta kaini bankuna sukayi ta buÉ—e min account, mu
na dawowa kuma suka bani waÉ—an nan wayoyin ina kunna su kawai Bappa kaga kuÉ—in da sukayi ta shigowa kawai kuÉ—i sunata shigowa cikin accounts É—in".
nayi maganar ina wawwaro idanuna alamun tsantsar mamaki.
Murmushi Bappa yayi irin nasu na manya kana
yace "HAMDAH kenan ai kuÉ—in kine yake shiga cikin asusun bankin ki, duk wani abun da kikaga yake faruwa duka, duk waÉ—annan mutane dasuke ta zirga-zirga da É—awainiya da ke, duk umurnine daga sama, duk kanin su an É—aurasu ne jagora akan lamarin, shiyasa
kikaga duk waÉ—an nan abubuwa suke faruwa duk abun da kikaga sunyi umurnine, sunce min ma gobe idan Allah yakai mu za'a fara kai ki guraren da akayi ayyuka wato guraren kaddarorin ki, kije