Showing 102001 words to 105000 words out of 135595 words

Chapter 35 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

arziki dan mota guda ce ta raka su da kayan tsaraba, bayan wan da nima nayi musu..

lokacin da suka iso gida Masa'ud ya shiga É—akin sa, yayi matukar mamaki haÉ—e da razana ganin SALEEM cikin É—akin

a kwance ya dukunkune cikin bargo sai rawar sanyi yayi, lokaci zuwa lokaci kuma sai yayi wasu tagwayen tari ya dafe kirjin sa da karfi yana matse idanunsa.

a bin da ya daÉ—a bashi mamaki shine kayan jikin sa, kayan da yazo da shi gidan ranar da zasu tafi

Abuja gurin HAMDAH, "Kenan tun ranar yana É—akin nan?."

Masa'ud yayi maganar a ransa, da sauri ya karaso bakin gadon yana faÉ—in

"Subhanalla Ya SALEEM baka da lafiya ne?."

da ido kawai ya bishi barate da yayi magana ba.

ganin yan da ya kuma rumtse ida

nunsa yana daÉ—a damke kirjinsa,

da sauri Masa'ud ya fito dan yaje ya sanar wa Mamie halin da SALEEM É—in yake ciki.

a sakiyar gidan ya haÉ—u da su Abbu da alama masallaci zasu tafi,

da sauri ya karaso in da suke yace

"Abbu Ya SALEEM bashi da lafiya ya

na kwance a É—aki na."

da sauri Abba yace "Subhanalla me ya same shi?."

ya juya da sauri ya nufi É—akin nasa Masa'ud ya rufa masa baya.

Abbu kam tsayuwa yayi yaÉ—an yi dimm kana ya girgiza kai yawucw masallaci abin sa..

Abba na shiga É—akin ganin halin

da yake ciki yashiga tambayar sa abin da ke damun sa,

ba wani kwakkwaran amsa ya samu a gurin sa ba dan tun da ya tambaye sa, me ke damun sa ya nuna masa kirjin sa bai kuma cewa komai ba duk tambayar da yake masa.

Abba ya É—aga waya ya kira Dr Farooq ya

ce ya zo yanzu.

batare da ɓata lokaci ba Dr Farooq ya iso.

bayan sudduba shi da yayi ya rubuta masa magani, Abba ya bawa Masa'ud kuÉ—i yaje ya siyo maganin ya kawo masa....

Abuja

Ina samun kulawa sosai wajen Ummi na, dan dole Ahmad

ya tarkasa ya koma gidan sa sai dai yazo ya duba mu ya koma.

yanzu bani da wata damuwa a rayuwa ta hankali na ya daɗa kwanciya, na daɗa yin ɓul-ɓul da ni na kara haske da sheki na kara kyau,

kullum ina tare da Ummi na hankali na a kwance..

Hajiya Lu

babatu na kira nayi mata aiken kuÉ—i ta turo min kayan gyara irin na masu jego.

kafin na cika arba'in kuwa idan ka ganni sai ka kara kallo na, shi kan sa Ahmad idan yazo yakan zauna ne yata kallo na, wai shi ya godewa Allah da ya kawo masa Ummi tamkar kar

a min kyau take,

dariya kawai na ke masa.

ranar dana ciki arba'in Ummi ta fara shiri washegarin ranar Ummi tace yau ba kwana sai Bauchi, na sha kuka na har na gaji, nace sai dai mu tafi tare,

tace a'a na bari sai jiki na ya daÉ—a karfi jaririn ma yadaÉ—

a kwari sai nazo zan fi jin daÉ—in zuwan...

direba ya shirya kayan ta cikin mota da kayan tsarabar ta da Ahmad yayi mata, da wan da nima nayi mata.

muna tsaye a parking space dukan mu gudan sai hawaye nake sharewa, cikin tura baki nace

"Allah Ummi sati

É—aya zan kara na zo."

tace "A'a HAMDAH kibari É—an nan ya daÉ—a yin kwari kada kirika kwasar sa kina yawo da shi bai yi kwari ba, kibari nan da wata uku lokacin yayi kwari sosai sai ki zo."

ido nawaro nace "Ummi har wata uku Allah ni dai a'a."

Inna Wur

o tayi murmushi tace "To in ban da abin ki HAMDAH wata uku yanzu nawa yake kamar gobe ne agurin Allah."

Ahmad kuwa sai washe baki yake adole yaji daÉ—i an ce ba yanzu zan tafi.

Ummi ta shige mota direba ya ja muna É—aga mata hannu har suka fice daga gida

n.

na juya jiki a sanyayi cike da kewar ta...

ina shiga parlour Ahmad dake biye da ni ya rungume ni ta baya,

baki na turu gaba ina yi masa hararar gefen ido.

murmushi mai sauti yayi kana, ya cusa fuskarsa a gefen wuyana na ya sumbaci fatar wuyana a han

kali yaÉ—an ja numfashi yace

"Kyakkyawa ta yaufa a shirya shirin karɓar bakwanci na."

baki na kuma turo wa tare da fizge jikina nace

"Ni ka kyale ni."

dariya yayi cikin zolaya yace

"Zo muje oh na rarrashe ki Ummi ce ta hana ki tafiya ko?."

baki na

murguÉ—a nace "Ina har murna kake." yace "Allah sarki Ummi Allah ya tsare miki hanyar ki, taji tausayin Ahmad da Ahmad shi yasa tace ki kula da su kafin, muje a fara bani nawa kulawar yanzu."

kafa na shiga bubbuga wa, ya janyo hannuna muka haura sama yana

dariya..

Bayan sallar isha, tsaye nake gaban mirror ina feshe jikina da turare bayan fitowa ta daga wanka,

Ahmad ya shigo ya iso ya rungume ni ta baya, daga cikin mirror ya kura min ido yayin da ya sako kan sa kan kafaÉ—a ta yana yimin kallon cikin id

o, sanin manufar sa sai na ɓata fuska na zame jiki na ina tura masa baki.

murmushi mai sauti yayi ya ruko ni yana faÉ—in

"Wai ba É—azu nayi rarra shin nan ba to zo na kara yanzu kam na Musamman ne, shi yasa nasa su Naseem sukayi bacci da wuri."

cak ya

É—aga ni ya dire ni kan gado,

ganin ya shiga zare kayan jikina da sauri nace

"Ban fa warke ba ni dai ka bari."

sai da ya zare doguwar rigar baccin jikina kafin ya É—ago har jikin sa na rawa yace

"Please kyakkyawa ta, kwanaki arba'in da Æ´an kai kiji ta

usayi na mana."

cike da shagwaɓa nace "Allah My zafi zai min kamar bai warke ba."

yace "To bari na gwada na gani idan bai warke ba sai na hakura, a hankali zanyi kinji ki daure."

kai na gyaÉ—a masa,

har jikin sa na ɓari yashiga shafari da sumbatar sa

ssan jikina,

ya birkice ya birkita ni sai na shiga mai da masa martani.

sai da ya jagula ni na jiku sosai kafin ya É—ago ya zare pant É—in jikina, nan ma sai da yayi ta wasa da HQ É—ina kafin ya haye kaina.

idanuna na rumtse san da ya shige ni da tunani

n jin zafin gurin É—in kin da a kamin, sai naji akasin hakan.

tamkar yau yafara sanina haka yayi ta sambatu yayin da yake ta sama da kasa a kaina.

ya sharin tsawon lokaci mai tsawo a kaina yana abu guda, nayi ta daure wa domin ganin ya sami nutsuwa dan n

asan yayi missing É—i na sosai.

sai da ya sami ingantacciyar gamsuwa kana yayi lamo a kaina, duk kanin mu numfashi muke sauke.

a hankali ya É—ago yayi kissing É—in goshi na yace

"Nagode sosai kyakkyawa ta Allah yayi miki albarka."

idanuna na lumshe tar

e da kuma buÉ—e su kan fuskarsa tare da yi masa murmushi, shima murmushin ya maida min kana yace

"Ina son ki kyakkyawa ta."

a hankali ya zare jikin sa ya mike ya É—ago ni muka shige bayi.....

washegari da safe ina manne da waya a kunne na muna waya da U

mmi,

Fauzan ya karɓi wayar muka gaisa da shi.

ina kashe kawar Ummi, kiran Mamie na ahigo wa waya itama sai da muka gaisa har da Nusaiba, dan tun da suka koma kusan kullum sai munyi waya da su har.....

Bauchi a ɓangaren Na'ima kuwa

tana zaune ciki

n bedroom É—in ta waya ce kare a kunnen ta tana magana da aminiyar ta Raliya, tana faÉ—in

"Aminiya nikam anya bokan nan ai kin sa na ci kuwa, nifa banga yan da ake ta faÉ—a kamar yankan kuwan ba, gashi bini-bini sai yace abada dubu É—ari kaza miliyan kaza

kin san har account É—i na yafara yin kasa kuwa,

ba wannan ba ma ban damu da koda kuɗin zai kare idan har zan sami biyan bukata duk abin da na mallaka zan iya ɓatar da shi har idan za'a kashe wancan shigiya annobar yarin yar, dan wlh ta zame min annoba

, jiya muna kwance da shi da daddare yana bacci yana kiran sunan ta, kin yanzu baya fita ko offece kullum yana É—aki,

daga zaran bacci ya É—auke sa zai fara kiran sunan ta, idan naji haushi na bubbuga shi ya tashi yana farka wa zai ruko ni yana faÉ—in

HA

MDAH, ke Aminiya ina cikin babbar matsala dan Allah yanzu muhaÉ—u agurin boka ai, ko nawa yake so na kara masa ni zan basa, nifi son ai kin da za'a yi sha yanzu maganin yanzu, bana son ai ki mai jinkiri shi yasa nake son ai kin boka na kan dutu, ban so mut

uwar sa ba da yana nan da duk haka bata faru ba,

dan Allah aminiya mu haÉ—u yanzun nan gidan boka gani nan fitowa."

ta kashe wayar ta mike ta zari mayafin ta da makullin mota tayi waje.

SALEEM na zaune gurin hutawar sa ya hango ta ta shige mota tayi waj

e,

da ido yabi ta har tayi waje, a zahirin gaskiya kuwa hankalin sa ba ya tare da shi, ya milla yayi nisa daga gare sa,

a hankali ya kai hannunsa ya dafe kirjin sa yayin da ya fara tari a hankali babu kakkautawa.

wani irin zafi da zugi zuciyar sa yake m

asa, a hankali ya mika hannu yaÉ—au É—aya daga cikin wayoyin sa da suke aje kan table É—in gaban sa wan da ya É—aura kafafun sa a kai,

yayin da hannunsa É—aya ke dafe a kirjinsa.

Dr Farooq ya kira bayan sun gaigasa yake Dr Farooq yake tambayar sa yaya ji

ki?.

bai amsa tambayar ya jikin da yayi masa ba sai cewa yayi

"Ka faÉ—a min sunan wani maganin da zan sha."

Dr Farooq yace "Wan can É—in baiyi maka amfani bane?, to gaskiya kazo asibiti kawai zai fi a duba ka da kyau a baka magani, Please Ya SALEEM ka z

o yanzu."

bai yi magana ba sai sauke wayar da yayi a kunnen sa,

a sannu ya mai da bayan sa jikin kujera tare da lumshe idanunsa har lokacin hannunsa É—aya na dafe a kirjin sa.

Dr Farooq yakira sa har sau biyu bai É—aga wayar ba, yana jin wayar tana vibr

ate bai ko buÉ—e idanunsa ba.

sai da yaji alamar shigowar message kafin ya buÉ—e lumsassun idanunsa ya É—au wayar yana duba sakon da ya shigo masa,

Dr Farooq ne ya ai ko masa da sakon cewa dan Allah yazo asibiti kada ya ɓata lokaci.

bayan da ya gama ka

ranta sakon sa sai ya mike ya kwashi wayoyin sa yanufi side É—in sa.

sai da yayi wanka ya shirya kana ya É—au makullin motar sa ya nufi asibitin, ko da ya iso asibitin.

bayan tambayoyin da Dr Farooq yayi masa kan ciwon nasa, Æ´an takaitartun amsoshin da

ya basa da shi yasamu damar yi masa gwaji kan abun da yayi hasashe bisa amsoshin da ya basa..

lokacin da Dr Farooq yaga result É—in test É—in ya jijjiga ba kaÉ—an ba,

ganin yana daf da kamuwa da ciwon zuciya,

hankalin sa a matukar tashe yake basa wasu s

hawarwari kan yan da zai gudanar da lamuran sa domin gujewa kamuwa da ciwon zuciya,

ya tausaya masa kwarai da gaske,

ya É—aurasa kan magani.

har gurin motar sa ya rako sa ya, yana daÉ—a jaddada masa yan da zai kula da shan maganin sa, SALEEM yana kokari

n shiga mota Dr Farooq yakuma duban sa yana faÉ—in

"Dan Allah Ya SALEEM ka kula da shan maganin ka, kuma dan Allah ka rage tunani idan Allah ya tai maka zai tsaya iya haka Allah ya sauwaka."

ya amsa da amin kana ya shige mota...

A ɓangaren Na'ima

kuwa

zaune suke a gaban sabon bokan su, sun naÉ—e kafa gaban sa kamar masu niman gafara,

sun kura ido suna kallon yan da yake ta wani surkullen sa, yayi zane kan kasa ya bubbuga ya share ya kuma zana wa.

bokan ya É—ago ya dube su yace "Zata mutu mutuwa

r wulakanci amma aljanun da zamu tura su sun ce suna bukatar jini rakuma kosassu guda goma kafin suje suyi ai kin."

kirji Raliya ta buga tace

"Rakuma guda goma kosassu ayanzu fa kuÉ—in ko wani É—aya zai kai miliyan uku."

bokan yayi wani irin dariya yace

"Bazaku iya ba ku tashi ku tafi."

da sauri

Na'ima ta gyara zama tace "Boka zamu iya."

wayar ta ta É—aga taduba balance É—in account É—in ta taga babu wani yawa sosai dan duk ta gama basa kuÉ—in.

ta yi masa transfer É—in duka kuÉ—in zuwa account É—in s

hi, kana ta aje makullin motar da tazo da shi a gaban sa tace

"Asai da motar a haÉ—a da kuÉ—in idan basu kai ba zan nemo cikon,

ni dai dan Allah boka ayi min kokari bana so a sami matsala, a iashe ta kawai shine samin kwanciyar hankali na, ko bacci mai d

aÉ—i bana samu yanzu."

boka yace "An gama mabi da matsala yau za'a sai da motar idan kuÉ—in ya cika, da daddare za'a bawa aljanu jinin rakuman a daren nan zasu kashe tai, dan kuma bai cika ba zamu neme ku."

suka mike suna ta zuba masa godiya a motar Ral

iya suka fito saga cikin dajin..

suna tafe Raliya ta juyo ta dube ta tace

"Aminiya amma yanzu idan boka yace a kawo ciko a ina zaki samu cikon?."

Na'ima tace "Agurin SALEEM ai da ma daga gurin sa suke fita, zan sa a É—auke Ameer a nimi kuÉ—in fansa a gu

rin sa dai-dai kuÉ—in siyan rakuman, idan ya bayar sai na bawa boka cikon kuÉ—in narike sauran."

dariya Raliya tayi tace

"Kai Aminiya daÉ—ina da ke kwakwalwar ki na ja, idan aka sace É—an sa kam ai da gudu zai kawo kuÉ—in babu gargada."

Na'ima tayi wani

murmushi mai cike da tarin makirci....

Abuja

Kullum a cikin lissafin tafin watannin ukun da Ummi tace na kara kafin nazo nake, sai nake ganin lokacin yayi min nisa. da kyar naga wata biyu yayi.

kullum idan muka yi waya da Ummi sa

i na ce mata

Allah Ahmad yayi wayo sosai yayi kwari nace kuma bari taji dariyar sa, sai nayi ta masa wasa yayi ta kyalkyalewa da dariya nace taji shi ko.

tace taji amma dai na bari na cikita wata É—ayan tukun..

idan Ahmad yaji muna waya da Ummi yarika

yimin dariya kenan sai yace wai Ummi ta fiso na zauna na kula da su..

ranar da wata É—ayan nan ya cika, tun da na farka da asuba ban kuma iya komawa bacci ba,

a kwatunan kayan mu na sauke waÉ—an da na shirya su tun sati É—aya daya wuce.

ranar Ahmad bay

a gida na, na kira sa a waya nace kasa mu fa mub gama shiri, yace na jira sa gashi nan zuwa.

ina zaune a parlour ya shigo su Nasmah suka rungume sa suna yi masa oyoyo, sai da ya É—aga ko wannen su sama kafin ya dire su yana bin su da dariya.

in da na ke

ya karaso ya É—auki Ahmad karami dake kan kafata yarika cillashi sama yana kwalkwale dariya,

ganin yan da ya shagala da wasa da yaron yana kuma biyewa su Naseem da suke taya sa wasa wa yaron, na turo baki gaba

nace "My rana fa zatayi kana so muyi tafiyar

dare ne."

zama yayi gefe na tare da manna min kiss a kumatu yace

"Kyakkyawa ta ki bar tafiyar nan yau."

ido na waro nace "Me ne!?."

janyo keken da ake saka Ahmad karami a ciki yayi yasaka sa ciki kana ya tura sa gefe ai ko da gudu su Naseem sukayi kan

sa suna yi masa wasa yana ta ɓalle musu da dariya.

janyo ni jikin sa yayi ya sakalo hannayen sa ya zagaye ni da shi,

a hankali cikin tattausan lafazi yace

"Ki saurare ni kiji abin da zan faÉ—a, ai tafiyar ba naki ke kaÉ—ai bace har da ni da su Bappa,ji

bi ina da wani zaman da zamu yi kuma mittin ne mai muhimmanci, nayi miki alƙawari idan mukayi mittin jibi washegari zamu tafi."

kai na langwaɓar gefe zan yi magana yace

"Kar kice komai kika iya jiran wata uku kwana uku ne zai gagara iye kyakkyawa ta?."

yadda yayi maganar a marairaice tare da langwaɓar da kansa gefe,

sai ya bani dariya murmushi nayi nace

"Amma Allah kwana ukun nan kam idan yazo babu fashi."

yace "In Allah ya yarda."

kai na girgiza nace "To Allah ya kaimu."

daÉ—a rungumo ni yayi ya

na faÉ—in

"Amin Amin." ganin yana shirin haÉ—e bakin mu nayi saurin kawar da kaina gefe, nace

"My yarannan fa suna nan." ido ya kashe min yace "Su da suke wasan su hankalin su baya nan."

fuska ta ya juyo tare da haÉ—e bakin mu, idanunsa a kan yaran gari

n hankalin su na kokarin dawowa kanmu sai ya zare bakin sa ya sake ni,

ya mike yana faÉ—in

"Kuzo muje musha ice-cream."

ya É—auki Ahmad karami ya dube ni yace

"Madam muje ko."

a sannu na mike kasan cewar da mayafi a jikina muka nufi gurin mota.

ya b

uÉ—e wa su Naseem gidan baya suka shiga, kana ya mai da marfin ya rufe sannan ya matso ya buÉ—e min gefen mai zaman banza, sai da na shiga kafin ya miko min Ahmad karami.

kana ya zaga ya huÉ—e driver seat ya shiga, yana kokarin ta da motar da sauri wani s

ecurity ya iso,yaÉ—an leko gefen da nake cike da girmamawa yace

"Barkan ku da warhaka."

Ahmad ya ce yauwa, yace "Madam dama wata ce ta zo, wai tazo niman taimako ne ansan da zuwan ta ne."

kai na girgiza nace

"Okay bari idan muka fita wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login