Showing 18001 words to 21000 words out of 135595 words

Chapter 7 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

an kawatashi na musamman.

wow masha Allah shima tsarin saman kamar kasan sai dai b

anbancin kalolin kayan dake cikin su, kalar kujeru da labulayen bedroom and parlour kasan white and ash da É—an ratsin lemon-green. saman shima 4 bedroom ne a cikin sa kalan kayan bedroom and parlour'n kuma white and sky-blu.

Antsara komai yadda yakamata

sai tashi da sassanyan kamshi mai haÉ—e da kamshin sababbin kaya yake.

kai gidan ya haÉ—u fa nidai bakina yakasa rufuwa wajen kallon tsaruwan gidan, bayan mun gama zaga lungu da sako na saman muka gangaro kasa anan muka yada zangon mu cikin parlour'n kasa

.

Kowa sai yaba kyau da tsaruwar gidan yake, É—aya daga cikin mutanen yadube ni kana yayi gyaran murya sannan ya ce

"Madam komai yayi ko? komai ya miki wannan gidan yayi miki? kokuma mu isa wani gidan?."

kallon sa nayi cikin rashin faminta sai kuma na

maida dubana ga Bappa danaji yana faÉ—in

"Duk da dai bataga sauran ba amma ga yanda take ta washe bakin nan ai ba a magana."

da sauri nace "Bappa gidan..". bai bari na karasa ba yace "Gidan ki wannan gidan duk girman ta nakine akwai kuma ire-iren su sun

a nan".

ido na waro kamar a mafarki nakejin zancen, "Wannan ya miki?". mutumin yakuma jefo min tambayar, kai nashiga gyaÉ—awa da sauri sai kuma naruko hannun Bappa ina faÉ—in

"Eh wlh yayi-yayi Allah Bappa gidan yamin kyau sosaiiiii".

Dariya Bappa yay

i yace "To sake min hannu kada ki ɓala".

ai ko sauran mutanen ma suka rika dariyar ganin yan da nake washe baki ina jijjiga hannun Bappa, Naseem da Nasmah dariya suka rikayi suna tsalle jikin Bappa kamar wan da sun san abun da ake.

Mutumin yacigaba d

a faÉ—in

"To masha Allah wannan side É—in shine naki a yanda aka tsara ginin gidan, sauran kuma ke kikasan yan da zakiyi da su, yanzu mu zamu koma mubarki ki huta zamu dawo zuwa gobe, domin sauran baya nai."

Sukayi mana sallama suka fita, suna fita, na

dubi Bappa ina waro ido nace

"Bappa wai da gaske wannan gidana?". Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in "DaÉ—ina da ke akwai shirme." hannu nashiga tafawa ina faÉ—in "Kai wlh gidan nan yayi min mugun kyau." ya ce "To sai ki goyashi kuta yawo tun da dai naki

ne." ido na waro tare da sa dariya nace

"Bappa gidan zan goya?." kanshi ya jinjina yana murmushi.

rungume Naseem da Nasmah nayi cikin tsananin farin ciki, sai kuma na sake su.

da sauri nace "Bappa ina su Inna wuro da Fatu?."

yace "Suna can ruga". nace

"Bappa shine bakazo da su ba kace su dawo nan suzo mu zauna da su a nan, kaji Bappa."

nafaÉ—a ina jijjiga hannun sa, "Kaji Bappa kace su zo". nakuma faÉ—a ganin yayi shiru bai ce komai ba,

yace "A'a HAMDAH su zauna acan zan koma ai nima".

ido nakuma w

arowa da karfi nace "Bappa ni kaÉ—ai za'a barni a wannan gari gudan, da ni kaÉ—ai zan zauna a gidannan ai dani daku zamu zauna."

nayi maganar ina nuna cikin parlour'n "Tap Allah bazan iya zama ba dan Allah Bappa kace su dawo nan, wannan gidan ai tsoro za

i rika bani ni kaÉ—ai a cikin sa, kaji Bappa?."

nafaÉ—a ina bubbuga kafafuna a kasa. "To babu damuwa zasu zo amma ba yanzu ba."

na ce "Bappa sai yaushe." ya ce "Bari dai mana a gama Hajiya HAMDAH."

dariya yake bani in naji ance Hajiya HAMDAH, ai ko na w

ashe baki,

yace "To meyasa bakisa hakorin hajji ba acan?."

"Kai Bappa,hhhh to zan sa in na kuma komawa."

"Allah ya kai mu ai kamar yanzu ne shekara zata kuma zagowa Allah ya nuna mana cikin masu rai da lafiya."

yayi maganar yana mikewa tare da cigaba

da faÉ—in

"To ni bazanje masallaci gashi ana ta kan kiran sallah, mutumin zo muje muyi sallah".

da sauri Naseem ya mike ya roko hannunsa suka fita.

Da sauri na mike inata daÉ—a waigen cikin parlour'n inshiga wan É—akin in fita inshiga wancan haka na

rikayi, daga nan kuma naja hannun Nasmah muka haura sama ina faÉ—in

"Bari naje na zaɓi bedroom ɗin da yafi min."

koda muka haura ɗakunan duka na shiga kana nazaɓi ɗaki ɗaya, nan cikin bedroom ɗin nabuɗe bathroom ɗin sa na shiga mai girma da tsa

ruwa kamar É—akin kwana.

kayan jikina na tuɓe duk da ban jima da yin wanka ba nacika ruwa cikin basin nashige ciki, lumshe idanuna nayi ina jin daɗin ruwan na ratsani, najima sosai a ciki kana na wanke jikina da sabulu mai sanyin kamshi da nagani cikin

bathroom É—in, sannan nafito.

Na sami Nasmah gaban mirror ta É—auki janbaki sai murkawa take a bakin ta.

dariya nayi ina faÉ—in

"Oh wannan yarin ya ke kam akwai ki da son janbaki".

itama baki ta washe tana cigaba da kwaɓula janbakin a bakin ta.

da s

auri na sauka kasa akwatin kayan mu na janyo nadawo É—akin, a sannu na isa gaban wardrobe dan na shirya kayan ciki, ina buÉ—e wa ido na ware cikin wardrobe É—in ganin kaya ashake a ciki, kama daga kan leshi atamfa material shadda dogayen riguna iri-iri, sa

i dai ba a É—inke suke ba,a hankali na zaro É—aya daga cikin dogayen riguna wan da suke jere gefe guda masu kyan gaske, na dawo gefen Nasmah na zauna, kana na sauya kayana da dogon rigar nan...

Tsabar farincikin da nake jin kaina ciki yau bazai misaltub

a, muna zaune har su Bappa suka dawo muka sauko parlour'n kasa muna ɗan taɓa hira dakuma kallon tv.

duban Bappa nayi sai kuma kamar an zabure ni na mike ina faÉ—in

"Bappa ina zuwa."

sama na haura in da na aje karamar jakata ta hannu na É—auko na buÉ—e

jakar naciro wayoyin da jiya aka bani wan da tun da na kunna su nakuma kashewa najefa cikin jakar, dakuma ATM É—in da jiya aka bani su a banki, nadawo in da Bappa suke da sauri nace

"Kagani Bappa jiya mutanen nan suka É—auke ni sukayi ta kaini bankuna su

kayi ta buÉ—e min account, muna dawowa kuma suka bani waÉ—an nan wayoyin ina kunna su kawai Bappa kaga kuÉ—in da sukayi ta shigowa kawai kuÉ—i sunata shigowa cikin accounts É—in".

nayi maganar ina wawwaro idanuna alamun tsantsar mamaki.

Murmushi Bappa

yayi irin nasu na manya kana yace "HAMDAH kenan ai kuÉ—in kine yake shiga cikin asusun bankin ki, duk wani abun da kikaga yake faruwa duka, duk waÉ—annan mutane dasuke ta zirga-zirga da É—awainiya da ke, duk umurnine daga sama, duk kanin su an É—aurasu ne

jagora akan lamarin, shiyasa kikaga duk waÉ—an nan abubuwa suke faruwa duk abun da

kikaga sunyi umurnine, sunce min ma gobe idan Allah yakai mu za'a fara kai ki guraren da akayi ayyuka wato guraren kaddarorin ki, kije ki gaggansu gobe za'a fara tafiya shi

yasa sukace kihuta yanzu."

kai na jinjina alamun gamsuwa, ikon Allah abun kamar a mafarki yake zuwar min.

knocking É—in da ake ne yasani mike wa nanufi kofar da nafi zaton tanan ake knocking É—in, na isa jikin kofar na buÉ—e,

wani nagani tsaye rike da b

asket har guda biyu a hannunsa, É—an risinar da kai yayi alamun girmamawa kana ya É—ago yayi min barka da warhaka, na amsa kana yace min order ne daga hotel É—in su akace yakawo nan gidan, kai kawai na girgiza kana nabashi hanya yawuce ciki.

dinnig table

ya isa ya aje kayan abincin kana yayi mana sallama yafita.

muna nan zaune a parlour sai wajen la'asar mukaje mukaci abincin, daga nan Bappa yakuma fita domin zuwa Masallaci shida Naseem.

Washegari da safe kamar yan da mutanennan suka ce zasu zo suka is

o,

suna zaune a parlour nikuma ina ciki domin kimsa su Naseem, ina gama kimsasu muka sauko nan muka É—unguma.

yau munsha yawo kaman kaman domin kuwa tundaga unguwar muka fara, wani gida mukaje sakanin sa daÉ—an rata da gidan da muke ciki, sannan muka wu

ce wasu unguwanni biyu duk kanin su da gidaje É—ai-É—ai, wan da an gama musu komai suna kulle,suka nunnuna min dakuma tabbacin nawa ne, nasha mamaki kwarai daganin manyan gidajen wai kuma a matsayin nawa.

daga nan wani tsalelen gidan mai muka je tun daga

can nahango ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) wan da aka rubuta da manyan harufa a saman gidan man, tunga nesa zaka iya hango shi ɓaro-ɓaro.

idanuna na lumshe tare dayiwa Ubangiji buwayi gagara misali tasbigi a kasan raina kana na buÉ—e,

Mun

zaga gidan man na yaba da tsarin sa kwarai yana rufe ne ba'a fara aiki da shi ba,

daganan kuma wasu gidajen man mukaje har guda uku duk masu É—auke da ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) daga nan muka kuma zuwa asibitoci suma masu É—auke da sunan

( *HAM'NAS International HOSPITAL* )

suma asibitotin guda uku a gurare daban da ban manyan gaske, sai dai duk a kulle suke anzuba kayan aiki komai da komai acikin su sai dai ba'a fara ai ki da suba.

daganan kuma makarantu da kamfanoni muka nufa duk kani

n su da tambarin *HAM'NAS* International School Of Science's And Technology, *HAM'NAS Store Complex's su ma duk ba'a fara ai ki da suba. sai kuna masallatai manya guda uku anzuba komai a ciki suma ba'a fara amfani da su ba.

Zuwa yanzu kam nidai komai g

anin sa nake kamar almara nafara yarda kan cewa komai da gaske ne, sai yamma muka dawo gida, mun dawo a gajiye suke faÉ—a min cewa muhuta nan da kwana uku sai mu fara tafiya guraren kaddarorin dasuke garurruwa nesa da nan, nace to Allah ya kaimu..

Damin

Bappa narikayi nace nidai yasa su Inna wuro da Fatu suzo kafin mutafi nan da kwanan ukun,

yace a'a abarsu tukun ba yanzu ba,

haka dai dole yasa direba yaje ya taho da su dan na tubure a la dole sai an kawo su, ko da direba zaije É—auko su nace yace musu

kada suzo da komai, dan cikin side É—in dana matsawa Bappa sai ya zabi É—aya daga cikin side É—in gidan wan da zasu zauna ciki, akwai kaya komai na bukata

sai suzo suyi amfani dashi abun da babu sai a karo musu kamar kayan sawa shi da babu a sauran side É

—in.

hakan kuwa a kayi ranar da su Inna wuro sukazo murna kamar nayi yaya, suma agefen su ba'a magana, na rungume Fatu inata murna, tarika É—aukar su Naseem cikin tsananin farincikin kuma ganin su.

a ranar ma Uncle Mahmoud yazo har da matarsa da yaran su

, dan su anan Abuja suke gun ai kin sa.

nan muka wuni da su wunin ranar yayi min daɗi matuka, sai narika jin su tamkar wani ɓari ga ahalina,

ganin su yaÉ—an rage min kewa da begen family na.

Yau asabar hakan yayi dai-dai da kwanaki ukun da zamuyi ta

fiyar, da sassafe muka É—auki hanyar suwa Kano, motoci biyu muka tafi dasu motar mu ni da Naseem da Nasmah dakuma Bappa,sai É—aya daga cikin jagororin ke zaune a gefen direba, É—aya motar kuma mutane huÉ—u ne a cikin ta suna gaba muna biye da su.

mun isa

cikin garin Kano da misalin ƙarfe 12:30pm sai da muka tsaya mukayi sallah kafin muka nufi inda zamu,

gidajen mai muka fara ziyarta kafin asibitoti dakuma kamfanoni.

bamufi awa biyu a cikin Kano ba muka É—au hanyar Kaduna a kaduna muka kwana, washegari m

uka nausa Katsina.

Sati biyu muka ɗauka muna yawon zuwa garuruwa ganin in da aka zuba ayyuka, masha Allah duk garin da mukaje daga gwamnatin su muke samun tarba da karɓa mai muhimmanci, daga karshe muka biyo garin Bauchi,

lokacin da motar mu tashig

a cikin Bauchi state, tashin hankalin da nashiga bazai misaltuba, wani irin tashin tsikar jiki da sanyi mai matukar shiga jiki su suka ziyarce ni, wani irin ɓari da kakkarwa nasomayi lokaci guda har hakorana suna garuwa da juna, sai kuma wani masifaffen z

ufa yashiga keto min, hankalin Bappa yayi musifar tashi ganin halin dana shiga lokaci guda,

cikin tsananin tashin hankali jin bakon yanayin daya ziyarce ni lokaci guda tamkar ƙwaƙwalwa ta zata fashe jin wani irin abu mai matukar nauyi da kara ya dankare

min a kai, kunnuwa na tamkar ana busa wani irin busa mai matukar kara da firgitar wa, da karfi nakai hannuna na toshe kunnuwana cikin matukar jin azabar dake kokarin tarwasa min rayuwa nashiga faÉ—in

"Bappa mu tafi Bappa kace musu kada mu tsaya Bappa mu

tafi wayyo Allah na".

kaina nashiga juyawa da karfi jin yan da zabar da nakeji na karuwa nan take nanimi tunani na na rasa.

cikin É—aga murya ganin numfashi nakokarin barin jikina Bappa yace

"Direba yi hanzari mufita a cikin garin nan yi maza da sauri!

".

gudu direba ya kara bai tsaya ba sai da muka fita a garin, gabaki É—aya, hankalin kowa yayi masifar tashi ganin halin da nake ciki,

Bappa ko karatun Kur'ani yasoma yanayi yana tofa min, hankali na bai dawo jikina ba har sai da mukabar eriya'n Bauchi g

aba É—aya.

A hankali narikajin abun da nake jin na sassauta har ya washe.

numfashi Bappa ya sauke tare da saida karatun da yake, kai ya girgiza tare da faÉ—in

"Kai mutum abin tsoro ne Allah kashiga sakanin nagari da mugu akwai hisabi ranan gobe kiyama".

yadubeni da kula yace

"Sannu ko HAMDAH".

kai na girgiza yace "Me kike ji yanzu?". nuna masa kaina nayi da hannu dan shi ke yimin ciwo sosai.

"Zai bari insha Allahu".

yayi maganar tare da buÉ—e tafukan hannunsa yasoma karanto Suratul (Khafi) aya go

ma na farkon surar haÉ—e da ayatul Qursi'yu ya tofa kana yashafamin a kan. cikin yar da da buwayar Allah naji ciwon kan na sauka.

Ko da muka shiga jahar plateau state, farkon shiga garin Jos NARKUTA. wasu zafafan kwalla ne suka gangaro kan fuskata tuno

da Mama mai awara, da sauri nayi yinkurin yin magana a tsaya amma abun mamaki sai naji harshe na yayi min mugun nauyi gaba É—aya jikina ya sake babu alamar karfi tattare da ni, abun da na fahimta tun lokacin da nayiwa Bappa maga shigar mu Bauchi zan kuma

wata maganar naji na kasa, har kuma yanzu ina jin yanayin...

da daddare muka shiga Abuja, da kyar da taimakon Bappa na iya sauka cikin mota muka shiga ciki.

Inna wuro ta firgita da ganin yanayi na, ko da Bappa yayi mata bayanin abun da ya faru, hankalin

ta yayi masifar tashi, yace ta taimaka min naje na kwanta, shikuma yafita can ya dawo da ɗan karamin ƙwarya da magani a ciki yabawa Inna wuro yace

"Kibata tasha babu komai insha Allah zata ware garin ne kwatakwata basa so tashiga sai dai tayi nesa da sh

i sun mance cewa Allah baya bacci".

Inna wuro tace "Ikon Allah wannan irin shiga sakani sai sakayyar Ubangiji".

ko da Inna wuro ta bani maganin inasha bada jimawaba bacci yaÉ—auke ni, ranar a kaina ta kwana, Fatu kuma tana tare da su Naseem a É—aya É—aki

n dake kusa da nawa.

washegari kuwa cikin yarda da buwayar Allah namike garau...

muna tare a parlour ni Inna wuro Fatu dan har lokacin basu koma side É—in suba, labarin garuruwan da mukajejje narika basu ina washe baki da faÉ—in

"Allah Inna wuro bakuga

abubuwan yan da sukayi kyau ba kai har da garin da ban taɓa zuwa ba".

nayi maganar ina washe baki, dariya suka rika min, nan

Bappa yashigo ganin jikina shima yazauna mukayi ta hira....

bayan kwana biyu

Mutane biyu daga cikin jagororin nan suka z

o su da wasu mata guda biyar sukace na zama a cikin su wan da zasu rika yi min ai ki,

mata ne irin wan da suke karkashin paundation, irin waÉ—an da mazajensu suka sake su dakuma wan da mazajensu suka rasu, akan É—auke su ai ki irin gidajen masu kuÉ—i É—in

nan, a cikin su na zaɓi guda uku dasukafi kwanciya min a rai, kana nace zan gwada ai ki da su.

É—aya na É—auke ta a matsayin mai kula da su Nasmah dakuma kula da tsaftar side É—in,

na biyun kuma mai girka abibci, sai kuma É—ayar na turawasu Inna wuro i

ta zata rika kula da tsaftar side É—in su dakuma girkin su.

nan suka kuma gabatar min da masu maza wan da nazo nasame su a cikin gidan, direba sai mai baiwa fulawa ruwa shi zai rika wanke mota, sai mai gadi dakuma mai kula da tsaftar farfajiyar gidan gaba

É—aya.

mun zauna da su na É—an wani lokaci na fahimci mutane ne masu kirki da rukon amana.

Haka rayuwa tacigaba da tafi, tuni akayi bikin buÉ—e masana'antu da masallatan nan manyan shuwagabannin Nigeria sun halacci torurrukan sun kuma bada gudummawar

su kwarai da gaske wajen ganin an É—ibi ma'aikata masu inganci.

Bayan wani lokaci

Tuni aka damkamin ragamar duk wasu kaddarori na ni nake bada umurnin ayi da kuma kar ayi, har kuma yanzu muna tare da jagororin nan su suke sanya ido kan ganin komai ya

tafi dai-dai.

tuni nasa aka baiwa Fatu uniform a É—aya daga cikin makarantu na, dan dama acan rugar ma tana karatun ta tacigaba a nan.

Zaune nake a parlour ina dudduba jerin sunayen mata da matasan da nasa a É—iba, a karkashin paudasion É—ina domin ba

su tallafin wasu kuÉ—aÉ—en da zai jamusu jari domin dogaro da kai na tura da kuÉ—aÉ—en tallafin izuwa asusun *HAM'NAS* paudasion.

a hankali na mike tsaye tare da yin mika haÉ—e da salati, wayoyina na tattara haÉ—e da sabuwar system É—ina, na haura sama,

kan bedside na ajiye su kana na haye gado dan bacci nake ji, ina so nayi baccin kafin su Naseem su shigo dan suna can side É—in su Bappa.

har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login