Showing 84001 words to 87000 words out of 135595 words

Chapter 29 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

wuce, suka zauna suna É—an tattauna lamuran su.

Abbu ne yamai da hankalinsa kan TV yana sauraran labaran almuru da ake gudanar wa a wannan lokacin, in da ake sanar wa kan manyan masu kuÉ—i da suke bada taimako da tallafi ga

marasa karfi, jinjina kai yayi jin ta in da taimakon ya fito yace

"Kai wannan matar Allah dai ya saka mata wlh tana da kokari sosai, ko wancan satin ma naji kalar taimakon da tayi na dubban nin É—arurruwan kuÉ—i ga mara sa karfi,

in dai za'a cigaba da s

amin irin su a Nigeria ai kasar mu zata cigaba ba É—an kaÉ—an ba,

dubi yan da take ta bada mai kamar kyau ta a cikin gari Allah dai ya kara mata buÉ—i."

Abba ya amsa da "Amin amin ai Yaya ko yanzu ma bakaga layin da ake yi a gidajen manta ba irin su kuma

kullum buÉ—e suke gani ba ci baya ba."

Abbu yace

"Kwarai da gaske Allah ya daÉ—a buÉ—a mata."

hirar suka cigaba da yi har sai da aka kira magriba kafin suka nufi masallaci.

bayan sallar isha da Abbu ya tafi side É—in Mamie hirar matar yayi ta mata da

irin kokarin da take,

sukayi ta sanya mata albarka da dukiyar ta.....)

Abuja

Zaune muke a parlour ni da su Naseem Aunty Rasheedat tayi sallama da kaya niki niki a hannun ta, Zulai da Talatu na biye da ita É—auke da wasu kayan,

ta Suka dir

e shi sakiyar parlour,

na dube ta daÉ—an mamakin ganin ta da manyan laidadi nace

"Sannu da zuwa Aunty Rasheedat."

tace "Yauwa HAMDAH ya nauyin jiki?."

murmushi kawai nayi dan nidai bana jin wani nauyin jiki cikin da bai girma ba ake tambayar nauyin sa.

zama tayi gaban kayan kana ta shiga ciro su cikin manyan laidodin kayan baby ne kala-kala a ciki haÉ—e da kayan wasa,

da gudu su Nasmah suka je in da take Naseem daya É—ago wani abin wasan baby yace

"Mamy kin kawo mana ne?."

Kuma tun sa ta ja tace

"A

'a zan kawo muku naku wannan na baby'n ciki ne, baku san Mommy zata samo mana yaro ko yarin ya ba."

tsalle sukayi cike da murna suna faÉ—in

"Yeee Mommy zata samo mana yaro."

Nasmah ta dubi Aunty Rasheedat ta dafa kafa É—ar ta tace

"Mamy yaushe Mommy

zata samo mana?."

yatsun ta shida ta nuna mata tace

"Saura wata haka ta samo nama."

tsallen murna tayi tazo in da nake da gudu tace

"Mommy guda haka zaki samo mana yaro."

ido na waro ganin ta É—aga yatsun ta biyar tana yimin nuni da su nace

"Akuya ce

ni."

dariya Aunty Rasheedat da Talatu da Zulai sukayi, Talatu tace

"Ai ba akuya kaÉ—ai suke haifan biyar ba idan Allah ya nufa sai kiga an haifo biyar É—in."

kai na girgiza nace "Ba amin ba wlh."

dariyar suka kuma.

Aunty Rasheedat tace "Muna so ko g

oma ne ma Allah yakawo su masu albarka."

ido na kuma waro wa ina faÉ—in

"Lallai ma."

ÆŠakin kayan wasan su Naseem tasa su Sulai suka kwashe kayan da tazo dashi, suka kai cikin É—akin suka jibge shi a gefe.

Bayan wata É—aya.........!

Mommyn Twins ce

8/19/22, 10:57 - Ummi Tandama😇: 27

Tun daga ranar da Ahmad yasami labarin ina da ciki, bai sake barina nayi wani abu da kaina ba.

ko wan ka baya bari na nayi shi yake yi min da kansa, ko naki nace ya bar ni nayi da kai na sa

i ya ce

bai isa na janyo masa a sara ba, shi da kan sa zai min.

koda six yake da ni a hankali yake bi da ni.

tun da Dr ya bashi shawarwari game da cikin kan abincin da zan rika ci,sabi da lafiya ta da ta abin da ke cikin. shike nan ya hana ni sakat da c

in abinci.

a rana sai yabani naci abinci kusan sau goma, dan yanzu idan ya bani naci anjima kaÉ—an zai kuma kara min.

yanzu kullum muna tare da shi ko yana gida na ko baya gida na,

idan yana gidan sa da sassafe zai zo bazai koma ba kuma sai dare.

was

hegari kuwa zai kuma dawowa da sassafen...

Kwance nake a kan dago na tasa É—an karamin ciki na gaba wan da yanzu watan sa huÉ—u kenan.

idan bama kasan da cikin ba, bazaka ce da wani halitta cikin cikina ba, dan bai wani fito sosai ba, bakamar irin

cikin su Naseem lokacin da ya kai watanni huÉ—u ya fi sosai kamar wan da yafi watan nin sa ba.

Ahmad ne ya shigo É—auke da plt a hannunsa, perpesun kayan ciki ne haÉ—e da ganyen ogu da dafeffen kwai a gefe, wanda yasha kayan kamshi da na yaji sai tashi da

kam shi yake,

ya dire plt É—in saman table kana ya hayo gadon ya zauna ya tankwashe kafafun sa a gaba na yashafo fuskata yace

"Kyakkyawa ta taso kici perperun gashi na É—ebo miki."

fuska na ɓata nace

"Ni na koshi ba É—azun nan ci ba, ni bana jin yunw

a yanzu."

ido ya waro yace

"To ai ba sai kinji yunwa ba, bakiji abin da Dr yace ba kirika cin abinda zai kara miki jini da kuzari da lafiyar baby na ba ga perpesun can cikin tukunya ko kwata baki ciba, kuma yanzu nasa Zulai ta kuma girka miki gwaten wak

e da hanta."

ido na waro nace "Nayi yaya da shi sauran perpesun ma kaje ka basu su ci ni nagaji da ci, kullum-kullum kawai mutum yayi ta ci."

yace

"Dan Allah ki taimake ni kitashi ki ci,cin waÉ—an nan abubuwan fa sune samin lafiyar ki data baby na, so k

ike a sami wata matsala? dan Allah ki tashi ki ci kada yayi sanyi."

ya saka hannu ya É—ago ni, ya tallafo ni ya ware kafafun sa ya sani sakiyar cinyar sa, kana ya mika hannu ya É—au plt É—in yasaka shi gabana, ya É—ibo perpesun a cokali zai kai bakina.



karɓi cokalin nace

"Ni zan ci da kaina." yace "To ci

maza dan Allah ki cinye duka."

nace "To Allah kaÉ—an zan ci dan bana jin yunwa."

yace "To ci dai."

a hankali nasoma ci, ganin na fara ci sai ya daÉ—a gyara zaman sa da kyau, a sannu ya tura hannuns

a cikin riga ta ya kife hannunsa kan ciki na, wani nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a hankali yashiga shafa cikin.

bai fi cokali biyar na ciki ba nace nakoshi.

da sauri yace "Please kyakkyawa ta kiÉ—an kara kaÉ—an."

nace "Allah nifa na koshi."

duk yan

da ya matsa kan na kara ko kaÉ—an ne naki daya masa sai na sa masa kuka, ai da sauri ya rungume ni yashiga rarrashi na..

Washegari tun da sassafe ya É—aga ni da kyar na buÉ—e idanuna dan bacci ne fal a ciki,

yace "Tashi muje kiyi wanka mutafi asibiti

yau zaki fara awu, dan likita yace cikin na cika wata huÉ—u yakamata ki fara yin awu kin ga yau Monday dai-dai kenan."

fuska na ɓata nace

"Ni bacci nake ji kabari ba yau ba."

da sauri yace "A'a ina, duk da dai baccin da awun duk suna da amfani amma dai

muje a duba lafiyar baby in mun dawo sai ki cigaba da baccin kinju kyakkyawa ta."

ya karashe maganar da tsi

gar rarrashi.

kai na gyaÉ—a masa a hankali.

murmushin nan nasa mai narka zuciya ya sakar min kana ya sauke bakin sa kan goshi na ya manna min k

iss,

idanuna na lumshi tare da kuma buÉ—e su, ya É—ago yana kallon fuska ta a hankali ya furta

"Ina son ki kyakkyawa ta."

idanuna na kuma lumshe wa a lokaci guda na buÉ—e, tabbas na gama yarda da son da yake yimin a koda yaushe ina hango sona acikin kw

ayar idanunsa.

idanunsa cikin nawa cikin sanyin murya yace

"Yaushe zaki faÉ—a min kema kina so na da bakin ki?."

kasa nayi da nawa idon batare da nace komai ba.

murmushi yayi yace "Ko a iya haka ma na gode."

duban sa nayi da fuskar tambaya jin ya faÉ—

in haka.

murmushi ya kuma tare da É—aga min gira kana yace

"A faÉ—a min É—in ne dai ajin ya hana amma gashi nan ina hango shi."

yasa yatsar sa karkashin idanuna.

kai na nayi saurin kawar wa tare da yunkurin mike wa, Æ´ar karamar dariya yayi ya taimaka

min na mike tsaye yayin da ya soma zolaya ta.

"Ajin nan ya ishe ni haka a ajiye shi a gefe a fito fili a faÉ—a min ana sona, tun kafin ajin ya tsinke dan wata jiya ta tare ni a hanya tace tana sona, nace ta bari tukun da wan da nake so idan bata ce tana s

ona ba zan zo na amshi soyayyar ta."

baki na taɓe dan yanzu na gama karantar kalar zolayar sa nace

"Ayya ai da ka amince mata kawai."

da sauri ya leko fuska ta yace

"To ai ke nake jira Æ´ammata idan baki faÉ—an kina sona ba sai na koma gurin ta."

"Yi

maza kaje ka sanar mata kada ka maka anan."

nafaÉ—a ina kokarin wuce sa, da sauri ya ruko ni yace

"Bari dai na É—an kara jira tukun."

ya janyo hannuna muka shiga bayi.

bathtub ya cika da ruwa mai É—umi,

kana ya tuɓe min kayan jikina, na shige ciki n

a zauna ina mai jin daÉ—in ruwan, na lumahe idanuna.

da sauri na buɗe idanuna jin motsin sa cikin ruwan sai ganin sa nayi shima a tuɓe,

ya É—au sosa da sabula yashiga wanke ni shima yana wanke jikin sa a haka akayi wanka,

kana ya ruko ni muka fito bed

room,

koda nazo sa kaya hana ni yayi sai da yagama sumbatar ciki na kafin ya saka min da kan sa.

muna gama shiri muka fito muka dadda an gama wa su Naseem shirin School.

a saman dinning duk muka yada zangon mu, sai da ya haÉ—a musu abincin da duk sukac

e suna so kafin ya juyo kai na.

perpesun naman zabbi ya zuba min haÉ—e da tea mai kauri yana kokarin zubo wani abun nace masa

ya isa wannan É—in ma ba iya cenyewa zan yi ba. ciki na ya shafo

yace "Yanzu fa zaki fara kamata yayi ki fara da mai yawa."

d

uban su Naseem yayi yakamo kumatun su yace

"Kanin ku yakusa isowa Yaya Naseem da Aunty Nasmah."

washe baki sukayi cike da jin daÉ—i Naseem yace

"Daddy ina kanin?."

ciki na ya shafa yace "Ya na nan yakusa fito wa."

da sauri Nasmah ta mike tazo kusa d

a ni tana kokarin jan riga ta sama.

hannunta na bige nace

"Ke meye haka?."

tace "Mommy danga kanin ne fa."

fuska na ɓata nace "Ka dani ko."

dariya yayi sosai kana yaÉ—an sakaita dariyar, ya dafa kanta yace

"Zaki gan shi?." kai ta gyaÉ—a tana washe b

aki.

yace "To ba ri ki ganshi."

juya kujerar da nake yayi yadurkusa kana ya saka hannu yana kokarin jan rigata sama, nayi saurin rike hannunsa nace

"Me ye haka?." juya hannun nawa yayi yarike cikin nasa kana yajan je rigar da É—aya hannunsa, yace

"Kib

ar yara suga É—an uwan su."

tafin hannunsa ya kife kan cikin yana É—an shafawa yace

"Nasmah zo ki gani ga kaninku a nan yaron yana nan a nan."

dariya sukayi har suna rige-rigen

taɓa cikin.

Naseem yace

"Daddy ni ban ganci ba."

yace "Yana cikin ciki

yakusa fita ku ganshi."

sallen murna suka yi suna faÉ—in

"Ye damuga yaro, Mommy data samo mana yaro."

kafa na shiga bubbugawa a kasa nace

"Kuma na fasa cikin abincin."

da sauri ya saki rigar yace

"Yi hakuri kyakkyawa ta ci mu tafi o."

sai da yayi ta

lallami na kafin na soma ci.

hannu ya saka muka ci tare muna ci yana karawa da dabara yayin da yake ta jana da wasa har naci da yawa sosai.

bayan mun gama muka fito waje in da Talatu ke biye da mu rike da school bag É—in su.

ko da akazo shiga mota dirj

ewa yaran sukayi suka ce sam moton Daddy'n su zasu shiga, fuska na É—aure nayi musu tsawa nace

"Maza ku shige kusha mota kutafi so kuke kuyi latti."

da sauri yace

"A'a a'a kyale su kushiga muje, Talatu sa musu jakar su cikin mota."

da sauri tace to.



ya buÉ—e musu motar suka shiga, Talatu saka musu jakar su cikin motar,

kana ya buÉ—e min nima na shiga, ya zaga gefen direba ya shiga ya ja motar, mai gadi ya buÉ—e get muka fice a gidan..

sai da yafara bi ta makarantar su da kansa ya sauka ya ruko hannu

nsu ya shiga da su cikin makarantar kafin ya fito muka nufi asibiti.

Muna shiga cikin asibitin batare da ɓata lokaci ba aka gama kimsa mana komai,

koda nazo shiga É—akin awu tare da shi muka shiga, yana tsaye yana kallon komai, idan yaga nurse É—in ta

É—an danna cikin sai yace wai tayi a hankali kada a sami matsala, a haka a ka gama muka fito muka nufo gida.

Tun daga lokacin idan wata ta zagayo lokacin zuwa awu yayi da shi muke zuwa kuma yana tsaye za'ayi komai....

Haka rayuwa yaci gaba da tafiy

a,

sosai Ahmad ke kula da ni baya kaunar yaga wani damuwa ko ɓacin rai tare da ni, bazai taɓa samin sukuni ba har sai yaga ya gusar min da damuwa ya sanyani farin ciki....

a yanzu cikina watan sa 7 yafito ɗas da shi, haka zai tasani gaba ya tuɓe min

riga yayi ta kallon cikin, yana ganin in da yake motsa wa, yayi ta sumbatar sa, idan nace ni na gaji ya kyale ni.

sai yace ai ba da ni yake ba da babyn sa yake, wai yana mika masa gaisuwa....

Zaune nake a parlour Inna Wuro tashigo rike da manyan kofun

a guda biyu, ta iso ta dire su a gaba na tazau na nata faÉ—in

"Sannu HAMDAH ya nauyin jiki." murmushi kawai nayi. É—aya kofin ta buÉ—e ta miko min tace

"Karɓi kisha maganin zaki ne dana bayamma zai taimaka miki sosai."

nace to na amsa nasha da É—an yaw

a ta karɓa sauran ta mika min ɗayan shima na sha.

ganin Ahmad ya shigo yasa ta mike wa tana faÉ—in

"Anjima ki kara sha shi zai zamo ruwan shanki za'a kawo miki wani anjima."

nace to

ya karaso ya gaishe ta ta amsa tana fita daga parlour'n.

ya zauna g

efe na tare da É—aga riga ta sama ya sumbaci cikin kana ya É—ago yana faÉ—in

"Mene ne Innar ta kawo miki shine ba tayi."

nace "ÆŠauka ka sha." buÉ—e marfin kofin yayi yaÉ—an kai bakin sa ya É—an É—ana yayi saurin aje kofin yana yamutsu fuska.

dariya na

yi nace "Ka kara mana."

yace "A'a ya ishe ni, amma meye wannan É—in?."

nace "Maganin zaki ne da na bayamma."

yace "Meye su É—in."

nayi masa bayani ta yanda zai fahimta.

yace "Oh to karɓa ki kara sha, ai naji tana cewa anjima ki kara sha shine ruwan s

han ki."

fuska na ɓata tare da make kafaɗa nace

"Ba yanzu nasha ba."

yace "To an jima kaÉ—an zaki kara."

nace "To kabari anjiman yayi mana."

yace "To ai gara dai na tuna miki tun yan zu kar anjiman yayi kice da saura."

dariya nayi ina faÉ—in

"Ai i

rin anjiman ka ne yanzu sai kace yayi."

shima dariyar yayi yace

"To shike nan a saka time kada lokaci yayi kice bai yi ba."

nace "Eh a saka." yace "Bayan minti 5."

"Tab banyar da ba yayi kaÉ—an."

"To na kara biyar a kai."

nace "Naki wayon." yace "To

ashirin yanzu kam ba kankari."

Ai kuwa duk bayan minti 20 zai sani na sha, ganin ya matsa min sai na gudu sashin su Inna Wuro.

har can É—in ya bini da kofunan yace wa Inna Wuro ta kara maganin wannan ya kusa kare wa.

nace

"Allah Inna Wuro kar ki kar

a ni nagaji da sha tun É—azu yake ta bani."

yace "Ina ance yazama ruwan shan ki ne."

"Shike nan shan ruwan babu adadi ni ciki na zai fashe."

Inna Wuro tayi dariya tace

"Idan ta shanye wannan da rana sai dare kuma sai a kawo mata wan da zata sha har ga

ri ya waye."

nan ne ya kyale ni amma yace mutafi na karasa shanye sauran.

nace ya tafi zan zo anjima, fir yaki sai da ya tasani gaba muka koma...

tun daga ranar kullum shi yake zuwa da kansa ya karɓo min ruwan maganin, yakuma tasa ni gaba sai na sha...

A bangaren Hajiya Karima kuwa

tsaye take ita da wasu maza guda hiyu, a cikin bedroom É—in ta, sunyi jungum-jungum kamar waÉ—an da aka aiko wa da bakin labari,

É—aya daga cikin mutanen yace

"Hajiya shima kawai a kunce masa tayar mota yabi uban sa i

nda yaje."

Hajiya Karima tace "Ai matsalar ba daga nan take ba, yanzu fa duk wata shirin mu ya kwaɓe idan aka kashe Ahmad tofa anyi ba'ayi bane, dan kuwa yanzu yasami magaji dole a mufara bi ta kan ita matar tasa mai cikin kafin shi."

É—ayan yace "To Ha

jiya me kike ganin za'ayi mushiga cikin dare mu harbe banza kawai."

tace "Ina ai bazai yiwu ba dan gidan ta da matakan tsaro iri-iri, akwai jami'an tsaro da masu gadi kuma ko wannen su yana da bindiga, shigan gidan zai bada wuya, dole dai mubi ta wata han

yar, ni a tuanani na kawai mu jira ta haifi cikin sai mu kawar da shi,in yaso duk mu haɗa har da ita mai azarɓaɓin yin cikin kafin shi Ahmad ɗin.

suka ce haka za'ayi,

nan suka cigaba da tattauna in da lamarin zai tafi musu batare da wata matsala ba..

...

A gurguje Please

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login