Showing 30001 words to 33000 words out of 135595 words

Chapter 11 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE



suke, yana kulle motar yadawo yashiga mazaunin direba yaja motar.

Munbar harabar makarantar da ɗan nisa kana na juyo na dubi su Nasmah dasuka gama kwaɓe jikin su da chocolate, ganin ina kallon su sai Nasmah ta miko min na hannuta tace

"Mommy akici".

cikin masifa nace "Ai sai kun sha duka ba kun iya kwaÉ—ayi ba bakusan mutum ba kuka ma binsa, waya sani ma ko mai satar mutane ne yayi gaba da ku wata kila ma badun na iso da wuri ba da yanzu yayi gaba da ku, yaje yayi kuÉ—i da kanku,

idan kuka kara gani

n mutum baku sanshi ba kuka bishi sai na zane ku, bare har ya baku abu ku karɓa sai na yanke hannun ku, yajaku mota zaiyi gaba da ku Allah ya so ku ai da kuna can Allah kaɗai yasan halin da kuke ciki, badun na iso da wuri ba, ɗan rainin hankali wai arik

a ai ko mai wayo yarika É—aukar ku to ina ruwan sa ma daku tukun, mttsss." nayi maganar tare da jan tsaki.

baki Naseem yawashe cikin É—an sallen murna daga zaunen da yake yace

"Ai Daddy yace dai caya mana mota."

wani irin faÉ—uwar gaba naji da ya ambaci

sunan Daddy da sauri nace "Kai Naseem waye kuma Daddy?." Nasmah ce ta caɓe zancen da faɗin

"Daddy daya bamu chocolate yace dai cayamin jigi haida mota da chocolate da yawa."

da karfi jin yan da zuciyata ke tafarfasa kai na ke sara min nace

"Kai ya is

a! idan na kara jin kalmar wani Daddy a bakin ku sai na fasashi, ku bani chocolate É—in nan."

nafaɗa ina karɓe chocolate ɗin hannun su na zuge glaas ɗin motar nayi wurgi dashi.

maganar Yakubu najiyo wan da tashin hankalin da nashiga ciki yanzu sama-s

ama nake jiyo shi yana faÉ—i

"Hajiya ai shi wannan mutumin bamai satar yara bane mutumin kirki ne, shine Ahmad Tijjani Sabil mai kamfanonin nan wan da ake nuna shi agidajen talabijin, ai ko É—azu dana kawo su makaranta na tarar da motar kamfanin shi tana

sauke kujeru dawasu kayan amfani na makaranta,ai kin sa kenan yana da yawan taimako kuma taimakon sa yafi yawa a inda yara suke."

"Ahmad Tijjani Sabil."

na mai-mai ta sunan a raina ina ta son tuna in da nasan sunan, sai a lokacin na tuna É—azu da safe ak

e labarai a kansa a gidan tv anan nataɓa jin sunan.

Naseem yace "Ai nima Daddy yace dai taya min mota in tuka akaina."

cikin tsawa nace "Ban ce kada naji wani ya kara min maganar wani Daddy anan ba?, rufamin baki idan ka kara sai na fasa ma baki bari ka

gani."

Yakubu kuwa ci gaba da zuba yake wan da ma gaba É—aya hankali na baya cikin motar da jikina gaba É—aya.

Muna komawa gida nakira *HAM'NAS* Store Complex nace a kawo min motar wasan yara guda biyu da wasu kayan wasa, batare da ɓata lokaci ba mot

ar ShopRite É—in ya iso, a É—akin kayan wasan su aka jibge musu,

ihun murna suka sake ganin motocin cikin tsallen murna Naseem yace

"La iyin motan da Daddy yace dai taya mana babba."

da sauri na mike daga kan kujerar da nake zaune cikin É—akin kayan was

an su, hannayen su duka na riko nadawo na zauna, inajin zuciya ta na min mugun É—aci da kuna a duk san da naji sun furta kalmar Daddy a bakin su,

duban su nayi dukan su nace

"Kuna ji ko Naseem Nasmah?, shi wancan mutumin ba Daddy'n ku bane baku sanshi ba

kuma ku bakuda Daddy, nice Mommy'n ku kuma nice Daddu'n ku bakuga na siya muku mota ba, idan kuka sake faÉ—ar Daddy bazan sake siya muku mota ba, kuma zan sa akwashi waÉ—an nan ma a tafi dasu, baku da Daddy nice Daddyn ku kunji ko?."

kai suka gyaÉ—a nace

"To maza kuje kushiga motar ku." ai ko da sauri suka ruga in da motar suke suka shiga,

ina tare da su a É—akin sai zaga É—akin suke a cikin motar, suna dariya.

numfashi nasauke ganin suna cikin farinci sosai, Nasmah ta danna motar ta motar tatafi tsuu

zata garu da jikin garu-bango da sauri na mike na tafi da gudu na taro ta, na ciro ta ciki ina faÉ—in

"To ya isa haka muje kuyi wanka kuci abinci sai kuma anjima zan sa afito muku da shi can tsakar gida kuyi wasan acan."

nayi waje da su.

Yau Juma'a da

wuri Talatu tagama yi musu shirin makaranta, narako su har sai da motar kaisu makaranta yafita kafin na juya a hankali, gaba É—aya yau jikina baya min daÉ—e a hankali na isa bakin swimming pool na cire takalmata gefe na zauna bakin swimming pool É—in na z

ura kafafu na ciki, a hankali nake motsa ruwan da kafata ina É—an lilashi ciki, wasu hawaye ne masu É—umi suka zubo kan fuskata banyi kokarin sai da su ko danne zuciya ta daga abun da take jiba, tun jiya nake jin kai na cikin yanayin ina so nayi kuka ko za

nji sassaucin abun da nake ji cikin zuciya ta, sai dai ban sami damar yin kukan ba saboda su Naseem, sam bana so nasaka musu rauni cikin zuciyar su, dan aduk san da irin wannan damuwar ta taso cikin zuciya ta zama nake a É—aki nayita kuka, aduk san da suka

ga ina kuka sun rika tambaya ta me ya same ni idan nayi shiru ban basu amsa ba ko nace musu babu komai suma sai su fashe da kukan su rungume ni muyita kukan.

tabbas ina ganin rauni da damuwa aduk san da hakan tafaru agare su, duk da kuwa kasan cewar su ya

ra wan da basu san komai ba, amma nasan akwan atashi idan hakan yaci gaba da faru zasu tashi da abun a ransu,

nasan É—aci da kunar dake tattare da kuncin ganin UWA cikin damuwa game da É—an ta, dan kuwa shike hanani sukuni a koda yaushe.

wasu hawaye ne m

asu zafi da kuna suka cigaba da wanke min fuska cikin jan sheshsheka nashiga faÉ—in

"Ummi na kizauna gidan Abba Ummi bazan taɓa yafewa kai na ba har idan nayi sana diyyar barin ki gidan Abba, Ummi na zancigaba da yin nesa dake har idan hakan zai sa ki ci

gaba da zama gidan Abba."

kuka sosai ya kwace min cikin muryar kukan nacigaba da faÉ—in

"Abba wlh ban ai kata zina ba ban taɓa ai kata zina ba, Abba zan cigaba da yin nesa daku har idan hakan zaisa Ummi na tacigaba da zama agidan mu, bana so nayi maraic

in uwa batare da tabar duniya ba,

Abbu Mamie Ya Masa'ud Auny Rafee'at Aunty Jaleela Nusaiba Fauzaun, kewan ku da begen ku yana hanani sukuni,kullum da ku nake kwana cikin raina,

shin haka kuma kuke kewata ina son ku ko da yaushe ina tare da ku a cikin zuc

iya ta,

ku yar da dani wlh ƴaƴana ba shegu bane, wlh Allah ban taɓa zina ba,

Allah sarki Inna ta da kina nan da kin faÉ—a musu kalar tarbiyyar da kikayi min wan da ko da agidan karuwai zan zauna bazan yi iskanci ba, bazan yi ba, bazanyi ba,

Ya SALEE

M Ya SALEEM Ya SALEEM me na tare muku kai da matar ka meyasa zaka rabari da *MAHAIFIYA TA* karabani da ahalina me nayi muku, me yasa zaka sheganta min Æ´aÆ´ana tsaftatattu ka dan ganta su da wani uba wan da bansan ko waye shiba,

duk hakan na menene da har

sai ka kazanta min ƴaƴa? ƴaƴa na ba kazan ta bane kamar yadda ka faɗa ƴaƴana tsaftatattu ne bazan taɓa yafe maka Ya SALEEM bazan yafe maka b...."

Kuka ne yaci karfi na nakifa kaina da guiwa na nayi ta kuka kamar raina zai fita.

najima sosai za

une a gurin ina ai kin kuka, mai cike da kuna da bakin ciki. da kanshi hawayen ya tsaya badun na tsai da shi ba, sai dai kukan zuci danake, a hankali na mike cikin matsananciyar ciwon kai wan da dakyar nake iya buÉ—e idona duka sabo da zafin ciwon kan, na

nufi ciki.

direct bedroom na shige kana shiga bathroom wanka nayi nafito na sauya kaya na zo na kwanta bakin gado,

karatun Alkur'ani na kunna cikin wayata a hankali nake bin karatun, a sannu narika jin zuciya ta tana samin salama da nutsuwa, a hankali na

rika jin bacci na fizgata ta, na lumshe idanuna.

can cikin baccin da ya É—auke ni da nisan ta baifi na minti 20 ba.

najiyo muryar su Nasmah, da gudu suka haye gadon suna faÉ—in

"Mommy mun dawo Mommy mun dawo."

ida nuna na rumtse da É—an karfi dan har l

okacin kai na bai bar yimin ciwo ba,

mike wa zaune nayi jin sun zube a jikina na É—ago su ina faÉ—in

"Wai har kun dawo? amma dai ba'a tashi ba ko."

nayi maganar ina duban agogo, karfe 12 har da rabi,nayi mamakin gani in da lokaci yatafi har haka, ranar

yau karfe 12 saura suke dawowa har sun dawo anyi musu wanka an sauya musu kaya.

lallai najima ina kuka har ban san lokaci yatafi har haka ba, tausayin kaina ya kamani, É—an guntun kwallar da ke kokarin sauka a idona É—aya nayi saurin kai yatsata na tare

shi kana na gyara zama ta ina faÉ—in

"Ashe dai lokacin tashin naku yayi, to yaya karatu yau ansha wasa ko."

nayi maganar ina shafa kansu.

baki Nasmah ta washe ta mike tsaye a kangadon tace

"Mommy yau Aunty'n mu tayi mana haka."

tarike kugu tare da gir

gizawa, dariya nayi ina faÉ—in

"Au kice yau Aunty rawa tayi muku."

"Ba haka bane haka ne".

Naseem yafaÉ—a tare da mike wa yarike kugu yasoma tsalle.

ido na ware nace "Kai kuce yau kunsha rawa." cikin tsallen yace "Eh ai hadda chocolate ma."

tsai da t

sallen da yake yayi sai kuma ya dira a godon da gudu yafita sai gashi ya dawo da School bag É—in sa, a tsakiyar gadon ya zazzage School bag É—in sai ga Chocolate masu yawa haÉ—e da littattafan sa sun zubo,

da mamaki nace

"Yau kuma Talatu kayan zaki tacik

a muku a jakar."

nakai hannu na É—ibo chocolate dasuka kai guda biyar kala daban daban, ga kuma wasu a gaban sa, da É—an mamaki nake kallon su dan asanina babu kalar waÉ—annan chocolate É—in acikin kayan cime-cimen su kalar nasu ba irin wannan bane.

"Kai

Naseem a ina ka samo waÉ—an nan chocolate É—in?."

nayi maganar ina duban sa, da sauri Nasmah tace

"Nima akwai nawa." ta dira agadon da gudu tayi waje, Naseem ko bai bani amsa ba sai kokawar buÉ—e laidar chocolate É—in yake.

ta shigo da school bag É—in

ta itama ta zazzage, nace

"Kai wai waya baku wannan abun haka, Talatu Talatu."

nashiga kwaÉ—awa Talatu kira dan na fara tunanin ko rikici sukayi mata gun shirya su tabuÉ—e wani katon É—in chocolate É—in daban.

Naseem da yakai Chocolate É—in baki ya kuts

ura yana É—aga kafaÉ—a alamun yana jin daÉ—in abun yace

"Daddy yace mucinye wannan duka dai kaya mana wani."

"Ai yace idan ka kaiɓa min baye kaya maka ba ni de bani da yawa."

cewar Nasmah tana kai wan da ta ɓare baki.

Ido da baki na waro da mamaki

tuno wan da suka taɓa kiran sa da Daddy a makarantar su nace "Wani Daddy mutumin nan ko?, a ina kuka san shi dan gidan ku da har zaku rika ce masa wani Daddy."

Naseem daya cika chocolate a bakin sa yace

"Ai Daddy yace kuma dai jo ya auke mu ya kai mu c

an guyin kifi babba."

cikin tsawa nace "Bana ce muku kada wani yasake baku abu ku karɓa ba? ashe bakuji ba so kuke nazane ku ko?, bana ce muku nice Daddyn ku nice Mommy'n ku ba, shi ba Daddy'n ku bane, baku san shiba shima bai sanku ba, bakuda Daddy nic

e Daddy'n ku, kuna jina dai ko?."

nariko kunnuwan su ina jijjigawa a hankali, suka gyaÉ—a kai.

shiru nayi tare da komawa na jingina bayana da jikin gado jiki a sanyaye nashiga maganar zuci

"Kuhi hakuri Æ´aÆ´ana ni zan cigaba da zame muku uwa kuma uba a

duniyar na."

jin kwalla nakokarin zubomin nayi saurin dakatar dashi...

A ranar nasa aka kawo musu chocolate dawsu kayan makulashe aka kara kan wan da yake gida.

washegari ranar asabar bamu wuni a gida ba yawon guraren shakatawa muka tafi, ni Faty Nas

eem Nasmah da kuma Talatu, sai direba. sai yamma muka dawo niki niki da kayan makulashe, washegari ranar Lahadi ma muka kuma fita, shima sai yamman muka dawo a part É—in su Inna wuro muka yada zango sai bayan isha muko koma side É—in mu, ai ko muna shiga s

u Nasmah suka ɓingire da bacci.

koda gari ya waye dakyar nata da su Talatu ta tafi da su dan yimusu wan ka da shirin makaranta, dan tare jiya muka kwana da su.

kamar kullum na rakosu muna É—agawa juna hannu suka fita.

ina komawa ciki wanka nayi nashir

ya cikin les copie colour da É—an ratsin gold ajiki,

da misalin karfe 10 da rabi nasauko kasa da mayafi akai na sai Æ´ar karamar jaka mai É—auke da wayoyina da wasu Æ´an kuÉ—i dana saka ciki,

dinning area na nufa, in da na tadda Zulai tagama shirya koma

i na breakfast, a É—an gaggauce nayi breakfast É—in, ina yi ina duba agogo, dan fita zamuyi da Bappa zuwa asibitin da ake ginawa dasunan Inna ganin yan da ai kin ke tafiya, ina saurin ne dan jiya nace mishi karfi goma da rabi zamu tafi nasan kuma yanzu hak

a yagama shiri ni yake jira.

koda na fita a kofar masallaci dake ta nan cikin gida na taddashi zaune, na karaso in da yake tare da gaida shi, daga nan muka shige mota muka nufi asibitin.

masha Allah asibiti yayi kyau saura kaÉ—an a kammala aiki, bamu bar

asibitin ba sai wajen karfe 12:20pm nacewa Yakubu muwuce makarantar su Nasmah mu É—auko su.

Abakin get É—in makarantar Yakubu ya faka mota yafita da sauri yana faÉ—in

"Bari naje na fito da su". yayi cikin makarantar da sauri, muna nan zaune can yafito

da sauri kamar zai kife kasa yakaraso gefen da nake yace

"Hajiya wai an zo an É—auke su."

ido na waro da mamaki nace "Wa yazo ya É—au kesun bayan kai muna tare da kai ina ce kai ne me zuwa É—aukar su."

Bappa yace "Zancen banza kai wani direban akayi m

usu sabo ne da zaizo É—aukar su? ko dai bakaji abun da suka faÉ—a da kyau bane?."

yace "Wlh haka mai gadin yafaÉ—a Bappa."

da sauri Bappa ta buÉ—e motar yafita ai ko nima da sauri nafita narufa masa baya har ina haÉ—awa da sassarfa.

babu kowa cikin maka

rantar sai mai gadi da masu kula da tsaftar makarantar sai shara da goge-goge suke, hankali tashe Bappa ke tambayar mai gadi, mai gadin yace

"Ai ko minti goma basu da tafiya ba duk É—azu muna tare da su anan da wasu É—aliban mota tazo tafaka nan bakin get

suna ganin motar suka zuba a guje zuwa gurin motar suna murna, da naso hanasu dan ganin ba É—aya daga cikin irin motocin da ake zuwa É—aukar su da shi bane, to ganin yan da suke ta murna sukayi gun motar a guje yasa nayi tunanin É—aukar su a kazo, dama ba

daga gida akazo É—aukar su ba!."

maigadi yakarashe maganar yana buga kirji.

Yakubu da gumi yafara keto mishi kamar zai fashe da kuka yace

"Ina ni ke zuwa É—aukar su kuma gani a gaban ka sai kuma hajiya wata rana,ko mutumin yasako irin fuskata ce ya zo."

Bappa yace "Amma kuwa abun da mamaki amma ya kamata lokacin da kaga ba É—aya daga cikin motocin da ake zuwa É—aukar su da shi bane yazo kama yayi kaje kaga ko waye ne,amma wani abun mamakin da kace wai sun je gurin motar da gudu kuma suna murna to ko w

ani ne daga gida yazo É—aukar su tun da sun san mun fita har da direba?."

ni dai kasa magana nayi sai ɓari da jikina yake cikin matukar tashin hankali tuni idanuna suka kawo ruwa kan kace me hawayen suka fara sauka.

murya na rawa Yakubu yashiga tafa han

nu da salati yana faÉ—in

"Dama ance yanzu masu garkuwa da mutane sun canza salo akwai wani abun da suke yi sai dai kaga mutum na ta binsu kamar ya sansu harsu tafi da shi, wayyo Allah Naseem da Nasmah ko dai sune."

cikin gwalalo ido mai gadi yace

"Wayyo

Allah nashiga uku wayyo ai kina shikenan dama ance idan aka sami matsala to abakin ai kina, ashe dama tsarin da masu garkuwa da mutane suka fito dashi kenan? shi yasa yarannan sukayi ta tsalle kamar doki suka ruga in da motar take, ashe jansu ake taciki k

amar kuran karfe."

ɓarin jikina ne yakaru yayin da zuciya ta ke bugawa da karfi gudun hawaye na yakaru.

Bappa yace "Kai ya isa haka Falyakum khairan au yasmuq, in sha allahu babu abun da zai faruku muje gidan mugani wata kila daga gida ne akazo aka É—au

ke su tun da sunsan bama gidan."

yadube ni yana cigaba da faÉ—in

"Kice Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un."

kalmar nashiga nanatawa kana muka juya gun mota, muka bar maigadin nan tsaye yana ta rafka salati dafaÉ—in shikam yau yasan ai kin sa yazo karshe

har in sace yaran akayi.

acikin mota Bappa yarika zuba addu'o'i yakuma hanani kukan danake shirin yi yace nayi ta faÉ—in

Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.

a haka muka isa gida.

Muna isa Yakubu yayi hon maigadi ya wangale get yana kokarin wucewa par

king lot nace

"Ka sauke mu anan."

dan gani nake kamar motar bata tafiya da sauri tsabar tashin hankali.

tun kan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login