Showing 108001 words to 111000 words out of 135595 words

Chapter 37 - HAMDAH BOOK4 COMPLETE

dama nace kazo ya faÉ—a a kunnen ka bazai bamu sako mu faÉ—a maka ba."

sai a lokacin Bappa yayi magana dan sai yanzu ya fahimci in da batun ya dosa, yace

"Kai yaro kace É—an

ka ne wannan ta ya aka yi ya zamo É—an ka bayan ga uba da uwan yaron anan?."

mari ya kai wa yarin yar yace

"FaÉ—a musu yan da kika yi kika siyar min da É—ana, a miko min shi na tafi ina da shara yau."

duban ta Bappa yayi yace "Ke yarin ya ya akayi haka

, da gaske É—an sane?."

hawaye ta shiga share wa tana jan hanci tace

"Eh É—an sa ne, dama..dama..dama lokacin ina da ciki ne da zan haihu shine iyaye na suka kore ni suka ce ba a gidan su ba, shine naje asibitin wannan."

ta nuna Dr Mukhtar dayake ta tsi

lli-tsilli da ido,

kana ta cigaba da faÉ—in "Shine na haihu sai waÉ—an nan suka kirani."

ta nuna Na'ima da Raliya sannan ta cigaba

"Shine suka ce suna son ɗan in dai yadda shi zan yi, shine wannan ta bani kuɗi ta karɓe sa."

ta karasa maganar da nun

a Na'ima.

Bappa ya dubi Dr Mukhtar ya sunkuyar da kai kasa yace

"Abun da ta faÉ—a haka ne shin a asibitin ka akayi haka?."

Dr Mukhtar ya shafa gefen fuskar sa daya kunbura in da bakwaren ya ya mare sa da adda, ya gyaÉ—a kai tare da faÉ—in

"Eh haka ne a

asibiti na ta haihu kuma ni na karɓi haihuwar, kuma wannan shine ɗan."

ya nuna É—an dake rike hannun Na'ima.

salati kowa ya sake cike da É—inbin mamaki, masu tafa hannu suna tafa wa masu salati suna yi.

Abbu ya dubi Na'ima yace "Mika musu É—an su."

jiki a sanyaye cike da taren jin kunya ta tura musu É—an.

bakwaren ya ja hannun É—an yana faÉ—in

"Taho nine nan uban ka, ke kuma wuce muje ko na tsastsaga ki anan."

ya kaÉ—a keyar yarin yar suka fita,

yaja Æ´an uwan sa Æ´an sara suka yi gaba.

Dr Mukht

ar ma yaja kafa ya fita tsimi-tsimi Raliya ta bi bayan sa...

Baya Ya SALEEM yayi yayin da hannunsa ke dafe da kirjin sa.

a hankali ya shige cikin É—akin Ya Masa'ud.

Mamie ta dubi Na'ima da take jin wani irin tsanar ta rai ɓace tace

"Shi yasa ko

dai-dai da rana ɗaya ban taɓa jin son ɗan nan ba ashe sabo da ɗan shege ne ba jinina bane."

Mamie ta juya ta nufi side ɗin ta rai ɓace.

shewa Aunty Rafee'at tayi tashiga tafa hannu, ta zo gaba Na'ima tana yi mata wani irin kallon sama da kasa

tace

"Ai dama karshen muna fuki jin kunya, duk wanda yace ruwan wani bazai tausa ba nasa ko lum-lum bazai yi ba, zakaran da Allah ya nufa da cara kuwa ko ana ga muzuro ga shawo sai ya yi,

wacce kika lankaya wa tayi ciki da auren ta kika kazan ta mata ciki, ga

ta a gaban ki ta zame miki abun kallon abin kwatance,

É—an shege zaki kawo mana cikin family bama bukatan bare a cikin mu,

fita mana agida makira algunguma kaÉ—an kika fara gani,

sai duniya tayi juyin masa da ke."

Aunty Jaleela tace "Kamar yanzu kuwa z

aki fara ganin aya, sai kin gwammaci mutuwa da rayuwar ki, fita a kace fita mana agida."

suka kaÉ—a ta har waje.

niko ina taaye ina kallon abin kamar a Film,

Bappa ya girgiza kai yace

"Duk wan da ya nufi wani da sharri a kwan a tashi kan sa yake koma w

a, Allah ka tsare mana imanin mu."

aka amsa da amin kana muka juya muka koma ciki.

kowa yana jinjina lamarin.

har muka zazzauna ana alhenin abun.

Bappa yana É—ago kansa idanunsa sukayi arba da wasu hotunan Inna guda biyu acikin glass É—aya, dake like

jikin garun parlour'n,

huf ya mike tare da nuna hoton da yatsa yana tafiya in da yake, cikin rawar murya Bappa yace

"Adda A'i."

da mamaki kowa ke kallon sa su Abbu suka mimmike tsaye,

ya juyo da sauri yana faÉ—in

"Wannan hoton a ina kuka samu?."

Abba

suka haÉ—a baki wajen cewa

"Innar mu ce ka santa ne?."

da sauri Bappa ya fita gurin mota yaje ya buÉ—e kana yabuÉ—e jakarsa dake cikin motar ya ciro wani hoto kana ya dawo cikin parlour da sauri,

ya mika musu hoton wan da yake iri É—aya da É—aya daga c

ikin hotunan,

da mamaki su Abbu suke kallon hoton iri É—aya da wan da yake jikin garun parlour,

Bappa yace "Dai-dai da rana ɗaya ban taɓa ajiye hoton a wani guri daban ba ko da yaushe yana cikin jakata sabo da girma da matsayin wacce take cikin hoton

a guri na,

Adda ta ce ita ta sha nono ta bar min,

lokacin da Bappan mu ya rasu ina É—an kara mi, sai Æ´an uwan Baban mu suka É—auke ni suka tafini, kasanceaar ni na miji ne, suka barwa Maman mu Adda A'i,

kamar yadda kuka sani mu fulani bamu fiye zama gu

ri guda ba, musamman fulani makiyaya, haka mukayi ta yin nesa da in da mamar mu take,har muka sallaka Nigeria,

tun da aka tafi da ni bansake haÉ—uwa da Maman mu da Adda A'i ba,

bayan wasu shekaru masu dama aka zo ma na da sakon rasuwan maman mu da kuma w

annan hoton, aka bani duk da lokacin da muka rabu da ita ina yaro ne sosai amma bai hanani gane Æ´ar uwa ta ba,

lokacin da girma ya same ni na dawo Nigeria da kaina ban san kowa ba hansan ta inda zan fara neman Æ´ar'uwa ta ba, rugar mu da na rike sunan sa

nayi ta bincike a kansa har naje rugar, duk wanda na tambaya sai ya cemin baima santa ba,

a haka na fauwalawa Allah komai nacigaba da addu'a Allah ya haÉ—u mu da ita, haka na rika ajiyar hoton nan harrrana mai kamar tayau,

ashe dai da rabon mugana ina A

dda A'i take tana ina?."

Abbu yace "Allah yayi mata rasuwa."

salati Bappa yayi sai ga hawaye a idon sa, kowa sai da yayi kuka tuno da Inna..........!

8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 32

Ummi ta rika bubbuga baya na tana faÉ—in nayi hakuri,

yayin da hawaye ke cigaba da zuba a idanunta.

da sauri na saki Ummi na juyo hawaye na zuba a ido na, na saki murmushi hawaye na zuba cikin matukar farin cikin ganin yau gani ga mahaifiya ta, na dubi Ahmad nace

"My ga Ummi yau gani ga Ummi na, Bappa Ummi

na ne Ummi na ne."

sai na kuma rungumar ta ina hawaye haÉ—e da murmushi.

wani irin farin ciki ne ya lulluɓe zuciyoyin su Ahmad yace "Barka da zuwa Ummi hakika mun yi farin ciki da zuwan ki."

Bappa ko Masha alhmdllh alhmdllh yake ta faÉ—a yayin da fuska

rsa ke bayyana jin daÉ—i.

security kuwa gaba É—ayan su kowa yayi zuruu.

Ummi ta share hawaye da gefen mayafin ta tace

"Duk da sun kore ni na ayyana a raina bazan yi nisa da nan ba sai na ga HAMDAH da take cikin gidan nan dan jiki na na bani kece kiyi ha

kuri HAMDAH."

na sake ta tare da faÉ—in "Ummi kiyi hakuri."

sai kuma na juyo in da security suke nace

"Uwa ta kuka yi wa wulakanci kuka hana ta shiga gidan duniya bana kiyama ba."

Ahmad ya É—aga murya cikin tsawa yake ce da su,

"A wani dalilin zaku ha

ta ta shiga bayan ta sanar da ku ko wacw ce ita!?."

suka haÉ—a baki wajen cewa "I'm sorry sir sabo da ba'a sanar mana da zuwan nata bane, kuma bayi zaton mamar Madam bace da gaske mun É—auka waÉ—an da suke alakanta kansu da ita ne kawai dan a barsu su shi

ga."

Ahmad yace "Sai kuma baza ku iya kira ko zuwa ku sanar a kwai bako a waje ko ansan da zuwan sa ba? wani irin banzar aiki kuke ne!,

an ajiye ku kurika wulakanta mutane ne a bakin get."

Bappa yace "Sam bai dace ba ya kama ta idan irin haka ta faru, h

ar idan ba'a sanar muku da zuwan bako ba, to idan yazo ba ku kore sa ba, ku nimi masaniya kan cewa an san da zuwan nasa ne sabo da wata rana zaku iya korin É—an gidan abun kuma ba zai yi kyau ba,

to ba gashi yanzu kunyi a kan uwar mai gidan ba."

Ummi tay

i murmushi cike da Dattaku tace

"A'a babu komai wlh, ai abakin ai kin su suke, kuma hakanne zai nuna tabbacin jajircewa kan aikin nasu, basu yi laifi ba sai dai kawai a kiyaye gaba."

security suka shiga bawa Ummi hakuri kamar zasu zuba goiwowin su kasa,

tace wlh har cikin ranta babu komai kuma bataji haushi ba dan a bakin ai kin su suke.

na ja hannun Ummi cikin farin ciki muka yi ciki in da na karɓi jakarta na rike a ɗaya hannuna.

da sauri Inna Wuro ta fito dan Faty taje ta sanar mata Ummi na ta zo, a

tare duk muka É—unguma mukayi cikin parlour,

Bappa yace shi zai shiga Masallaci bari su yi salla zai shigo su gaisa,

a parlour Ahmad ya mika min Ahmad karami yace shima bari ya je yayi salla.

gaba É—aya baki na yaki rufuwa farin cikin da nake jin kaina

ciki tamkar anyi min albashir da aljanna.

a kan kafar Ummi na dire Ahmad karami, Ummi ta rike sa ta na faÉ—in "Yaya sunan sa?." nace Ahmad.

tace Masha Allah Allah ya raya da imani."

su Talatu suka shigo parlour'n suna kwasar gaisuwa da tayani farin cik

in zuwan Ummi na.

Ummi ta kurawa Naseem da Nasmah ido da suke ta tsalle gefen ta sunayi wa Ahmad karami kawa, ta dube su da murmushi tace

"Yaya sunan ku?." kusa da ni Naseem ya zo ya kawo bakin sa kunne na yace "Mommy ita yaya sunan ta."

ido na waro ta

re da saurin toshe kunne na wai shi a dole magana a hankali zai yi kada kowa yaji amma kamar ihu yayi min cikin kunne.

dariya duka parlour'n a É—auka, nace

"Mama na ne fa kun gaishe ta kuwa, sunan ta Ummi."

murmushi Ummi tayi yayin da ta kasa janye idan

unta kan yaran, ta janyo hannunsu tana faÉ—in

"Bari na faÉ—a muku sunana kuma sai ku faÉ—a min naku, suna na Ummi ku ya sunan ku?."

Naseem ya washe baki yace sunan sa Naseem ita kuma sunan ta Nasmah.

ai ko Nasmah ta shiga bubbuga kafa kasa wai ita zata

faÉ—i sunan ta da kanta.

Ummi tace "To faÉ—a min naji ban ji nashi ba."

ta washe baki tace Nasmah.

ai ko surutun su suka shiga cike ta da shi, suka rika bata rabaran da bata san tushin sa ba, har da labarin gobe Dadday'n su yace zai É—auke su da kanin s

u ya kai su ya kara siyo musu lilon doki.

Nasmah ta wawwaro ido tace

"Kuma muna da wani har guda haka kuma Daddy'n mu yace zai kara mana guda haka."

tayi mata nuni da yatsun ta huÉ—u da kuma biyu wan da za'a kara musu.

Naseem yace "Zo kiga lilon dokin

mu yana kusa da É—akin É—awisu ne fa."

yayi maganar shima yana wawwaro idanu

Ummi tace "To sai gobe zan je na gani."

Nan da nan nasa su Zulai suka cike ta da kayan ci da sha..

Su Bappa da Ahmad suka shigo su ka zauna bayan sun gaisa da Ummi akayi ta

hira.

gaba ɗaya nakasa zaune na kasa tsaye farin cikin ganin Ummi na yasa bakina ya kasa rufuwa farin ciki na yagaza ɓuya, ina jikin Ummi na naki matsawa ko nan da can,

a ɓangaren Ummi ma haka abun yake farin cikin da take jin kanta ciki yau bazai mis

altuba, sai kallon É—iyar tata take, yan da ta kara girma ta zamo cikakkiyar mace, ga Æ´aÆ´an da take ganin su a gaban ta wai duka Æ´aÆ´an HAMDAH ce, Allah mai iko buwayi gagara misali.

Bappa ya mike yace a barta ta huta ya fita, Inna Wuro Faty Talatu Zu

lai duk suka yi mana sai da safe suka tafi.

cike da girmamawa Ahmad ya mike ya lura Ummi nauyi take ji yasa ta kasa cin komai a gaban su, ya dubi su Nasmah yana faÉ—in

"Naseem Nasmah kuzo muje mu bar Ummi ta huta."

ya ja su suka haura sama.

nace "Ummi

muje sama kiyi wanka kici abinci ki huta."

tace "A'a nan ma ya ishe ni ba sai na haura ba."

murmushi nayi dan nasan ganin Ahmad ya haura ne, na mike na É—au jakarta nace

"To ki shigo nan Ummi." nayi maganar ina nufar É—aya daga cikin bedroom É—in cikin

parlour'n.

ta biyo bayana rike da Ahmad karami da yayi bacci,

É—akin a gyare yake tsaf dan kullum sai su Talatu sun gyara É—akunan duka.

Ummi ta rika bin cinin É—akin da kallo kana ta shinfiÉ—a Ahmad kan gado ta shige bathroom ni kuma na fito parlour,

abincin da aka kawo mata bata ci ba na kwashe na kai mata É—akin,

ina zaune ta fito tayi wanka haÉ—e da al'wala, na shinfiÉ—a mata sallaya, ta gabatar da salla.

tana idarwa na zuba mata abinci tana ci muna hira sai da naga taci abincin sosai kafin na mi

ke nafita.

na haura sama na tadda tuni su Naseem sunyi bacci Ahmad yana kwance a gefen su.

yana gani na ya mike ya janyo ni jikin sa, goshi na ya sumbata kana ya É—ago da murmushi yace

"An ga Ummi shine za'a mai da ni marayan gasken-gaske ko?."

dariya

nayi tare da jan É—an karamin gyamun sa nace

"Maraya kuma kana da ni da Aunty Rasheedat kake kiran kanka maraya."

hannunsa ya sakalo ta kugu na ya daÉ—a haÉ—e jikin sa da nawa kana yace

"To a sallame ni dan yau nasan ba lallai naji É—umin jikin kiba."

murmushi nayi nace "Ai kuwa kamar ka sani gurin Ummi zan kwana."

yace "Na sani ai kuma na yafe dan nasan a yanzu Ummi ta fini bukatar ganin ki kusa da ita,amma fa zan yi fama sosai na rashin ki kusa da ni."

nace "Kaje guje gurin Aunty Rasheedat mana nim

a bana so na barka kai kaÉ—ai."

yace "A'a ai da ni za'ayi murnar ganin Ummi'n nan." yayi maganar yana jan kumatu na.

dariya nayi kana a sannu na kai lip's É—i na ka nashi, sai da na ai ka masa da kwararan sakwanni na wan da nasan zai sami bacci cikin nut

suwa kafin na zame jikina na koma gun Ummi...

Ina shiga na tadda tana waya tana faÉ—in

"Yanzu haka ma ina cikin gidan a É—aki ina shirin kwanciya Yaya."

na karaso ciki da sauri tun da naji tace Yaya yasan Abbu ne take wayan da shi.

daga cikin wayar c

ikin matukar farin ciki Abbu yace

"Ina HAMDAH ina HAMDAH take?." Ummi da bakin ta ya kasa rufuwa tace "Ga ta nan bari na bata."

ta mika min wayar tana faÉ—in "Abbu'n ku ne." a gefen ta na zauna tare da kara wayar a kunne nayi sallama,

Abbu ya amsa yana

faÉ—in "HAMDAH HAMDAH kece?." wasu zafafan hawaye ne naji sun zubo min a hankali naji saukar hannun Ummi kan fuska ta tana share min, sai na saki murmushi mai sauti nace

"Ni ce Abbu ina yini."

Abbu yace "Alhmdllh ita ce." hele najiyo daga cikin wayar da

hayaniya idanuna na lumshe nakuma buÉ—e wa jin muryoyon Æ´an uwa na, Abbu yace

"Masha Allah alhmdllh sannu sannu HAMDAH sai mun zo maganar waya bazata wadatar da mu ba."

muryar Aunty Rafee'at najiyo tana faÉ—in

"Abbu bani inji muryar ta." tace "HAMDAH.

" nace "Na'am Aunty Rafee'at." sai kawai ta fashe da kuka, nima kukan na fashe da shi.

Abbu ya karɓi wayar yana faɗin

"To yanzu kam hankali na daf da kwanciya Rafee'at Jaleela kowa ya tafi gida sai kuma ranar tafi."

cikin shessheka Aunty Rafee'at tace

"Abbu Ina gobe ne zamu tafi."

yace "A'a sai jibi kuje gobe a shirya jibi a tafi."

farin cikin da na tsinci kai na ciki bazai misaltuba jin muryoyin Æ´an uwa na.

Abbu ya kashe wayar, Ummi ta rika rarrashi na ganin naci gaba da kukan har sai da taga na

daina kukan.

ranar kusan kwana mukayi muna hira da Ummi...

washegari da kaina na shiga kitchen muka shirya abun breakfast iri-iri, na kwashi na Ummi na kai mata cikin bedroom É—in da take, na É—au na Ahmad na kai masa sama, sai da na tayasa wanka kafin y

a barni na sauko.

ni dai a É—akin Ummi nayi wanka dan na sauko da kayan da zan sa da na Ahmad karami, Ummi da kanta tayi masa wanka ta shirya shi.

su Naseem ne suka shigo da shirin tafiya school Ahmad na biye da su,

cike da girmamawa ya tsunkuya ya gaid

a Ummi da tambayar ta gajiyar hanya, ta amsa fuska a sake. nan ma Ummi tayi ta kallon yaran har suka fita, tabbas yaran suna mata mugun kama da SALEEM musamman Naseem yafi kama da shi sosai,

a ranta take faÉ—in ko dai sune cikin da ta tafi da shi, sai kum

a ta kakkaɓe zuciyar ta da wannan tunanin, bayan ga ubansu nan tana gani,

ai dama HAMDAH kama suke da SALEEM dan Æ´aÆ´an ta sun yi kama da shi ba abun mamaki bane.

na lura da kallon da Unmi take ta yiwa su Nasmah, nasan tarin bambayoyi ne tare da ita

musamman kan yaran, sai dai har yanzu bamuyi wannan hirar da ita ba.

bayan munyi breakfast tare da Ummi, muka fito parlour.

Inna Wuro ta shigo, dan yanzu bata kwana cikin side É—in nan tun da mukayi bakwai sai dai da safe ta shigo tayiwa Ahmad karami wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login