Showing 6001 words to 9000 words out of 135595 words
fito da shi, ya mikawa Ya SALEEM hannu suka gaisa ba yabo ba fallasa Ya SALEEM ya ams
a masa gaisuwar, kana ya gaida su Mamie sannan ya wuce dasu É—akin da aka ajiye jaririn wan da yake karkashin kulawar na'urori..
Can suka hango jaririn cikin kwalba
wan da ake saka jariran dabasu kai watannin haihuwa ba, yanata wutsul-wutsul da kafafun
sa.
murmushi Raliya tayi a kasan ranta dan ganin shirin su yana tafiya yan da ya kamata.
da sauri Ya SALEEM ya karasa jikin kwalbar yana leka cikin kwalbar.
su Ummi ma gaba É—ayan su suka karaso jikin kwalbar,
Ido Mamie ta kurawa jarijin da ake kiran s
a da bakwaini gashi dai ba wani girma yake da shi ba É—an kankani ne, sai dai yanayin sa da wayon faskarsa ya girmi na bakwaini.
kai ta girgiza tare da juyawa ta kalli likitar tace
"Wannan shine bakwaini an ya ma kuwa anyi lissafin cikin nan dai dai ko
dai tara ne an ɓata lissafin kaga yaron da wayon sa."
da sauri Raliya tace
"Bai cika tara ba bakwai ne ai ko jiya ma sai da mukayi lissafin watannin da ita, yau kuma sai ga haihuwa kingan shi ai É—an misilili da shi".
Ummi tace "Ai kuwa gashi É—an kank
ani irin su idan suka tashi girma sai an gansu dan sai anci tuwo an koshi kafin a iya É—aukar su".
Ya SALEEM kam duk baya jin su dan ya gama shagalta da kallon yaron wai shine yau da É—a, wannan É—an nasa ne, wani murmushi yayi a kasan ransa wan da har sa
i da yabayyano kan fuskarsa.
Aunty Rafee'at data kafe yaron da ido tarr sai lokacin tayi magana.
"Wai wannan yaron shine bakwaini gaskiya wannan baiyi kamada bakwaini ba sai dai in ku kuka ɓata da lissafin".
tayi maganar cikin gatsali.
wani kallon s
ama da kasa Raliya ta bita da shi. Aunty Rafee'at ma irin kallon ta wasa mata tare da girgiza kai tana cigaba da yi mata wani kallon shekeke, sannan ta juya ta fita a cikin É—akin bayan ta gama ai kawa Raliya kallo masu cike da ma'anoni da yawa..
ko minti
30 basuyi a asibitin ba Mamie tace sutafi, haka dai suka fita suka koma gida.
Haushi da bakin ciki kamar Na'ima tayi yaya, wai ace kalar gaisuwar da surukar ta zata yi mata kenan, babu wani gaisuwa mai nuna tausaya wa babu wani nuna farin cikin samo ma
ta jika da tayi.
Raliya tace "Ni da É—ina da ke gajen hakuri dan Allah kibar wannan maganar kiyi shiru, ke kam dai ba kin haihu ba ina ruwan ki da su, wan da kika haifa masa ne idan ya miki zakiji zafi,ina ruwan ki da su ba wa É—an su kika haifa ba, can t
a matse musu ke meye damuwar ki, kinga wannan shegiyar yarinyar
zan nuna mata ni Æ´ar bariki ce cikakkiya ma kuwa ciki da waje na,
wai shegiyar Rafee'at É—innan kinga wani kallon da take min,
kinga wani kallon da take min kuwa, zan nuna mata halina bat
a sanni bane."
Na'ima tace "Him in dai wannan Rafee'at É—in ce ta wuce sammanin ki, wannan yarin yar da kike gani nima inada cikin ta kuma zanyi maganin ta, zan je musamman gurin boka domin yamin maganin ta,
zatagane da ni take rabu da ita mance da ita d
an wlh sai ta gane kuskuren ta."
Jin an murÉ—a handle yasasu yin shiru da zancen nasu,
Na'ima ta gyara kwanciyar ta kamar ɗazu, ta daɗa marairace fuska da shagwaɓe fuska.
ya karaso bakin gadon yadube ta kana yace
"Ya jikin?". cikin makirci da sal
on iya kirsa tace
"My SALEEM kaga É—an mu ko,ya bani wahala yaron nan,
É—an ka yabani wahala My SALEEM da kyar na iya haifo shi."
gefen fuskarsa ya shafo tare da naÉ—e hannun sa É—aya a bayan sa,
"ÆŠa na."
yafaÉ—a a kasan zuciyar sa yayin da yake jin
wani abu yana tsarga masa mai kama da farin ciki, can karkashin kasan zuciyar sa kuwa, jin wani abu mai nauyi yake yana kokarin tasowa sai kuma yanayi biyun suka shiga kokawa da junan su, yayin da farin cikin ya danne wancan nauyin da yake jin nauyin sa na
yau yafi na kullum. har sai da yakai hannu ya dafe kahon zuciyar sa.
daga Na'ima har Raliya ido suka zuba masa ganin yan da ya dafe kirjin sa da karfi tare da rumtse idanunsa,
wani abu ne ya gilma masa cikin duhuwar kwayar idanunsa da suke a rufe, wani
irin bugawa kirjin sa yayi kamar an fizgi zuciyar sa, sai yarika ganin wasu abubuwa guda uku masu haske suna yi masa yawo cikin ido yayin da bugun zuciyarsa ya tsanan ta, dai-dai lokacin da yaga abun suna daÉ—a tunkaro sa tamkar suna tahowa gare sa,
a z
ahiri kuma idanunsa a buÉ—e. sai kuma a sannu suka rika yin nesa dashi sai da sukayi nesa dashi sosai kana duhu takuma gilmawa sakanin su.
cikin tsananin karfi ya ware idanun sa, jin muryar Na'ima tana faÉ—in
"Ya dai My SALEEM?".
hannayen sa bi
yu ya cusa cikin sumar kansa kana ya burzar da wani huci mai zafi daga bakin sa
"I'm sorry."
ya faÉ—a tare da juyawa yabar É—akin da sauri, yayin da yake jin zuciyar sa naciga da yi masa nauyi, acikin Æ´an kwanakin nan hakan yana yawan faruwa da shi aka
i-akai, musamman in ya kwanta bacci yarika irin wannan mafarkan kenan, sai yari ganin haske guda uku suna dumfaro shi sai sunzo daf da shi sai su bashi baya yayin da duhu kuma zatazo ta mamaye hasken.
abun da yake gani cikin mafarkin sa shi ke kokarin zuwa
masa a zahiri, to ko bacci yafara a tsayen har ya fara mafarkin?.
yarika jefowa kansa tambayoyin da bashida amsar su..
Bayan sa Na'ima tabi da kallo cikin takai ci, a tunanin ta ɓarin jiki zaiyi idan yaji ta haihu, idan yaga ɗan kuma murna zai yi ba
adadi, sai kuma gashi sai wani shashshan kamshi yake,batare da ya nuna farin ciki da hakan ba.
A can kuwa bayan komawar su Mamie suna tare a parlour kowa na faÉ—an albarkacin bakin sa.
Mamie kam sam taji wannan É—a bai kwanta mata a rai ba,
kwata-kwa
ta taji É—an baya cikin ranta, tana yi masa wani irin kallon da ita kaÉ—ai tasan ma'anar sa.
Aunty Rafee'at fuska ta yamusa ganin su Fauzan da Nusaiba na ta murna wai matar Ya SALEEM ta haihu zasu sha suna tace
"Dalla kurufa mana baki, ni wallahi wannan
É—an ma kwata-kwata bai min ba wlh ya É—auko jinin uwar sa, ni bai min kama da bakwai niba haka bakwaini yake,sau nawa nake ganin Æ´aÆ´an da ake haifarsu wata bakwai sai ace wai wannan É—an wata bakwai ne, to can ta matse mata sai taje ta ta fama taje ca
n tayi ta haifar bakwaini ita ta sani".
kai Mamie ta girgiza.
Aunty Jaleela tace
"Ai wlh nima Aunty Rafee'at ɗan baimin kama da ɗan bakwai ba, sai dai idan ko sun ɓata lissafi ko kuma wani munafurcin ta ke kullawa ciki yafi wata bakwai tace bakwai t
o meye amfanin hakan, meye na cewa ciki wata bakwai bayan tasan cikin yafi bakwai É—in".
Ummi ko cemusu tayi
"To ku in ban da abun ku ta yiwu ta ɓata da lissafin ne in mutum ya ɓata da lissafi kam shi zai rika lissafi kuma alhalin ba haka bane, ai ba w
ani abu bane kakan iya ɓata da lissafi, kuma ai ana iya haifar wata bakwai yayi rai me lafiya ma yatashi har yafi ɗan wata taran kwari da kuzari, kar ku mance fa a asibiti ta haihu in ba bakwai ba taya za'ayi a sashi a kwalba likitan ai yafiku sanin me y
ake, Allah dai ya rayashi da imani".
"To amin".
cewar su dakaji amin É—in kasan baikai can kasar zuci ba...
Bayan kwana uku
tun da sukaje sau É—aya basu kara zuwa ba sai ranar da ta cika kwana uku shima da kyar Ummi tasa Mamie suka koma asibitin, ana
n suka tadda Æ´an gidan su Na'ima, nan ma basu wani jima ba suka baro asibitin.
satin su Na'ima biyu a asibitin, zaune suke da kawar ta Raliya Na'ima ta dubeta tana faÉ—in
"Kai Raliya wlh nagaji da zaman asibitin nan haka,
wai shin dole ne sai mun yi w
ata biyu a asibitin nan, dole wai saimunyi wata biyu wlh nagaji da zaman asibitin nan, wai dole ne har sai É—an yacika wata tara kafin mu koma gida, gaskiya asan yan da za'ayi kije ki sami Dr asan yan da za'ayi gaskiya, wlh nagaji da zaman asibitin sati fi
yu fa ina nan,gaskiya kije ki same shi asan yan da za'ayi nakoma gida."
Raliya tace
"Gaskiya nimafa nagaji da sintirin yau asibiti gobe asibitin nan,kullum kenan mutum na hanyar zuwa asibiti alhalin duk kanin ku lafiyar ku lau, jariri yana nan yana shan
madarar sa ke kina nan kina narkar abincin ki,
nikam mafa inada wasu a hannu wlh ina da wan da na karɓi kuɗin su, akwai wan da na karɓi kuɗin sa na kwana uku gashi nan ko wuni ɗaya bamuyi da shi ba, sakanina da shi da daddare mu kwana shi da yaso mu
je Abuja muÉ—an shana,
gaskiya bari naje na samu Mukhtar asan yanda za'ayi ki koma gida, nasamu naje su fanshi kuÉ—in su".
ta karashe maganar tana mikewa tsaye ta fita ta nufu office É—in Dr.
Bayan Raliya sun gama tattaunawa da Dr Mukhtar yace
"To
gaskiya akwai yadda za'ayi zata iya komawa gida abisa ita ta tirsasa tagaji da zaman Asibitin, nikuma sai na bada wasu shawarwarin da zata É—auru akai bayan ta koma gidan".
nan suka tsara yan da abun zai tafi.
a ranar da yamma suka sami sallama suka koma
gida, bayan shariÉ—oÉ—i da shawarwarin da Dr ya bata a gaban Æ´an uwan ta da kuma gogan wato SALEEM.
Tun da suka koma gida yaron kullum a kwance yake idan akazo barka ma sai tace ba'a É—au kar sa sabo da likita yace, kada a rika yawan sa masa hannu, sa
i dai azo a ganshi a kwancen kawai acikin bargon da kullum yake dukunkune a ciki.
haka tayi ta rainon É—an da masu da ita da É—an ma'aikatan ta da kuma Æ´an uwan ta, koda waÉ—an da suke kanta sukaga nonon ta ba ruwa basu kawo komai ba sai cewa sukayi ai
dama gaka wasu matan suke sai an nimi magani.
tuni aka nemo maganin wanke nono da ku ma ruwan nono, kan kace me ruwan nono yakawo tashiga shayar da É—a.
lokacin da suka cika wata biyu,wato É—an yacika wata tara kenan washegari tahaÉ—a wani gagarumin taro
.
biki irin na masu ji da naira, biki akayi na gani na faÉ—a naira tayi kuka, ranar SALEEM katuwar saniya ya yanka da katon rago,
yaron yaci sunan baban Na'ima.
ko da taji sunan da ya raÉ—a masa sam bata so ba dan taso yayi wa babansa ne takwara.
yac
e mata shi halacci yayi mata yasa wa É—an sunan mahaifin ta.
ranar kuwa kaÉ—an ya rage Raliya suyi faÉ—a da Aunty Rafee'at kan cewa da Aunty Rafee'at tayi yaron ma ko kama da su baiyi ba duk da kuwa girman da yake ta karawa,amma ko alamar kama da su bayay
i sai dai in ya É—auko zuriyar uwar sa dan ko kama da uwar tasa ma baiyi ba.
shike nan kawai suka kama zasuyi faÉ—a, wai akan me yasa Aunty Rafee'at zatace haka ai duk wan da yaga É—an yaga SALEEM, dan kuwa farin SALEEM É—in ma ya É—auko tun da kuwa yayi
kama da uban sa ai ba sai yayi kama da dangin uban sa ba. cikin masifa da bala'i da tsagwaran bariki Raliya take maganar.
Aunty Rafee'at ma kuwa bata yi mata da sauki ba tayi mata wankin babban bargo.
Allah ma ya taimaka Ummi tazo sunan ita ta raba faÉ—a
r. ta kora Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela tace duk su tafi an yafe musu sunan, dan ganin abun na daÉ—a girma dan har Aunty Jaleela tashiga faÉ—ar....
After 1 year
Acan kasar Saudi
Da sauri na fito daga cikin bedroom cikin hanzari jin kira
n da Ukhtee take kwaɗa min, abakin kofa mukayi kiciɓus da ita, fuska na kwaɓe ganin tana yi min dariya
"Ni gaba É—aya kin firgita ni na É—auka wani abun ne".
nayi maganar cikin harshen larabcin da nake É—an tsinta a gurin ta.
murmushi tayi tare da ru
ko hannuna
tace "Zo ki gani ga É—an'uwan ki yazo shi yace nayi mishi magana da ke".
tayi maganar ne cikin yaren ta da kuma yanayin da zan fahimta, dan yanzu ba laifi nakan fahimci abun da ake faÉ—a da larafci har nakan iya É—an gwamusa wa wajen yin magan
a da bashi da tsawo mafi sauki.
ta janyo ni muka nufi parlour.
turus nayi ganin wan da yake zaune a parlour'n su Naseem da Nasmah sun zagaye shi sai zuba masa surutu suke.
sai kuma nayi murmushi tare da karasowa cikin parlou'n ina faÉ—in
"La Uncle M
ahmoud kai ne yaushe ka zo?".
dan yanzu kunyar kirashi da sunan sa nake.
shima murmushin yayi yana faÉ—in
"Ban jima da isowa ba,Naseem yace min kina bacci da zaije ya taso kine nace a'a yabar hajiya ta huta".
baki nawashe ina zama kan kujera jin abun d
a ya faÉ—a
nace "Uncle Mahmoud kenan wai hajiya, hajiya kuma".
yace "Eh mana hajiya kai, taya za'a taso hajiya a bacci lokacin tashin ta baiyi ba ai dai gara abar hajiya tayi bacci da kyau da kyau".
dariya kawai nayi kana nace
"Sannu da zuwa ya hanya?
yasu Bappa da Inna wuro da Fatu".
yace "Hanya lafiya lau, sai dai badaga gida nake ba, amma dai Duk suna Lafiya".
Naseem da Nasmah suka mike a jikin sa sukabi bayan Ukhtee aguje sukayi side É—in Mammaa.
janyo table É—in da ya É—aura system É—in sa a kai
yayi, yajuyo shi ta gabana yana faÉ—in
"To hajiya komai fa ya kammala, shiya sa ma na dako musamman tun daga Nigeria zuwa nan na sarnar miki ki kuma ganewa idonki, ba sai an kira ki a waya an sanar miki ba."
Ido na kurawa system É—in, ganin bidiyoyi
sunata bayyana cikin system É—in, masu É—auke da tamfasa-tamfasan gidaje wane a turai motoci gidajen mai masallatai makarantu haÉ—e da kamfanoni da dai sauran su.
cikin tsananin mamaki na dubeshi nace
"Wannan fa Uncle Mahmoud?".
nayi tambayar ina nuna c
ikin system É—i. yace "Ah ai kin ki ya kammala wakilci a ka naÉ—a ni domin a kawo miki kiganewa idon ki musamman nataso domin shi".
da É—in bin mamaki nakuma kallon hotunan dake bayyana kan system É—in kana na maida dubana gareshi nace
"WaÉ—an nan É—in?.
"
yace "Kwarai kuwa sune,nakine sun kammala yanzu ke kawai muke jira ki koma abubbuÉ—e su, sannan kuma ba a gari É—aya akayi su ba a state da dama ne nacikin kasar mu Nigeria, ga jerin sunayin garirruwan da akayi gine ginen a cikin sa".
ya daddanna sys
tem É—in,sai ga sunayen garuruwan sun bayyana da kuma abubuwan da akayi a kowa ni garin.
yace "Kin ga yanzu zaki koma Nigeria a dai-dai dan kullum sai Bappa yayi maga, yanzu ma yace mu dawo tare sai dai ni bagida zan koma ba zan wuce Uganda tare da abokan
aiki na, akwai wani abun da zamuje muyi a can".
kai na jinjina dan nifa har yau ganin abun nake kamar wasa nace
"Him..Him.."
kasa magana ma kawai nayi sai Him. nake ta faÉ—a ina kallon ikon Allah,yayin da nakeyi wa Ubangiji buwayi gagara misali tasbihi
a can kasar zuciya ta.
rufe system É—in yayi kana yace
"Kin ga abubuwa yan da suka kammala ko, ko mai masha Allah, yanzu wani suna kike ganin za a sakawa kamfanoni da gidajen mai dai duk sauran kaddarori, wani suna kike ganin ya dace a saka musu, domin
idan akaje yin katin gayyata da sanarwa ayi amfani da wannan sunan, da zai zamo shine sunan duka kaddarorin".
Shiru nayi yayin da na saka yatsa na guda kan kuma tuna nayi sama da ido na alamun tafiya duniyar tunani, tare da É—an kyafkyafta idon.
kana nay
i kasa da idon cikin washe baki nace
"Yauwa na tuno sunan da nake so a saka masa *HAM'NAS*".
nayi kaganar cikin zakuwa ina cigaba da washe baki.
yanayin yadda nake maganar sai da ya bashi dariya ya ce
"To meye ma'anar *HAM'NAS* É—in kuma".
fuskata nar
ufe da tafin hannuna cikin muryar dariya haÉ—e da zakuwar jin yadda na haÉ—a kalmomin suka tafi normal nace
"Kaga ma anar sa, HAM sunana ma'ana HAMDAH, NAS kuma Naseem and Nasmah".
dariya sosai ya sake yana faÉ—in
"Kaga yarin ya mai basira, tabbas wanna
n suna yayi kuwa ba shakka *HAM'NAS* Co Fitroleum Nigeria Limited *HAM'NAS* Intranational School Of Science And Technology *HAM'NAS* Store Complex *HAM'NAS* Clinics *HAM'NAS* International Hospital, Eh ba shakka lallai sunan yayi *HAM'NAS* Allah ya taimaka
yayi jagora".
tsabar zakuwa kasa kuma cewa komai nayi sai baki na da yakasa rufuwa..�
A ranar da yamma Mahmoud ya wuce Uganda........�
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:50 - Ummi Tandama😇: HMD
🅿�3
Yau juma'
a babban rana, ranar da duk kanin al'ummar musulmi suke farin cikin zuwan sa, al'ummar Annabi suna ta kai komo hada-hada da shirye-shiryen tafiya masallaci domin sallar juma'a.
da sauri Ummi tafito daga cikin bedroom É—inta sanye da mayafi akanta, fuskart
a É—auke da yelwataccen annuri, da ka ganta kasan tana cikin matsanancin farin ciki. da sauri ta nufo bakin kofa,
lokacin Fauzan yasako kansa da gudu kaÉ—an yarage yayi karo da Ummi,
Ummi ta ce "Kai Fauzan bazaka rika yin abu cikin nutsuwa ba ko."