Showing 48001 words to 51000 words out of 135595 words
sai ya d
awo uku, zuwa lokacin na gama fihimtar har da ita yarin yar nake son sake gani.
nayi mamakin kai na matuka,
wata rana dana fita muka kuma haÉ—uwa da su a kan hanya ta ta zuwa mittin,
a tunani na ganin da nayi musu wannan rana shike nan zuciya ta zata h
uta da tunanin abun da bai shafe ta ba, amma ina bayan rabuwar mu da su sai naji tamkar kara min ake.
Bayan wasu kwana biyun sai nasa ayi min bincike a kan su wato ita da yaran dana ke yi musu kallon kannen ta ne,
nayi mamaki matuka lokacin da labar
in su ya iso min, dajin waÉ—an nan yara nata ne ma ana ita ta haife su.
mamaki na shi ne ganin ta kara ma sosai, nasamu cikakken labarin su, da duk kanin bayanan tarihin rayuwar su..."
shiru yayi tare da jan numfashi ya sauke, sannan ya ce
"Labarin su m
ai cike da ban tausayi na girgiza da jin lamarin, sai dai a yanzu su ba abin tausayi bane, dan Ubangiji ya zartar da ikon sa gare su..."
A hankali yashiga bata labarin su kamar yan da aka kawo mishi cikakken tarihin su, bai ɓoye ko rage mata komai ba k
amar yadda baiyi da farko ba, bayan gama shaida masa abin da aka sanar masa a kan su sai ya cigaba da faÉ—in
"Kin san wace ce wannan yarin yar?."
kai ta girgiza jiki a sanyaye yayin da idanun ta suka cika da ƙwalla tap suna shirin zubowa.
taji bala in
tausayin su da jin labarin su jikin ta yayi matukar sanyi.
ya ce "I ta ce mai Company *HAM'NAS*."
ido ta waro ta ce "Mai Company *HAM'NAS* mai *HAM'NAS* Nigeria Limited?."
"Kwarai kuwa ita ce."
kai ta jinjina tare da faÉ—in
"Allah mai iko wan nan shi
ne sakayyar da mafificin rahama yayi mata sakamakon cin jarabawar da ya É—aura mata tabbas labarin rayuwar ta abun a tausaya ne, a da yanzu kam Allah yayi mata sauyi da mafificin rahamar sa."
sai gata tana hawaye cikin matsanancin tausayin labarin rayuwa
r HAMDAH da taji, har da jan sheshshe ka.
ta kai hannun ta share hawayen ta tare da faÉ—in
"Allah kayi mana mai kyau kasa mu dace duniya da kiyama."
ya ce "Amin." sai ya saki hannun ta yakoma ya kwamta tare da lumshe idanun sa.
a sannu ta gyara ita ma
sai ta kwanta gefen sa tare da yin pillow da damtsen hannun sa, a hankali takai hannun ta kan fuskar sa, a sannu tashiga shafa gefen fuskar sa, in da kayataccen saje ke kwance a gurin lub-lub gwanin ban sha'awa.
duban sa tayi da kyau cikin kulawa a hankal
i ta ce
"Aboki." idanun sa da suke lumshe yaÉ—an buÉ—e su a kanta sannan ya amsa da
"Na'am." in da ya am sa can cikin kasan mako shin sa, laɓɓan sa ne suka motsa tanan ta fahinci ya amsa kiran nata.
idanun ta cikin nashi, sannan tace
"Aboki bayan sa
nin labarin ta kuma sai me baka karasa bani labarin ba."
idanun sa ya lumshi cikin son kawar da zancen ya ce
"Wani labarin kuma ai na gama baki labarin."
murmushi tayi tare da faÉ—in
"Baka kara sa ba da saura dan acikin duk kanin labarin da ka bani bak
a bani asalin gundarin labarin ba, kawai dai ka ce min kana
jin wani abu a kanta mene ne shi?."
"Ba ko mai fa." yafaÉ—a a takaice yana gyara kwanciyar sa, tare da juya wa ya fuskanci jikin garu, yana faÉ—in
"Zanyi bacci ki tai maka min kisa yayi daÉ—i."
hannun ta ta cusa karkashin gashin kansa ta bayan keyar sa, yana jin haka da sauri ya juyo dan yasan jan masa sumar zatayi da karfi bawai tayi masa yan da zaiyi baccin ba.
dariya tayi tana faÉ—in
"Ai da baka juyo ba Aboki yau aski zan maka."
ido yaÉ—a
n waro ya ce "Aski da hannu."
farr tayi da ido ta ce "Zan nimo abin yin askin ai taɓawa nake naji ta in da zan fara."
ya ce "FaÉ—i gaskiya dai Æ´ar guntun muguntar ce ta motsa."
dariya takuma in da shi kuma ya murmusa yana kokarin mai da idanun sa ya l
umshi tayi saurin dakatar da shi ta hanyar faÉ—in
"Me zaka ɓoye min ne iye sai fa ka karasa bani labarin nan dan baka gama bani ba."
shiru yayi bai ce komai ba,
Murmushi tayi tare da faÉ—in
"To ni bazan karasa baka labarin, tun da yau ka aro hijabi ka
sakata sakanin mu, zan yaye ta yanzu dan babu ita sakanin mu har gaba da abadan."
É—an numfashi ta ja tare da cigaba da faÉ—in
"Tun da ka sanya ido kanta Ubangiji yayi ikon sa,ya datsa maka sonta, a lokacin da baka taɓa sammanin a kwai ranar da hakan z
ata kasan ce da kai ba, dan kai a tunanin ka ni kaÉ—ai ce Ubangiji ya dasa maka sona cikin zuciyar ka, babu wata macen da zata kuma samin gurbi cikin zuciyar ka,
ka mance da cewa Allah shi ne sarkin mulki mai yin yadda yaso da bayin sa, nasan ka da son ya
ra amma son da kake yiwa waÉ—an nan yaran na daban ne, kana yi musu irin son da uba yake yi wa Æ´aÆ´an sa, haka ne ko?."
tayi magaran tana duban sa da murmushi sosai kan fuskar ta.
numfashi ya sauke kana ya janyo ta jikin sa sannan ya ce
"Haka ne." ya
faɗa dan babu ɓoye-ɓoye ko karya sakanin su, ko yan zu ma dayayi kokarin yin hakan sabo da wani dalilin yasha wuya sosai da fama da abun cikin zuciyar sa.
wani yelwataccen murmushi ne ya baiyana kan fuskar ta, kana ta ce
"Kana son ta?." kai ya gyaÉ—a
alamar Eh sannan ya ce
"Amma abar maganar domin bana jin zan iya haÉ—a ki da wata."
gyemun sa taja, sai kuma ta ɓata fuska sannan tace "Haka Allah ya ce, bana son ka canza daga halin dana sanka baya yi maka kyau,
dama kan haka kake masaltawa zuciyar ka
aje damuwar da bata saba ba, shine har kake son ka koyi karya ko?,
kana son ta, tun daga farkon labarin ta naji nima ina son ta ina son Æ´aÆ´an ta, ita ta musamman ce yarin ya karama mai halin man ya ba kasafai ake samun irin su a duniya ba, ni ma ina so
n ta, zan ku ci gaba da son duk wani abun da kake so har idan bai saɓawa Shari'a ba har karshen rayuwa ta zan cigaba da son sa."
mike wa zaune yayi ya lankwashe kafafun sa kana ya dubi ta da É—in bin farin ciki da jin daÉ—in kasan cewar ta cikin rayuwar
sa ya ce
"Haki ka babu wan da yakai ni dace da samun mace ta gari, da ace kowani na miji irin ki ya samo a matsayin mata shi da damuwa ko tashin hankali bazai gansa ba har karshen rayuwa, Allah yayi miki albarka matar aljanna, faran tamin da kike Allah ke
ma ya faran ta miki fara Æ´ar duma-duma ta."
"Ameen Ameen ameeeeeen."
tafaÉ—a tana jan É—an gyemun sa irin na gayun nan.
sai kuma da sauri ta saki gyemun ta ce
"Ka faÉ—a mata kana son ta kuwa?."
kai ya girgiza ya ce "Ban faÉ—a mata ba."
ta ce "To me
ya sa?." ya ce "Sabo da baza ta amince ba."
"Kamar ya, zakace bazata amin ce ba, baka tin kare ta da batun ba ka bata laifi." tayi maganar tana rike haɓa.
kuma tun ta yaja kana ya ce
"Um to tana da masifa tsiwar tsiya ce da ita."
dariya tayi sosai ta
re da tafa hannu ta ce
"Masifa haÉ—e da tsiwa kuma, a'a kada kayi wa kanwa ta fin tsayi." shiko murmushi yayi yana faÉ—in
"Allah idan ta fara tsiwa sai kin sha mamaki."
dariyar ta kuma ta ce
"Zata amin ce kai dai je ka latsa ta kuma ka gani in sha Alla
hu zata amin ce, wata mace ce zataki tayin ka duk haÉ—uwar ta da dukiyar ta kuwa,
ai mijin nawa da farin jinin sa aka halitto sa, shiyasa ma har gida ake kawo masa hari, wannan bazawarar taka ma jiya ta zo."
dariya duk kanin su suka fashe da shi, zillo t
ayi gefe ganin yami ko hannu yana kokarin ruko ta, tasan sarai baya so tari yi masa maganar ire-iren waÉ—an nan matan da suke kawo masa hari.
janyo ta yayi jikin sa ya rungume yana faÉ—in
"Zakiyi baya ni." dariyar take tana daÉ—a shige wa cikin jikin s
a.
Kissing yashiga ai ka mata yana faÉ—in.
"Hakika nayi dace da mace ta gari Æ´ar uwa ta jini kawa kuma abokiyar shawara,
tabbas duk wan da yasa mi mata kamar ki yagama more yaruwar sa har gaba da abadan,
ke matar aljanna ce insha Allahu da yar dar All
ah zamu shiga aljanna ni da ke da kafafun mu."
Baki ta turo gaba ta ce
"To HAMDAH fa?."
ya ce "To har da ita." mumushi tayi tare da daÉ—a rungume shi ta ce
"In sha Allahu kuwa Allah ya tabbatar mana."
ya am sa da amee. nan suka shiga nuna wa junan su
tsantsar kauna da soyayya in da zancen ya sauya suka lula duniyar ma'aurata...
Wane ne AHMAD?......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:56 - Ummi Tandama😇: Ina fita daga cikin motar na shige cikin asibiti, batare da na jira fitar sa ba,
y
abuÉ—e wa su Nasmah yaruko hannun su suka biyo baya na, a kusan tare muka shiga cikin parlour'n asibitin.
cike da girmamawa ma'aikatan asibitin suka shiga yi mana maraba da zuwa,
direct office É—in Dr ya nufa bayan yace nazo mu shiga.
kamar bazan bisa
ba har sai da yakai bakin kofar office É—in kafin na biyo shi,
Dr na ganin mu ya mike da sauri yana amsa sallamar da Ahmad yayi.
Dr yace "Barkan ku da zuwa bismilla."
yanuna mana kujeru biyu da suke fuskantar juna wan da suke gaban table É—in sa, sai d
a muka zauna kafin shima ya koma mazaunin sa,
bayan gaisuwar da ya mika mana cikin girmamawa kana ya shiga yiwa su Naseem da suke like jikin Ahmad wasa.
Dr ya dubi Ahmad yace "RankashidaÉ—e an shirya za'a iya gudanar da aikin yanzu?."
yace "Eh." batare
da ɓata lokaci ba Dr ya kirawo wasu Nurse's biyu mace da na jiki, in da macen taja jini na namijin kuma yaja nasa.
muna nan zaune can da É—an jimawa suka dawo da Result É—in test É—in,
suna mikawa Dr suka fita, Dr yashiga buÉ—e takardun, shiru yayi tar
e da duban mu dukkan mu kana ya kuma mai da idanunsa kan takardan,
da sauri Ahmad da gaba É—aya yanayin sa ya sauya a Æ´an sakanni yace
"Yaya dai Dr me ke faru!?." yayi tambayar da yanayin shiga damuwa, jim kaÉ—an Dr ya É—ago da murmushi yadube mu yana
faÉ—in
"Komai dai-dai babu wata matsala."
Ahmad ya sauke wani dogon numfashi kana ya mike tsaye fuskantar sa É—auke da murmushi mai bayyana zallan farin ciki, Dr ya mika masa hannu yana faÉ—in
"Allah ya sanya alkhairi yabada zaman lafiya."
da sauri ya
ce "Amen amee ameeeeeen ya rabbil izzati."
ya mikawa kowa result É—in sa.
har gurin mota Dr ya rako mu sai da muka shige mota sannan ya koma ciki.
yaja motar muka fice daga harabar asibitin.
har lokacin fuskarsa sa na bayyane da zallar jin daÉ—i da far
in ciki,sai zuba murmushi yake. niko lokaci zuwa lokaci sai na ja karamar tsaki dan acike nake tam.
ya juyo gefen da nake ya dube ni da murmushi kana ya mai da idanun sa kan titi yace "Kyakkyawa ta kin ji albishir mai daÉ—i ko, ina cikin farinciki sosai d
a kika sami kyakkyawar sakamako a kaina, ina da tabbacin zaki daÉ—a samin nutsuwa dajin inganci lafiya ta,
baki ji yan da naji ba É—azu da Dr nan yayi shiru bai faÉ—i result É—in ba yana kuma kallon mu,
tunani na É—aya ace nine keda wata matsalar shike n
an nasan baza a bani ke ba, niko ban damu ace kina da wata matsala ba ahaka nake so kuma zanyi rayuwa da ke."
annurin fuskarsa yakuma faÉ—aÉ—awa sannan ya kuma dubana yana faÉ—in
"Kyakkyawa ta bazakiyi farin ciki da jin result mai daÉ—i ba dajin ingancin
lafiya ta."
baki na murguɗa nace "To ni inaruwana da wani ingancin lafiyar ka, mutum da lafiyar sa an sa yaje an wani ɓula masa jiki akarin banza, ."
nayi kwafa ina kawar da kaina gefe.
da sauri yace "Yihakuri Madam na tabbatar kina da lafiya dan
kisan lafiya ta yasa mukaje asibitin ayi min afuwa a gafarce ni, juyo ki kalle ni ki tabbatar da gaskiya ta kinji kyakkyawa ta."
daÉ—a kawar da fuskata nayi ina cuno baki gaba haÉ—e da murguÉ—a masa bakin,
murmushi mai sauti yayi yana leko fuskata... awa
ni katon ShopRite ya tsaya yajuyo gefen da nake yace
"Kyakkyawa ta sauko mu shiga."
ko kallo bai ishe ni ba bare yasa ran amsawa ta.
tare da su Naseem suka shiga can suka fito niki-niki da kayan ciye-ciye...
Muna isa gida tun kan ya karasa dai-dai ta p
arking nakai hannu jikin matfin motar zan buÉ—e najita gam, sai da ya dai-dai ta parking É—in batare dana dube sa ba nace
"BuÉ—e min." nafaÉ—a a takaice,
jin yayi shiru baiyi magana ba ya sani juyowa gefen da yake a kufule, karaf muka haÉ—a ido da sauri
na janye ido na, shiko numfashi ya sauke tare da faÉ—in
"kin ki faÉ—a min in da kike so ayi shagalin bikin mu."
"Da zai fi maka karike tambayar ka kadai na dami na da ita, danni babu abin da zai kai ni gurin wani biki."
ya ce "Shike nan an daina damin k
i duk yan da kike so haka za'ayi,
wai duk wannan lallen wani akayi kai gaskiya naji daÉ—i na, amma yayi kyau sosai fa, shine ba'a faÉ—a min nabada kuÉ—in lallen ba bayan an san hakki nane, kawo na kara gani dole ma na biya kuÉ—in sa."
yakai hannu ya kamo
nawa yana cigaba da faÉ—in
"Kice zan sha kallo gobe amma bari na fara tun yau."
da sauri nayi yunkurin fisge hannu na jin wani irin shock lokaci goda ya sarga min, sai dai yan da ya rike hannunan ban sami damar iya fizge wa ba.
"Sake min hannu Malam ka
buÉ—e min kofa nafita." nafaÉ—a ina ta kiciniyar kwatar hannun nawa. yace "To naji amma muga wayar ki."
"Adalilin me zan baka waya ta?."
"Aro zaki bani yanzu zan duba abu na baki."
gyara rukon wayar nayi a ɗaya hannu na na ɓata fuska nace "Ka sakar mi
n hannun kakuma buÉ—e min kofa."
numfashi ya fesa yajuya baya ya dubi su Naseem gaba É—aya hankali su na kan kallon katun É—in da ya saka musu a wayar sa tun fitar su daga ShopRite É—in nan.
kana ya dawo da kallon sa gare ni a hankali yaÉ—an rankwafo in
da nake har ina jiyo kamshin sa sosai, idanu ya lumshe tare da kuma buÉ—e wa a kaina, da sauri na rumtsa idanuna ganin yana ta kokarin saka nasa cikin nawa, ga yan da yamatso ni sai nake jin jikina yayi min nauyi wani abu mai kamada kasala nata kokarin zi
yartata,
"Ka sake min hannu ka buÉ—e min kofa." nayi maganar cikin É—an É—aga sauti yayin da idanuna ke rumtse.
yace "Zan sake ki zan kuma bude miki bayan kin bani aron wayar ki."
da sauri na mika masa wayar dan yana yin yanata daÉ—a shiga ta.
ya amshi
wayar tare da sakar min hannu, a tare muka saki numfashi mai sauti, nayi saurin gyara zamata na matsa tajikin kofa sosai.
shima zaman nasa ya gyara kana yashiga latsa wayata daga bisani yaÉ—au É—ayan wayar sa shima ya daddanna sannan ya mika min wayata y
ana faÉ—in
"Na biya kuÉ—in lallen da aka tsara min É—in nan."
yana rufe baki kuwa saiga shigowar alat na 1 million.
fuska na yamutsa, shiko murmushi yayi tare da buÉ—e min kofar, nafita da sauri ina tafiya ina kunkuni,
bayan na yabi da murmushi har na
ɓacewa ganin sa, yafito ya buɗewa su Nasmah yace musu su shiga ciki shi bari ya tsaya yayi salla dan lokacin ana kiran sallar magriba...
Ina shiga na tadda su Aunty Nasiba natakan ai ki sukayi min barka da dawowa na amsa inayi musu sannun su da aiki
.
koda na haura sama kayan jikina na narage sannan na fita na shiga ɗakin da su Hajiya Lubabatu suke, tana ganina tace "Yanzu nake kan maganar ki yauce rana ta karshe ga sauran kayan ki da yawa ga su dai na haɗa karɓi kisha yanzu cikin dare kya karasa
sauran."
tamika min cup mai haɗin magunguna ciki, na karba ina yamusa fuska na sha nan ta sani na kwaɓe kayana tashiga mulke ni da wasu sinadaran,
har wajen karfe biyu na dare idanun mu biyu dan a daren akayi min gyaran gashi,
bamu muka kammala komai
ba sai wajen karfe huÉ—u na asuba bayan ta wanke ni da ruwan turare nan na wuce É—aki na,
nafaÉ—a gado dan gaba É—aya idona rufewa yake sabo da tsabar bacci,
na gyara kwanciya ta ina kunkuni kasan raina
"Haka kawai a hana mutum bacci akan karin banza."
batare da ɓata lokaci ba bacci yayi awon gaba da ni....
Can cikin bacci najiyo muryar Faty tana bubbugani da kiran suna na,
mika nayi tare dayin salati na bude idanuna.
fuska na ɓata nace "Faty meye haka mutum yana baccin sa zaki kama tada ni."
ka
i ta langwaɓar gefe tace
"Ayya Adda HAMDAH kiyi hakuri Bappa ne yace nazo na tada ki yayi ta kiran wayar ki baki