Showing 114001 words to 117000 words out of 135595 words
sa murnar fitowar makudan kuÉ—a É—en sa.
yashige mota muna É—aga wa juna hannu har ya fita,
numfashi mai karfi na sauke san da motar sa ta ɓace wa gani na, jiki a sanyaye na juya muka k
oma ciki....
Da misalin karfi 6 da yanma,
har zuwa wannan lokacin ina dai nan ne amma gaba É—aya yanayin baya min daÉ—i,
kiran Ahmad ne ya shigo waya ta da sauri na É—aga tare da yin sallama.
ya amsa yana faÉ—in "Kyakkyawa ta mun gama komai na ka
rɓo kuɗin gasu a mota, sai dai banki yanzu sun tashi zan kai su gida gobe zan sa a kaisu banki."
"Masha Allah mun gode wa Allah, amma My kai kaÉ—ai kake tafi babu security?."
yace "Tare da su muke, ina zuwa."
ya faÉ—a tare da É—an yin shiru,
jin abu
n da yake faÉ—awa security yasani faÉ—in,
"My mene ne?." yace "Wasu mota ne guda biyu suke bayan mu tun É—azu na lura kamar biyo mu suke, ina son sanin ko su waye ne."
jin yana kokarin kashe wayar da sauri nace
"My kada ka ci gaba da tafiya da su ku ca
nza hanya ni dai hankali na bai kwanta ba kaji dan Allah."
yace "To yan da kika ce haka za'ayi kyakkyawa ta."
ina tsaye cikin É—aki rike da waya sai kaiwa da komo wa nake da kyar na samu na iya zama, tafiya da kuÉ—i masu yawa a mota irin haka a kwai hats
ari sai dai saukin ma É—aya yana tare da jami'an tsaro.
da sauri na É—aga waya shigo war kiran sa yace
"Kyakkyawa ta na iso gida ta hanyar canza hanya kamar yadda kika faÉ—a."
numfashi mai karfi na sauke nace "Kai alhmdllh amma wlh duk a tsorace nake h
ar naji hankali na ya kwanta."
yace "To je kiyi salla kiyi mana addu'ar dace wa da rahamar Allah nima masallaci zan tafi yanzu."
nace to...
Da misalin ƙarfe goma na dare ina kwance sakiyar yara na yayin da waya ke kare a kunnena kamar kullum, a duk s
an da Ahmad baya gida na to muna tare da shi a waya, ko yanzu hira da shi muke ta waya.
hamma nayi haÉ—e da mika tare da yin salati nace "My bacci." yace "To sai da safe kiyi baccin ki mai daÉ—i."
murmushi mai sauti nayi nace "Kai ma haka."
na kashe way
ar,na bi yaran da addu'a nima na shafa na gyara kwanciya ta, wani irin faɗuwar gaba naji da sauri na dafe kirji na, a hankali na fara nanata kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un³.
gaba É—aya bacci ya kairace a idona ina dai kwance shiru.
can wajen
karfe 2 na dare har lokacin ina kwance idanuna kuma biyu,
da sauri na janyo waya ta dake tsuwa karkashin pillow, ganin mai kiran nawa yasa ni saurin mike wa zaune na kai wayan kunne na tare da faÉ—in
"My." yace "Baki bacci ba kyakkyawa ta?." nace "Na kas
a nakasa yi My."
numfashi ya É—an sauke tare da faÉ—in "Ko na zo ne." kai na girgiza da sauri nace "A'a dare yayi sosai."
yace "To ki tashi kije kiyi al'wala kiyi nafila ko da raka'a biyu ne kiyi addu'a zakiyi Baccin."
nace to. yace "Ina su Naseem?."
"
Ga sunan suna bacci."
"Shafa min kansu duka ki sakawa Ahmad wayar a kunne."
nace "Yana bacci ai." yace "Eh sa masa."
a hankali nayi yanda yace na saka masa wayar a kunnen sa, magana ya soma yi a hankali yace
"Ahmad Ahmad Tijjani Sabil, kada ka bari wan
nan sunan ya mutu, kada ka sake duniya ta mance da wannan sunan duniya ta cigaba da faÉ—ar waÉ—an nan sunayen, kamar yadda nayi tsayuwar daka domin ci gaba da É—aukaka sunan Tijjani Sabil da har yau duniya basu mance da shi ba,suna kuma yi masa addu'a a ko
da yaushe,
Allah ya dauwamar da albarka cikin rayuwar ka kai da Æ´an uwan ka."
da sauri na É—ago wayar a kunnen sa ganin yana motsi, nace
"My me kuma ya kawo wannan maganar a daren nan?."
murmushi mai sauti yayi yace
"Kiyi hakuri kyakkyawa ta."
nace
"Na me fa?." yace "Ba komai rayuwar ce dai dole sai da hakuri, Ahmad yana son ki da kaunar ki."
numfashi na sauke zuwa yanzu maganganun sa na tun waye war garin yau da kuma yanzu sun fara da mi na, suna son su haÉ—e su cunkushe da yanayin fargaba da faÉ—u
war gaban da na ke ji.
nace "My nima ina son ka da kaunar ka."
yace "Nagode kyakkyawa ta, kin san me?."
nace "Sai ka faÉ—a." yace "ÆŠazu ban zo da kuÉ—in nan gida ba a hanya na kira manajan banki yazo sai mukayi canjen mota na bashi nawa wan da kuÉ—in y
ake ciki na karɓi nashi, shi ya tafi da nawa gidan sa gobe zai shige da shi banki."
nace "Ai ma hakan yafi gara da ka bashi kaga idan zai tafi ban kin sai ya tafi da shi yafi sauki ma."
jin ya É—anyi shiru baiyi magana ba nace
"My kai ma bacci kake ji
ka kwanta sai da safe."
yace "A'a naji karan buÉ—e get ne."
nace "A cikin daren nan?." "Ai nima shine na gani bari naje na ga ko waye mai gadi ke buÉ—e wa get da daren nan ina zuwa."
ya kashe wayar tare da duban qRasheedat dake kwance a gefen sa, ya mik
e ya sauko a gadon ya fito.
a hankali yake tafi ya har ya fito, ga mamakin sa sai yaga an kakkashe wutan gefe da gefen gidan har zuwa lungunar dake cikin gidan duk wutan a karkashe, iya wutan dake can bakin get da kuma na hanyar shiga side É—in sa da na R
asheedat ne kawai a kunne.
can ya hangi security kwakkwance a gurin zaman su duk suna bacci ko wannen su ya yada bindigan shi gefe suna ta sharar bacci.
gefe can kuma karnukan gadi ne suna zazzaune sai fidda harshe da ciccire ido suke.
motsi yaji a ta g
efen sa in da babu hasken wuta a gurin, a hankali ya mai da duban sa gurin ya kurawa gurin ido sosai, inuwar mutum ya hango tsaye a gurin. da sauri ya waiga É—aya gefen sa nan ma yakuma hango inuwar mutum, a hankali yayi baya yarika tafiya da baya da baya
cikin hanzari ya koma ciki, da sauri ya shige bedroom É—in sa,
ya isa jikin gado ya saka hannu sa kasan gado yaja sai ga drower ya bayyana yaciro bindiga ciki ya mai da drower ya É—ago yana gyara rukon bindigan a hannunsa.
Rasheedat ce tayi juyi tare da
ware idanun ta a kansa, da sauri ta mike zaune tana faÉ—in
"Aboki lafiya?." yace
"Æarayi sun shigo gidan nan." ido ta waro da sauri ta duro a gadon tana faÉ—in
"Ina security suke har ɓarayi suka sami damar shigowa gidan nan?."
yace "Akwai matsala sun
a nan abin mamaki duk kanin su bacci suke."
ya juya da sauri yana kokarin fita tasha gaban sa da sauri tace
"Aboki ina kuma zaka je?, a'a kada ka fita, kayi waya wasu jami'an suzo, kasan da abin da suka zo,
hakika da abin da suka taka tun da har kaga su
ka iya samin karfin guiwar shigo wa gidan nan duk tulin tsaron da ke gidan nan."
yace "Nasan abun da ya kawo su kuÉ—in nan ne kuma baya gidan nan ma zan je naji da su."
ya juya da sauri.
da gudu ta bi bayan sa ta rungume shi ta baya tana faÉ—in
"Aboki
kada ka fita ka tsaya na buÉ—e maka kofar baya ka fita ta can dan Allah kada kaje."
juyo wa yayi ya rungume ta yace
"Kawa ki zauna duk abunda zakiji kada ki fito, kiyi min addu'a kinji."
kai ta shiga girgiza wa tare da sakin kuka tana faÉ—in
"Aboki kad
a ka je na roke ka ka fita ta kofar baya."
jikin sa ya zare daga nata, lokacin da aka fara harbi cikin gidan, ya tallafo fuskarta yace
"Kiyi min alkawarin ba zaki fito ba duk abun da kika ji, kizauna cikin ɗakin nan ki kulle kanki bazan taɓa barin su s
ushigo ciki ba zan kare ki da yardar Allah,sannan kuma bulet bazai iya ɓula ginin gidan nan ba ko da ace sun yi yunkurin yin harbi cikin nan, kada ki fita kizauna a nan."
harbi aka cigaba dayi cikin gidan ta ko ta ina, Rasheedat ta daÉ—a kankame shi tana
faÉ—in kada ya fita.
da sauri ya sake ta ya fita.
ita ko kuka ta kuma sake wa ta durkushe a gurin, sai kuma ta mike da sauri ta isa ta kulle kofar, ta koma bakin gado tana cigaba da kukan..
A hankali cikin sanÉ—a Ahmad ya fito
yayin da ya gyara ruk
on bindigan sa da kyau.
harbin yashiga mai da musu daga inda yake laɓe suka rika musanyar wuta sakanin sa da ɓarayin.
kara ɗaya daga cikin ɓarayin yayi lokacin da harbin Ahmad ya same shi, ya zube a gurin,
kaimi ɓarayin suka kara akan harbin da suk
e, cike da tafasar zuciya cikin hanzari Ahmad yafito daga in da yake laɓe, yana fita daga gurin kuwa wani yayi saitin sa ya sake masa harbi a gefen kirji.
dafe gurin yayi cikin jin azaba da raÉ—aÉ—in shigan bulet jikin sa,
cikin tsananin tafasar zuciya
da kunar rai yayi gaba da gaba da su in da yakuma samin nasarar harbin mutum biyu a kafa,
cike da tsananin mamaki ya tsaida harbin da yake ganin amintaccen mai gadin sa, yana nuna shi wa wasu ɓarayi huɗu da suke tsaye da hannu,suka juyo tare da saita s
hi da bindiga.
kafin ya dawo da ga mamaki mai haÉ—e da tunanin daya tafi, sai ji kake tau-tau saukan harbi a cikin sa har sau biyu, kara yayi tare da damke cikin sa da jini ke tsiyaya, yayi tangal-tangal kafin ya isa kasa ya harbe su gaba É—ayan su su hu
É—un nan har da mai gadi cikon na biyar, a tare suka zube kasa mutattu.
yana kwance a kasa yana sakin wani irin numfashin wahala wan da yafi kama da na fitar rai...
Ina zaune a kan sallaya bayan na idar da nafila kamar yadda Ahmad yace min nayi zan
sami bacci,
gaba É—aya ilahirin jiki na babu karfi tamkar an zare min laka.
na janyo wayata lokacin karfi biyu da rabi,
na danna number Ahmad tare da kara wayar a kunne na, yayi ta ringing har ya yanke bai É—aga ba, kuma mai da kiran nayi shima har na c
ire rai da É—aukar nasa dan nafara tunanin bacci yayi.
wani irin razana da zabura nayi jin muryar sa yana faÉ—in
"Kyakkyawa ta sun harbe ni sun harbe ni......!
Mommyn Twins
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 34
Bappa yace "Allah
mai girma da
É—aukaka ashe dai jikata ce HAMDAH, a she dai jika ta ce nake zaune da ita cikin rashin sani, alhamdulillah masha Allah, hakika É—an adam baya fidda rai da rahamar Allah, ashe wata rana zan haÉ—u da jinina ga jiko ki na ga Æ´aÆ´a na, kuzo na
n Æ´aÆ´a na Allah yayi muku albarka."
ya janyo su Abbu jikin sa yana ta sanya mu
su albarka,
Abba ya nuna goggo Hauwa yace "Wannan ita ce kanwar mu."
Bappa yace "Taho nan kema."
Goggo Hauwa ta mike tana sharar kwalla taje in da yake su Abbu suka ce ta
bbas Inna tana faÉ—in tana da kani amma bata san in yake ba sun rabu tun suna kana na.
tabbas nima Inna tasha faÉ—a min tana da É—an'uwa sai dai tun suna kana na aka raba su yanzu bata san in da yake ba..
Uncle Mahmood farin ciki ya gama lulluɓe shi yau
shima gashi cikin ahlinsa.
haka akayi ta farin ciki yayin da farin cikin ya gusar da alhinin da Na'ima ta sakawa mutane...
Ahmad ya dube ni kasan cewar yanzu a kusa da shi na zauna, yace
"Ina taya ki murna na karuwar ahlinki, sai naji ina ma ace nine i
yayena da Æ´am'uwa na suke zagaye da ni haka."
kai na rausayar ina mai jin tausayin sa, na sauke hannuna kan nashi dake saman hannun kujera nace
"Allah ya haÉ—a ka da su a jannatir firdausi."
murmushi yayi tare da faÉ—in amin amin....
A ɓangaren N
a'ima kuwa tana fita a gidan, a hargitse cikin matsanancin tashin hankali ta tsari mai napep.
tayi gidan bokan ta,
tana zuwa ta shaida masa abun da ke faruwa.
bokan yace taje ta kawo cikiton kuÉ—in aiki yanzu ta dawo a rufawa kowa baki su mance da abund
a ya faru, a kuma kashe HAMDAH.
tace to ta fita abujajan ta dawo gida,
domin É—aukar kuÉ—in da Raliya ta bata aro ta kaiwa boka.
tana shiga gida ta dadda SALEEM a parlour da magunguna da gorar ruwa a gaban sa da alama yanzu yagama shan maganin.
tana ko
karin wuce sa tashiga É—aki, ya dakar da ita ta hanyar kiran sunan ta
"Na'ima." ya kira sunan ta batare da ya dubi in da take ba.
sai da hantar cikin ta ya kaÉ—a, jin yan da ya kira sunan nata a sama,da jin amon sautin sa da babu wasa ciki.
a fusace ya
mike tamkar fusataccen zaki yayi kanta,
tana ganin haka ta shiga ja da baya tana kokarin gudu,
da sauri ya cakfo ta tare da shako wuyan ta har saida idananun ta suka fiffito waje,yayin da numfashin ta yake kokarin barin jikin ta.
wasu tagyayen maruka ya
shiga shinfiÉ—a mata nan da nan fuskarta ya canza kala.
sai kuma ya sake ta da sauri tare da dafe kirjin sa da hannayen sa biyu, yashiga yin tari a hankali ya durkusa kasa.
Na'ima ko yana sakin ta da sauri tayi baya tana maida numfashi tare da shafa wuya
n ta da fuskar ta daya sauya masa kamanni...
hannun sa ya É—aga yayin da taren ke ci gaba da zuwar masa ya nuna ta tare da faÉ—in
"Fita tafi na daina ganin ki, ki sani har aba na haramta kaina gare ki, fita min a gida tafi na daina ganin ki,
kije Allah
ya haÉ—a ki da hukubar duniya dana kiyama."
numfashin sa ne ya soma fizga yayin da maganar tasa tashiga harÉ—e wa.
wani kururuwa Na'ima ta sake tace
"SALEEM kasan abun da kake faÉ—a kuwa, kana nufin ka sake ni sakin da baza ka sake dadowa dani ba har ab
ada,
haba SALEEM kada ka min haka wlh duk abun da nayi sabo da son ka nayi, ina son ka bana kaunar wata ta raɓe ka sabo da son da nake maka,
wayyo Allah SALEEM meyasa baka cewa HAMDAH ka haramta kanka har abada da ita ba, wayyo Allah na nashi uku
dan A
llah SALEEM kada ka min haka."
dagudu ta juya ta shiga É—akin ta, laidar kuÉ—in da Raliya ta bata aron sa ta É—auka tana faÉ—in
"Boka kai zaka iya min komai kai zaka fitar da ni cikin wannan hali, dole SALEEN ka cigaba da zama dani dole boka yasa ka ka z
auna da ni."
tafito da sauri, har lokacin yana durkushe dafe da kirjin sa.
tayi waje da gudu, tana duba mai abun hawa, babu ko alamar su a unguwar.
da kafa ta rika tafiya tana sauri kamar zata tashi sama bana ko ganin gaban ta burin ta kawai ta isa guri
n boka,
har ta fito babban titi zata sallaka ta koma É—ayan gefen dan ta tari abun hawa,
wani mai babban mota ne ya sako kai bata ankara ba sai ji kake keeeee motar tayi ciki da ita..
salati mutane suka fara akayiyo in kan titin a can karkashin motar a
ka ciro ta, gaba É—aya halittar ta ya canza sabo da sabar jin ciwo, bata ko motsi tana kwance kamar gawa.
wasu suna faÉ—in ta mutu wasu suna faÉ—in bata mutu ba,
aka kwashe ta aka garzaya da ita wani mafi kusa da gurin....
Da daddare duk yanda A
hmad yaso yatafi masaukin da yasa a tanar masa shi da security sa, su Abbu suka hana suka ce ya zauna a cikin dangi dan shima ya zama É—an uwa,
duk da sun san gida kamar nasu kam yayi wa Ahmad Tijjani Sabil kankanta.
parlour'n da su Abba suke zama su tat
tauna nan akayi masa masauki, kasan cewar akwai bedroom's ciki har guda uku, shi É—aya Bappa É—aya Uncle Mahmood É—aya.
sashin Inna na gidan kuma akayi wa security masauki ciki,
inda mu mata kuma muke cikin sauran sashin wato sashin Ummi da Mamie, dan su
Aunty Rafee'at ma anan gidan yau sukace zasu kwana....
Washegari duk a sashin Mamie muka hallara kamar jiya, anan mukayi breakfast, ana zaune ana ta hira,
Bappa yace a kira masa Ya SALEEM kowa na nan shine kaÉ—ai ba ya nan,
ya kama ta yazo ya gan sa
dan ganin da yayi masa jiya ko a hanya ya gansa yanzu bazai gane sa ba.
Ya Masa'ud ne ya kira sa a waya
ya ɓata lokaci mai tsawo kafin yazo.
yashigo sanye da kananun kaya a jikin sa Black jeans da yellow t-shirt.
kallo É—aya nayi masa na É—auke kai,
ya É—an rame ya kara haske gashin kan nan nasa nanan yalan-yalan baki sutuf sai sheki yake, sai dai ya É—an hargitse da alama bai sami damar tace shi ba ya fito.
fuskar nan tasa a É—aure tamau yanayin nan nasa da yanayin suffarsa yana nan yana biye da shi
.
Bappa yace "Zo zauna nan kusa da ni SALEEM kaga yan da Allah yake ikon sa ko ashe ku jinina ne."
Ya Masa'ud ya washe baki yace
"Ya SALEEM ashe shine kanin Inna da take faÉ—an nan, jiya kawai sai gashi da É—ayan wancan hoton Inna."
ya nuna hoton ta da
ke like a jikin garun parlour'n yana mai cigaba da washe baki cike da farin ciki.
shiko Ya SALEEM bai yi magana ba sai