Showing 39001 words to 42000 words out of 244256 words

Chapter 14 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

451

uwanta Yaya Al'amin da shine Ubanta shine uwarta kuma shine gata daya datake dashi a duniya da bata taba iya tsallake umarninsa,
Ba ita kadaiba hatta Mommy uwarsu data haifesa itama shine uwa kuma ubanta hakama danta kuma gatanta da itama a yanxu sai abinda yace din suke bi sbd rayuwarsu da suke gudanarwa babu kowace irin hayaniya sai kwanciyan hankali da nutsuwa da rufin asiri.
A anguwansu babu me doguwan muamala dasu duk da ana zaune dasu kalau da mutuntawa sbd sunada girmama manya da kuma mutunta kowa,
Sunada kamun kai basada rawar kai hakama Al'amin yanada wani irin farin jini da girma sosai a idanuwan duka manya dattijawan anguwan dama matasa da yara sbd yanda yake da kokarin kare mutuncin qanwarsa da mahaifiyarsa tareda rashin rowa da girmama kowa,
Yanada kulawa da tattali tareda wani irin tsanani mai karfi a gurin tarbiya da kulawa da mutuncin SANAAH dan hakanne ma batada qawaye sam dan baya barinta zuwa koina daga makaranta sai gida.

Mommy ta zama weak sosai batada wani karfin hayaniya yanxu sbd kadaicin daya gama zama rayuwarsu da yanzu sike jin dadin abarsu tinda basa cikin kowace irin matsuwa da kunci hakama yaranta suna cikin aminci a gabanta dan haka batada damuwar komai saina damuwa da kadaicin rashin kowa a rayuwarsu saisu.

Duniyar Jeerahs datasu ta dade da rabuwa a duniya daban daban dan kuwa a yanzu babu familyn dayake jeerahs wani irin karfin iko da power da suna,
Sir Hakeem jeerah da shine yake jiya yan siyasa,ya juya gwamnati ya juya manyan tycoons ya juya manyan addini da duk wani kakin kasar babu wanda baida iko me karfi na juyasa da damar iya saukesa da dorasa ya zama tsohon da ake tsoro sbd karfin ikonsa da kaifin raayinsa da duk duniya babu me iya sauyasa,
Zafinsa da kaifinsa ya saka karfin ikon dayake dashi qara zafi da karfinda ba yayansa ba hatta duniyarsa shakkarsa akeyi,
Mutum ne da bai taba hada suna da mutuncin ahalinsa da komaiba,
Akan mutunci da girman sunan ahalinsa zai iya daukan kowane irin mataki mai zafi da kaifin gaske,

Duk masu son ganin abin tir ko wani tarihi ko abin bacin suna daga jeerahs sunyi iya bincikensu na shekara da shekaru basu samu ba hakama yan jarida da labarai sunyi sunyi su samu wani labarin yadawa akan jeerahs amma babu sbd karfin ikon da familyn kedashi yayi yawan da duk abinka bazaka iya samo ko zaqulo wani abinda zai girgiza girma da matsayi tareda karfin da suke dashi ba sbd kaman kafirin aljani haka Sir hakeem jeerah ya riqe martabar jeerahs din kuma yake tsaye qyam da riqeta koda zai rasa ransa bazai bari a taba samun abin fada ko bata suna daga zuriarsa ba da wani zai iya daga ido yayiwa jeerahs kallan da babu daraja da girmamawa bare shakka ba a cikinsa.

Dan haka a duk kowane bangare ko lungu da sakon da zaa ambaci sunan jeerahs kai tsaye kasan magana ce akan masu WEALTH,POWER,CLASS,PRINCIPLES da rashin tsoro da shakka tareda bada girmamawa,
Sir Hakeem jeerah da duka yake riqe da wannan aqidun masu karfin da duniya ta sani ansan 'DA daya garesa wanda duk wani tycoon da masu qasar a hannu suke son muamala dashi ta kulla businesses da huldolin matakan qasashe shine wanda duk abinda ahalinsa suka mallaka yanada kusan fiyeda dashi dan kuwa tasa dukiyar ta wuce ta ahalinsa dan shi a tasa ce shi kadai datake mallakinsa bata mallakin taro ba,
Ya tara dukiya da taka matsayin da kowa yake tsananin son ganinsa ma amma hakan abu ne mai wuyar da bakama da tabbacin a wace qasar zaka gansa kuma duk tsawon wannan shekarun babu wanda ya taba ganinsa a qasar Nigeria ya tako kafarsa bare iyalinsa da basuma san yaya qasar take ba ba kowa bane face FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH of the US navy wanda mazan faman gaske suka sauke kai idan aka ambaci sunansa bare bayyanarsa,
Mutumin da bai taba shakka ko tsoro bare kaucewa harbin abokan yaqi ba,
Mutumin da kunnuwansa da gangar jikinsa da idanuwansa basu san komaiba kaman karfin qarar guguwan Submarines,missiles dasu torpedoes da guguwan karfin oceans da suka saka rayuwarsa bata san komai ba daya wuce hakan sai kuma familynsa da sune bai taba hadawa da komaiba dan sune rayuwarsa da batada wani hayaniya a cikinta.

Matarsa itace mace daya dayake so sona soyayyar da duk duniya baisantaba kawai dai yasan matarsa itace macensa daya datai ishi rayuwarsa ta gama cike masa kowane gurbin da ake tinanin mace na cikewa a rayuwar namiji,
Bayan ita sai yarsa da itama babu kamarta a ransa da idanuwansa,

Iyayensa kuwa har bayan daya zama babban mutum su duka ukun suna akan rayuwar da suke kai tin shekarun baya babu kowane irin walwala da sakewa bayan umarni da order kawai wadda a yanzu su kansu suna basu girmamawa ta wani bangaren sosai tinda yakai girma da matsayin da duniya take tsananin girmamasa sbd matsayin dayake dashi da dole kowa ya basa girmamawa,

Dukiyarsa rabinta na qasar mahaifinsa Nigeria ana kulawa da ita dan hakannen ya sake saka akai masa wani irin sani duk da baya qasar sbd irin manyan companies dayake dasu a qasar da kuma hannayen jarin da duk wani babban kamfani yanadashi a ciki dan haka koyaushe yan jaridu da manyan qasa da manyan tycoons na qasa fatar zuwansa Nigeria suke da ganinsa dan ko America kaje kasan bama ganinsa zakai ba idan ba kanada saa ba dan haka ganinsa yakeda wuyar gaske dan zai iya tafiyarsa ruwa yayi watanni bai fito ba yana tsakiyar manyan ruwa cikin jirgi da manyan securities dinsa duk a yanzu aiki ya masa qasa sosai sbd yakai matakin da babu aiki a gabansa sai bada umarni ga manya wanda shi ake kira da Fleet admiral of the navy.

DA WANNAN KOWA YA SHIGA SABUWAR RAYUWAR DA AYANXU KOWA YAKE KAI CIKIN AMINCI DA KWANCIYAR HANKALI...BISMILLAH.
#MAMUH

GANIN IDO
Mamuhgee
1k
Vip 5k
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

26
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
A daidaita ce tayi parking kofar gidan dayake cikin kuryan karshen layin da har ya zama lungu sbd yawan mutanen anguwan,

Fes layinsu yake da tsafta babu kowace irin kwata ko qazantar bola ko ruwa sbd gabaki daya layin akwai hadin kan tsafta da kiyayewa sbd kusan kowa gidansa ne bana haya ba dan haka babu gayya fes gurin yake hakama babu hayaniya da kwamacalar yara qanana da zaka iya gani ma da irinsu qazanta,

Majalisun manya ne da tsoffin anguwa sau shaguna guda biyu rak dake layin sai masalaccin dayake kusa gap da gidansu,

Koda napep din ta tsaya da yamma ne akwai mutane kusa da kofar gidan a xaune kan babbar tabarmar dake shimfide ta zaman da sukeyi dan haka koda ta ziro kafafunta a natse sanye da black original black crocks bata waiwaya inda sike ba a natse ta qarasa fitowa sanye da doguwar riga black fuskanta sanye da mask da brown jersey veil nade a kanta kudinsa kawai ta ciro daga backbag dinta ta miqa masa tareda wucewa cikin gida kai tsaye tana sauke ajiyan zuciya me sanyi ta isowa gida a gajiye da kuma yar yunwa sbd sam tanada aqidar rashin cin abinci a waje.

Cikin kamun kan datake dashi dayake hade da wani irin sanin darajar kai dayake cikinta kaman ba Marainiya ba ta shigo gidan da sallama me nutsuwa tana kallan Mommy dake zaune a tsakar gidan kan lallausan dadduma me kyau da girma sosai wadda suke zaunawa akai tana dan karanta wasu littafan addini da glasses dinta na qarin gani me kyau dayake dan bayyanarda sauran kuruciyarta itama tayi fresh da ita fatarta ba alaman wahala da tsufa da rashin gyara sbd a rayuwar rufin asiri da kulawa da tattali babu abinda Al'amin ya gaza basu itada SANAAH wadda itama kai tsaye idan ka kalli fatarta da dabiunta da wani irin class datake dashi bazaka dauka ba yar mai kudi bace shiyasa abokan karatunta suke respectin dinta daidai misali ba wulaqantawa hakama kusan da yawansu tana tsananin shiga ransu da shaawan son hulda da ita amma sam ba wata sakewa daga gareta tanada kame kai sosai daga hayaniyar qawance ko yawan muamala me yawa da mutane sbd kusan tarbiyan da Yaya Al'amin din ya dorata akai ne kuma shiyasa ta tsare darajar kanta fiyeda komai sbd ya sadaukar da komai nasa dan bawa rayuwartata darajar da zata wuce kowane irin rashin daraja,

A yanda ya tsaya a rayuwarsu shi tasa rayuwar ta zaka abar tausayi da mamaki dan kuwa kaman mahaukaci akan nema ya koma sedai duk sati haka SANAAH din zata zauna da kanta tayi masa gyaran farce da wankin kafafunsa dan basa kulawan daya kama ace shima yana samu duk da yanada tsaftarsa amma nema na neman haukatasa.

Dagowa mommy tayi a natse tana kallan SANAAH din wadda ta qaraso gurinta tana bude baki da sautin muryanta da shima yake cikeda kamun kai da nutsuwa tace

"Mommy barka da gida"

Da kulawa da kauna me karfi mommyn ta sake kallanta tana amsawa tareda dakatawa da karatun tana matsar da jakar SANAAH din data ajiye mata gabanta tana zare takarminta tace

"Al'amin ya sameki a waya kuwa?
Ya kirani yana tambayar ko kin dawo nace masa aa?

Qarasa zare takarminta tayi tana nufar kofar dakinta tace

"Ya kirani harma yaje ya kaimun daman kudin wani contribution ne da zaayi"

Qarasa shigewa dakinta tayi tana zare kayan jikinta duka ta dauro towel dinta me girma ta fito tana dan lumshe ido sbd wani iska me dadi daya sauka a fatarta da fuskanta datake jin gajiya sosai har lokacin.

Wanka taje tayo ta fito tareda alwala ta koma daki ta shafa mai sama sama da turarenta me sanyi na oud me dadi ta saka doguwan riga mara nauyi da hula ma mara nauyi a kanta ta fito taje kitchen ta sako abinci a plate ta dawo ta zauna gefen mommy tana fara cin abincin a natse suna magana da mommyn dake tambayarta me zaayi da kudin ne na contribution ita kuma tana fada mata suna firarsu hankali kwance cikin jin dadi.

Sallar magrib akai sukai sallarsu ana,
SANAAH na gamawa ta miqe ta shiga kitchen dan dumama abincin sbd Yaya Al'amin dayake buqatansa da zafi dan idan ya fita tin safe baya dawowa sai dare.

Shinfaka ce jallof da cabbage a ciki dan haka sama sama tai masa warming nata tana juyewa a kula ta fito daga kitchen din ana sallar ishai dan haka sallah sukai suna idarwa ba jimawa ya shigo gidan sanye da riga da wando da suka dan tsufa suka kode sosai yana waya da qaramar wayar hannunsa ya qaraso ya zauna akan kujeran dake gefen mommy ta roba yaci gaba da wayar tsawon mintina kafin ya kammala.

Kallan mommyn yayi ya gaidata yana amsa gaisuwan SANAAH datake masa cikin kulawa.

Fira suka dan fara yana dariya suma kusan duk dariyar sukeyi musamman SANAAH da a cikinsu ne kadai take iya sakewa tayi fira da dariyarta hankali kwance.

Wanka ya tashi yaje yayi ya saura kaya zuwa jallabiya yazo ya zauna tsakiyarsu yana fara cin abinci suna sake cigaba da firarsu.

Wayar SANAAH ce dake gefen mommy tayi haske tana fara ringing sunan wanda yake kiran ya bayyana kai tsaye akan wayarta wanda ya saka dukkaninsu kallan wayar suna yin shiru.

Kallo daya Yaya Al'amin yayiwa wayar ya dauke kai yana cigaba da cin abincinsa zuciyarsa na da fuskansa suna sauyawa baice komaiba.

Mommy ma fuskan yaya Al'amin din ta kalla bayan kallan wayar tukuna ta maida kallanta akan SANAAH wadda ta kafe wayar da ido kafin ta miqa hannunta a natse ta dauko wayar tareda dauka a natse ta dora wayar a kunnenta tana bude baki da muryanta dake sake kashe kowace gaba da gangar jikin me kiran tace

"Yes"

Numfashi da ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwa dayake tattare da izza ya sauke jin yanda a koyaushe muryanta takeda wani irin karfi ga zuciya da gangar jikinsa ya bude baki da nutsuwa yace

"Ina kofan gida"

Shiru tayi na seconds kafin ta dan bude baki tace masa ok.

Kashe wayar tayi tana ajiyewa ta dago ta kalli yaya Al'amin ta bude baki tace

"AA yana waje"

Cikin yanayi na rashin bawa zancen da wanda ake zancen akansa mahimmanci yace

"A dawo lafiya"

Yana fadar hakan ya dauki ruwan data ajiye masa yana kaiwa bakinsa yafara sha.

Mommy da itama a yanzu ta gama fahimtar abinda yaya Al'amin yake nufi akan lamarin AA dayaqi ci yaqi cinyewa bude baki tayi tace

"Basai ya leqo gaidani ba ina gaidasa kawai."

Ajiyan zuciya SANAAH ta sauke tana miqewa ta shiga dakinta ta sako hijab me girma sosai har qasa akan kayanta yana qamshi me dadi da nutsuwa ta fice.

Wata lafiyayyar BMW ce black me daukan ido ko a cikin dare pake a kofar gidan daga gefe ta nufa tana isa shine ya bude mata motar daga ciki ta shiga a natse ta zauna tareda rife kofar.

Tinda ya bude motar ya zuba mata fararen idanuwansa yana mata wani irin kallan daya kasa dauke idanuwansa akanta har sai data juyo ta kallesa da idanuwanta da suke da haske da wani irin sanyaya gangar jikinta namiji duk zarrarsa har lokacin ya kasa dena kallanta a natse da wani irin miskilancinsa dayake tattare dashi shima wanda yakeda zafin kai da rashin bawa kowace mace mahimmanci ba idan ba uwarsaba amma SANAAH KHALIL ta zama macen dazaice kai tsaye kaddararsa dan kuwa wani irin jinta yakeyi maqale a cikin wani lungun zuciyarsa da bazai iya barin kowane irin namiji mallakarta ba hakama shima bazai iya mallakarta ba sbd zamtowanta yar marasa karfi ko kadan,

Duniyarsa da tata akwai tazara me nisa da karfin gaske da yake ganin duk yanda yake mutuwa da nacin tsananin sonta kaman rai bazai taba iya aurenta ba,
Bazai iya aurentaba sbd background nata hakama bazai iya barin kowa ya aureta ba zata zama tasa har abada koda hakan na nufin sedai tayita zama budurwansa koma macensa amma auren sam yayi yayi da zuciyarsa da raayinsa ya cusawa kansa aurenta ya kasa hakan sbd bai hada girman kansa dayake ganin yanada duniya a hannunsa dayake juyawa son ransa a cikin iko da isa da lokaci ba,
Yanada sunan da girmansa ya wuce ace ya auri macen da batada kowane irin suna da power ba a familynsu,
Yanada tarin dukiya da arziki da kyau da girman ajin data ko ina ya wuce yaqare da auren macen da bakowa bace ta fito daga asali da tarin talauci da kaf danginsu babu wanda zaa daga a kalla a matsayin mutum me daraja da girman da zaace yayi daidai da zamowa sun hada zuria,

Yana tsananin son SANAAH wadda takeda wani irin class da rashin daukan raini daga kowa,
Bata da shakkar kowa akan darajar kanta da sanin class din,
Bata taba zamowa koma baya ba ga dukkanin abinda kowace mace mai class da gata da wayewa da kamewa ke buqata ba,
Tanada wani irin kyau da class na daukan hankalin da bakowane namiji ne zai iya kallanta ma yayi tinanin fara cewa yana sonta ba sai wanda yakeda cikakkiyar zarra kamarsa ba,

Kyanta yakai harya wuce dukkanin inda yake son macensa takai,
Tsarinta da zafin kanta datake dashi dashi kansa bata damu da dukkanin abinda yake dashiba kokuma matsayinsa da power dayake dashiba daqyar ya samu tafara kallansa bayan tsawon lokacinda ya dauka yana bibiyarta da tsananin son mallakarta a matsayin macensa.

Bata tana kula kowane namiji ba sbd sam babu wata soyayya ko namijin da duk duniya yake gabanta sai akansa tin bayan rasuwar Nasir dinta,

Shima aranar daya fara ganinta a school dinsu a ranar zuciyarsa ta mutu kai tsaye akanta da kuma daukan ita din yar babban family ce sbd yanda tsarinta yake sai daga baya ya san ba kowa bace face qanwar datake samun dukkanin gata daga yayanta da baida karatun komai sai ayyukan wahala.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

27
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login