Showing 66001 words to 69000 words out of 244256 words
kalli wayar tareda zuba mata ido harta kusa yankewa tukuna ta sauke numfashi me dumi tana tattaro nutsuwa da walwalan dole ta sakawa kanta dan kada ya san abinda ya faru sun boye masa sbd kawai kwanciyan hankalinsa ta dauka a natse tareda ambatar sunansa cikin kulawa.
Da wani irin farin ciki dayake basa nutsuwa mai karfi yace
"Mommy an angama daurin auren SANAAH"
Ajiyan zuciya ya sauke mai sauti yana fidda sautin murmushin daya saka nauyin dake kirjin nata itama jin ya fada ya sauka da sanyi da farin ciki mai hadeda nutsuwa.
Bude baki tayi komai yana wucewa lokaci daya daga gareta tace
"Allah ya sakawa auren Albarka da farin ciki mai dorewa a cikinsa har mutuwa ya saka aure ne dasai mutuwa ce zata rabasu ya kuma bata kariya da aminci itada mijinta"
"Amin,Amin" Yaya Al'amin ke furtawa cikin farin cikin da jin dadin daya rasa inda zai saka ransa sbd burinsa mafi girma a duniya tinda ya zama uba ga ahalinsa shine aurar da SANAAH cikin mutunci da martaba da gata kuma duka burin ya cika duk da ba shine ya aurar da ita da hannunsa ba yana jin kaman shi dinne sbd girmansa na matsayinsa da Dad jeerah ya basa na saida ya tambaya izininsa da tambayar auren daga garesa ya bada ya amince tukuna.
Aure ne da akai da wanda ya isa haihuwan SANAAH din koma ya haifeta tinda yana da 'yar datake shakeru daidai da ita amma bai damuba sbd yasan waye shi a baya a shekarun baya kuma yasan Auren da Dad ya daurawa SANAAH bazata taba wulaqanta ba a gurin dattijo Fleet admiral RAHEEM JEERAH kodan uwarta da Maamah da zata ji auren daga daga idan Allah yasa tana lafiya a raye.
Bude baki yayi a natse yace
"Mommy tinda SANAAH din bata san da cikakkiyar maganar aurenba ki mata nasiha ki fahimtar da ita hakan shine nutsuwan da zamu samu mu dukanmu akan mutumin dayake bibiyarta gashi kuna guri daya dashi gashi a yanxu duka a karkashin mutum daya muke dan haka aurar da ita shine babbar kariyar da zaa bata a hanasa sake binta matiqar ya san hakkin Allah da kiyaye fushin Allah akansa din,
Mudai muna farin ciki munyi murna da samun nutsuwan zuciya da hakan dan haka itama sauki da walwala da nutsuwan da zata bawa kanta shine amincewa da karban kaddararta hannu bibbiyu da rashin kowace damuwa tinda daman babu wani datake so ko yake sonta a qasa dan haka auren wadda baka sani ba bazai zama damuwa ba ko illa,Allah ya sakawa auren albarka me dorewa"
"Amin" mommy tace tana sake jin gamsuwa da nutsuwa da duka kalamansa dan haka damuwanta da rashin walwalanta ta qarasa yayewa yana mayewa da farin ciki sosai duk da batada wanda zata nunawa ko inda zata ta nuna daga ita sai safiya suka fara bayyanarda farin cikinsu hankali kwance.
SANAAH duka wannan abin har lokacin tana dakinta bata fitowa ta dawo hayyacinta amma tsoro da jin komai na gidan da rayuwar ya fita zuciyarta tanajin duniyarta ta riga ta juye ta zama abar tsoro sbd babu inda zata ta samu nutsuwar farautarta da Samad yakeyi.
Tana cikin damuwa mai tsananin gaske da ko a dakinta wani lokacin motsi mai tsayi tsoro yake sakata,
Safiya ce ta hada mata abinci lafiyayye a tray takawo mata dakin kaman yanda ta saba sedai yau fuskanta cike take da farin ciki da walwala sabanin kwanakin da itama take cikin tsoro da fargaban data ganin harsu masu aiki ma zasu iya fuskantar hakan.
Dago idanuwanta masu kyau da sukai fayau sukai laushi da mutuwan jiki tayi ta saukesu a kan safiya data ajiye babban tray din akan table tana tana dagowa ta kalleta da kulawa tace
"Ki daure dan Allah kici kadan"
Bata iya cewa komaiba dan gyada mata kai tayi cikin rashin kuzari tana zaune a tsakiyar gadonta rabin jikinta a rufe sanye da wata riga mara hannu fatar jikinta sai daukan ido take sbd haske da lafiya.
Zuba mata komai safiya tayi ta juya ta fice taje ta kawo mata iced coffee datasan tanaso ta sake juyawa ta fice.
Bata motsaba daga inda take tsawon mintina sai ga mommy ta bude dakin ta shigo itama cikeda nutsuwa da walwala da kulawa ta qaraso har bakin gadon ta zauna tana kallan SANAAH din wadda tana ganin Mommy idanuwanta sukai ciko da hawaye jikinta na sake sakewa.
Kamota mommy tayi da kulawa da kauna ta janyota jikinta ta rungume tana dan shafa kanta dayake a bude ba komai akai ta bude baki da sigar rarrashi da bata nutsuwa tace
"SANAAH ki nutsu kiji abinda zan fada miki,
Kinsan dai a yanzu duniya bayan ni da yayanki bakida mai girman matsayi bayan Alh jeerah ko??
Damu dashi a yanxu mune muke da tsabanin son baki kariya a rayuwar nan kuma mune zamuyi duk abinda zamuyi dan baki kariya da rayuwa me aminci,
Burina da yayanki a koyaushe shine baki kariya ta hanyar aurar dake cikin aminci da martaba wanda har yau wannan burin shine mafi girman buri a zukatanmu...
To Allah ayau ya cika mana hakan,
Abinda ya faru yanzu ya saka Alhaji jeerah Aurar dake ga babban 'dansa wanda yake tamkar uba ga Samad wanda duk duniya shi Samad yakejin kaman zai bauta masa da hakan mai yiyuwa ne dan kawai ya baki kariya ta har abada daga Samad din kuma insha Allah kin sameta dan haka ni da yayanki munyi naam mun aminta mun kuma samu nutsuwa da farin ciki da hakan,
Kada ki daga hankalinki kada ki shiga damuwa ko tashin hankalin auren daya hau kanki ba sani sbd wanda ya daura miki auren ya wuce hakan a gurinki ki cire komai ki amsa da biyayya da tarbiyan da kike da ita sbd bazai taba miki abinda zaki cutuba kinfi kowa sanin hakan dan haka matsayin daya baki na 'yarsa duniya ma tasan da hakan kema ki nuna ke 'ya ce ki amsa ki masa bayayyya koda ba 'dan cikinsa ya aura miki ba ko waye ya aura miki ki kasance me biyayya da nuna girmamawa,
Insha Allah Allah zai kawo miki sauya a cikin wannan auren,
Zaki samu ribar biyayyar da zakiyi,
Ko baki samu komaiba a cikin auren insha Allah zaki samu kariya da nutsuwa da aminci..."
Dagowan datai niyar yi daga lokacinda Mommy ta furta kalman aure akanta ta kasa sbd sauran kalaman da suka biyo bayan,
Bata taba tsammanin aure akanta ba yanzu ko a kusa sbd halinda take ciki na farautar masu sonta ma da Samad yakeyi,
Bata taba tinanin ma zata auru a yanxu ba sbd matsalolin dake cikeda rayuwarta,
Wane irin aure ne akai mata kai tsaye a rana tsaka cikin kwanaki kalilan?
Auren sadaka ne akai mata sbd bata kariya daga Samad kenan,
Auren da babu shiri babu tsammani babu neman shawaran wanda ma akaiwa sadakar tata kenan,
Wace rayuwa ce take ciki wanda zata qare a tsakanin ahalin jeerahs da wanda ya lalata rayuwarta ya dangana ta ga qarewa da auren wanda baimasan da auren daya hau kansa ba.
Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka ciko idanuwanta suna kasa saukowa sbd jin wani irin yanayin da batada ikon nunawa ko fada sbd wanda shine ya zartar da wannan girmammen hukuncin akanta wanda kuma bazata taba iya dagowa ta kalli kowace hukuncin zai yanke akanta ba.
Mommy ma da sai a lokacin tausayin SANAAH ya zuwar mata sbd kowace mace duniya bazata taba son aurenta yaxo mata a hakan daga sama kaman dai ba lamarin da zata qarashe rayuwarta a cikinsa ba hakama da mutumin da ba yaro ne ba qarami yanada iyalinsa dayake so da rayuwarsa dasu kawai a jeho masa wata macen wadda ba lallai ta taba samun ko rabin matsayin da matarsa take dashiba a gurinsa.
Ajiyan zuciya ta sake tana sake dan rungume SANAAH a jikinta da rasa abin fada bayan shafata data ringa yi ahankali tana aika mata da kaunarta da kulawanta da lallashinta ta hakan wanda yake shigar SANAAH din tana sake jin jikinta na mutuwa sosai.
Wayar Mommy ce tayi ringing ta dago a natse taga Al'amin ne kuma tasan SANAAH din yace zaiyi magana da ita dan haka daukan wayar tayi kai tsaye tareda saka handsfree tace masa SANAAH din na sauraronsa.
Cikin kulawa mai tsanani da kaunarsa data bayyana a cikin sanyi da nutsuwa ya ambaci sunanta da wani irin sautin daya sakata fasa kukan daya taho mata mai karfi tana rintse idanuwanta tareda qanqame jikinta.
Shiru mommy tayi shima Yaya Al'amin din ahiru yayi kukanta na ratsasu jikinsu yayi sanyi.
Kukane takeyi mai tsananin karfi da qaramin sauti kanta na qasa muryanta har wani yankewa yakeyi tana koke dukkanin quncin dayake dunqule a kirjinta.
Tsawon lokaci ta dauka tana kukan babu wanda ya hanata sai data sassauta dan kanta tukuna mommy ta zari tissue dake gefen gadonta kan bedside tafara goge mata hawayen shi kuwa Al'amin cikin kulawa da kauna mai karfi yafara rarrashinta yana mata maganganun dasuke ratsata da bata nutsuwa da bata sassaucin abinda take ji da kuma rungumar sabuwar kaddarar da bazata iya dagowa tace batasoba amma har cikin zuciyarta bata shaawan aure ko hulda da kowane namiji sbd Samad ya cire mata kowace irin kauna da shaawan auren namiji amma kuma auren da Dad ya daura mata da kuma auren da yaya Al'amin da mommy suke kauna to tabbas ta gama karbansa hannu bibbiyu duk da tana fatar sauyi mafi alkhairi a gaba.
Dukkaninsu maganganun da yayi musu sun basu kwanciyan hankali da nutsuwa da sake karban rayuwar data samesu dan haka sake saka baki mommy tayi ta qara bawa zuciyar SANAAH rarrashi da sukuni tukuna sukai sallama.
Da kanta ta tirsasa SANAAH din ta bata abinci taci kadan ta sake shan magani ta sauko gadon ta shiga toilet tayo alwala ta fito tayi sallar laasar da akai suna magana.
Tana idarwa zaunawa tayi shiru tana shiga tinani mai zurfi damuwanta ta ragu sosai.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee
42
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.
*******
Acan bangaren Dad jeerah kuwa bai dawo gida ba sai yamma lis sbd baqi sosai suka halarci daurin auren wanda akai gayyata a qanqanin lokaci amma manyan mutanen da suka aje komai nasu suka halarto daurin auren sunada yawa dan haka ne akai cikar da babu wanda yai tsammani,
Koda ya dawo securities ma tayasa murnan daurin auren da akai a qanqanin lokaci sukai duk da basu san waye mijin ba sundai san yau ne daurin auren Yarsa SANAAH wadda kowa ke girmamawa a cikinsu sbd zamanta 'yar da Sir jeerah da kansa yake kauna.
Umma ce ta fara jin daurin auren daga garesa bayan data taho bayan ya gama hutawa bayan dawowan tasa hankalinsa kwance zuciyarsa fes da wani natsatsen farin cikin bayana shekaru masu yawa yau dai ya nuna nasa ikon akan 'dansa shima,
Ikon da daga 'dan har uwarsa basu isa su sauya ba ko nuna rashin jin dadinsu sbd sanin tinda ya daura ko mutuwar Raheem din ce kadai zata raba auren amma ba dan adam ba ko waye kuwa,
Hakama a yanzu ne yakeda cikakkiyar sani da nutsuwan 'dansa yayi aure
Auren daya daura masa a matsayinsa na ubansa ba wanda uwarsa mace ta daura masa.
Ummah kasa motsawa tayi tsabar mamaki shock din jin auren da idan taji daidai Fleet Raheem jeerah aka daurawa da kuma SANAAH,
Auren da kila mahaifiyarsa zatafison ace wani balain ne ya fado masa yayi jinya ya warke akan yayi aure hakama matarsa da zata iya ransa ma tsabar wani masifaffen kishi akan ace yayi aure musamman yanxu datake ganin sun zama manya yarsu ta zama budurwar dake shirin zama likita amma ace yayi aure aurenma da saar yarsa wadda zatafi baqin cikin hakan dik ranar da Allah ya kaddareta da ji dan kuwa su dai har abada bazata taba ji ba a bakinsu sbd kadama ayi balain dasu idan an tashi dan tabbas lokacin fuskantar juna tsakanin Jeerah da dr fammah yayi tinda daga karshe danta yayi abinda duk duniya ta tsana ko jin sunansa wato qarin aure kuma da yar asalin Nigeria gaba da baya wainda ta tsana.
Rasa abin fada Umma tayi sai kawai tabi auren da adduar Allah ya sanya alkhairi.
A bangare daya kuma dadin hakan taji sosai sbd baqin cikin da Samad da uwarsa zasu shiga da wanda ita kanta Meenah wahab zata shiga sbd bata taba daukansu da mahimmanci ba bare basu girman daya kamata a matsayinsu na matan uban mijinta dan haka hakan ya mata dadi sosai dan tasan tako ina baqin ciki da tashin hankali ne zaaita zubawa wanda zai saka da dama wasu samun sallama.
Tana baro bangaren Dad samun kanta tayi da wucewa kai tsaye bangaren Hajiyar Samad wadda ta rasa sukuninta da kwanciyan hankali a cikin kwanakin a tsorace da fargaba take sbd shirun Dad ba alkhairi bane ko kadan.
Tana ganin Ummah ta danne baqin cikin datake ciki da damuwa ta dan sake tana nuna hankalinta kwance yake da walwala ta mata sannu da zuwa.
Da walwala sosai itama Umma ta gaisa da ita tana kin zaka daga tsaye tace
"Ba sai na zauna ba zan wuce nace bara na sanar miki kije kiyiwa Alh barka da arziki da taya murna Yau aka daura auren 'yarsa SANAAH da Fleet RAHEEM dan kila baki sani ba"
Shiru hajiyar Samad tayi kaman bata fahimta ba sai data juya zancen taga ta kasa ganewa kafin ta dago ta kalli Umman tana dan neman rikicewa da kuma kasa boye rikicewanta tace
"Wane Raheem din?
Da kuma wace Sanaar??
Umma da bazata iya doguwar hayaniyar tashin hankalinba juyawa tayi tana cewa
"Fleet admiral RAHEEM JEERAH"
Tana saka kai Samad na shigowa ko gaidata bai iya yiba sbd jin abinda ta fada ya qaraso cikin palon yana kallan hajiyarsa ya bude baki yana zama yace
"Godfather naji ana ambata"
Tsabar rikicewa hajiyarsa bata san lokacin datace
"Aurensa aka daura da SANAAH dinka ayau mun shiga uku wace sabuwar masifar ce wannan?
Wlh tarko aka nada maka wanda zai kasheka da gaggawa....hada kayanka ka tafi tin a.........
Kallanta yakeyi da duka idanuwansa batareda ya motsaba sbd bai yadda ko kusa da wannan zancen ba da har abada bazai taba yiyuwaba wai Godfather dinsa da aure a irin tsarin rayuwarsa da babu gurin shigar kowane irin mutum ma sbd ahalinsa basason yawa su kansu bare qarin aure.
Tayaya ma?mutanen da basa wani son wani ma yazo cikinsu ya zauna yayi rayuwa bayan iya su to ta ina zai iya kallan wata macen bare qarin aure,
Hakama tayaya SANAAH datake saar yarsa aure zai yiyu a tsakaninsu....
Dauke kansa yayi daga kallan hajiyar yana miqewa tsaye zai fice sbd gabaki daya ta rasa kanta tinda abin ya faru a kwanakin kullum cikin tinani da zullumi kala kala take.
Riqosa tayi da karfin gaske tana kallansa tace
"Bakaji abinda na fada bane?
Kanajin Auren da aka daura?
Wlh ba aure ne ba kai akaiwa tarko wannan auren,
Baka jina ne???
Wani mummunan daci da baqin cikin kalmar auren datake furtawa ya hadiye sbd da ace wani ne yake maimaita kalman an daurawa SANAAH aure da zai iya hallakasa da hannuwansa amma hajiyarsa dan haka ya sake hadiye wani dacin mai karfi ya kalleta da idanuwansa da suka sauya yace
"Hajiya babu auren da zaa daurawa Godfather da kowa a duniya bama wai SANAAH ba,
Babu aure a yanzu kuma babu shi har abada dan haka ki dena wannan tinanin yayi nauyin dama yake kaman haramun"
Kallansa takeyi da tsananin takaici itama da baqin cikin data rasa abin fada amma itama tanason tabbatarwa dan haka ta wucesa ta fita tana dan gyaran mayafin tsadaddiyar abayar dake jikinta ta nufi bangarensu SANAAH sbd tasan bazata iya zuwa bangaren Dad ba kai tsaye ko hauka ce ta haifeta.
Tana isa bangaren ga mamakinta Umma na bangaren tana taya mommy murna wadda take amsawa cikeda farin ciki da sakewa da walwala tana godiya hankali kwance.
Ganin yanayinsu ya saka hajiyar itama tattaro karfin hali da danne tashin hankalinta da baqin cikinsu da takaicinsu ta dan saki fuska cikin karfin hali tana gaisawa da Mommyn kafin ta bude baki tace
"Sai mukaji abinda yake faruwa,
An daura auren ne ko zaa daura ne?
Allah ya nuna mana"
Umma data gama karantar halin datake ciki murmushi mai sanyi da nutsuwa ta sake kafin hankali kwance tace
"An daura tin dazu bayan jumaa sedai fatar Allah ya nuna mana tarewa lafiya idan lokaci yayi"
Miqewa tayi tanawa mommy sai anjima ta fice.
Hajiya datai mutuwar zaune tana kasa yadda har lokacin sake bude baki tayi ta tambayi mommy itama mommyn ta tabbatar mata da an daura.
Bata san lokacin data miqe ba ta fice batareda cewa komaiba mommy ta bita da kallan mamaki da fatar Allah yasa kada ta sake zuwar mata.
Tana baro can bangaren tsabar rikicewa da rudun tashin hankali kai tsaye bangaren Dad ta nufa tana zuwa yana palonsa na kurya zaune cikin hutawa yana waya da wanda