Showing 120001 words to 123000 words out of 244256 words

Chapter 41 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

441

ya saka hannunsa kawai ya dagata ahankali tareda juyawa ya dorata akan table din dining din yana rankwafowa ya mata rinfa gabaki daya.

Saurin kallansa tayi tana dan fito da idanuwanta ta kallesa shima ita yake kallan yace

"Sorry konuwan zan gani idan da buqatan zuwan Dr ok???

Girgiza kai tayi tana bude baki tace

"No,na warke,
Fammah zata ringa dubamun"

Dagowa yayi a tsanake yayi mata wani kallo da jinjina mata kafin yace

"Ok,lemme call tazo ta duba mun yanzu to.." ya qarasa maganar yana kallan cikin idanuwanta kafin ya juya alaman daukan wayansa daya aje gefe..

Da sauri ta riqosa batareda tasan tayi hakanba.

Jin hannunta a nasa ta dora masa ta kamosa ya sakasa dawo da kallansa akan hannun batareda ya dauki wayar tasa ba boyayyan murmushi na kamasa.

Hannun nata ya kama da hannunsa daya ya hade da nata da wani sanyi da nutsuwa da mannewa sbd tafin hannuwan ya hade yana jin yanda jikinta da koyaushe yakeda dumi yake ratsa ya saka hannunsa daya yakai akan rigarta ya dan daga yana kai fuskansa gurin ya kalla yaga babu abinda gurin ko fatarta tayi zai kai hannu gurin ya taba ta riqe hannunsa da sauri da dayan hannunta tana girgiza masa kai kaman zatai kuka ta kallesa shima ita din yake kalla ya sakar mata dayan hannun dayake riqe dashi ya dora dayan nasa akan wanda ta riqe masa yana dan sake matsota sosai yanda qamshinsa ya ringa shigarta direct taji kirjinta na sauya bugu ta kasa riqe halin da zuciyarta take neman sakata ta dago ta sake kallansa sai a lokacin taga idanuwasa sun sauya sosai kaman wanda bai yi bacci ba sam..

Faduwa mai karfin gaske gabanta yayi ta sake kallansa batareda tasan tayi hakanba.

Janyewa tayi ahankali tareda saukowa kai tsaye qasa daga table din batareda ya matsa ba dan haka kusan kai tsaye kaman cikin jikinsa ta sauko dan haka ya saka hannuwansa biyu duk ya kama fuskanta datake kokarin hana yanayinta bayyana ya kalleta da kyau ya fahimci sauyinta da son buqatan tabar gabansa dan haka yakai bakinsa kai tsaye gefen fuskanta ya goga mata lips dinsa kafin ya bude baki yana riqe da fuskanta har lokacin da wani lafiyayyan sauti mara amo ko kadan sai taushi a cikinsa yace

"Na kwana da ciwon kai"

Yana gama fadan hakan yakai bakinsa yayi kissing goshinta kai tsaye yana shafa wuyanta yace

"Ku kula da kanku"

Yana gama fada mata hakan ya sake duba agogon hannunsa yana sakinta sbd baida time sosai.

Barin gurin zaiyi batareda ya tsaya cin abincin data kawo dinba yaji sautin muryanta harya kai kofa a kasalance da boye daci da damuwanta tace

"Ga Breakfast din anan"

Cak ya dan dakata yana jin wani feeling na samun nutsuwa da jin wani iri ya juyo ya kalleta kai tsaye a natse tukuna ya juyo ya dawo ya zauna yana bude baki a tsanake yace

"Ok"

Motsawa tayi dole tinda ba yanda zatai ta zuba masa dan daidai sbd gane kaman sauri yakeyi.

Tana gama zuba masa ya dauki oats dayasha madara sosai da zuma kadan yasha tareda meat balls daya shima sai boiled veg spoon daya yana cinye na bakinsa a natse ya dauki tissue ya goge bakinsa kafin ya miqe tsaye ahankali tareda kai hannu ya shafi hannunta data kawo masa ruwa dashi daga kitchen ya karbi ruwan ya ajiye akan table yace

"Thank you" yana cewa hakan ya wuce batareda yasha ruwan ba.

Itama ficewan tayi tana bayansa tana tafiya kadan kadan dan bazata iya binsa a baya ba kamshinsa da wata irin kwarjinsa neman zubar da ita a hanya sukeyi.

Imran dake sanye da wasu black designer outfit dior da farin glasses a tsaye tareda securities dake jiransa suna hangosa suka gyara tsayuwansu suna kasa kallansa sbd kwarjininsa koyaushe kaman yana sake karfi ne da bazaka taba iya kafesa da ido ba idanuwanka bazasu iya dauka.

Tana ganin hakan tai daurin dauke hanyar da zata kaita bangaren su mommy da sauri batareda ma kowa yaga inda ta fitoba.

Tana isa har lokacin ba kowane ya tashi ba dan haka dakin Mommy ta nufa ta shige ta kwanta ahankali tana jin bama zata iya cin abinci ba a yanxu.

Su kuwa motocinsu kai tsaye ficewa sukai daga JEERAHsV zuwa airport cikin lafiyayyan speed din dasuke buqatan isa akan time.

Zaune yake a bayan motar da ake jansa din shi kadai sai Imran dayake gaba yana duba ipad dake hannunsa yana tsara schedules din Fleet din tin kafin su isa sbd kadama wainda basa cikin schedule su saka ran zasu samu ganinsa.

Fararen idanuwansa ne masu kyau da tada tsigar jikin matansa ya dan juya kadan ya kalli wayarsa dake gefensa datai haske alaman shigowan sako ya dauke idanuwansa daga kai yana miqa hannu a kame ya kashe wayar gabaki daya tareda yin shiru yana jin nutsuwansa na ninkuwa da samun sukuninsa.
Suna isa airport babu bata lokaci akai komai suka wuce jirginsu ya tashi.

**Daga lafewa dakin Mommy bacci ya dauketa itama dan haka koda ta tashi kowa ya tashi harma kowa yayi breakfast rana ta fara yi.

Fitowa tayi tafara zuwa ta gaida kowa taje ta zauna a island din kitchen tai breakfast dinta da safiya a kitchen din tana dan kokarin mata fira.

Tana cikin yi Fammah ta shigo tana karasowa gurinta ta sako kanta ta bayanta tana cewa

"Na tashi bacci banga Babyta ba,I'm missing you already,idan kika tafi gidan prof ya zanyi da rayuwata"

Qarasa maganar tayi tana rungume SANAAH din kaman wata baby tana tsokanarta.

Dariya safiya take musu tana cewa

"Gwara dai prof ya hakura ni bana yinsa"

SANAAH kuwa fammah din takewa dariya mara sauti tana juyowa tace

"Karma ki fara da maganar prof tinda safen nan"

Dariya fammah tayi tana sakinta ta dawo gabanta tana karban spoon din hannunta ta diban Noodles din datake ci da scotch eggs takai bakinta taci ahankali tana cewa

"Idan ba prof ba wa??"

Hararanta SANAAH ta dan yi tana hana kanta zuba mata idanuwanta dake son kafeta da kallansu mai sanyi.

Tare suka ci gaba da cin abincin batareda dauko wani spoon ba fammah nata yiwa SANAAH maganar prof da tsokana suna dariya da safiya ita kuma tana jinsu tayi musu banza har sai da suka gama suka fito kitchen din suka tattara suka koma bangarensu sbd SANAAH din datace suje dakinsu yau batason fira a bangaren su mommyn sbd hayaniyar firarsu.
#MAMUH
09033181070
GANIN IDO 2026
Mamuhgee

71
Suna isa bangaren a lokacin ne Mum ta fito ta tashi bacci ta shirya ta fito tana qamshinta da kyanta datai cikin doguwan riga dan itace kayansu daman.

Wayarta dake hannunta ta kalla tana dawo da kallanta kan Fammah tace

"Dad dinki yayi tafiya fa yama yita kirana da safen nan nayi bacci ban daga ba,da ciwon kai ya kwana yau sosai nama dauka zai hakura da tafiyar yaga Dr may b amma ya wuce"

Cikin kulawa da kauna fammah tace

"Yanxu bazan samesa ba sbd yana hanya idan ya isa zan kirasa naji lafiyansa"

"Ok,ok" kawai Mum din tace tana maida kallanta kan SANAAH tace

"Ai SANAAH ce ma takai masa breakfast,
Kin gansa koda kika kai?
Yaji sauki ko??

Kallan Mum din SANAAH tayi tana ma rasa amsar bayarwa sbd yanda tambayar taxo mata a bazata amma ganin suna kallanta da jiran amsa sai ta bude baki tace

"Eh" kawai tana kama nutsuwanta da kyau.

Murmushi Mum din tayi tana jin dadi da wucewa dining ta zauna taci abincinta hankali kwance tana gamawa ta fice tayi gurinsu Dr Mum dan gaisawa dasu.

Su kuwa daki suka wuni yau SANAAH na lafe gefn Fammah kaman mara lafiya ta koma mata kaman baby daman haka take mata ta saba da shagwabarta amma yau duk ta sake narke mata.

Abincin rana ma yau a daki safiya ta kawo musu daman haka takeso ta zauna musu fira tinda batada sauran aiki.

Zaunawa tayi ta ringa musu fira Fammah na saka baki sunayi SANAAH na sauraronsu da murmushi akan fuskanta tana sauraronsu.

Sai yamma suka tafi bangaren mommy suka zauna acan tareda su saida sukaci abincin dare suka koma sukai shirin bacci suna hawa gado Fammah ta dauki wayarta ta saka kiran numbern Dad dinta ta America dan tasan yanzu da ita zata samesa.

Ringing kuwa wayar ta fara dan haka ta saka handsfree tana gyarawa SANAAH gashinta daya dan yi gefe da qananun kalba a kanta tana cewa

"Ya kamata muje Saloon"

Daukan wayar yayi a natse muryansa mai kauri ta sauka a wayar yana cewa

"Yes Fammah"

Cikeda farin ciki da kauna da kulawa tace

"Yes Dad ina wuni?
Yaya gajiyan tafiya?
Ka isa lafiya?

Numfashi ya sauke a natse mara sauti a natse yana fahimtar wayar a handsfree take sbd yanda muryan famman ke dan amsawa kadan dan haka ya dago idanuwansa da suke farare tas daga file din dayake hannunsa daya yana karantawa ya kalli wayar hannunsa ya danyi baya da bayansa ya jingina a natse sautin daya qarawa muryansa zama deep da zama strong yace

"Lafiya kalau alhamdllh,
Yaya kuke?
Kuna lafiya?
Yaya jikinku??

Murmushi fammah tayi tana sake gyara zamanta da dora hannunta akan SANAAH tana sake gyara mata gashinta tace

"Lafiya muke Dad,
Babu me rashin lafiya a cikinmu,
Kana America ne Dad?

Shiru yayi a wata irin tsanake kunnuwansa na nutsuwa da sauraro komai kankantar motsin dazai iya faruwa ta bangarensu sbd jiran jin alaman taji gaisuwan tasa wadda yayi jam'in da yasan zata san da ita yake idanuwansa a tsaye kan file din hannunsa amma kunnuwansa da nutsuwansa da zuciyarsa na kan abinda yake jiran ji.

Ita kuwa tinda ya bude baki yafara jerowa fammah tambayoyin tayi shiru lafe a gefen famman datake batareda ta motsaba saida kalmansa ta karshe ta ratsa kunnuwanta da wani irin nutsuwa da kaifin daya sakata motsawa ahankali tana saka hannunta qasan rigarta ta dora tafin hannunta akan fatar cikinta tana rife idanuwanta ahankali wanda kai tsaye motsinta ya isa cikin wayar ya sauka a kunnuwansa take ya sake wani lafiyayyan mayen murmushin tabbatarda abinda ya sani tana lafe jikin fammanta kenan kuma ta jisa dan kuwa yasan matiqar taji abinda ya tambaya din zata motsa ta taba gurin kokuma janyewa daga gurin wanda hakan zai sakasa jin motsinta gashi kuma hakan ta faru.

Sautin murmushinsa mai wata irin sanyi da nutsuwa da tsari da kamewa da steez ya saukar musu wanda ya saka SANAAH bude idanuwanta ahankali ta kalli wayar wani irin kallan da shi bazata taba iya masaba mai cool yanayin data sake narkewa gefen fammah tana kasa dauke kyawawan idanuwanta akai tana jin muryansa yana magana da fammah wadda kusan kowace kalman tana sane da maanar dayake jeho mata sbd yasan tana nan tareda fammah a lokaci.

Koda suka gama wayar fammah cikin farin ciki take sosai sbd yanda tayi fira da Dad dinta duk da bata wani gane wasu maganganun nasa ba.

Kwantawa sukai batareda SANAAH ta furta komaiba har bacci ya dauketa mai sanyi.

Washe gari da safe suna breakfast shine da kansa ya kira Mum wadda taketa wani jin farin ciki da nuna isan itace mai Fleet.

Duk wayar da sukai su SANAAH din suna zaune suna jinta suna cin abinci harta gama ta ajiye wayar tafara musu surutun batason ya dade sbd indai zai dade zata bisa saisu dawo tare.

Fammah ce ta yanke zancen Mum din da sanar da ita tayi magana da Dad jeerah akan zai samar mata daman attending wani babban program na doctors da zaayi da manyan doctors na qasa da wata qasar zasu halarta a lagos kuma sai wanda yakeda matsayi da babbar hanya ne ma kadai zasu iya attending a cikin upcoming doctors dan haka ma iya yayan manyan qasa ne masu power zasu iya zuwa ga wainda ke shirin zama doctors dan taro ne na doctors din bama ka taba tsammanin ganinsu ba.

Mum na jin hakan tayi farin ciki sosai ta kuma ji tana tsananin buqatan fammah da ita kanta su halarci 6days program din dan haka take ma taji tana buqatan fara shirin zuwa.

Fammah ma sosai take tsananin farin cikin samun damar halartar taron dan haka SANAAH ma tana tayata murna sosai duk da ita bazata samu daman binta ba kila.

Dr Mum ma tayi farin cikin hakan dan hakan zai taimakawa Fammah din a cikin karatunta.

Yau Mum bata je koinaba bayan taje ta gaidasu dawowa tayi suka zauna bangarensu tanata wayoyi da gida akan auren da zaa yi na kaninta da shine kadai takeda.

Fammah da SANAAH kuma futa sukai sukaje gyaran kai suna gyaran kafa da dan karamin siyayyar abunda suke buqata sai yamma suka dawo.

Suna dawowa bangaren mommy suka sauka suka zauna a palon tareda kowa dayake nan suna maganarsu.

Hannu Dr Mum ta miqawa SANAAH tana nuna mata kusa da ita tazo nan ta zauna tana cewa

"SANAAH ki dena dadewa sosai idan kin fita ba kyau karki manta kinada miji kinji"

Shiru kowa yayi a palon hadda Mum data sake baki tana kallan Dr Mum din cikeda mamaki dama tsananin shakka zatai magana Fammah ta yanketa da shirun kowa da cewa

"Grandpa ne fa yayi mata mijin kuma wlh batasonsa a dena maganarsa munada candidate dinmu"

Dariya Mum tayi tana cewa

"Ai kuwa dai indai hakane Dr mum inama ina bayan baby SANAAH dan Allah kada ayi mata auren hadi sam bai kamacetaba a bari zamu kawo miji"

Dr Mum rasa abin fada tayi sai kawai ta sake murmushi tana kallan Meenah kafin ta kalli SANAAH wadda tayi saurin qasa da kai tana dan kama yatsunta,

Maamah kuwa fuskewa ta dan yi tana taya Meenah dariya mommy ma murmushin karfin hali ta sake.

Da haka aka juya zancen da Meenah ta fara jarawa bayani tana cewa bazaa bawa SANAAH duk wanda bataso ba dan Allah.

Tin kafin ishai suka iso bangarensu fammah ce ta fara wanka kafin SANAAH tukuna sukai sallah.

Shirin bacci sukai SANAAH ta saka riga da wando na bacci maroon da suka kwanta mata ta hawo gadon ta zauna gefen Fammah tana daga wayarta itama tareda duba chats dinta a natse kaman daga sama taji bayyanar muryansa a cikin kunnuwanta tsanake yace

"Hi doc"

Wani irin zirrrrr taji cikin kunnuwanta xuwa zuciyarta ta dago idanuwanta ahankali ta kalli wayar Fammah dake gabansu ba tsammani idanuwansu suka shiga cikin na juna batareda shi kansa yayi tsammanin ganinta kai tsaye ba daga daukan wayan fammah din wadda kiran yake VidCall ne.

Da farin ciki fammah ta daga hannu tace

"Hey Dad,ina wuni?
Yaya kake acan??

Dauke idanuwansa yayi daga inda suke a natse yana tsaidasu akan fammah din yace

"Alhamdllh,
Yaya kuke?
Ya Mum naki and her Baby"

Kallan SANAAH Fammah tayi wadda ta janye ahankali daga jikinta tana kokarin kwantawa gefe ta janyota tana cewa

"Gata nan Dad she's always acting and behaving like a baby shiyasa Mum take kasa kiranta da baby"

Qarasa fadan hakan tayi tana jan kumatun SANAAH din kadan dan kulawa wanda ya saka SANAAH dan ture hannunta cikin wani yanayinta daya sakas tsaida kallansa akan farin hannunta tas daya sauka akan na fammah tana dan tureta ahankali tana hana idanuwanta sauka akan wayar sbd jikinta ya mutu tana hana kasalarta bayyanuwa.

Magana yakeyi da fammah a tsanake yana zaune a lafiyayyan luxury sitting room dinsa dayake gidansa na America din.

Duk maganar da sukeyi da fammah bai kuma kallan SANAAH ba amma kowace motsi da bugawan zuciyarta dake fita yana ankare dashi wanda itama a jikinta taji hakan dan hakane itama bata dago ba tayi shiru da wayanta a hannu gefen fammah tana kallan sakwannin sabuwan number na shigo mata wadda take saka ran Prof ne sbd batai saving numbernsa ba har yanzu hakama bata taba replying massages nasa ba.

Suna gamawa a natse ya furta

"Ku kula sosai ok?,gudnight"

Suna kashe wayar SANAAH data rufe idanuwanta cikin sanyi bata sake motsawaba bacci ya dauketa a hakan sedai fammah data gama chatting dinta ta dan gyarata ta kwanta itama.

****bayan tafiyar nan tasa kullum a kwai daidai lokaci daya daya ware yana waya da 'yarsa sedai bai sake kiransu Videocall ba sedai normal voice call.

Satinsa biyu da tafiya babu ranar da baya jin motsinta a kusa da fammah waya kuma bai taba magana da itaba sbd kusan gabaki daya ta koma kaman wadda ta rasa bakinta ko magana bata iyayi yanzu tayi wani irin sanyi da qarin rashin son hayaniya,

Koyaushe tana daki sai idan taje gurin Dr Mum dake wani irin nuna mata kauna da tattali kaman baby qarama ga wata irin kulawa datake dan kusan da ita da Dad jeerah kowa kokari nuna mata kaunar datafi ta kowa.

Fammah ta koma tamkar itace sanyinta dake bata nutsuwa dan kuwa koyaushe itace take kallo kallan da bata gajiya dayi mata mai sanyi ita kuwa tarairayanta takeyi tana ganin kaman SANAAH na mata kaunar da bata iya boyewa ne shiyasa duk ta sauya mata zuwa kaman jaririyan baby.

Dad ya samar mata daman attending program din dan haka aka shirya tafiyarsu da Mommy wadda itace zata raka Fammah din sbd kada tayi tafiya ita daya bayan angama komai Mum dinga tace zataje dan haka tafiyar dole g
Ya zama su uku ne zasuyita.

Dr Mum taso ta hana Meenah tafiyan amma yanda ta yanke son attending itama ya saka ta kyaleta aka hada komai na tafiyar tasu tareda ware musu securities da zasu tafi dasu da kuma tanadar musu wani lafiyayyan luxury 5star hotel da zasu sauka Fleet kuwa dollars ya qara zubawa kowannensu a acct duk da basama buqatan kudin.

Ranar da zasu tafi SANAAH kaman zata shiga jinya sbd rashin kuzari da kasala dan haka da ita aka kaisu airport tana dawowa ta sake narkewa a dakin Dr Mum wadda taketa jinta har cikin ranta.

Washe gari still ba kuzari ta farka haka ta wuni har Dare tayi shirin baccinta taci abinci kadan ta nufi dakin Dr Mum tayi kwanciyanta.

Tana daukan wayarta zata dan dudduba taji bazata iyaba ta ajiye tareda rufe idanuwanta taji an buga kofar dakin an bude an shigowa safiya ce cikeda girmamawa ta kalli Dr Mum tace

"Dr Mum Maamah ce tace a sanar daki Dad din fammah yana palo"
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

72
Dan shiru Dr Mum tayi da jin sakon da Safiya ta kawo na dawowan Fleet din wanda itama taji daga sama hakama bata taba tsammanin dawowan nasa ba a yanxu sbd ta dauka zaiyi kaman wata biyu haka amma duka duka baifi sati uku ba da kwanaki ya dawo.

Kallan safiya tayi tareda amsa mata mata da taji.

Juyawa safiya din tayi ta fice daga dakin,

Waya Dr Mum din ta dauka dage gabanta ajiye akan table ta saka kiran Maamah.

Maamah na dauka a natse hankalinta kwance tace

"Na riga na gama komai nayi shirin bacci 'danki ya tafi shima nasan yana buqatan hutawa sbd tafiyan daya dawo yaje ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login