Showing 153001 words to 156000 words out of 244256 words

Chapter 52 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

458

aika masa tea din da 'yarsa ta saba kai masa wani lokacin itace zata kai ta gaidasa ta dawo wani lokacin kuma safiya take aikawa hankalinsu kwance itada safiya babu ruwansu da draman auren SANAAH din sun zama yan kallo sunbar iyayenta da rashin sanin wane mataki suke akai ga Raheem dinma kowa kaf duniya ya kasa samunsa baya buqatan kowace hayaniya dayasan dole zaayi ba bazai dauka ba sam.

*****Ranar datai kwana shida da isowa qasar aka dauko masu gyaran yan matan gidan wainda a gurin hidimar zaa iya tsaida musu nasu mazajen auren daga manyan mutane da manyan masu power dan haka asalin masu gyaran da sai yayan manya ko jinin sarauta akewa aka dauko musu.

Dayake tsari da kaman layi ake bi dan haka yan mata hudu ne akan layin bada aurensu a gurin hidimar dan haka su hudun ne kadai zaa yiwa wannan gyaran amma Mum tai doublen kudin masu gyaran ta saka SANAAH a cikinsu sbd cikar da nufinta da niyarta.

Tashi hankalin SANAAH tayi sbd sam batada raayi hakama batajin ma tana buqatan wani sabon gyara dan wanda sukai a Nigeria ma bai saketaba haryanxu wani glowing da daukan ido takeyi,
Cire jin nauyin Mum din tayi ta sanar mata bata buqata cikin yar magiya.

Qin karban magiyarta Mum din tayi tace batason shirme kawai taje tayi abinda ta sakata.

Bataji dadin hakan ba sosai har cikin ranta amma fammah data rarrasheta da kulawa da tattali ya sakata amimcewa kawai sbd batajin zata iya qin jin magiya Fammah duk da itama Mum din tana jin nauyinta sosai da ganin girmanta.

Wuni daya sukai a cikin wani kebantaccen daki babba ana kaman steaming nasu yanda kowace gyaran zata shiga jikinsu direct sosai,

Abubuwan da aka wuni ana musu ita kaman ma zazzabi suka fara sakata sbd jin tayi jikinta yayi dumi yana zafi dan haka da dare tea dinma bata sha sbd anbasu wasu ruwan abubuwan kaman madara sun sha wanka tayi da ruwan da aka hada mata tai sallar ishai da shirin bacci ta kwanta.

Washe gari ma haka suka wuni kuma tin daga ranar sam bata sake saka Mum a idanuwanta ba sbd busyn data zama villah din ta cika sosai da jamian tsaro kala daban daban sbd manyan dake ciki.

Kwana uku akai ana musu gyaran aka gama amma ita kam zazzabi ne ya shigeta sbd gyarane da ita kanta yayi mata yawa take gani dan kuwa a cikin kwanakin abunda ake basu ita kam buga jikinta sukai dan jininta baida karfi sabanin sauran da lafiyarsu kalau babu abinda sukeji sun koma kaman wainda ko kallansu zakai saika wanke idanuwanta sbd tsabar wani daukan ido da sukeyi da sirrintaccen kyau da wata qamshi mai sanyi da rashin karfi ko kadan.

A ranar da aka gama ne akai musu wani lallen larabawan qasar mara yawa kadan mai kyau da tsari shi baiyi baqi ba sosai kuma ba ja bane hakama ba maroon ba haka yayi kaman dark brown a fararen fatarsu mai kyau hadda Fammah da Mum ranar akai lallen wanda take suma kowa ya sauya koina ado ne mai daukan hankali.
#MAMUH
09033181070
[06/06, 11:47 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

92
Da daddare SANAAH data batajin dadin jikinta har lokacin tana gefen Fammah cikin shirin bacci jikinta yayi dumi sosai ba zafi ba,

Wayar Fammah dince tai ringing wadda ke ta gefen SANAAH.

SANAAH bata motsaba sai dai fammah dince ta kalli wayar tana ajiye ruwan robar hannunta data bude zata sha tace

"Dad" da mamaki da farin ciki sosai a fuskanta takai hannu ta dauka daga inda wayar take ta sana handsfree tana cewa

"Dad,is that you??
Kasan yanda nayi missing naka?
Layinka are not going through and naso zuwa gidan Abbun but SANAAH bata iya zama ita haryanzu bata sakeba ko abincinmu sam bata iya ci sai Tea"

Shiru ne ya ratsa wayar wanda ya saka fammah kallan wayar zatai magana muryansa ta ratso wayar da cewa

"Is she okay??

"Yes Dad kawai dai rashin cin abincin ne,
Yaya kake Dad?
Mum is busy amma kullum saita kira"

"Lfy kalau alhamdllh,yaya kuke?

"Lfy kalau Dad kana gidan Abbu ne ko Dad zanzo na ganka gaskia???

"Yes" yace a taqaicen da muryan ta ratsi Kunnuwan SANAAH wadda take jin kowace sautinsa dake fitowa daga wayan tana shigarta ta kasa motsawa sbd tana motsawa tasan saiya sauka a kunnuwansa.

Shi kansa dayake zaune acan bangaren yasan tana kusada famman tana kuma jinsa dan haka dukansu sukai shiru sai da Fammah ta sake cewa "Hello Dad"

Sallama yayi mata kai tsaye yana cewa ta kula da kansu su dika,

Yana kashewa kai tsaye Ms Meenah ya kira itama wadda tana ganin kiransa taji wani sanyi da zazzafar kewansa ta rifeta ta dauki wayar tana zaunawa bakin gado daman ta gama shirin bacci tana dauka cewa tayi

"Hey my love,finally zan jika,
Yaya kake?
Ya gajiya?
Ya hanya?

A natse babu hayaniya ya amsa mata yana tambayarta ya take itama tareda yaya hidiman bikin.

Cikeda zumudi ta amsa tana marairaice muryanta da wata irin magiyar da kaman zata masa kuka tace

"Fleet dan Allah ko so dayan nan ne ka cika wannan Al'adar tamu tin ta kakanni sbd bayan Zad banda wani makusancin da zaka mun hakan ka taho cikin villah dinnan idan yaso ranar da aka kammala ka tafi,please please My love"

Idanuwansa da sauya mintina kalilan da suka wuce na wayar da yayi dasu fammah ya dago a hankali da wani irin slow yana yin shiru kafin daga sama kaman saukan aradun da bata taba tsammaniba a rayuwarta taji yace mata gobe insha Allah yana tafen.

Wani miqewa tayi cikeda mahaukacin mamakin da batadan lokacinda ta zari abayarta ba ta zuba tana ficewa daga dakinta tana kasa yadda da abinda taji sai data fice tace

"I love you my love"

Kashe wayar tayi kafin ma taji komai daga garesa da zai saka ya sauya raayin zuwan.

Kai tsaye bangaren musamman da aka ware na manyan sirikan babban familyn masu power ta isa daman akwai bangaren da bata taba barin anshiga ba sbd shine wanda take masa tanadi tsawon shekaru na fatan yaxo bikin Zad dan haka tana bude bangaren komai na cikinsa sabo dal hakama tsari ne da akai na musamman dayake shirye da komai babu wanda ya taba sauka duk bayan kwana biyu ake budewa a gyara a rufe.

Masu aiki ta kira ta saka a cikin daren suka sake gyarawa tukuna ta koma dakinta ta kwanta tana jin kaman zata taka kan jariri.

Koda gari ya waye da farin ciki sosai ta tashi ta damqawa masu aikin komai na kulawa da bangaren Fleet din ta fice zuwa wata hadimar tana jin kanta a sama sbd a karan farko da Fleet zai nunawa ahalinta na qasar Morocco kaf matsayinta dan kuwa duk manyan da suke cikin villah din fleet shine mai asalin power din.

Fammah ma tinda ta tashi yau busy take sbd yau ne ake asalin babban event din bikin wanda zaa zubar da asalin dukiya da nuna zinari ba komai bane.

SANAAH bata damar da fammah ba yau tabarta taji da hidiman gabanta a natse dan haka tana daki tana hutawanta da dan dube dube a ipad dinta da itace take cire mata kadaici.

Da yamma masu kwalliyansu suka iso aka fara yiwa Mum wani irin shirin daya sakata sauyawa gabaki daya xuwa asalin balarabiyanta mai kyau da wasu irin sarkokin zinari masu kyau da wayewa sosai ta fito harabar gidan tana waya zata shiga mota daidai nan motocin Fleet jeerah suka sako kai a harabar tana ganinsu take tasan shine dan haka ta fasa shiga motar tana jin wani farin cikin gaske dan haka da ta nufesa tin kafin ta isa aka bude masa motar ya sako kafarsa dake sanye da Santoni leather Oxford shoes brown ya fito gabaki daya cikin kamewa da kwarjini da nutsuwa.

Rungumesa kawai tayi a natse tana kai bakinta zatai kissin gefen fuskansa ta tina da makeup dinta da bata buqatan tai komai sbd itace takeson ta zama star.

Da farin ciki ta masa sannu da zuwa Zad da wasu manyan familyn da manyan mutanen dake aure a familyn suka iso gurinsa cikeda girmamawa da mamakin da kowa ya kasa nunawa suka tarbesa take aka kira aka qari securities a villa din sbd zuwansa wanda take kowa yafara jin wannan karan yabar tarihi sbd FLEET ADMIRAL JEERAH zai cike al'ada.

Bangarensa suna nufa wanda akaiwa gyaran musamman kana bude kofar palon wani sanyi da kamshi mai dadi ne zai bugeka.

Hanyar wucewa bangaren gabaki daya imran ya zuba securities dinsu wainda aka warewa gefe daya dayake kusa da nasa su da imran wanda dakinsa yake cikin inda suke shima.

Duk yanda takejin kewa da tsananin buqatansa bata iya tsayawa ta cusawa kanta hakan ba sbd gaskia tana buqatan tafiya sai dai idan ta dawo duk da kusan bikin na dare ne dan sai tsakiyar dare ko zaa gama sa dan yanzu haka anyi magrib amma ango baima isa ba yana gidan tinda dashi aka tarbi Raheem din.

Sallama tai masa ta fice yabita da kallo a natse sbd yasan koda yace ta tsaya kada ta tafi ba tsayawan zatai ba dan haka baima bude baki ya hanata tafiyanba duk da yanajin yanayin na buqata da iyali.


Tana barin bangeren tsaro ya qaru sbd Imran ya bada umarnin kada wanda ya wuce hanyar.

Fammah batasan Dad dinta yana Villah dinba sunata shiri angama musu makeup wadda sama sama akaiwa SANAAH batason mai yawa sun shirya cikin wata doguwan gown ta bikin larabawa ita dark maroon ne a jikinta sai fammah kuma fara da golden.

Karfe takwas da kusan arbain aka fara bikin wanda kusan kowa ya watse tsit ana gurin bikin.

Driver ne yaxo daukansu fammah da sukai na karshe tareda wasu yayan yan uwan Maman Mum su uku da sukazo bikin.

Basason takura ko kadan dan haka Mum fammah ta kira akan a aiko musu wani driver din.

Kai tsaye Mum din tace

"Dad dinki na nan villah din ku karbo motarsa daya kokuma ku taho kawai ku baro SANAAH ga Maleek nan zan aiko mata saiya daukota ita kadai inason su gaisa kafin su iso a hanya"

Fammah da bataji komai akan hakan ba tace shikenan.

Motar suka shige SANAAH da daman jin take kaman bazata iya zuwaba ta amince su tafin kawai niyarta ta komawanta ciki tinda Ammah na nan ta tayata fira kafin a dawo bikin dan kwalliyar ma damunta takeyi a fuska.

Suna wucewa ta wuce ciki ta nufi dakin Ammah.

Fammah kuwa suna isa gurin ta kasa karbi wayar Mum dinta sbd tabarowa SANAAH tata ta saka kiran Dad dinta wanda ya sauka yana fitowa wanka kenan ta sanar masa sun baro SANAAH ya saka driver ya kawota.

Shiru yayi kafin ya bude baki yace

"Meyasa baku tafi tare ba??

"Mum tace a barta zata turo uncle Maleek yaxo ya dauketa ita kadai ya kaita zasu gaisa"
#MAMUH
09033181070
[07/06, 6:02 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

93
Shiru ne ya ratsa wayar wadda ya dago idanuwansa da wani slow da nutsuwa ya bude baki yace

"And who is dat???

Da mamaki fammah tace

"Uncle Maleek Nuh"

Baice komaiba ya katse wayarsa yana ajiyewa ya tsaya a gaban mirror din dayaje dakin mai girma batareda ya shafa komai ba ko nufar kayan da zai saka dan shiryawa.

Tsayuwan mintina biyar yayi batareda yayi komaiba idanuwansa sun sauya yanayinsu gabaki daya wani irin zufa ne daya tsatsafo masa a jikinsa kadan kadan yana gangarowa daga lafiyayyar fatarsa,

Wayarsa miqa hannu ya dauka ba kowace hayaniya sbd ko maganan bayason yi ya saka kiran Imran.

Kalma biyu kawai ya furtawa Imran din ya kashe wayar ya juya ya koma bathroom sbd wani zafi ne yake fesowa daga jininsa yana bawa gangar jikinsa jin yake bayajin sanyi ko kadan wata zazzafan zafi ne yake bin jikinsa dayake fidda wata irin zufar daya sake sakarwa kansa ruwan shower masu dan sanyi.

Imran kuwa kai tsaye yana kashe wayar fitowa yayi sanye da wasu kayan shima dan haryayi shirin hutawa,
Kai tsaye ciki ya nufa dan yasan hanya da kuma ciki sbd matiqar suna qasar to Fleet na zuwa gaida Ammah kakar Ms Meenah din.

Babban palon farkon ya iso ya tsaya a kofar yayi knocking.

Dayake koina yayi tsit babu kowa sai kai tsaye masu aikin dake kitchen suka jiyo bugun dayansu ta iso ta bude kofar tana ganinsa ta bayyanarda girmamawanta sbd tasan babban yaron Fleet ne tinda suna zuwa kuma itama ta jima shekaru a familyn tana aiki.

Gaidasa tayi ya amsa kai tsaye da sanar da ita taje ta sanar da Ms SANAAH ana kiranta.

Juyawa tayi ta nufi hanyar dakinsu taje bata ganta a dakin ba ta dawo ta nufi dakin Ammah tana zuwa kuwa ta taddata zaune a dakin dan haka ta sanar mata kai tsaye ta juya ta koma ta sanar masa ta koma kitchen.

SANAAH da sam bataso mai daukan nata yazo ba numfashi ta sauke tana jin jikinta na sake mutuwa da kewan gida da jin bata cikin kowace walwala.

Tashi tayi taiwa Ammah sai ta dawo ta fice daga dakin makeup dinta kai sanyi da kyau kaman lokacin akai mata abarta.

Tana fitowa bataga kowaba dan haka ta fito daga palon zuwa harabar gidan dan duba motar data zo din...

Kafin ta isa Imran dayake jiranta ya bayyana a gefenta yana gaidata da turanci.

Dan juyowa tayi ta kallesa kadan tana mamakin ganinsa sosai wanda har sai da hakan ya bayyana ta gaidasa itama tana jin kaman sanyi ya ratseta sbd daga karshe dai taga wani dayake na gida dan sam ta kasa sakewa da samun nutsuwa a cikin ahalin gidan.

Hanya ya nuna mata suna tafiya da magana sama sama a tinaninta inda motar da zasu tafi da ita suka dosa sbd batama kawo a ranta daidai wannan lokacin da ake can ana fara hidimar ace Fleet na nan ba dole kila ya isa dan halartar taron.

Mantawa tayi da cewan wani zaa aiko mata ba Imran ba wadda ta yadda da kila Fammah ce ko mum suka aikosa a tafi din da ita tinda wanda akace din zaa aiko ma kila driver ne wanda bata sani ba ita tsoron ma mutanen da bata saniba takeyi.

Hanyar da suka kama kebantacciyar da suna isowa kusa taga securities dinsa a hanyar ya saka gabanta faduwa ahankali ta danso dakatawa sbd takunta dayayi sanyi ta dan kalli imran din tana kasa iya masa tambayar datake cike zuciyarta.

Kofar palon imran yakai hannu a natse ya bude mata bayan sun tsaya cak a bakin kofar wadda ta kasa motsawa bare daga kafarta ta shiga ta kuma qi kallan Imran din dan batason yaga yanayin data shiga na mutuwan jiki.

Daga kafarta tayi a natse da sanyin jiki ta saka a ciki tana shigewa da mataccen jikin da yayi sanyin datake tabbatarda na sauyawan bugun zuciyarta ne dan tin kafin ta sakasa a idanuwanta idanuwanta ke wani irin sanyi da zuciyarta data sauya bugawa da wani irin nutsuwa da samun sukun.

Rufe kofar imran yayi yana barin gurin ya da sake bada umarnin babu wanda zaibi ko hanyar.

Imran kai tsaye ordern abincin daya saka a wani lafiyayyan luxury Restaurant dake da Nigerian dishes a menu nasu ya koma yana jiran isowan order din dan yasan kowace lokaci motar kawo abincin zata iya isowa.

Daidai wannan lokacin Motar Maleek ta sako kai harabar gidan yayi parking tareda fitowa cikin brown kayansa masu kyau da suka zauna jikinsa fresh dashi shima balarabe mai kyau da kwarjini.

Ciki ya shige kai tsaye ya isa har gurin Ammah ya gaidata ya buqaci SANAAH din wadda batanan.

Dakinta akaje aka dubo masa ita amma batanan.

Wayarsa ya daga yana fitowa harabar gidan yana dubata ya saka kiran wayar Ms Meenah dan sanar da ita baiga SANAAH din ba.

Wayar na hannun fammah har lokacin dan haka kai tsaye itace ta dauka da yarensu ya sanar da ita SANAAH bata nan.

Cikin dan hankalinta daya dauku a gurin bikin sosai tace masa ya kira wayarta tana hanun SANAAH din yaji inda take.

Kashewa yayi ya nemo numbern Fammah din ya saka kira wadda tafara ringin a hannun SANAAH datai kasa wucewa can cikin dakin ta kuma kasa juyowa tana tsaye ta rasa gane ma abinda take ji gashi bata gansa ba babu kowa a lafiyayyan qaramin palon da babu abinda yake tashi dai kamshinsa da sanyin Aircon.

Daga hannunta tayi tana kallan wayar hannun nata taga sunan Uncle Maleek din a rubuce dan haka ta danyi tinanin sunan dataji kaman anfada ne zaizo daukanta dan haka ta daga a natse tareda kai wayar kunnenta ta bude baki zatai magana da muryanta mai dadi da zata ratsa wayar zuwa kunnen Maleek din ba tsammani cikin wani slow taji an birkitota a lokaci daya tareda saukan bakinsa a nata ya rufe muryanta da har sautin yafara fitowa.

Wani yarrrr taji jikinta yayi na kaman tsigar jikinta zata tashi gabaki daya sbd kwata kwata batai tsammanin kowaba a tafe bayanta bare shi din...

Dantsen hannuwanta ne a riqe da hannuwansa bakinsa na rufe da nata din yayiwa wani riqon dataji azaba na shigarta sbd kaman ma baisan yana mata wannan muguwan riqon azabar ba dan haka ta dan motsa tana tana son kwacewa amma ba qaramin riqo bane dan haka ta motsa bakinta zata budeshi tai magana amma motsawan da budewan bakin nata akan nasa dayake kai ya saka bakinsa shiga kai tsaye cikin nata yayi mata wata irin tsotsa daya data saka numfashinta fita da wani irin yanayi mai karfi da tayar da tsikan jiki wanda har wayar datake hannunta hakan ya ratsa.

Subucewa wayar hannunta tayi qasa wadda kiran Maleek din yake kai bai yankeba.

Sassauta riqon da baisan ya mata ba yayi yana sake bata wata fitinanniyar tsotsan da kafafunta sukai sanyi suna kasa daukanta sbd duka abinda ta rasa gane kanta a kwanakin suna taso mata musamman dumin jiki na abubuwan da ita kanta tasan sune suke bata wannan yanayin da aka ringa basu suna sha gata jinin be karfin nasu ba.

Jinsa a jikinta ya saka jikinta jin dukannin nutsuwa da samun zazzafan yanayin da batasan ma tana jinsa ba.

Maleek da kansa yayi mummunan sarawa da jin abinda yaji din kasa yadda yayi da kuma cikakkiyar fahimtar me yaji duk da babu kalma ko daya data ratso wayar amma numfashi da nishin dayaji ya sakasa a babban rudani da kasa gasgatawa dan haka ya kashe din ya sake saka kira.

Ringing wayar ta fara wadda kafa kawai Raheem ya saka ya shurata ta bugi bango ta dauke wuta gabaki daya tana fashewa batareda ya saketaba ita kuma sai a lokacin ta dago idanuwanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login