Showing 105001 words to 108000 words out of 244256 words

Chapter 36 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

478

zai fada yana bude baki zaiyi magana aka bude murfin motar gefen da Maamah take dukansu suka kalli gurin Fleet dinne da kansa daya fito da kansa dan tarbansu da kuma hana hayaniyar da zata iya tashi na Dr Mum da zata ga kanta a nan.

Maamah na ganinsa ta saki ajiyan zuciya sbd batasan ta inda ma zasu fara tausan Dr Mum ba amma sbd wasu lokutan da dama idan ya shimfida mata magana a kame takan bi sbd girmansa da kwarjinsa da zamansa a yanxu wakilinta dan har aurenta shine yanxu yakeda ikon bayarwa sbd yawanci idan manyancin da tsufa yazowa iyaye suna bin yayansu ne wasu lokutan kuwa duk zafinsu.

Bude baki bakinsa yayi kwarjinsa na sanyin safiyar yana cike idanuwansu da kirjinsu da nutsuwa da kamewansa da babu hayaniya ko doguwan sakewan hayaniyar a tsakaninsu yace

"Barkanku da sauka Maamah"

Fitowa Maamah tayi tana kallansa da nutsuwa da kulawa da girmamawa tace

"Barka ABDULRAHEEM"

Dr Mum ya zagaya da kansa ya budewa motar tareda kallanta da idanuwansa da suka sakata daure fuskanta sosai tsananin bacin ranta da wani radadin zafi na tirnike fuskanta da kirjinta ta bude baki cikin asalin zafin da yana iya jinsa a yanayin kafin tace komai ya bude baki a tsanake yace

"Dr Mum kiyi hakuri anan zaku zauna tinda zaman bame dadewa bane zaku koma babu kowace gurin da zan baku kariya da kulawa daya wuce inda nake zaune,
Ba a gurin kowa kuka zo ba ko zaku zauna sai a gurin 'dan da kuke da iko dashi so please Dr Mum ba wani buqatab stressing kanki kiyi hkr da hakan"

Maamah ce ta dawo gurin Maamah din tana kallanta tafara magana a natse cikeda kulawa da kokarin kwantar da balain da masifar datake gani suna neman bulluwa.

Imran gefe ya koma shima cikeda nutsuwa da jiran kowace umarni ko hukunci.

Securities ma nesa suka je suka tsaya suna bawa hanyar kariyar da har sai su Maamah din sun shige.

Tashin hankali ne yake neman ballewa sbd mummunan bacin ranta daya bayyana wanda ya saka Fleet da kansa sauke kansa qasa yana karban kowace zazzafan kalmanta data aiko masa batareda yace komaiba har sai data gama ta kalli Imran da jajayen idanuwanta tace ya kaita babban Lodge kawai.

Kallan Fleet Imran yayi cikeda girmamawa sedai ganin Fleet din baiko dagoba ya sakasa maida kansa qasa shima yana kasa motsawa.

Dagowa RAHEEM din yayi ya kalleta a natse ya bude baki yace

"Basai anje koinaba ki shiga ki jira in the nxt 24hrs zaa samar da gidan da zaiyi daidai da zamanki da saka komai da zai baki nutsuwa da walwala just 24hrs insha Allah."

Hakan daya fada ya saka Maamah qara saka baki da sanyaya harshenta wanda kuma maganar Fleet din haka take yankakka ce dole ko bataso saita jira kaman yanda yace din kenan.

Zazzafan Numfashi ta sauke tsabanin zafinta na qaruwa da wata irin baqin ciki da takaici tareda dana sanin zuwa Nigeria din kwata kwata.

Kayansu aka fitar suka tinkari bangaren wanda suna isowa kofar palon shiga bangaren masu aikin ciki su biyu suka bude kofar acike da girmamawa suna musu barka da zuwa kansu a qasa.

Ciki akai da kayansu daga nan Imran ya juya shima yana shiga har palon ya juyo yabarsu su huta tukuna sbd suna buqatan hakan kafin yan gidan kowa ya tashi.

Yana ficewa Bedroom aka kaiwa kowannensu kayansa tareda basu daman hutawa koina tsit wani qamshi mai dadi da sanyin qamshi ne yake ratse koina tareda sanyin AC.

Tsarin komai irin tsarin da akasan tanaso ne akai hakama komai tamkar anje anga yanda tsarin gidansu na Morocco ne,

Tana cikin bacin rai da radadi mai tsananin gaske dan haka wanka da sallar asubar dake kansu kawai tayi ta kwanta dan yin bacci sbd bata hada komai yanzu da lafiyarta tin a wancan karan bata yadda da duk abinda zai kawo matsala ga lafiyarta musamman idan tabari baqin cikin jeerahs ya sake taba lafiyarta a karo na biyu tayi asara dan haka hutu da warwaren kai take buqata kafin ta iya fuskantar komai.

Maamah ma tana gama komai kwantawa tayi baccinta dan haka koina ya sake daukan tsit kaman babu kowa a bangaren sai su Nafeesat dake kitchen suna aiki.


*****Guraren karfe goma su Mum suka hau Dining cin abinci itada Fammah ne suka fara isowa table din,

SANAAH data saba zuwa late yauma fitowa tayi tana tafiya ahankali a natse fuskanta na wani narkewan datake jan kafa tana jin kaman ta ficewanta tayi bangaren mommy batareda taje dining dinba.

Yanda takeyi da fuska tana sake jan kafa ya saka batama san ta kawo gurin bangon da zai isar da ita kofar shiga dining room dinba kanta ya tafi zai bugi bango ahankali ba zato tafin hannunsa ya sauka a goshinta yana hana kanta buguwa sedai bayan hannunsa ya bugi bangon ahankali.

Dagowa tayi ahankali da dan faduwan gaban da bai bayyana a fuskanta ba da yanayinta ta kallesa da idanuwanta gabaki daya.

Nasa idanuwan ya saukar mata ya kalleta da kyau kafin ya saka hannunsa daya ba tsammani ya kama tafin hannunta yayo baya da ita tareda sake kallanta ya bude bakinsa yace

"Meyasa bakya kallan gabanki?

Wuyanta ya gangara da idanuwansa ya kalla da tinanin ko batada lafiya ne amma bai kai hannunsa wuyan nata ya taba ba ya maida kallansa akan fuskanta ta sauke nata idanuwan ahankali sbd bazata iya daukan kallan fuskansa ba a lokacinda nasa idanuwan suke kallanta.

Rikicewa ma tafara kokarin yi dan haka a rashin sanin abin yi ko fada ta bude bakinta tace

"Ina kwana"

Sautin muryanta haka yakejinsa koyaushe kaman na Baby da koyaushe Nasir yake magana da ita abaya dan haka a duk lokacinda muryan ta ratsa kunnuwansa lokutan dayake tareda Nasir ne suke dawo masa da feelings din dayake tsakaninsu da rabin jikin nasa dan hakane baya taba iya jin saukan muryanta a kunnuwansa batareda ya dago ya kalletaba wanda hakan matsala ce babba a gurinsa.

Kafe idanuwan nasa suke akanta yana kallan kowace numfashinta dayake fita yana komawa ahankali.

Juyawa yayi yabar gurin yana shigewa kofar dining room din wadda Mum na ganinsa ta miqe ahankali tana isowa gurinsa ta rungumesa ahankali daidai nan SANAAH ta sako kai itama tana kallansu a natse.

Fammah ma tasowa tayi zata iso gurin Dad din wanda ya zare Ms Meenah daga jikinsa yana rungume fammah wadda take gaidasa tana kallan SANAAH data isa ta zauna batareda ta kalli kowaba a cikinsu.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

63
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Zaunawa sukai har lokacin SANAAH bata dagoba saida Fammah ta dora hannunta akan nata tana ambatan sunanta ahankali.

Dagowa tayi tareda kallan Fammah din tana tsayar da idanuwanta akanta tana kallan fuskanta cikin wani sanyi da nutsuwa tsawon lokaci kafin ta sauke ajiyan zuciya ahankali tana bude baki da yanayin yanda ita kadai sai yaya Al'amin takewa hakan kaman zatai kuka ahankali sosai babu me ji idanuwanta nayi kaman zasu ciko da wasu hawaye tace

"Banajin dadi cikina na ciwo bazan iya cin komaiba"

Tana qarasawa ta sauke idonta qasa kasa taba komai akan dining din.

Fammah ajiye spoon din hannunta tayi tana juyowa ta kalli SANAAH din gabaki daya kafin tace komai Mum dake kallansu tace

"Lafiya kuwa?
Meke faruwa ne?

"Mum cikik SANAAH na yana ciwo"

Kallanta Mum din tayi da kyau tana cewa

"Baby SANAAH sosai ne yake ciwon??

Girgiza kai tayi ahankali tana cewa

"No Mum ba sosai bane,bari naje na dan kwanta kila zai dena"

Miqewa tayi ahankali tana kokarin juyawa Mum tace

"No Baby SANAAH dole kina buqatan cin wani abu sbd shine zaisa ma kiji sauki sauki"

Rufe idanuwanta tayi ahankali tareda sauke wata ajiyan zuciya zuciya da numfashi mara karfi na rashin zabin daya wuce ta koma ta zauna ahankali...

Fammah ta zuba mata tea mai zafi ta bata a cup ta karba tana sha ahankali tareda dan cin yamballs kadan.

Suna gamawa Dad dinne yau ya fara gamawa yabar dining din.

Mum ma gamawa tayi ta miqe tabi bayansa tana masa maganar yau takeson tarewa sabon bangaren da aka gama.

Dakatawa yayi daga tafiyar dayake yi ya juyo ya kalleta dakyau kaman bazaiyi magana ba sai kuma yace

"Su Maamah akaiwa gyaran bangaren itada Dr Mum kuma sun iso yau da asuba"

Cak ta tsaya daga tafiyan datake yi ta kallesa da kyau shima ita ya kalla daidai nan Fammah da SANAAH suka fito Famman na riqe da hannun SANAAH wadda take kaman baby wani lokacin a gurin fammah.

Farin ciki ne mai tsananin gaske ya rufe Mum din ta bude baki tace

"Dr Mum ta iso yanzu haka kenan tana tareda mu"

Dan sama tayi da kafafunta ahankali takai bakinta gefen fuskansa tayi kissing dinsa cikin farin ciki ta wuce da sauri tabar palon tana ficewa zuwa gurinsu Dr Mum.

Fammah dataji abinda Mum dinta ta fada na zuwan Dr Mum itama qarawowa tayi gabansa tana sakin hannun SANAAH ahankali tace

"Dad Dr mum ce ta taho??

"Yes" ya furta mata yana sauke idanuwansa a bayanta
Itama bata tsaya komaiba ta wuce tana bin bayan Mum dinta.

Takowa SANAAH tayi ahankali tana giftasa zata wuce idanuwanta na qin kallan inda yake,

Taku daya tayi daga gurinsa hannunsa ya sauka akan hannunta yayi mata riqon daya sakata tsayawa cak batareda ta juyoba tsigar jikinta n dan tashi daga yanda fatar tafin hannunsa mai dan sanyi kadan ta sauka akan fatar hannunta yayi mata riqon da fatar jikinsu ne ta hadu da juna a tsanake.

Kadan ya matso ahankali ya sako kansa cikin wuyanta gefen fuskansa ya kara a fatan wuyan nata batareda sun hade ba yaji babu alaman zafi a jikinta na ciwon da aka ambata dan ya dago idanuwansa zai janye ita kuma jun saukar dumin numfashinsa mai zafi akan fatan wuyanta ya sakata juyowa sai fuskansu ta hade dogayen hancinsu suka gogi juna ta ja baya da wani sauri sbd yanda numfashinsa ya shigeta kai tsaye da karfi tajisa har cikin kwakwalwanta...

Bayan datai da karfi ya sakata kusan faduwa ya sake riqota yana dawowa da ita kirjinsu ya hadu kadan haduwan da saida kirjinta ya gogi nasa ta rintse idanuwanta da sauri tana sake janyewa shikuwa idanuwansa ya sauke mata ya bude baki zaiyi magana ta juya da sauri ta nufi kofa sbd iya bakin daya bude dumin ciki ya daki gefen fuskanta da fatan kunnenta jin tayi gabanta yana bugawa da karfin gaske dan haka bazata iya sauraron saukan muryansa a kunnuwanta ba.

Harta fice bata juyoba tana kuma jin kaifin idanuwansa akanta dan haka ta qara sauri ta fice daga palon tabar bangaren gabaki daya tayi na mommy tana isa gaida mommyn kawai tayi tana wucewa bedroom dinsu ta nemi guri ta zauna akan sofa ta nutsu tana jin ciwon cikin gaske yana kamata.

Bata fitoba bare ta sanar da Mommy zuwan da akace Dr Mum mahaifiyar Dad din Fammah din tayi dan haka Mommy bata saniba tanata shaaninta.

Sai bayan tsawon lokaci har azahar tayi tukuna ta fito bayan tayi sallah ta tadda Mommy palon zaune tana waya dan haka ta zauna tana kokarin saka kiran itama.

Acan bangaren su Dr Mum kuwa murna ce da farin ciki ya cike na ganinsu itama Dr Mum din ta dan sassauto ta boye fushi da bacin ran datake ciki ganin fammah da Meenah din sunata murnan zuwanta dan haka aka hau fira da murna batareda kwata kwata su Mum din sun tina fadawa Su Dr Mum din tareda wa suke a gidan ba.

Kasa hakuri Dr Mum tayi yamma na kokarin yi ta Nemi ganin Dad jeerah wanda daman yau zaman nasa na jiran kiranta ne dan haka tana neman ganinsa kai tsaye ko isar masa da sakon Ms S beyiba ya bata daman zuwan dan haka ko data baro bangaren sanye da doguwan rigar Morocco maroon kala da rufarta akai ta nufi bangaren nasa tana gap da ficewa daga inda jerin bangarorinsu suke a jere Hajiyar Samad ta fito danye da atampar Exclusive super da lafayar tsadaddiyar lace zata fita idanuwanta suka sauka akan asalin balarabiyar macen data sanyata dakatawa cak ta tsaya tana kallanta batareda Dr Mum dinma ta ganta ba bare sanin da ita a gurin kawai dai Imran ne a biye da ita dan bata rakiya zuwa can din.

Bude idanuwanta da suka shige kaman na kashe kwarkwarta Hajiyar tayi tana sake kallan Dr Mum da Kyau tanason sanin ina suka samu larabawa bayan Meenah da suke da ita.

Kamannin Fleet take kokarin ganin suna neman bayyanar mata akan fuskan matar harta bacewa ganinta dan haka taji bama zata iya fitaba sai tasan me gidan nasu yake ciki dan kila dangin Meenah ne sunzo indai hakan ne gwara taje ta san yanda zata sanar da maganar auren wa meenah sbd su tayata zuba tashin hankalin da zasu babbakawa villah din wuta tsabar kishi da tashin hankali kafin su tafi.

Bangaren Meenah din ta nufa kai tsaye amma babu kowa sai mai aikin da suma aka kawo musu tana aiki.

Juyawa tayi ta nufi sabon bangaren da akace meenah din na can tana isa kai tsaye ta shige tana jin ranta fes hakama tana fatar daga yau balai ya balle kowa ya rasa zaman lafiya da walwalan da aka saka ta rasa.

Tana shiga babban palon da sallama tsarinsa ne ya sakata fara dakatawa da wani irin mamakin tsarinsa dayake kusan daban dana kowa tinda shi saida aka sauya har ginin.

Maamah ce ta fara dagowa ta kalleta da nutsuwa da dan mamaki amma kuma sai tafara kokarin sake fuska dan gaisawansu sabanin su Mum da suke kallanta da dan daidaita tasu sakewan dan gaisawa da ita.

Hajiyar kuwa tana sauke idanuwanta akan Maamah ta ganeta sbd itace Uwar Fleet da suka sani.

Gurin zama ta fara nema da kanta ta zauna sbd jin tana shiga confuse da lissafin ganinta da matar data gani ta wuce....

****Dr Mum tana isa babban palon dayake nasa na hutawansa ta musamman sake daure fuskanta tayi da kyau da wani irin zafi da quncin dayazo ya danne kirjinta dan haka tana sako kai a asalin palon yana zaune cikin nutsuwa da kwanciyan hankalin jiran nata dan haka ya dago idanuwansa masu kwarjininsa tin kafin ya manyanta ya saukesu akanta yana mata kallan da tin daga ranar da suka rabu a palon mahaifinta bai taba samun damun ganinta in one haka ba tsawon shekarun sai ayau karan farko tana gabansa.

Dagowa tayi da nata idanuwan da suke cikeda zafi da baqin cikin shekaru da haryau bai saukaba ta kallesa kallan dayake tattare da cike da zafin dayake gani a bayyane.

Ahankali ya miqe tsaye daga zaman dayake cikin wata irin nutsuwa yana kallanta har lokacin harta iso gabansa ta dauke idanuwanta da kallanta daga kansa tana tana daidaita baqin cikinta tareda danne duk abinda take ji ta kallesa tana sake maimaita sallamar datai kafin shigowanta.

Amsawa yayi anatse kafin ya nuna mata gurin zama yana komawa ya zauna shima itama ta zauna tareda sake kallansa tana cire komai dayake tsakaninsu kokuma daya taba shiga tsakaninsu ta watsar sbd yanxu babu sauran duka wannan kaman yanda Fleet ya fada babu abinda ya rage bayan mutumcinsa shi dayake tsakaninsu.

Numfashi ta sauke tana sake sauke ajiyan mai sanyi da nutsuwa ta kallesa ya bude baki shima a sake da nutsuwa babu nuna komai yace

"Barka da zuwa Nigeria Dr,
Fatan kun sauka lafiya kuma kun baro mutan gidan lafiya"

Bata taba ganin mutum mai iya taku da sarrafa kowace manufa da iko ba irinsa dan haka itama ta sake watsar da komai ta dan sake yanayinta ta kallesa tace

"Lafiya kalau Alhmdllh,
Mun sameku lafiya?
Ya family?

Wani lafiyayyan murmushi ya sake yana shinshino irin abinda yake gudana a jini da kirjinta data danne ta boye sbd duniya babu wanda ya mata sanin daya mata.

Suna gama gaisawa ta bude baki zatai magana ya rigata cikin tsanaki da walwala da cewa

"Dr duk abinda yake tafe dake nayi miki alkwarin zan biya miki shi,
Maganar auren Fleet ne insha Allah
Na miki alkwarin zan raba wannan indai hakanne abinda ya kawoki tin daga qasar Morocco zuwa Nigeria"

Kallansa tayi da sauri da mamaki mai tsananin gaske wanda bai boyuba na jin maganar dayake fada kai tsaye cewan zai raba mata auren da kansa.

"Yes Dr,ai shine abinda kike buqata amma ki fada da kanki din nikuma zuwa gobe zan cika miki burin hakan"

Bacin ranta dan fara fitowa yayi tace

"Kasan da hakan meyasa ka jira har saida nazo?
Meyasa baka tambayeni tin ina can ba saina fada ka cika hakan?
To tinda har kasan hakan mezai saka har sai goben ka raba auren ayau tinda kaine ka basa matar sbd rabasa da matarsa,
Bazan taba karban aurenba dan haka indai har kalamanka hakan suke to araba auren nikuma wlh ko a goben zan bar qasar na koma inda na fito"

Murmushi mai sanyi da nutsuwa ya kalleta da kyau ya sake sakin murmushi mai tsantasar nutsuwa da kwanciyan hankali sake yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login