Showing 222001 words to 225000 words out of 244256 words

Chapter 75 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

444

shima mai hawa daya.

Dr Mum tinda aka gama komai kowa ya watse bata iya zuwa bangarensa ba sbd batajin dadi kadan mura takeyi dan haka bai ganta ba sai washe gari da safe taje takai masa breakfast ya zuba mata idanuwansa yana kalla tareda sauke ajiyan zuciya da numfashi mai sanyi yana daga hannunsa daya cikin kulawa da tarin soyayya mai karfin datake cikin jininsa ya miqa mata yana kallan idanuwanta data dago dasu masu haske ta kallesa tana jin wani irin nauyi da mutuwan jiki na rufeta.
#MAMUH
09033181070
[24/06, 11:51 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

140
Ahankali ta maida idanuwanta akan hannunsa daya miqo mata ta kalla da wata irin sanyin dataji jikinta ya qara sanyi da jin idanuwanta suna cikowa da wasu hawayen da batasan lokacinda suka taho ba tana kasa motsawa harya motsa ahankali shima yana isowa da hannun nasa akan nata ya dora yana sakawa cikin tafin hannunta ahankali ya hade tafukan hannuwan nasu tareda sauke wata ajiyan zuciyan data fito daga kowace iskar dake cikinsa yana qanqame tafin hannuwan nasu itama rintse idanuwanta tayi ahankali da dan karfi hawayen dake cikinsu suka digo ahankali suna sauka akan bayan hannunsa dayake qanqame da nata ya zuba musu ido da idanuwansa da sukai jajir yana jin Dr fammah itace tasa kaddarar da bazai taba iya cin jarabawa akanta ba.

Bai sake hannunta ba daya saka a cikin nasa ya janyota jikinsa ahankali ya mata wata halal runguman daya shigar da ita jikinsa sosai yana jin tsigar jikinsa na tashi har cikin kansa tareda jin kamshinta kai tsaye cikin hancinsa zuwa kansa karan farko bayan shekaru.

Ita kanta rufe idanuwanta tayi tana sake jin hawaye na zuwar mata na samun kanta a tareda wanda bata taba saka ran sake dawowansa rayuwarta ba.

Shiru sukai a hakan tsawon lokaci kafin ta iya janyewa ahankali tana barin jikinsa ta hada masa abincin tana miqa masa cup din tea mai kamshin data hado masa a cikin breakfast din.

Amsa yayi yana hadawa da hannunta ya riqe a cikin nasa daya tukuna yafara sha yana kasa dauke idanuwansa daga kanta cikeda samun nutsuwa da kwanciyan hankali.

Sai daya ci komai ya koshi tukuna ta baro bangaren ta dawo nata tana shiga duk taji itama kaman batada lafiyar dan haka dakinta ta shige bata fito ba sai yamma lokacin SANAAH zazzabi take dan ji dan haka koda sukai sallan magrib abincin da safiya ta gama hadawa da komai na Dad a ciki Dr Mum din ta kalli SANAAH dake lafe a palon tace

"Ki hadawa Fleet nasa ki kai masa dan banajin ana aika masa abinci daga bangaren Maamansa"

Shiru tayi cikin damuwa da rashin son zuwa sbd batason taje ta hadu da matarsa a gurinsa dan haka ta dan lafe tana bude baki tace

"Suna kai masa may b ma anriga ankai"

Dauke kallanta daga kanta Dr Mum tayi tana maida akan wayar hannunta tace

"Eh kije ki masa tinda babu tabbacin"

Shiru tayi tana jin jikinta na sake sanyi dan haka safiya dataji hakan kitchen ta koma ta hada masa nasa a tray da komai a tsare ta ajiye.

Sallar ishai sukai suna gamawa kowa ya shige sbd kusan daman hakan sukeyi.

Wanka tayi tayi shirin baccinta kaman bazata ba sai kuma ta daure ta sako doguwan hijab ta fito ta nufi kitchen ta dauka a natse ta fice.

Dr Mum ma data kira Fleet din ta sanar masa SANAAH zata kawo masa abinci sbd tsoron kada matarsa tai wani abin gwara ya san da zuwan SANAAH din tana gama fada masa sallama sukai ta kashe wayarta tana shiga wankan itama.

Tana fitowa cikin doguwar riga ta shirya mai kyau da rashin ado ta fito ta tafi kaiwa Dad abincinsa dayake jiran a kawo masan dan kuwa har wata yunwa yakeji.

Ko data iso bangaren koina tsit tini Mr S yai sallama dashi ya tafi hakama ya bada umarnin securities kowa kada ya tafi ko hanyar bangaren Dad din hutawa zaiyi sbd hayaniyar kwana biyu da rasuwan da akai dan haka koina tsit yake babu komai da kowa.

Ko data shiga palon farko shiru babu haske sosai iya aircon ne kadai ke aiki da wata kamshi mai sanyi,

Kai tsaye palonsa na kurya ta daga kafafunta tana takawa da nustuwa ta shige bayan ta saka hannunta daya ta bude tana shiga shima babu wani haske sosai ta rufe kofar tana isa inda zata ajiye abincin akan dining dinsa mara girma da tsari ta ajiye ahankali tareda juyowa a natse tana kallan koina ta tako kafarta tana dawo tsakiyar palon tareda kasa daga kafarta ta isa kofar master bedroom dinsa datasan yana ciki sbd bata taba shigarsa ba tinda take duk da kusan a jiyan an sauya komai na dakinsa an saka komai da komai sabo fil.

Tsayuwan datai a gurin tana shiga dan tinani ya saka harya fito batasan da hakan ba saida ya iso gabanta ya saka hannunsa daya ya kama nata a natse yana kaiwa bakinsa cikin wata nutsuwa ya sauke maga kiss mai sanyi yana kallan fuskanta data kallesa itama tana dawowa hayyacinta.

****SANAAH ma a natse ta isa bangaren Fleet din wanda tana shiga koina babu haske sosai dan haka kai tsaye hanyar bedroom dinsa ta nufa tana takawa ahankali da shakkar isa sbd batasaniba ko matarsa na ciki batason damar dasu da kanta daga abinda zata iya gani dan haka a bakin kofar bedroom din ta tsaya bayan ta shiga palonsa na kurya ta sauke idanuwanta qasa da numfashi ahankali ta daga hannu zatai knocking sai kuma ta dakata tana fasawa ta juya ta ajiye tray din akan table dayake palonsa zata juya ta nufi kofa ta fice ya bude kofar bedroom din nasa sbd jikinsa daya basa da kuma dan motsinta daya ji.

Bude kofar ya sakata dakatawa tana kasa juyowa kirjinta na wani irin nauyin gaske taji idanuwanta ma mata wani radadi da cikowa da hawaye ta sauke ajiyan tana kasa juyowa har lokacin saida ya tako ahankali yana isowa bayanta hunnunsa daya kawai ya saka ya zagayoya ta bayan yana janyota jikinsa ya mata wata kyakkyawar rungumar data rintse idanuwanta hawayen dake ciki suna saukowa sbd saura kadan zuciyarta ta dena bugawa daga abinda taji tanaji akansa.

Shi kansa wata lafiyayyar ajiyan zuciya mara sauti ya sake yana qarasa zagayota da hannun nasa daya yana sako kansa gefen wuyanta suka lumshe idanuwa a tare.

Jin digar hawayenta akan hannunsa ya sakasa juyowa da ita ahankali ya kalli fuskanta ta dago itama kallo daya tai masa ta fasa masa kuka kawai wani kishinsa na neman buga zuciyarta ta fada jikinsa ta qanqamesa.

Kai tsaye a cikin idonta yaga menene yake cinta dan haka rungumeta yayi yana dan qanqameta tareda bude bakinsa yace

"I love you"

Sake shigewa tayi jikinsa kukanta na kasa tsayuwa haka kawai.

Ganin hakan ya dago kanta yana kallan fuskanta sai kawai ya sake murmushi mai kyau da tsari daya qarawa fuskansa kyau yana tallafe fuskanta da hannuwansa biyu ta bude idanuwanta dake hawaye ta kallesa ya kuma sake mata murmushi mai kyau ta turesa tana juyawa da karfi zata fice ya mata riqo daya tareda juyota gabaki daya yana fizgota ta fado kansa fuskansu na hadewa da bakinsa a nata lokaci daya ya mata wani lafiyayyan kiss da tsotsa ta minti daya cif kafin ya saketa tai baya zata zube sbd kasa tsayuwan datai da kafafunta sbd ba qaramar tsotsan data ratsa kowace jijiyan jikinta yayi mata mai sanyi.

Tarota tayi da hannunsa daya yana saka daya a wuyanta ya kamo wuyanta yana kallan cikin idanuwanta yace

"You OK????

Girgiza masa kai tayi da wata salon daya ke nuna ta gama mutuwa akansa da kishinsa ya sake sakarda wata mayen murmushi yana sama da ita ya juya zuwa bedroom dinsa suka shige yana zare hijabinta da jefar dashi yana dorata akan gaban mirror din dakin mai girma ya ware kafafunta ya shiga tsakiyarta ya tsaya yana sake kamo wuyanta da hannunsa daya yana mannota fuskansu ta hafe ya shaqi numfashinta da wani slow yana wata lumshe idanuwan da suka fara buguwa da kewanta ya bude baki yana goga lips dinsa a fatar wuyanta yace

"I cant live like this..."

Hannunta daya ta daga ahankali tana dora akan kirjinsa tana dan turesa kadan ta bude baki tace

"Dr Mum na jiran komawata"

Dan dakatawa yayi daga shinshinarta dayake yana shaqa ya dawo da fuskansa saiti da tata yana hadesu ya bude baki lips donsa na gogan nata yace

"Ko data turo ki tasan bazaki taba komawaba yanxu,
Ko acan baya tasan da hakan take turoki ai so zan kula mata da yarinyarta a daren yau da safe zan kai mata ita da kaina"

Da wani sauri ta kallesa da mamaki da wata dariyar dake zuwan mata data kasa yi sbd abinda yake mata yana sakata jin jikinta na karban shock ta bude baki tace

"Haka kake daman???

Murmushin da baisani bane ya kufce masa yana dago idanuwansa ya kalleta da wata dariyan da baimasan yana yi ma mai daukan hankali da rashin sautin data sakata kallansa itama tana murmushin ganin dariyansa.

Bakinsa yakai kunnenta ya fada mata wasu kalaman da suka sakata rintse idanuwanta da sauri tana dariya da saka hannu zata dan turesa ya riqe hannunta yana sake mannota jikinsa yana saka bakinsa cikin nata ya mata wani fitinannen kiss daya sakata zagayo kansa tana shaqan kamshinsa dataji ya bata wata nutsuwa da sanyin ruhi ta kuma shaqarsa shi kuwa ya dake kama bakinta suka fara kissing juna da wata lafiyayyar so da shauqin juna.

A gaban mirror din ya sake manneta suna raba juna da kayan jikinsu yana mata wata lafiyayyan mannuwan datake sake mannuwa da jikin mirror din tana zagayesa da hannuwansa tareda yin baya da kanta suna samun juna da wata shauqi me karfi.

Anan sukai wata lafiyayyar love din da suka qarasata a cikin gadonsa suna gamawa ko motsawa bataiba daga gurin tai masa bacci.

Saida baccinta ya danyi karfi kadan ya miqe ya fada bathroom yana fitowa ya saka doguwar wandon bacci kawai ya kwanta.

Da asuba ma haka sukai sallah suka sake koma bacci bayan sunyi wasansu.

Karfe tara na safe harma da mintina 40 SANAAH ta tashi daga baccin tai wanka ta shirya ta fito a ta tadda safiya ta kawo musu breakfast ta jere shikuma yana palonsa zaune yana waya mai mahimmancin dataga ya nutsu sosai yana bayani da bada umarnin da take ta fahimci harkan soldiers dinsa ne dan haka ficewa tayi ta nufi palon da aka jere musu komai.

Fasa zaunawa tayi ta fice dan zuwa sauya kaya ta sako wasu sbd na bacci ne jikinta.

Tana fitowa kaman daga sama saiga Meenah wadda itama isowanta kenan kaman a mafarki taga SANAAH din take kowacensu gabanta yayi mummunan faduwa dan haka cak SANAAH ta tsaya tareda dan dago kanta kadan tana kallan Meenah din ta bude bakinta daqyar ta iya cewa

"Mum ina kwana"
#MAMUH
09033181070

141
Wani irin baqin ciki mai tsananin zafi da nauyin gaske ne yaxo ya dannewa Ms Meenah kirjin dataji kaman zatayo aman zuciyarta da kalaman SANAAH din bayan radadin daya dabaibayeta yana tafasa a jininta na ganinta ta fito bangaren fleet din dake nuna alaman a gurinsa ta kwana.

Wani mugun ja idanuwanta sukai take tana sake tsayar da kallanta akan SANAAH din wata wuta na tasowa da karfin gaske daga cikin kwakwalwanta zuwa kirjinta da jininta batasan lokacinda ta daga hannu saukewa SANAAH din wani mahaukacin marin sunan data kira dashi na Mum wanda Safiya data kawo gurin kawo musu sauran breakfast sakin kayan hannunta tayi da sauri tana janye SANAAH din baya ba tsammani dan haka iskan marin mai karfin gaske ne ya sauka a fuskanta kawai ta dago da wani irin firgita ta kalli Meenah din idanuwanta na sauyawa da wani irin tashin hankali da mamaki harma da faduwan gaban abinda bata taba tsammaniba.

Kanta Meenah tayo wanda ya saka Safiya sake janyeta da karfi tana harsuna baya zasu fadi kaman daga sama aka bude kofar palon suka juya dukansu da karfi sai ganinsa sukai a tsaye idanuwansa tsaye akan Meenah din wadda ta juyo gabaki daya tana kallansa da wani irin zafin kishin daya taso yana kasheta gabaki daya sbd irin sauyawan dayayi ya qara wata haske da lafiya da sauyawa kwata kwata kaman bashi dinba take ta sake waiwayowa ta kalli SANAAH tana bude baki cikin jin kaman zata mutu a gurin tsaye tsabar baqin ciki tace

"Fleet akan wannan duka kake kokarin cireni daga rayuwarka???
Akan macen da wani ya gama da ita ya rage maka kake........

Kafarsa daya ya sako wajen ba tsammani da wani irin mummunan dacin kalamanta dayake kokarin gane me take fada ya mata kallan tsantsar takaici ya daga hannunsa daya ya nuna mata hanyar wucewa yana kasa iya ce mata komai sbd bama zaiyi kowace magana da itaba dan tagama kaiwa karshen hauka.

SANAAH kuwa jin maganar Meenah din wani sarawa kanta yayi da karfi sbd ita kanta zuwa yanzu ta fara yadda babu lafiya kwata kwata a cikin kwakwalwan Mum din dan haka batama iya sake kallanta ba juyawa tayi zata bar gurin tabasu guri Mum din ta fizgota da dan karfin data dawo da karfi tana yin baya ya rigeta da hannunsa daya yana bude baki da kokarin hana kansa bayyanarda fushinsa gabaki daya dayake tasowa yace

"Are you just mad or stupid?
Me kikeyi?
Kina tinanin duka haukan da kikeyi ke kadaice mahaukaciya ko ke kadaice kika iya haukan?
Kada ki kuskura ki bari na bude bakina nayi magana akanki sbd zata zama maganar karshe ne ta har abada"

Hanya ya nuna mata da hannu yana barin sauran maganganun dayake son furta matan sbd SANAAH da safiya dake gurin bayason furta mata su.

Wani hucin baqin ciki mai tsananin gaske ta kuma fitarwa tana yiwa SANAAH kallan karshen tsana da baqin ciki tace

"Duka sbd wannan sauran wanin kakemun wannan Fleet??
Akan macen da saida qaninka ya gama lalatawa baso dayaba,
Akan macen da......

Wata muguwar tsawa mai karfin gaske data saka gidan amsawa Maamah dake kitchen dinsu tana aiki da kofar bayan a bude jin tsawar tayi da tsananin zafin dayake tafe a cikinta ta ajiye abinda ke hannunta ta fito da san sauri tana zagayawa ta hangosu ta iso da sauri daidai lokacin da ya saka hannu zai kai akan Meenah din koina jikinsa na wata irin rawa da fizgan gaske tayi saurin taresa tana kallan meenah din da sauri wadda ta kuma bude baki tana cewa

"Idonka ya rife kenan baka gane sauran wani bane lokacinda ka...

Kwace hannunsa yayi daga na Maamah ya sauke mata lafiyayyan marin data zunduma wani mahaukacin ihun da batasan ta zunduma ba sbd shigarta da yayi hancinta na ballewa da habo ta dago da karfi jikinta na wani irin rawa da jijjigar tashin hankali da baqin ciki taqi yin shiru zatai magana Maamah ta daka mata tsawa daidai isowan Dr Mum gurin tareda Mommy wadda tana ganin fleet a gurin ta dakata tana juyawa Maamah da ranta yayi mummunan baci itama da bacin rai tace

"Ashe bakida hankali da tinani Meenah?
Jahilci ne yake cinki ko me?
Menene kike fada?
Wace mummunan magana ce wannan?
Ashe kema ba mace bace da zakiwa mace yar uwarki hakan??

Idanuwa a rufe tana kasa riqe kanta tako ina da baqin cikinta da zafinta tace

"Dukanku kunsani cewa sbd fyaden da Samad yayi mata Dad ya aurawa Fleet ita da.....

Dr Mum ce ta katseta ta hanyar cewa

"Sai me to??
Mun sani kuma mun yadda mun karbeta a hakan sai me ya rage??

Da wani kallan tsana da takaicin karshen maqura take kallanta ta furta mata hakan wanda hakan ya saka Meenah kallan fleet da karfi tana cewa

"Kaji"

Kallan tsana da baqin ciki da takaici tareda wani azababben zafin dayake danne kirjinsa da rufe jinsa da ganinsa da sukai dif ya kalli meenah din kafin ya kalli Dr Mum da baqin cikinta tini ya saka idanuwanta jajir ya juya gurin SANAAH wadda tayi mutuwar tsaye ganinta na daukewa itama sai ya kasa kallanta ya jikinsa ya dauki wata sabuwar rawa mai karfin gaske kafafunsa na kasa riqesa ya dafa bangon kofar da sauri da hannuwansa dake rawa sosai kaman.

Mommy ma da zancen ya isa har inda take tajisa rufe idanuwanta tayi ahankali hawaye na ciko idanuwanta da wani radadi mai ciwo.

Zamewa SANAAH tayi a gurin zata zube jikinta na rawa itama da wasu hawaye masu zafi da suka gangaro mata ta kalli Fleet din wanda ganinsa ya dauke taji duniyarta ta tsaya cak kawai ta zame Dr Mum da Safiya da tini tafara hawaye itama sukai saurin riqeta Dr Mum na janta da zafi suka juya suka bar gurin.

Maamah ma cikin tsananin fushinta dabai taba fitowaba ta saka hannunta daya ta damqi Meenah zata jata subar gurin Fleet ya bude bakinsa daqyar ya furta

"Maamah a hada kayanta duk abinda takeyi gobe zata koma Morocco"

Maamah datakejin kaman ta rufeta da duka janta tayi da karfi ta tafi da ita har dakinta ta saketa tana bude baki zatai magana sai kuma ta fasa ta juya zuciyarta na tafasa.

Maamah na ficewa cikin baqin ciki hawaye suka gangaro mata ta daga wayarta bata tsaya komaiba ta nemo video din da samrah ta tura mata ta tura masa a wayarsa kai tsaye tareda shiga group din jeerahs family ta turasa batareda tinanin komaiba ta jefar da wayar tana jin gwara kowa ya shaqi bakin cikin da zaiyi ajalinsa.

SANAAH kuwa suna shiga palon dr mum kasa zama tayi ta wuce daki daqyar tanajin kafafunta sunyi nauyin gaske da kirjinta tana shiga rufe kofar tayi tana silalewa qasa ta zauna tanajin hawayenta na tsayawa cak.

Dr Mum ma zaunawa tayi tana kasa cewa komai tsabar takaici da baqin ciki.

Maamah ma haka ta zauna tanajin kaman zuciyarta zata fashe sedai Mommy ce tayi karfin halin shiga kitchen tana qarasa aikin zuciyarta da nauyi sosai itama.

Basu san abinda Meenah tayiba na sakin video din a cikin ahalin jeerahs sbd batasan kowaba anan Nigeria da zata yada masa video din kai tsaye ya tayata yadawa kanta gabaki daya ya toshe.

Hajiyar Samad ce datake zaune tana wayoyinta hankali kwance da dariya tana gamawa ta fara dube dubenta a waya tana isa kan dining zataci abincin rana itada Nabeela yar riqonta tana fara cin abincin idanuwanta suka sauka akan videon wanda ta bude kai tsaye take abincin bakinta yadawo mata da wani irin azababben karfin gaske yana biyowa harta hancinta yayi mata cikin kai shaqe a take tana neman mutuwa jikinta na jijjiga da karfin gaske.

A rikice nabeela ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login