Showing 195001 words to 198000 words out of 244256 words
da idanuwanta sukai jajir sun ciko da wasu zafafan hawaye masu tsananin radadin abinda yake faruwa takawa da gudu ta isa gaban Dad dinta daya fice hayyacinsa gabaki daya ya tashi daga fleet Raheem mahaifinta kwata kwata data sani ya koma kaman qaramin yaron dayake kallo mutanen dayake tsananin so a duniya zasu tafi su barsa akan idonsa tafiyar dazai rasasu har abada wani ihun kiransu yakeyi yana nuna tsananin karfi amma mutanen da suka riqesa sunfi su shida sun nuna nasu karfin sun kasa sakesa.
Tana isowa gabansa da wani irin karfi ta fada jikinsa ta qanqamesa tana fasa kuka mai tsananin karfi tana kara riqesa itama dan bazata iya ganinsa ya shiga wutarba ta fara kokarin kiran sunasa amma gabaki daya ya rasa hankali da tinani da ganinsa da jinsa.
Imran ne cikin tashin hankali da tsananin sauri ya bawa sauran soldiers din umarnin buga kofar a budeta sbd wutar bata riga tayi yawa a ciki ba daga wajenne tafi yawa.
Ankira firefighters tini dan haka Imran dinne ya fara jiqa jikinsa gabaki daya da ruwan dake harabar gidan cikin wata kyakkyawar roundabout dake tsiyayar ruwa tukuna ya ja baya sosai ya tafi da wani irin gudun gaske ya banki kofar da kafafunsa amma bata bude ba.
Sauran securities din gidan da duka sauran ahalin gidan maza da maaikata kowa tini ya fito suka ringa shiga ruwan suna jiqa kansu da tsananin sauri suna zuwa da gudun gaske su banki kofar wadda ta kulle ko motsawa batayi amma sbd yanda wannan nayi ya koma baya wannan yazo da gudu ya banka shima haka suka ringa yi hankali tashe da tsananin karfi ga wutar sai qara yawa takeyi imran yi yakeyi yana ihun kada a kuskura a saki Fleet da Dad wanda karfinsa shima baiyi qasa ba ko kadan bai dena tsananin haukan son kwacewaba.
Samad ma bai dena kokarin fadawa ba cikin tsananin haukar data juyar da kansa bayaji baya ganin komai hakama hajiyarsa ihu takeyi suna qin sakinsa tana neman zarewa sbd wutar ta qarasa zafafan gaske zafinta jinsa sukeyi sosai suna wani zufan daya saka suke kasa riqe samad din da kyau ihunta da haukacewan datake yi shi ya sake saka yanayin cikin mummunan rikicewa da tashin hankalin daya fiddo Umma hankali tashe ta iso jikinta na rawa taga yanda wutar ke ciki ta juya da sauri ta kalli inda Dad yake yana rasa kansa da manta shi waye gabaki daya wuyar yake son shiga sbd wadda take ciki data fi masa rayuwarsa.
Jin tayi kanta ya sara yana mata wani mugun nauyi har saida jiri ya dan debeta tana kasa dauke idanuwanta daga kansa muryansa harta fara toshewa sbd karfin yanda yake kiran sunan Dr fammah din wadda acan ciki dikkaninsu sun fito cikin tashin hankali daga dakunansu sbd hayaqi da wani irin zafin daya saka jikinsu wata mummunan zufa take fitarwa kaman ruwan sama sbd azabar zafin wutar.
A palo suka hade hankalin kowannensu a tashe suna kasa isa kowace kofa sbd wutar tariga ta shigo ta zagaye koina.
Dr Mum ce ta riqe SANAAH wadda Maamah ta kamo ta fito da ita jikinta na tsananin rawa hakama ko gani sosai basayi ga karfinsu dayake neman qarewa sbd tari da hayaqin dayake shiga huhunsu zamewa SANAAH tayi a gurin ta yanke jiki ta fadi sbd batada lafiya daman sai ita tafara fara somewa.
Mommy ma fara kasa jan numfashi tayi ta durqushe a gurin tana dafe kirjinta jikinta na kakkarwa
Kafin dukkaninsu su qara shiga mummunan tsoro da tashin hankali Maamah ma zubewa tayi a gurin Dr mum datai kokarin kama dukansu karfinta kasawa yayi itama ta zube gurin tana dafa kowannensu da girgizawa tana ambatar sunansu tafara tari sosai bata ganin komai sbd hayaqi da wani irin azababben zafi,
kofar da ake bugowa da tsananin karfi da tashin hankali ya fara sauka kunnenta ta dan daga idanuwanta ta kalli gurin duk da bata ganin komai ta motsa tanason isa gurin kofar duk da akwai wuta sosai amma ta kasa motsa koda hannunta tana kokarin somewan itama.
Jijjige kofar akai wadda saida akasha wuyar gaske maza sun jigata tukuna ta fadi wani zafin wuta ya bugo wajen a lokacin ne Imran ya sake zuwa da gudu ya jiqo jikinsa kafin ya iso tini Fleet yayi wani irin kakkarfan yunkurin daya fixge gabaki daya ya tafi da wani irin gudun gaske yafada ciki take imran ya zari zanin hajiyar Samad data jefar qasa ya jiqosa da wani tsalle ya fada ciki ya laftawa Fleet a jiki wanda harya isa inda suke baya gani wadda hannunsa ya fara sauka akai ya sunkuto gabaki daya yayo waje da ita sauran soldiers din nata zubowa kofar ruwa dan kashe musu hanyar da zasu fito.
Imran ma sunkuto wata yayi sauran securities dinsu biyu ma tini suka fado ciki kowa ya dauko suka fito ana zubo musu ruwa masu yawan gaske.
Dr Mum ce a hannun Imran wadda idanuwan Dad da sukai wani mummuman ja na sauka akanta aka sakasa ya kwace da karfi ya mata wata irin fizgowa daga jikin Imran din ta dawo jikinsa yana ambatar sunanta da da tsantsar tashin hankali koina na jikinsa jijjiga yakeyi ta bude idanuwanta ahankali dakyar ta kallesa jikinta na sakewa gabaki daya tana somewa.
Wata irin runguma yayi mata da daukanta gabaki daya ya juya yana barin gurin yana mantawa da komai da kansa ma,
Kafin yace komai tini Mr Sideeq ya juya da gudun gaske ya dauko key duk a rikice ya fita ya juyo da mota da saurin gaske tini suka fice villah din da mugun speed.
Fleet ma SANAAH ce a hannunsa da yana fitowa daman bai tsayaba dan ko gani bayayi sunanta yake kira da wani irin sauri yana jijjigata a jikinsa imran ma a haukace ya fito da mota da wata crazy reverse aka bude motar da sauri imran ya fita security dinsu daya ya fada yaja da gudun gaske suna bi bayan su Dad.
Imran Maamah da Mommy aka saka masa a wata motar tareda safiya data fada motar itama yaja suka fice da nasu gudun gasken.
A lokacin ne samad ya juya da gudu shima zai dauko key Meenah dake tsaye tayi mutuwan tsaye tana kallan abinda yake faruwa ta kasa motsawa idanuwanta a kafe kan Fleet din da bata taba saninsa ba jininta ya daskare tareda gangar jikinta bin Samad tayi da kallo a zuciyarta tana jin tafasa da tsantsar kunan abinda ya saka jinin jeerahs su uku suke tsananin son SANAAH tsakanin Dad,Fleet da Samad.
Hajiyar Samad din daga ita sai rigar baccin dake jikinta ba zani akai kafafunta na hadewa tabi bayan samad tana sake rikicewa da tashin hankali da ihun kiran sunansa yana shiga ta fada palonsa ta zare key ta fito da sauri ta dannawa kofar key ta baro gurin da gudunta tana jin kaman ta dora hannu akai tayita ihu sbd yanda baqin ciki yake neman kasheta a take da abinda danta ya tashi yi da yanda Dad jeerah yau ya kasa riqe Dad jeerah dinsa HAKEEM JEERAH dinsa na asali ya bayyana.
Fammah da duk ta fice hayyacinta itama tashi tayi daga qasan data fadi sbd watsin da Dad dinta yayi dasu ta nufi gurin Mum dinta dake tsaye daidai lokacin firefighters motocinsu suka iso suna shigowa harabar gidan ta kama hannunta dayake tsananin rawa tafara janta dukansu kafafunsu rawa sukeyi tabar gurin da ita zuwa bangarensu suna shiga ta rufe kofar mum ta xame a gurin qasa ta fasa wani masifaffen kukan daya saka fammah tsayawa cak daga inda take tana durqusawa batareda ta juyoba ta saka kanta a kafafunta ta fasa wani irin kukan itama.
Kuka sosai mai tsananin karfi da jijjiga jiki Mum din keyi tana jin wani irin azababben radadin da duk duniya babu abinda yakaisa zafi da radadi a kirjinta tana qanqame kirjinta da dafe kanta da kaman zai tarwatse.
Sun jima a wannan yanayin tana wannan kukan fammah na yin nata na tausayin iyayen nata duka biyu da damuwan rayuwan da suka samu kansu rana tsaka ta tarwatsewan zama duk da ta kasa kama kowane tinani akan iyayen nata harma da kananninta da SANAAH batasan me zata kama ba me zatai tinani akansa sbd dai auren andaura kuma maauratan sun karbi junansu hakama kakanninta sun aminta suna kuma son auren ga mahaifiyarta bata yadda da ko daya ba a cikin hakan to ita batada kowace tinanin kamawa bayan jin kaman rayuwan tana isarta.
#MAMUH
09033181070
[17/06, 1:53 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
123
Asibiti kuwa tin kafin su isa Imran ya dannawa Dr Akin waya ya sanar dashi Fleet suna hanya wanda tini suka fito harabar asibitin da nurses da masu daukan patients din da zaa iso dasu din suna jiransu a shiry cikin gaggawa.
Motar Dad tin daga nesa Mr Sideeq ya buga wani mahaukacin horn din daya saka maigadi wangale makeken gate din suna isowa haka suka wuce da gudu ciki suna parking ko bude kofar basuyiba motar fleet dayafi Mr Sideeq wani irin gudu tayi parking kai tsaye kaman baby Fleet ya fito da SANAAH dake jikinsa ya nufosu aka tarbesa tin bai isoba da stretcher ta asibiti aka dorata tareda yin ciki da ita lokacin aka tura dr mum itama saiga su Imran suma su Maamah akai ciki dasu gurin ya dauki tsit babu me iya magana ko zama babu wanda yayi a tsaye suke kaf dinsu jijiyan kai dana hannuwan Fleet sun wani irin fitowa manya manya dashi fuskansa da hannuwansa sunyi wani irin jajir.
Dad kuwa katuwar jacket mai tsayi da kauri Mr Sideeq ya kawo masa ya dora akan kayan baccin dake jikinsa masu kauri da hular sanyi sbd wani sanyi dayake ratsowa tsakiyar daren duk da suna wani lafiyayyan kebantattacen daki da aka kaisu.
Babu wanda ya fito daga dakin emergency din sai bayan dan lokaci dr Akin ne ma ya shigo da dr bushrat sai dr Nafeeu suka kalli su fleet din da Dad kafin Dr akin ya fara bayanin dukansu babu abinda ya samesu numfashinsu ma ya dawo daidai hakama babu konuwa ko daya a jikin kowannensu kawai dai zafi ne mai tsanani ya bugesu da hayaqi dan haka zuwa safe ko asuba ma zasu iya farfado insha Allah.
Imran ne yayi masa godia yana dan magana sbd fleet kwata kwata babu maganar da zata iya fitowa daga garesa yanxu kila sai zuwa goben hakama Dad shiga yayi ya dubasu tukuna ya fito aka koma gida dasu guraren asubar ma kenan sbd yana buqatan ganin likitan shima a duba bp dinsa daya riga ya sauka daga hanya saiya kwana biyu ana daidaita sa.
Fleet kuwa a asibitin sukai asuba saida gari ya fara haske saiga Maamah ta fara tashi tukuna Mommy sai Dr Mum daga baya dan haka ajiyan zuciya ya sauke a natse idanuwansa da fuskansa har lokacin jajir baiyi cewa komaiba daqyar sautin muryansa data toshe ya furta musu sannu da tambayar babu abinda sukeji suka tabbatar masa da basa jin komai.
SANAAH ce bata farka ba haka aka kwasosu a ambulance suka dawo gida inda kai tsaye bangarensa aka kai SANAAH su Mum kuwa bangarensu na farko da Meenah din take ciki aka kaisu tana dakinta bata fitoba batama san andawo dasu ba sbd fammah ta rufeta a ciki ta waje sbd kada ta sake wani abin.
Fammah ce ta isa dakin da Dr Mum take ta dubota wadda tayi weak sosai bata iya magana doguwa ta qaraso gurinta ta zauna ahankali tareda bude baki tai mata ya jiki.
Zuba mata idanuwanta Dr Mum din tayi cikeda wata irin tausayi da tsananin kauna sbd tana ganin damuwa da kunci bayyane kwance a cikin idanuwan Fammah din dan haka ta gyada kai ahankali tareda dan ware hannunta daya ta rungumeta tana sauke ajiyan zuciya.
Daga gurin Dr mum dayan dakin taje ta dubo Maamah da Mommy kafin ta fito ta koma dakinta ta zauna ahankali tana kasa fita zuwa dubo Dad dinta da SANAAH wadda kai tsaye tasan tana can bangarensa.
Dr kuwa likita biyu ne suka taho kansa aka dubasa sbd ba qaramin hawa da rikicewa bp dinsa yayi ba amma duk da hakan saida ya tafi har bangaren ya duba Dr Mum wadda yana shigowa har dakin dago idanuwanta tayi tana daga kwance bayan ta danyi wanka ta shirya taci abinci kadan da maganin itama jininta daya dan hau ta kallesa ahankali tana sauke masa idanuwanta da wani irin sanyin dataji na Allah bai dauki rantaba ayanxu batareda ta sake ganinsa ba sbd sunfi kwanaki yana fushi dasu basu haduba sai a asibitin shekaran jiya da cikin SANAAH ya zube sai kuma a daren jiyan da harta cire rai daga rayuwa.
Shi kansa wani numfashi mai sanyi da babu sauti ya sake yana bude baki kai tsaye ya mata ya jiki tana amsawa bai iya cewa komaiba ya juya ya fice su Maamah da mommy a palo fammah ta kirawo masa su suka fito ya musu ya jiki ya fice daga bangaren.
Yana isa bangarensa umma datake zaune tana jiransa dan yana fita tana shigowa kallansa tai da idanuwanta da sukai jajir tana sauke wani numfashi mai sanyi kafin ta bude baki tai masa ya jiki ya kalleta da idanuwansa da sukai jajir wani daci da nauyi yana toshe da maqoshinsa ya bude baki ya amsa yana kasa ce mata komai itama sbd wutar bacin rai da baqin cikin dayake cin jini da kirjinsa.
Ciki ya wuce bedroom dinsa kai tsaye ya daga wayarsa ya kira Mr Sideeq ya sanar dashi yaje da kansa babbar asibitin mahaukatan garin a taho masa da manyan likitocinsu da motar daukan mahaukatansu yana buqatan miqa musu Meenah a fara duba masa kwakwalwanta a tabbatar masa da idan tanada hauka ko babu sbd yasan hukuncin yankewa.
Mr Sideeq kuwa da daman yasan abinda zai faru kenan dan haka kai tsaye ya buga mota da kansa tareda securities biyu ya nufi asibitin.
Ummah ganin yanayinsa tasan babu sauki ko kadan a kone yake da tsantsar bacin rai da fushi mai tsananin dan haka ta lallaba tabar bangaren ta koma nata tana jin kaman zuciyarta zata zazzago qasa sbd baqin cikin datake diba na shekaru a wannan auren da bata ganewa komaiba.
Mr Sideeq na isa asibitin ga mamakinsa daya daga cikin motocin Fleet ya gani a bangaren tarban manyan baqi na asibitin wadda ya kalla da mamaki yana shiga ciki saiga Imran wanda shugaban asibitin gabaki daya da kansa ya fito ya tarbesa yana masa iso dan haka da tsantsar mamaki Mr Sideeq ya iso ya kalli imran wanda ya baice masa komaiba dole yabi bayansa tinda abu dayane ya kawo su shine buqatan babban likitan asibitin kwararre akan mahaukatan.
#MAMUH
09033181070
[17/06, 1:54 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
124
Tinda ya dawo da ita daga asibitin ya kwantar a tsakiyar gadon dakinsa ya rabata da kayan jikinta ya goge mata jikinta da towel sabo da ruwan dumi ya saka mata rigarsa mai kauri sosai tareda rufeta ya zuba mata ido yana mata wani kallan dayake tafiya da kowace bugawan da zuciyarsa keyi da tsantsar zafi da wuta.
Miqewa yayi ya fada bathroom din ya sakarwa kansa ruwan sanyin gaske idanuwansa a bude ruwan na shiga har cikin idanuwansa suna sauka kansa.
Har lokacin jajir idanuwansa da fuskansa suke hakama jijiyoyin jikinsa da kansa basu koma ba.
Yana fitowa kaya masu dan kauri ya saka a lokacin ne ta farka ta bude idanuwanta ahankali tareda wani kasalallen tarin daya sakasa jiyowa da wani irin kallo ya sauke mata idanuwansa data kalla ahankali tana sauke ajiyan zuciya ahankali batareda ta motsa ba.
Gabanta ya iso a cikin sanyi da rashin karfi ko kadan da shock din daya shiga da tsananin tsoron da bai taba shigaba a rayuwarsa ta fuskantar rashinsu dazaiyi akan idanuwansa ya zauna ahankali bakin gadon datake kwancen yana kasa dauke idanuwansa daga kanta ya saka hannuwansa biyu duka ya dagota ahankali bai tsaya komaiba ya sakata cikin jikinsa ya mata wata irin kyakkyawar rungumar data sakata rintse idanuwanta tana jin yanda hannuwansa dasuka zagayeta suna wata irin rawar data bayyanarda shock din daya shiga na matakin karshe.
Ahankali taji jikinta yayi sanyi zuciyarta datake cikin tsananin damuwa da qunci tana cikewa da tausayin kansu ta rufe idanuwanta hawaye masu sanyi suka gangaro daga cikin suka saike ajiyan mai sanyi da tsananin kasala a tare.
Tsawon mintina suka dauka ahakan yana rungume da ita a cikin jikinsa kafin ya saketa a natse ya sake zuba mata idanuwansa da tanajin tsananin zafin tension dinsu har a jikinta ya kama hannuwanta duka biyu a cikin nasa ya bude baki muryansa datai wata kauri da tsantsar shaqan dayayi yace
"How are you feeling now??
Kina jin any discomfort?
Yaya kike ji?
Akwai inda yake miki zafi??
Dagowa tayi ta kallesa da idanuwanta ahankali kafin ta dan girgiza kai tana bude baki ahankali tace
"No"
Dagata yayi gabaki daya ya nufi bathroom da ita yakaita har gaban ruwan zafi daya tara mata a bathtub ya tayata cire kayan jikinta ta shiga ahankali tana dan kamasa ta zauna ciki ahankali tareda sauke numfashi mai sanyi ahankali kafin tace yaje zata iya da kanta.
Fita yayi ya fitar mata da kayansa da zata saka harta gama ta fito ahankali daure da towel ya kamota jikinsa a natse yana tayata goge jikinta ya taimaka mata ta saka komai ya zaunar da ita a bakin gadon ya fice yaje palo ya dauko breakfast din safiya ta kawo ya dauko mata.
Yana shigowa dakin Zaunawa yayi a bakin gadon tareda ajiyewa ya dauki tea cup din mai dan zafi yakai bakinta yabata tasha ahankali tana kallansa da idanuwanta da suke sake shiga tsabanin damuwa.
Ms Meenah kuwa babu wanda ya nemeta dan kuwa babu wanda yakejin bai gama da itaba musamman dr mum da bata buqatan sakata a idanuwanta kwata kwata dan haka koda Fammah budeta ta fito da ita takai ta dining duka ba kowa tsit kakeji sbd da safe an dan shigo dubasu Mum din daga sauran bangarorin villah din.
Abinci ta hadawa mum din da kanta tareda bude baki tace
"Mum dan Allah ya isa haka,
Kiyi hakuri mu taru mu dauki kaddara wlh bazan iya rayuwa ina kallanku a cikin wannan halinba ke da Dad,
Ya dauki fushin da bamusan wane mataki zai iya dauka ba akan wannan babban tashin hankalin Mum rayuka hudu kika so dauka ki rabasu da duniya
Mum ni kaina wlh na kasa yadda da wannan abin"
Dagowa Mum din tayi ta