Showing 147001 words to 150000 words out of 244256 words
jin tafi jinta a cikin zuciya da kirjinta,
Hakama batasan tayaya zata kasar da babu wanda zata iya sakewa dashiba a cikin yare da al'adar da ba nata ba ga uwa uba shi wanda bazata iya sake hada idanuwanta da nasa ba sbd har yau basu taba sake ganin junaba bata kuma shiryawa sake hada fuskanta da nasa ba ko a kusa.
Dr Mum ta lura da yanayin nata daya sauya jikinta yayi wani irin sanyi da nuna batada raayin tafiyar dan haka tai kaman bata gane ba sam ko fahimta sbd tafiyar itace maslahar datake fata idan ba hakan ba Hakeem bazai taba dena daga musu hankalin raba aurenba dan haka tafi farin cikin Raheem din ya tafi da SANAAH din kafin dawowansu zata samu ta lallaba Hakeem din yabar maganar.
Dafa SANAAH din tayi da kulawa da kauna mara sirki tace
"Kada ki damar da kanki tinda kinsan baki gama warwareba hakama kada ki takura kanki idan kinje ki saki jikinki tinda ga Raheem nan you'll feel safe ga kuma fammah da itama zata kula dake sosai na sani,
Dad dinki yasan da tafiyar tini kin sani dan haka ba lallai ki samu ganinsa ba yanxu dare yayi hakama da asubanma ba ganinsa zakiyiba ki bari idan kun isa saiki kirasa nima da safe zan masa bayanin kinso ganinsa tinda yasan da tafiyar da wucewan naku"
Shiru SANAAH tayi tanajin jikinta na sake sanyi ta dan sauke numfashi mai sanyi tana gyada kai ahankali wanda ya saka Dr mum sake murmushi tana sake dan dafa hannuwanta da kulawa da jin dadi tace
"Thats my Baby"
Safiya da itama hakan ya mata dadi sosai tana kallan SANAAH da dariyarta da fatan ma kada ta dawo shikenan Dad din fammah ya tafi da ita miqewa tayi ta fice dan hado mata luggage din tafiyan.
Dr Mum cigaba da kwantarwa da SANAAH hankali tayi da wata irin kulawa da kaunar data saka SANAAH jin ta karbi tafiyan a zuciyarta da nutsuwa.
Dr Mum na barin dakin Maamah ta shigo tareda wasu LV suitcases guda biyu marasa girma sosai ta tura gefe tana qarasowa gurin SANAAH din Safiya na bayanta dauke da tray dayake dauke da wani maganin daban da Maamah din ta hadawa SANAAH datake hada mata kullum dan yanayin jikin nata.
Bata tayi tana cewa ta karba tin yanada dumi ta shanye.
Jiki a mace ta karba tana dan bata fuska ta fara sha ahankali maamah din da safiya na mata fira dan hanata shiga damuwan barin gida tin yanzu.
Sun dan jima sosai kafin safiya tai musu saida safe ta fice ta wuce dakinta.
Maamah ma shirin bacci tayi ta kwanta tabarta lafe a kujera tana son yin waya sosai amma ba daman hakan sbd Maamah ce ta karba wayanta wanda da alama kilan ya fada mata hukuncinsa ne.
Dad takeson kira sosai ta masa sallama amma ba daman hakan haka ta miqe ta shiga bathroom ta fito tayi shirin bacci ta kwanta jikinta duk yayi dumin da koyaushe kwana biyun haka yake dan dumi sbd yanayin maganin da ake bata sai ya zamana jikinta baya sanyi ko kadan koyaushe a dan dumi yake.
Da asuba Maamah ce ta tada ita tai wanka da ruwan zafi tana fitowa har Safiya ta dan hado mata light breakfast wanda chips ne da plain egg.
Sallah tafara yi kafin taci abincin kadan wanda Maamah ta sakata ci kafin ta bata magani a cup mai dumi ta sha kadan amma maamah ta sakata shanyewa.
Dr Mum ce ta fito itama ta iso dakin lokacin tini maamah ta gama sakata shiryawa...
Gaida dr mum tayi da sanyin jiki tana qarasa saka ipad dinta a handbag dinta dake gefenta ajiye.
Miqewa tayi ta nufi dakin Mommy wadda bata fitoba tana zaune tana lazimi.
Tana shiga gaidata tayi kai tsaye tana qarasa ta zauna kan sofa tana daukan wayar mommyn dake aje gurin ta nemo numbern Dad ta saka kira kai tsaye.
Bata shiga ba ta kuma sake saka kiran still bata shiga,
Shiru tayi kafin ta sake danna kira babu alaman ma wayar na kashe dan haka ta fara neman numbern Mr Sideeq daidai nan Maamah ta shigo tace tafito Raheem ya kira motocinsu are ready.
Faduwa gabanta yayi da wani irin karfin daya saka jikinta sanyi daga sunansa kadai da Maamah din ta ambata.
Mommy hannu ta miqa ta karbi wayarta tana qarasa adduarta ta kalleta tace
"Ki tashi mana kada ki barsu suna jira,
Allah ya tsare yakai lafiya a dawo lafiya"
Dago idanuwanta da suka sauya take tayi ta kalli Mommyn kafin ta miqe tsaye ta bude baki tace
"Amin" da qaramin sauti a taqaice tukuna ta juya ta nufi kofa ta fice.
Safiya ce ta ja suitcases nata ta fita dasu tin daga nesa security daya ya qaraso ya karbi kayan daga safiya sbd bazata samu daman qarasawa har gurin motocinba dan Fleet din yana ciki already dan haka daga nan ta tsaya cak Maamah ce ta qarasa har kusan gurin mota da ita tin kafin su qaraso aka budewa SANAAH din motar da Fleet yake ciki a zaune cikin wasu fitinannun brown Armanis marasa kauri sosai da suka maidasa kaman saurayi.
A natse ta shiga aka rufe kofar take aka ja motocin suka nufi babbar gate din ficewa wanda tin daga nesa aka wangale musu shi suka fara ficewa da wani irin speed.
Airport suka nufa kai tsaye sai a lokacin da suka hau titin dayake tsit ba mutane sosai sbd duhun asubar taja wani numfashi mara sauti ko kadan na zuciyarta data sauya bugawa tinda lokacinda ta sako kafarta motar zuwa zaunawanta qamshinsa daya gama kama cikin motar gabaki daya ya shigeta take kokuwa da riqe bugun zuciyarta dayake bugawan da ta sani ba nata bane...
Hadiye numfashin tayi tana sake riqe nutsuwa da kamun kanta da rashin hayaniyarta ta bude baki da wani irin sauti mai nutsuwa da sanyinta tace
"Ina kwana?"
Imran da shine yake driving din motar da kansa kuma shi kadai ne a tareda su sake taka motar yayi yana qara wani lafiyayyan speed,
Fleet kuwa da muryan tata ta ratsesa batareda tsammanin zata yi maganar ba sbd yanda ta gujewa duk wata hanyar haduwa dashi ko ganinsa a kwanakin kwata kwata wayarsa dake hannunsa ya dan dakata daga scrolling yana duba sako ya dago a natse tareda juyowa kadan ya sauke mata idanuwansa da suna saukar mata taji kaman an zuba mata ruwan sanyi ta dan qanqame hannunta a gefen rigarta tana hadiye wani numfashin daya sauka a idanuwansa ya qarasa sauke mata kallansa gabaki daya a cikin wani slow da nutsuwa.
Bude bakinsa yayi ba tsammani taji ya amsa a taqaice yana dauke idanuwansa daga kallanta sbd kowace fitar numfashinta da shaqarsa da idanuwansa basa tantancewa hakan yana tabbatarda yana samun matsala dan haka bai sake kallanta ba ya maida hankalinsa akan wayarsa ya bude baki yace
"How are you?
Yaya jikinki?
Wani irin nauyi da kunya ce mai tsanani suka rufeta data kasa iya amsawa da bakinta saidai ta dan gyada kai daqyar ta furta
"I'm ok,thank you"
A cikin muryan nata da bata fito ba sosai yaji kunyarta data basa mamakin gaske ya sake dakatawa yana dago idanuwansa ya kalleta take taji wata sabuwar kunyar me tsanani ta sake rufeta da batasan lokacinda ta daga hannunta daya ta rufe idanuwanta ba tana juyawa da fuskanta gefen windon tana jin kaman zata rasa kanta da irin nauyin datake ji.
Bai iya dauke idanuwansa daga kanta ba sbd mamakin kunyar datake ciki sosai,
Jin idanuwansa akanta kunya da nauyi na neman sakata shiga tsaka me wuyar sani da hawayen da suka ciko idanuwanta ta dan bude bakinta kadan da qaramin sauti tace
"Plss" batareda ta iya juyowa ba bare janye hannunta.
Bai dauke idanuwansa ba da suka kasa yadda da abinda suke gani sai dayaji kamewansa na barazana ya dauke idanuwansa yana dan furta "YA KADIR" da sautin da bai fito ba ko kadan.
Babu wani magana ko doguwan motsi data sake tashi a motar har suka isa airport wanda jirginsu ne zai tashi a lokacin na sauka a lagos sbd acan aka samu ticket na jirgin Morocco din dan haka dole can zasu tafi sai yau da rana jirgin Morocco din ya tashi.
#MAMUH
09033181070
[05/06, 1:07 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
88
Da securities dinsa da babu kowace sauki a lamarinsu indai gurin aikinsu ne aka bude masa mota ya fito tareda SANAAH din dake gefensa sanye da straight skirt daya lafe a jikinta da rigar da itama take kwance a jikinta bawai matsewaba brown itama sai babbar kimono abaya dake kan kayanta mai kyau da tsadan gaske sai mayafin rigar datai rolling da handbag dinta a hannunta ana biye dasu da kayansu a baya hannunta ya kama a natse sbd lura da bata son mutane sosai Duk da suna tafe ne securities a bayansu da gefensu.
Kai tsaye suna shigewa departure baa bata kowace time ba suka shige..
Koda gari ya waye sosai Mr Sideeq bai shigoba da wuri sai rana sosai dan hakanne babu wanda yasan Fleet ya bar qasar sai securities sai daya shigo securities suka sanar masa baiyi tinanin Dad bai saniba dan haka baiyi gaggawar sanar dashi ba ya shiga office dinsa na villa din dan gudanar da wasu mahimman aikin dake gabansa bayan ya isa ya gaida Dad kenan wanda har lokacin baisan meyake faruwaba.
Dr Mum kuwa tinda taga sun wuce baccinta ta koma sbd tasan Hakeem bazai saniba da wuri tinda bame samun ganinsa sai yamma yawanci ko dare.
Sai da suka hantse rana tafara fitowa sosai suka tashi tai wankanta ta fito ta xauna tai breakfast dasu Maamah suna firarsu hankali kwance anan ne Maamah ke fada mata dole fa anyiwa Dad laifi saita hakura ta tausasashi akan hakan idan ba hakan ba fushin da zai kuma dauka lamarin zaiyi muni.
Ita kanta Dr Mum din tasan da hakan dan haka daman dole zata je da kanta ta tabbatarda baiyi fushin da zai komai zai iya lalacewa ba.
A bangaren daya mommy itadai ta danne ta boye ne amma tana addua da fatan yanda sukaje lafiya su dawo lafiya batareda Ms Meenah ta gane komaiba sbd komai zai iya faruwa acan gwara idan sun dawo anan gaban kowa ta gane zaa iya samun daman bata hakuri da rarrashinta da fahimtar da ita hakama batason fammah taji babu dadi.
Safiya kuwa da fammah ke waya da SANAAH a wayarta haka tana ganin kiran fammah a wayarta ta kasa dauka har kiran ya yanke tana kallo da rasa sanin me zata fada mata sbd batason tafada cewan sun taso kila ba yanzu zasu isa ba taje ta lalata komai dan haka kiran na yankewa tai saurin kashe wayar tana dafa kirjinta tace
"Likita kiyi hakuri bansan ya zance miki ba"
Aikinta taci gaba da yi mommy ma tashigo suka ci gaba tare suna firarsu da sakewa yanda suka saba babu maganar nuna safiya din baiwarsu ce mai aikinsu sun riga sun sake mata.
****koda jirginsu ya sauka a lagos lokacin tashinsu zuwa Morocco daga ban Imran ya duba ya sanar da Fleet din akwai sauran 3 and half hour kafin tashin jirginsu dan haka a natse suka isa lafiyayyan lounge din airport din dake a tsare suka zauna securities dinsa na daga dan nesa kadan dan basu space aka kawo ruwan shan SANAAH din mara sanyi da tambayar abinda take buqata ta girgiza kai bata buqatan komai tana zaune kusa dashi har lokacin bai sake hannunta ba yana sarke a cikin nasa yana waya a natse cikin iko da kamewa da alamar wasu umarni ne na gurin aiki yake badawa masu girman gaske.
Ya jima yana wayar kafin ya kashe ya juyo ya kalleta a natse da idanuwansa da suka sake saka jikinta mutuwa da wata irin gajiyan zaman datake ji sbd tinda ta fito batada kuzari sbd damuwa da rashin sakewa ko kadan.
Yanayinta ya sake kalla tareda shigar da idanuwansa a cikin nata ta janye nata cikin nutsuwa tana dan juya kanta kallan wani gurin batareda tace komaiba.
Kai tsaye ya karanci yanayin gajiyanta da zaman da kuma rashin sakewanta da kuma yiyuwan ko zata buqaci bathroom,
Wayarsa ya daga ya saka kiran Imran wanda kalma daya ya fada masa take aka tanadar masa da Vvip suite lounge dake cikin airport din dake bangaren daban inda babu kowace hayaniya sai nutsuwa da kana isa gurin zaka tabbatarda na vvips dinne dan kuwa securities dinsa ma daban ne da ba kowane ake barin ma yabi hanyar ba dan haka koda aka tanadar masa kayansu acan aka baro su iya su kadai suka nufi lounge din yana riqe da hannunta suna tafe cikin nutsuwa da wata irin kamewa da steez dinsa da har zuba yake dan dukiya da hutu da power data gama kama jininsa koina ga wani irin kwarjininsa dayake cike idanuwan securities din da suke wucewa da manyan gurin da wasunsu suka rakosa dan isar dashi lounge din sai imaran da basa securities din biyu da suke tareda shi koina.
Koda suka isa imran ne ya rigasu isowa kofar vvip first suite lounge din da aka bude masa da wata irin girmamawa ya fara shiga da idanuwansa kai tsaye yayi scanning dakin wanda wata luxury ce take ihu a dakin dan kuwa gyaran dayake cikinsa ya tabbatarda Fleet admiral nasu zai iya zaman jiran time din da zasuyi a cikinsa.
Fitowa yayi yana bawa Fleet din daya iso daidai lokacin yana saka kai a natse da SANAAH wadda duk take a sanyaye daganan kowa ya dakata suna masa fatan hutawa lfy.
Gabaki daya barin gurin sikai su imran ne sika koma can farkon shigowa hanyar gurin suka zauna shi kuma yana tsaye yana waya da wasu manyan baqinsu dake buqatan ganawa da Raheem din wani sati na sama mai zuwa.
A natse ta taka ahankali tana takawa da wata irin sanyi ta nufi sofa zata zauna yana bayanta idanuwansa akan yanda take tafiya ahankali kaman batason yi babu abinda ya dawo kansa da idanuwansa irin tafiyarta a ranar data zama cikakkiyar macensa.....
Dauke idanuwansa yayi daga tafiyar tata datake jin idanuwansa akanta hakan ne ya saka kafafun nata kasa kuzarin tafiya daidai ta dakata cak tareda dan jan wani numfashi mara sauti tana kasa juyowa tana kuma kasa qara daga kafa....
Hannunsa daya kawai taji a cikinta ya ziro daga bayanta a natse ya dora ya mannota jikinsa ahankali da wata irin nutsuwa yana hade bayanta da kirjinsa suna haduwa da wata lafiyayyar sanyi....
Ajiyan zuciya mai sanyi da rashin sauti ya ajiye yana dora kansa a kafadarta ta wuyanta numfashin ajiyan zuciyar daya sake furzowa yana sauka akan gefen fuskanta ta lumshe idanuwanta ahankali tana jin xuciyarta na warwarewa ahankali daga rufewan datai mata mai karfi.
Qamshinta ya shaqa ahankali yana dan sake matseta jikin nasa ya bude baki yace
"Bakya buqatan tafiyar ne????
Direct maganar a kunnenta ta shiga tareda duminta dan haka bude idanuwanta tayi ahankali da slow ta girgiza kai tareda bude baki da qaramin sautin da baida kara tace
"No"
"Then meyasa nake ganin kaman bakyason zuwa?
Ta dan yi kafin ta bude baki tace
"Inason zuwa ne sbd ganin fammah.....
#MAMUH
09033181070
[05/06, 1:08 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
89
Wani lafiyayyan murmushi ne ya kubce masa mai wani irin kyau da sanyi dataji sa har a fatan jikinta ya juyo da ita ahankali ya kalli fuskanta da itama shi ta dago ta kalla a karan farkon da batai saurin dauke idanuwanta ba duk da tanajin kaman kowace digon ruwan jikinta suna narkewa
Wani murmushin daya kusan saka kafafunta kasa daukanta ya sake mata a fuska yana riqeta da kyau da kallan cikin idanuwanta data kasa riqe wutar kallan ta janye su daga kansa ba tsammani taji yakai bakinsa gefen kunnenta yace
"Meyasa zaki zabi kallan copy bayan ga original din a gaban.....
Wani mugun faduwan gaba tayi tareda dagowa da sauri ta kallesa idanuwansa ya saka cikin nata fuskansa da sauran murmushinsa da zai iya rabata da bugun zuciyarta ta bude baki batareda tasan ta furta
"Fammah nake so fa ba.....
"Ba Dad nata ba right?? I understand" ya fada yana katseta da zancen datake fada dik a rikice kaman zata fasa kuka sbd kunyar da tinda take bata taba jintaba.
Zare jikinta tayi da sauri tana qara taku daya zata nufi kujeran zama ya kama hannuntada tafin hannunsa ta dan qwace tana qin juyowa.
Rasa abinyi tayi sbd kunyar dake neman kasheta da wata irin damuwa sai kawai idanuwanta suka ciko da hawaye yana juyowa da ita suka gangaro ta bude baki tace
"Fammah nake....
Bai bari ta qarasa ba ya dora lips dinsa akan bakinta ya mata wani light kiss ya dan dago ya kalli qwayar idanuwanta yace
"Ait Naji and i get it,i understand"
Yanda yayi maganar ya sakata sake shiga tashin hankali ta sake tsiyayo wasu hawayen da suka sakasa daukanta ya isa kan italian leather sofa dake suite din ya zauna tareda dorata akan kafafunsa yana kallan idanuwanta da suka sake cikowa da hawaye ya zuba musu idanuwansa yana musu wani kallan da akan idonsa ta lumshe idanuwanta suka gangaro ahankali kan fuskanta yakai hannunsa daya suka diga akai ya kallesu kafin ya dago ya kalleta wasu yaga sun taru zasu sake saukowa kunya na neman kasheta da baqin ciki kafin su saukowa ya bude baki ya ambaci sunanta da wata muryan data saka hawayenta sauka da wani irin gudun da diga daya sukai yakai fuskansa cikin tata yaja qamshinta da numfashinta suka shiga har cikin kansa ya mata wata matsewan data dora tafin hannunta akan hannunsa dayake zagaye da ita batareda ta saniba tana sake qasa da kanta.
Sake jan numfashi nata da kamshinta yayi kansa ya karba ya bude idanuwansa da suka dan sauya take ya fara goga fuskansa a fatan wuyanta ahankali tareda bude bakinsa ya ambaci "Ya Kadir" da sautin da bataji komaiba.
Wata guga da yawa fatan wuyanta zuwa kirjinta da fuskansa ya sakata riqesa da dan karfi tana janye wuyanta zata sake miqewa daga jikinsa ya bude baki ya furta mata "No don't" a cikin tsakiyar kunnenta da wani slow daya sakata jan numfashinta da sauti tana kamosa sbd ficewan dayaso yi daga kirjin nata numfashin.
Hakan datai ya sakasa bude idanuwansa da kai tsaye sun sauya da sanyi ya dora bakinsa akan nata ya fiddo harshensa yayiwa lips dinta wata lasar data saka tsigar jikinta tashi gabaki daya Zuciyarta na sake bijire mata.
Sake lasar lips din nata yayi ya hadiye wasu yawu a maqoshinsa da sautin wucewansu ya saka tsigar jikinta sake tashi ya kama kanta yayi