Showing 198001 words to 201000 words out of 244256 words
kalli Fammah din da wani irin jajayen idanuwanta kafin ta bude baki tace
"Akwai wanda bai cancanci mutuwan wulaqanci bane a cikinsu?
Akwai wanda ba azzalumi ba maci amana a cikinsu?
Akwai wanda baici amanar rayuwataba har abada a cikinsu?
Rintse ido fammah tayi tace
"Ko me sukai Mum basu cancanci kisa ba a hannunki,
Kisan rai fa Mum?
Kashewa fa?
Mum pls"
Wani baqin ciki ne mai tsanani ya tasowa meenah din tai wani irin watsi da duka kayan gabanta dake table din tana dakawa famman tsawan gaske jikinta na rawa tace
"Idan nice na haifeki bazaki taba sake saka bakiba akan wannan maganar,
Idan nice nayi naqudanki ban yafe ki kuma saka bakinkiba ko shiga sbd bazan taba yafewa abinda akaimun ba sbd kabilanci da cin amana datake a jininsu,
Ita Dr mum data zabi aci amanata da ita ta manta cewan ba dadi tinda ita da akai mata tattarawa tayi ta bar auren
Abinda bazan taba yiwa kowaba a duniya shine barwa kowace macen Fleet,na zabi zama komaima amma wlh saita bar min mijina kota bar duniyar."
Miqewa tayi tabar gurin ta ficewa daga bangaren gabaki daya ta nufi bangarensa idanuwanta a rufe,
Fammah kasa motsawa tayi daga inda take zaune tinanin na toshewa gabaki daya akan Mum din tata.
Tana isa bangaren nasa daidai lokacin motocin asibitin mahaukatan na shigowa harabar gidan tareda doctors dinsu guda biyu da masu daurewa sbd tinanin haukar tuburan take.
tana bude kofar palon kai tsaye kitchen ta nufa ta dauko wuqa sabuwa dal mai kaifin gaske tana nufar dakinsa idanuwanta a rife hankalinta na sake gushewa gabaki daya.
Tana isa palonsa bata tsayaba bedroom dinsa ta isa ta bude kofar da kofar tana boye wuqar bayanta ta sako kai tareda tsayawa cak kafafunta na wata irin zufa da rawa sbd abinda idanuwanta suka ganar mata yana zaune da SANAAH din a cikin jikinsa ya mata wata nutsatsiyar runguma da shigarwa jikinsa sunyi shiru kowa da damuwa da tinanin dayake kirjinsa.
Dagowa yayi ya sauke idanuwansa akan kofar kallo daya yayi mata ya rintse idanuwansa ahankali yana kokarin riqe kansa daga makashin dayake jin zai iya zama
SANAAH kuwa zare jikinta tayi a cikin nasa da dan sauri ba karfi sosai a jikinta tana qasa da kanta da sauri jikinta na dan rawa.
Miqewa yayi tsaye idanuwansa jajir hannuwansa na fara wata rawar da fushinsa da zafinsa ke kokarin fin karfin control dinsa ya nufota tana ganin hakan tayi kan SANAAH da wuqar da tsananin gudu tana jin kanta na kamawa da wata wuta.
Bata isaba ya saka hannunsa daya yayiwa wuqar wata damqar data yankesa sosai jininsa ya zuba har a fuskan SANAAH din wadda ta zuba ihu da karfi.
Kama Meenah din yayi tareda juyota ya dauketa da wani mahaukacin marin da take hakoranta biyu na gefe suka futa a take,kunnuwanta suka dauke wuta sai wani jiniyar da suka dauka hakama idonta daya take jini ya kwanta masa taji kaman an daga Caterpillar an buga mata akai take ta kife a gurin idanuwanta basa ganin komai da rarrafe baya hayyacinta ta fito tana isowa waje ta saki ihu mai karfi ta zube a gurin.
Yarta ce kawai ta fito a rikice tayo kanta daidai lokacin Likitocin suka iso kanta zata tafi da ita dan dubawa fammah ta riqeta da karfi tana girgiza masu kai cinin tsananin tashin hankali.
SANAAH da jikinta ya dauki rawa sosai saukowa tayi gadonsa tana isowa gurinsa da tsananin tsoro da rikicewa sbd jinin dayake fita hannunsa sosai.
Fammah ce ta shigo cikin tashin hankali dan sanar dashi abinda yake faruwa a waje amma tana ganinsu ta tsaya cak tareda maida kallanta akan Hannun Dad din dayake zubarta jini sosai tayo kansa da tsananin sauri tana ambatar sunansa.
Itada SANAAH din suka dora hannunsu akan nasa suna hana jinin fita kafin fammah a rikice tace SANAAH ta dafe bara ta dauko first aid box.
SANAAH fitowa tayi dashi yana kallanta da ganin yanda ta rikice ya janye hannunsa yana miqewa zai fita ta riqosa da sauri tana zata bude baki ya katseta da wani yanayi mai tsananin bayyanarda wuta ce take cin jininsa yace
"I'm ok"
Sake binsa SANAAH tayi daidai fammah na dawowa da box din sbd har lokacin jini fita yakeyi ga hankalinta na rabuwa biyu da Mum dinta da aka tafi da ita wadda takejin zuwa yanzu kaman akwai abinda yake damun Mum din kodai shock din ya taba kwakwalwanta dan haka zata bisu asibitin tasamu sanin menene matsalar mahaifiyarta.
#MAMUH
09033181070
[18/06, 10:18 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
125
Da sauri fammah din ta kama hannun Dad din nata daya suka isa kujera SANAAH ta zaunar dashi tana miqawa fammah hannunsa mai zubar da jinin tana kallan fuskansa datake babu rahama ko daya zafi ne yake cikeda kirjinsa ta dan sauke numfashi ahankali mara sauti hankalinta itama dik baa kwanceba ta koma gefensa daya tana dora hannuwanta duka biyu akan hannunsa daya daya dan juyo ya kalleta da idanuwansa da suke jajir tai masa wani kallan da tashin hankalinta yake a bayyane ya hade yatsunsu guri daya yana maida kallansa akan fammah datake dressing din hannun nasa daya jikinta duk yana rawa da tsananin tashin hankali da wani irin quncin datake ji mai tsananin dayake neman buga kirjinta akan abinda ya sake faruwa din da Mum.
Hannun nasa mai yankar yai amfani dashi ya kama hannunta cikin nasa itama tareda dagowa da jajayen idanuwansa ya kalleta itama shi din ta dago ta kalla take wani iri kuka mai tsananin karfi ya taho mata koina jikinta na sake daukan rawa ta rintse idanuwanta tana kukan sosai.
Rungumeta yayi a cikin jikinsa da hannun daya yana kissing tsakiyar kanta ahankali batareda ya iya furta komaiba sbd zuciyar data gama cinyesa babu kalman dazata fito masa.
Sakinsa tayi tareda kama hannun ta gama dressing dinsa kafin ta dago idanuwanta da sukai jajir harma da kumbara ta kalli hannunsa daya dayake sarqe dana SANAAH wadda take kallan fammah din tin dazu jikinta a tsananin mace zuciyarta na cikin wani irin kunci da damuwa.
Dauke idanuwanta tayi ahankali daga hannuwan nasu wanda sai lokacin SANAAH ta lura da kallan ta zare hannunta da sauri a cikin nasa tana miqewa tsaye ahankali hawaye na cikowa idanuwanta.
Shi kuwa miqewa yayi ya nufi bedroom dinsa dan sauyo kayansa da duka suka lalace da jini.
Yana barin gurin Fammah ta miqe tsaye tana juyawa zata fice SANAAH data kasa hakuri da riqe kanta da wani irin sauri da tsananin damuwan datake jin kaman zata kasheta ta isa bayan fammah din ta bayanta ta rungumeta da karfi tana fasa kuka mai tsananin ratsa zuciya tana qanqameta da bude baki tana cewa
"Ki yafemun fammah bazan iya daukan fushinki ba da rabuwa dake dan Allah kiyi hkr,
I'm very sorry"
Rintse idanuwa fammah tayi tana jin wani nauyi da radadi a kirjinta wanda ita kanta tasan zata cutu matiqar gaske rabuwa da SANAAH din amma bazata iya kallantaba a yanzu bayan duka wannan abin dayake faruwa wanda tin farko da ko ita an sanarwa zata iya sanar da mum dinta cikin fahimta da sanin yanda zata fuskanci komai amma itama SANAAH ta zabi soyayya akan amintarsu da kusancinsu,
Ta tambayeta ta kuma tambayarta akan ta fada mata meke faruwa amma ta zabi boye mata sai yanzu da komai ya lalace aka kai gabar da auren iyayenta ma tasan bame rayuwa bane matacce ne dan kuwa a yanxu da Mum ta kusan kashe uwar data haifesa da uwar da bai hadata da kowa ba tayaya zai iya cigaba da zaman da ita.
Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata daga idanuwanta da har radadi sukeyi tanajin kukan SANAAH din wadda takeyi sosai kaman ranta zai fita saima yanzu ne ta samu yin kukan da tinda komai lalace batai irinsa ba dan kuwa jikinta har rawa yakeyi tana kukan mai tsananin karfi.
Itama famman kukan ne ta kasa riqewa tafara yinsa mai karfi tana qanqame jikinta da SANAAH ke rungume da ita har lokacin ta baya.
Sun jima ahakan kafin fammah ta zare jikinta ta fice daga palon tana isa bangarensu dakinta ta wuce ta fada ta rife tana zamewa kasa ta cusa kanta cikin kafafunta.
SANAAH dinma fitowa taso yi ta bita amma babu wasu kayan arziki a jikinta ta juya da sauri dan zuwa dakinsa ta samo abin rufa amma tana shiga ya gama shiryawa janyota kawai yayi ya zauna da ita tareda rungumeta yana hanata fita koina da taqaitacciyar maganar da sam bayason yi dan ko fita sosai muryansa bata yi.
Dr Mum da sukasan SANAAH na can bangaren hakan yafi musu kwanciyan hankali duk da sunsan an tafi da Meenah din wadda gabaki daya saida kowa yasan zaa tafi da ita sbd haukan data ringa zubawa tana kwacewa amma babu wanda yabi ta kanta aka tafi da ita ko fuskan kowa bata gani ba sai Hajiyar Samad wadda itama bata bayyana ba gabaki daya tana dai addua da fatan Allah yasa ana zuwa a banka mata allurar mahaukata ta qarasa haukacewa batareda ta dawo hayyacinta ba bare ta samu fadawa mijinta Samad yace SANAAH tasa ce kokuma ma yasan Samad ya taba saninta.
Ana tafiya da ita kuwa tin a mota suka daureta a gadon da zaa isa da ita tana wani irin ihun da fizge fizge daga karshe allura sukai mata wadda ta saka jikinta sakewa a take tana rufe idanuwanta ahankali daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba.
SANAAH komawa taso yi gurinsu Dr Mum amma sam bai bari ba duk rigimar dataso yi duk da batada karfin rigimar karshe dai anan su Dr Mum din sukazo suka dubata anan ne suka san abinda ya faru duk da bawai SANAAH din ta fada bane ganinsa da hannu a daure yasaka Maamah tambayan abinda ya samesa.
Jin hakan data faru din ya saka Maamah jin gwara zaman SANAAH din a gurinsa for now tinda a bangaren Meenah din suke yanzu.
Da daddare zazzabi ne ya taso mata jikinta yayi zafi sosai kuka da damuwan datake ciki dan haka magani ya bata bayan taci abinci tukuna sukai shirin bacci suka kwanta tana cikin jikinsa yana rungume da ita sukai bacci yana jin zafin jikinta na shigar jikinsa har kusan tsakar dare sosai tukuna zazzabin ya sauka dan haka ya dan qara musu Ac kadan suka samu bacci mai nutsuwa ya daukesu.
Washe gari da Safe da kansa ya nemi Fammah wadda ta tashi da shirin zuwa asibiti sbd jiyan ma taje amma bata samu ganin Mum dinba.
SANAAH na bacci bata tashi ba dan haka daga shi sai Fammah dinne a palonsa ya riqe hannunta cikin nasa yayi magana da ita sosai cikin kaunarta mai girma datake ransa da jininsa ya kuma fahimtar da ita abubuwa da dama akan lamarin tareda bata tabbacin yana yiwa SANAAH So daya kai tsaye da bazai taba iya rabuwa da itaba batareda boye mata ba sbd bayason kowace irin tinani shiga kanta koda daga bayane dazai hana zuciyarta da tinaninta sukuni.
Shiru tayi jikinta yayi sanyi sosai taji gabaki daya tana buqatan break daga kowa da komai zuwa gaba idan kanta da zuciyarta sunyi digesting komai dan haka kai tsaye ta shiga jikinsa ya rungumeta ta bude baki tace
"I need a break from all this Dad ina fatan zan samu wannan daman"
Numfashi mai sanyi ya sauke tareda sake rungumeta yana kissing tsakiyar kanta yace
"Imran will arrange everything"
Bude baki tayi cikin tsananin sanyin jiki da radadin dayake tsananin cinta tace
"Dad nasan akwai hukuncin daka tanadarwa Mum akan abinda tayi,
Dad kayi hakuri ka sassauta mata sbd ba haka take ba a baya,
Dad ina rokon mahaifiyata taci albarkacina idan har a hukuncinka akwai na kasa cigaba da zama da ita ka maidata kasarta acikin rashin hayaniyar da zata taba mutuncinku Dad,
Kayi hakuri dan Allah ka yafe mata Dad"
Shiru yayi batateda yace komaiba saima wani ja da idanuwansa sukai sbd irin kauna da son dayakewa yarsa yana jin radadin abinda takeji a tareda nasa radadin na abinda uwarta tai masa.
Baice komaiba shafa kanta kawai yayi ta miqe daga jikinsa ta fice sbd batason SANAAH ta fito ta tadda ita dan bata son ganinta a yanxu tukuna sedai zuwa gaba kila.
Tana ficewa kai tsaye gurin Dad jeerah ta nufa wanda shima tana shigowa kallo daya yayi mata yaji tausayinta da danne wani irin tsananin zafin mahaifiyarta dayake ji dan kuwa badan Fammah din ba kaf duniya baiga wanda zai sakasa ragawa Meenah ba wadda ya danne bacin ransa mai tsanani ya miqata a duba kwakwalwanta dan kuwa hukuncin doka yaso ta karba na rayukan dataso dauka amma sbd barin lamarin a cikin gida kada ya fita ya sakasa riqe kansa ya tsaya a hakan amma akwai hukunci daya da bazata wucesa ba shine barin masa gida matiqar lafiyarta kalau.
Numfashi ya sauke ya kalli famman ya bude baki yafara da mata bata hakuri tareda mata wata nasiha da sanar da ita daga SANAAH har Raheem babu me laifi sbd shine ya daura musu auren batareda yadda ko izininsu ba sama da shekaru ma kowa yaso a raba auren wanda shine asalin zuwan Dr qasar datai alkawarin bazata taba sake takowaba amma sbd Meenah da kwatar mata aurenta daga wata macen ta tako qasar amma Meenah bata duba itace ta haifar mata mijin ba kuma bata duba kaunar data nuna mata ba ta cinnawa matar wuta.
Shiru Fammah tayi idanuwanta jajir sbd kukan ma ya dena zuwa kwata kwata tana jin maganganunsa da suka sake sakata jin rayuwarta na duhu sosai duhun datake buqatan tafiya daga tsakiyar iyayenta da bazata iya kallansu suna sake zama abinda bazazu taba komawa kaman baya ba har abada.
Dago jajayen idanuwanta da suka bushe tayi ta sanar dashi tana son tafiya hutu koma ina ne kafin ta samu warwarewan kanta ta dawo daidai da kowa musamman SANAAH da ayanzu ko kallan juna bazasu iya ba.
Yayi naam da hakan shima kai tsaye sbd tabbas bazaiso ta ringa ganin abinda yake faruwan ba a tsakanin iyayenta da haukar da mahaifiyarta keyi da kuma hukuncin da zasu iya dauka akan hakan dan haka kai tsaye ya yanke shawarar turata Italy gurin AL'AMIN wanda ya zama dan qasar yanzu taje can zau kula da ita kafin komai ya lafa.
Numfashi ta sauke ahankali tana aminta da hakan tareda masa godia ahankali kafin ta rokarwa Mum dinta sassauci da kuma rokon alfarmar ya kira a bata daman ganin mahaifiyarta idan taje.
Bayani yai mata na cewan bazata taba ganin Meenah dinba sai zuwa jibi idan angama binciken lafiyarta an tabbatarda batada kowace matsalar kwakwalwa gida zaa dawo da ita da kansu dan haka tayi hakuri sbd itama zata samu nutsuwa idan ta tabbatarda matakin da lafiyar mahaifiyar taya yake.
Da wannan sukai sallama ta fito ta shige dakinta ta rufe kanta bata fito ba sai dare da Mommy taje da kanta ta sake bata hakuri da rarrashinta ta fito da ita ta kawo mata abinci da kanta ta bata taci kadan safiya ma tana tareda ita a lokacin suka dan zauna da ita har dare sosai tukuna suka barta ta kwanta.
#MAMUH
09033181070
127
Ita kanta SANAAH cak din data tsaya kasa motsawa tayi sbd Yaya Al'amin dinta duk da tana ganinsa koyaushe a waya suna vidcall a zahiri yayi mata sauyawan da kwakwalwanta ta kasa dauka dan haka ta sake bude baki da sautin daya isa kunnensa daga inda yake tsaye ta ambaci sunansa da tsantsar mamakinda jikinta yake sakewa.
Juyowa yayi gurin dayaji sautin muryan da shima mamakin ne a fuskansa idanuwansa suka sauka akansu su dukan take wani kyakkyawan murmushi ya sauka a fuskansa yana gaurayewa cikin nutsuwa da asalin farin ciki kafin ya tsayar da idanuwansa akanta wadda tini idanuwanta duka ciko da wasu hawaye ya tako zuwa gurinsu yana zare hannuwansa dake aljihunsa ya ware mata hannu ta tafi da gudu ta fada kaman wata baby yana rungumeta itama ta qaqamesa hawayenta na farin ciki na gangarowa tace
"Ya Al'amin" da wata sanyayyar muryan da Fleet yajita ta ratsesa ahankali ya dan dauke idanuwansa daga kansu yana maida akan Fammah wadda itama ahankali ta dauke nata idanuwanta da suke kan Al'amin din tin dazun tana dan kallan Dad dinta ahankali wanda ya dan sake matse hannunta dake cikin nasa yana sakar mata murmushi mai kyau da tsari wanda ya manta rabon daya fito daga fuskansa sbd tashin hankalin da aketa fama dashi a kwanakin.
Ita kanta ahankali ta dan sake murmushin karfin hali suna takowa suka isa gurinsu Al'amin din ya saketa ahankali yana maidata gefen jikinsa ya kalli Fleet da girmamawa sosai da sakewa tareda nutsuwa da wayewa da murmushi akan kyakkyawar fuskansa datake sak data SANAAH yace
"Bansan gabaki dayanku kuke ba,welcome to Italy Fleet"
Cikin basa sakewa da aikata abinda musulunci yace fleet din ya miqa masa hannu a tsanake yana kallansa yace
"Thank you Mr Al'amin"
Hannu Al'amin din ya miqa masa sukai sallama yana kara masa barka da zuwa qasar kafin ya kalli Imran ya miqa masa hannu shima suka gaisa a sake da tsantsar ilimi da nutsuwa.
Fammah ya kalla wadda ta dan sauke kanta daga kallansa tana dan sake dagowa suka kalli juna ya sake mata murmushi mai kyau da sakewa tareda kulawa sosai yace
"Rabin Ran SANAAH barka da zuwa ko?
Murmushin karfin hali tayi tareda dan kallan SANAAH din wadda itama ita ta zubawa ido tana kalla tukuna ta maida kallanta kan Al'amin din ta bude baki tace
"Thank you Yaya Al'amin"
Juyawa sukai gabaki dayansu zuwa mota Fleet ya kalli SANAAH wadda take ta shiga farin ciki sosai tana mantawa da duka damuwa da quncinta tanata faraa da murmushin haduwa da dan uwanta kuma ubanta Al'amin.
Wani sanyi shima yaji ya ratsesa na ganin sauyawanta zuwa farin ciki sosai dan haka dan murmushin da bai fitoba ya sake yana miqa hannunsa ya kama nata ahankali suna tafiyar ta juyo ta kallesa da idanuwanta dake cikeda farin ciki ta sakar masa wata murmushi me kyau tana bude baki kadan tace
"Fammah na kusa fa"
Famman ya kalla wadda take gefen Al'amin ana isowa gurin motocin kai tsaye ta Al'amin din ta nufa wadda kuwa ya bude mata gaban motar da kansa ta shiga ya rife yana juyowa yaga SANAAH ta dan tsaya tana dan kallan motar sbd fammah data shiga idan ta shiga ciki zasu iya komawa yanayinsu dan haka ta dan sake murmushin karfin hali tana basarwa daman Fleet bai sake hannunta ba har lokacin dan haka ta juya suka shiga tasa motar da zata daukesa wadda tini Imran ya bude musu