Showing 102001 words to 105000 words out of 244256 words
fidda tsananin kamarta da mahaifin nata tana kallan dawo da kallanta akan SANAAH wadda ta dago ta kalleta Murmushinta na qaruwa take SANAAH ta dauke kallanta daga kanta tana cigaba da dan cin abincin sama sama kafin tasha ruwa tace she's full ta miqe tabar dining din.
Da daddare bata iya zuwa gurin Dad ba sedai ta kirasa a waya lokacin ma yana tareda Dad din ta gaidasa ta sanar basa batajin dadi amma da sauki sukai sallama da kulawa.
Dad na gama wayar ya dago ya kalli Fleet wadda bazaka taba sanin akan dad ko aa tinaninsa da hankalinsa yake sbd yanda yake karanta sako a wayarsa a natse da kamewa da wata irin girma da kwarjini.
Numfashi Dad din ya sauke a karo na uku bayan wainda yayi kafin kiran SANAAH ya shigo masa na zancen da RAHEEM yaxo masa dashi.
Bude baki yayi a tsanake sbd dagaske kenan Dr fammah zata iya zuwa Nigeria bayan shekarun baqin ciki da girmama tsanar dataiwa qasar da wainda suke cikinta.
"Babu kowane dalilin zuwanta kaman yanda na santa da dagewa da rashin hakura ga dik abinda ta kudurta bayan akan maganar aurenka da SANAAH ne,
Zata taho ne bazata tafi ba saita tabbatarda babu auren,
Bazata taba hutawaba da zubar da makaman yaqinta ba sai ta raba auren dani mahaifinka na daura maka sbd a koyaushe duk baqin cikin da zata sakamun shine yake sassauta nata baqin cikin na shekaru shiyasa ban taba damuwaba ko jin dacin yanda ta nema maka auren farin sbd na bata daman yin duk abinda zai sassauta baqin cikinta,
A yanxu kuwa tana damara ne da yaqin da batasan kanta zata yaqa da kanta ba sbd matar da zata dauro damarar yaqin fixgewa daga rayuwar 'danta dayake raye itace matar 'danta da baya raye.
Dagowa FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH yayi da wani irin nutsuwa da slow ya sauke idanuwansa da suka saka Dad din da kansa daukewa ganinsu ya saukewa Dad din batareda yace komaiba.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee
61
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.
*******
Numfashin manya Dad jeerah ya sake saukewa kafin ya yanke nasa hukuncin dayake tareda umarni yace
"Bazaa nema mata masauki a koina ba matiqar a qasar nan kuma nan garin zata sauka,
A cikin matana ne akwai wadda babu aure a tsakanina da ita amma sbd mutuncina da nata mutuncin dana zuriata ban bari tabar JEERAHsV ba tana ciki a zaune karkashin kulawata da ikona,
Hakanne itama a gareta matiqar ina raye da kuma iko bazata taba iya zama ba a inda ba cikin JEERAHsV ba sbd anan ne mutuncinta yake da girmanta da kuma ikonta yake,
Koda babu aure a tsakaninmu ta sani mu ahalin juna ne da duk abinda yake tsakaninmu bazamu taba goge hakan ba dan haka duk gyaran da zaayi mata kasa ayi mata anan cikin JEERAHsV
Akwai bangaren dayake tsakiyar na Zainab da Hajiya khadija a sauya mata tsarinsa zuwa tsarin da zai mata dadin zama a gyara mata ta zauna zan zauna na jira abinda duk ya kawota taxo dashi"
Fleet da baisan mexai iya cewaba sbd hayaniyar iyayensa zata sake tashi kenan duk da sun manyanta amma haka lamarin nasu yake motsawa dan haka baya wani shiga sbd rayuwarsa daban take da tasu,
A tasa rayuwar babu hayaniya da tashin hankali sai miskilanci da tafiyar da komai a tsarinsa na baturen ruwa da bai hada komai da peace dinsa ba,
Sabanin su dasuka kasa hakura da juna indai akan duk abinda zai taso ne kowa zai iya kokarinsa gurin nunawa dan uwansa ikonsa akan dansu da sam basu wani damu da farin cikinsa ba ko amincinsa shiyasa a bangaren ahalinsa a gurin 'yarsa kawai yake samun cikakkiyar sukuni da kaunar da batada kowace irin sirki ko manufa dan ko matarsa tanada manufofinta akan soyayyar datake masa dan kuwa matsayin datake dashi na matar Fleet admiral RAHEEM JEERAH of the Us navy bata hada matsayin da komaiba tana tsananin alfahari da bugun gaba da hakan tareda dagawa da jin bazata taba iya rasa matsayinba ko yadda wata ta amsa irin sunan da sunan RAHEEM JEERAH.
Baro gurin Dad din yayi yana zuwa bedroom dinsa wanka yayi ya fito daure da towel a qugunsa da tabawa daya zaa masa ya warware ya fadi sbd yanda yake daurasa shiyasa kusan matarsa ta riga ta gama mutuwa da shaawansa data zamar mata jarabawa sbd akwai abubuwan dake tattare dashi da matiqar ta gansu bata iya riqe shaawanta akansa dan hakanne ne kusan yawan muaamalansu neman datake masa yafi wanda yake mata dan ko cikin kwayar idanuwansa ya sauke mata take tsigar jikinta take tashi taji tana tsananin buqatan jinta a jikinsa musamman idan ya fito wanka kallo daya takewa murdadden jikinsa da koina kusan jijiyoyin karfi ne a bayyane nan ma bata iya hana kanta tsananin kwadaituwa da mijinta.
Shiryawa yayi cikin kayan bacci dogon wando kawai da wani mayen qamshinsa dayake tashi a jikinsa ya kwanta.
Yana kwantawa Ms Meenah ta shigo dakin sanye da kayan bacci itama masu tsayi har qasa da ciki data sama silk blue kala.
Isowa tayi ta zauna dayan gefen gadon sbd ta riga daman ta gamo komai na shirim baccinta ta haye gadon gabaki daya tana qarasa rage hasken dakin ta matsa cikin jikinsa ta shige masa ahankali.
Washe gari SANAAH da lafiyarta ta tashi dan haka tana yin wanka kafin kowa ya tashi tabar bangaren tayi gurin mommy.
Tana zuwa dakin Mommyn ta shige ta kwanta tana gaida mommyn dake zaune tana waya da Al'amin.
Tana gama wayar da kulawa ta kalleta tana mata ya jiki idanuwanta akanta.
"Naji sauki" ta furta tana janyo mata wani zancen suka fara kafin suka koma maganar yaya Al'amin dayake ta samun cigaba acan ahankali ahankali arziki da damammakin cigaban rayuwa suna samuwa.
Anan ta wuni harma dasu Mum din dukansu anata fira da abubuwansu hankali kwance.
Acan bangaren Fleet kuwa Imran ya sanarwa Dr Mum zata taho a cikin JEERAHsV zata zauna kuma.
Imran dayake shima Dr Mum din ta kirasa ta sanar masa yayi musu shirin tahowa Nigeria din dan haka take ya shiga aikin duka biyu na nema musu komai na tahowa da kuma na aikin bangaren da zaayi wanda kusan zubar dashi akai zaa mata sabon ginin da zaiyi daidai da duk abinda takeso.
Sauran mutanen villah din sunga anata sabon aiki a bangaren wanda yakeda girma shima kuma aikin imran ne a tsaye a akai da qwararrin maaikan daya dauko amma babu wanda yasan aikin na menene dan haka Mum ta fara murnan ko ita akewa bangaren dan tanason ace tanada nata bangaren wanda take ciki sedai ta ringa zuwa bangaren mijinta kwana sbd tana matsayin matar Fleet RAHEEM JEERAH guda da zai iya siye Villa din da yan canjin da ba komai bane a gurinsa ba amma ace batada bangarenta mai zaman kansa dan haka koma ba ita akewa ba to ana gamawa itama zata buqaci gaskia a ware mata nata bangaren su baro na Raheem ya zama tirakarsa ce shi kadai.
Hajiyar Samad dataga ana bangaren abinda yazo ranta shine SANAAH zata tare kenan maganar auren bayyana zatai dan haka ta ringa jin wani irin dadi da farin cikin jiran ganin tashin hankalin da zaayi sbd babu abinda take jira yanzu kaman Ms Meenah ta gane auren ta tsani SANAAH da uwarta wanda ita hakan ne zai bata daman shiri da Meenah din sbd tana neman wanda zasu hada kai su hana SANAAH da uwarta da sukai sanadin mutuwan auren zaman lafiya da kwanciyan hankali.
SANAAH da mommy kuwa tashin hankali da tsoro suka shiga mai girma na ganin aikin da akeyi din wanda zai iya yiyuwa tarewanta zaai magana dan haka suka shiga tinani mai zurfa da yar shakka.
Rage zama sosai bangaren SANAAH tayi sbd zuciyarta da a yanxu batada sukuni sam a bangaren zaman dole takeyi musamman indai zaa hau dining ta ringa jin rashin nutsuwa kenan duk da babu wanda ya taba gane abinda take ciki dan kuwa ko a dining a tsanake take komai.
Tana gaidasa batareda ta iya kallansaba ko bawa situation din mahimmanci ba sbd yanda Mum ke kokarin cusa sabo a tsakaninsu da kaunar dake ganin ya kamata t shiga tsakaninsu sbd ita da SANAAH dinma takeson su tafi idan har zasu koma duk da batajin shaawan komawa koina a yanzu itama zata zauna Nigeria tukuna gaskia.
A duk lokacinda SANAAH ta bude bakinta ta fidda sautin muryanta ta gaidasa a dining sai ya dago idanuwansa a natse ya kalleta dasu taji kaifin su a jikinta tukuna yake amsawa a taqaicen da muryansa ke qara mata kaifi bayan wanda idanuwansa suka sakar mata dan hakane bata iya sake cewa komai a table harta gama tabar gurin sbd tana bude baki a gurin zata iya rasa kalamanta.
******aikin bangaren da akeyi qanda dukiya ce Fleet din ya bada dama ake zubawa kaman baasan zafintaba,
Cikin kwanaki kalilan aka gama komai aka zuba furnitures din da kudi sukai kukan gaske gurin siya aka tsara komai irin tsarin da Dr Mum zatai rayuwan jin dadi da walwala da kwanciyan hankali tareda nutsuwa itada Maamah.
Masu aiki aka tanada guda biyu aka zuba a bangaren kafin ma su iso dan haka tafiyar itama ta kammala komai ya zama ready batareda ya sanarwa Mum din inda zata zaunaba hakama imran bai sanar mata kawai dai an sanar mata komai is ready.
A ranar da jirginsu zai taso tai waya da Ms Meenah amma bata sanar da ita tana zuwa ba dan haka har lokacin kaf bayan Fleet da yaransa sai Dad babu wanda yasan wacece a tafe.
Dad jeerah sabbin gyare gyare da sauya abubuwa da dama na villah din ya saka a sake duk babu abinda ya lalece dan koyaushe cikin kashewa villah din kudi ake dan hakane take kaman ka shiga turai akoda yaushe.
Ana gama komai aka zuba komai Hajiyar Samad farin cikinta ya tsananta ta kashe kunne tana jiran dirar masifa da balain da zai tarwatsa jeerahs.
Mum ma kawai fara shirin tarewa sabon bangare tayi batareda jiran a ce mata komaiba.
SANAAH ma da Mommy ranar da aka gama komai fara jiran abinda zai biyo baya sukai cikin fargaba amma babu wanda yaga alaman kowace damuwa ko nuna ma sunsan da aikin a gurinsu.
Ranar Friday da tsakar dare gap da asuba jirgin da Dr Mum da maamah suke ciki ya sauka a qasar Nigeria
Qasar da bata taba tinanin har abada zata sake zuwanta ba,
Qasar data tsana fiyeda komai da kowa,
Qasar data rabata da farin cikinta da walwalanta har abada,
Qasar da aka rife mata 'danta daya dahar ta bar duniya bazata dena radadi da quncin rashinsaba wato Nasir dinta,
Dan da shine yafi kusanci da shaquwa da ita fiyeda dan data haifa da cikinta.
Numfashi mai zafi da rashin sauti ta sauke tareda miqewa daga zaunen datake suna fitowa jirgin itada Maamah wadda itama ta sauke wani zazzafan numfashin samun kanta a cikin qasarta ta haihuwa,
Qasar da aka rufe 'danta da iyayenta,
Qasar da batada kowa a cikinta a yanxu bayansu SANAAH da bazata taba tafiya batareda ta nemesu ba.
##MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee
62
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.
*******
Motocin securities din Fleet ne suka iso Airport tin cikin dare dan tarbonsu hadda Imran wanda shi daga baya ya iso da motar da zai dauki su Dr Mum din da kansa.
Koda jirgin ya sauka Imran fitowa mota yayi da kansa ya isa arrivals ya tarbesu da kansa,
Bullowan Dr Mum sanye da jallabiya da handbag dinta a hannunta idanuwanta sun sauya sosai sbd abinda takejinsa a kirjinta na sauka qasar da dukkanin radadinta yake dawowa farko.
Maamah ma sanye take da black jallabiyar da jakarta a hannu ta sauya sosai kaman asalin baqar balarabiyar itama sbd hutu da lafiyar dasuke ratse a jikinta da kuma kwanciyan hankali.
Da girmamawa mai girma da kulawa Imran ya iso gabansu yana bude baki yace
"Barka da Sauka"
Maamah ce ta kallesa tana bayyanarda sakewa da kulawa ta amsa da cewa
"Mun sameku lafiya?"
Murmushi yayi yana amsawa tareda sake gaida Dr Mum wadda ta bude baki ta amasa tana kallansa daci gaba da tafiya a natse.
Suna doso inda motocin suke duka securities din suka qame da kyau suna dan sauke kallansu daga kansu suka musu barka da sauka da tsantsar girmamawa ga iyayen Ubangidan nasu.
Kofofin Motar aka bude musu a lokaci daya a tare na baya Maamah ta shiga ta gefen da Imran ya bude mata Dr Mum kuwa zagayawa tayi dan kofar da dayan security ya bude mata ta shiga aka rufe.
Shiga motar imran yayi tareda tayarwa tini securities suma motarsu dake gaba ta tashi dan haka suka bar Airport din kai tsaye.
Hanya Maamah ke kalla a natse sbd gari ya fara wayewa yayi haske,
Duk yanda maamah tasan gari da hanyoyi komai ya sauya mata sbd shekarun ba kadan ba rabonsu da nan din dan haka ansamu sauye sauye masu girma da yawan da komai ya zamar mata baqo batama gane koina.
A bangaren Dr Mum kuwa bata iya kallan koina ba hankalinta na kan wayarta data fiddo jaka tana dubawa amma ba network ma akai sbd ba layin qasar bane dole yanzu a nema mata layin qasar nan kafin ta tashi tafiya.
Batajin doki ko farin ciki ko walwalan komai na kasancewanta a qasar Nigeria din daidai wannan lokacin,
Bacin rai da daci ne kawai take ji a cike da kirjinta da idanuwanta na zuwanta dama dalilin daya saka zuwan nata dan kuwa idan batazo dinba batasan iya girman da matsalolin rayuwar gidan RAHEEM zasu kai ba tinda yana auren sakaryar macen da batada tinani sai son taqama da nuna isa da dagawa da haukar sonsa kawai ba lissafin yanda zata riqesa wa kanta ita kadai taxo tanata barar da kai a tsakanin kishiya da matan uban miji da uban mijin kansa da ba kaunarta yakeba.
Hanyar xuwa JEERAHsV aka kama daga Maamah har ita Dr Mum din babu wanda ya gane hanyar dan hakane ma basu wani damu ba hankalinsu na kan juna suna maganarsu.
Security checking point na farkon shiga anguwan ne da suka iso da tarin soldiers ke gurin aka bude musu suka wuce ana qame musu ya saka hankalin Maamah dan karkata da inda zuka iso din dan haka suna dosar main gate na shiga JEERAHsV dake rubuce a gefe da manyan baqin rubutu mai kyau da akai kalan Black and Gold ya saka Maamah jin gabanta ya buga da dan karfi ta juyo ahankali ta kalli Dr Mum wadda sam bata dagoba hankalinta na kan jakarta datake duba wani abu a ciki.
Wangale musu gate din akai tin kafin su qaraso dan haka suna qarasowa kawai shigewa sukai a daidai wannan lokacin ne Dr Mum ta dago tana kallan harabar inda suke wadda takeda girman daya wuce ace gidanta ne ita kadai sbd girman yayi yawa hakama tsarin da komai da idanuwanta ke gani kaman tsarin gine ginen villas din turai ne dan haka ta kalli Imran a lokacinda ya wuce kurya sosai har zuwa inda bakin hanyar bangaren da zata zauna yake ta bude baki cikin shiga nazari tace
"Imran ina ne nan din?
Parking yayi tareda jin nauyin abinda