Showing 54001 words to 57000 words out of 244256 words

Chapter 19 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

446

tsiyayo masa ya kalli Sir jeerah din da nasa idanuwan suke jajir akansa take yaji yana neman hadiye zuciya ya mutu sbd tashin hankali dan haka daqyar ya iya bude baki yace

"Eh nasansa da kuma kanwar tasa"

Shiru ya dan yi yana rasa ta yanda zai basa amsar tambayar ta biyu wanda take daidai da iya rasa ransa ya bude baki da wani nauyin bakin dake rawa zufansa na sake gudu yace

"Tsautsayi da kaddara ne suka shigo lamarin kuma babu abinda yakai ga faruwa a tsakaninmu"

Da wani karfin halin dayake neman faso kirjinsa ya qarasa zancen yana kasa dagowa ya kalli mahaifinsa.

Sir jeerah daya gama nutsar da zuciyarsa akan rashin hayaniyar da lamarin kai tsaye ya danne fushi da bacin ransa da bayyanarsa ba kyau yace

"Kanada raayin aurenta a matsayin matar da kakeso zaka daraja???

Shiru ya dan yi kansa a qasa cikeda shakkar hukuncin dazai hau kansa amma kuma can qasar zuciyarsa haryanzu bayajinta a matsayin matar dazai iya aura ga kuma wani tsananin sonta dayake cinsa dan haka ya dan dago kadan batareda ya iya kallan sir jeerah dinba ya girgiza kai a natse.

Kafesa da ido Sir jeerah yayi na tsawon mintina kafin ya bude baki ya sake maimaita tambayarsa da kyau yace

"Zaka aureta a matsayin matar da zaka so ka daraja na aura maka ita da kaina????
Ka nutsu ka fahimci tambayar danake maka,
Zaka aureta????

Dagowa yayi yana jin tsoronsa da tashin hankalinsa na raguwa ya girgiza kai tareda bude baki yace

"Aa bazan iya aurenta ba"

Numfashi me sanyi a natse sir jeerah din ya sauke tareda juyawa ya kalli Mr S dake gafensa yace a tafi dashi bai zabi sassaucin ba.

Hakan daya fada kuwa shine hukuncin daya hau kan Samad wanda yana fitowa tini aka wuce dashi aka rufe inda babu duk duniya wanda zai sani idan ba sir din da mr s ba sai babban sojansu.

Rufesa akai cikin mummunan azabar da a cikin qanqanin lokaci ya sauya kamanni hakama babu wanda ya sani ko mahaifiyarsa bata saniba sbd ko a waya bata samunsa tin tana kokarin danne damuwanta har ta shiga tashin hankali sbd kwanaki sai tafiya sukeyi ba labarinsa hakama Dad din yaqi cewa komai.


****Mr S da kansa yaje har gurin aikin Yaya Al'amin ya daukosa ya kawosa gurin sir jeerah wanda ya kallesa da kulawa ya tabbatar masa da a yanzu SANAAH zataci gaba da zuwa makaranta shi zai dauki nauyin cigaban karatunta har gamawa kuma shine zai bada aurenta insha Allah idan har hakan ta kama.

Godia Al'amin yayi tareda samun cikakkiyar kwanciyan hankali daga nan kuwa SANAAH ta koma karatunta hankali kwance duk da har lokacin yan anguwa na mata kallan wata iri.

Kusan wata daya harda kwanaki a cikin kwanciyan hankalin da suka dan samu da komawar SANAAH karatu wanda yayi daidai da lokacin da Samad jeerah yayi a rufe cikin mummunan yanayin daya sakasa jinya a asibiti sosai kafin ya dawo hayyacinsa da wata irin sabuwat maitar soyayyarta dayake jin a yanzu kam kozai rasa ransa zai aureta amma bazai iya taba rayuwa batareda mallakarta ba.

Yau ta dawo da yamma sosai a adaidaita aka ajiyeta kofar gidansu tana fitowa wata black BMW na parking bayanta wadda ta saka gabanta mummunan faduwan daya sakata jin kafafunta na nauyi sbd idanuwanta Samad jeerah ne suke ganar mata ya sauya sosai sbd bai gama dawowa yanda yake ba daga fitowansa.

Bata sake juyawa ba ta nufi kofar gida kai tsaye zata shige a rikice har kafafunta na wata irin rawa tsoro mai tsananin gaske da firgici duk suna shigarta lokaci daya.

Kokarin saka kanta cikin gida takeyi da sauri daidai lokacin Samad ya iso gurinta da sauri idanuwansa a rufe da tsananin kewar ganinta da sonta me zafin gaske.

Yana shan gabanta daga cikin gidan cikin wata irin saa yaya Al'amin na fitowa.

Shi kansa yaya Al'amin din yana ganin Samad wani jiri ne ya kusa dibansa sbd sarawan da kansa yayi dan haka da sauri ya dafa bango yana kallansa da kyau da idanuwansa sukai jajir a take zuciyarsa na daukan wata tafasa me karfi.

SANAAH na ganin hakan itama da sauri tayi gurin yaya Al'amin Samad ya miqa hannu zai riqota ba tsammanin su duka wani mummunan naushin kakkarfan namiji ya sauka akan fuskan Samad din da take jini ya balle hancinsa ya dago da karfi a zafafe kafin yayi komai Yaya Al'amin din ya sake sakar masa mugun naushi yana turosa waje jikinsa na rawa da fizgan bacin rai da baqin ciki yace ta wuce ciki yayi waje kan Samad din yana sake yin cikinsa da wani mugun duka kaman mara hankali dan kuwa komai dawo masa sabo yayi.

Mutanen dake gurin tasowa sukai ganin tashin hankalin dake faruwa sbd wani irin naushi tako ina Al'amin ke sakarwa Samad wanda yake shirye da mutuwa akan bazai taba rabuwa da SANAAH ba.

Cika gurin ya fara yi kan kace me gurin ya rikice wasu dake cikeda baqin cikin abinda ya faru tin wancan lokacin suka taya Al'amin dukan Samad din a gurin kokarin rabawa.

Kamar abinda ake jira take aka ringa daukan videon da babu bata lokaci aka sakesa a media.

Motar hukumace ta iso gurin a rikice sbd fadan ya zama babba kokarin kashe samad din akeyi koda suka iso yayi mummunan jigata a hannun Al'amin wanda shima a gurin yan sandan suka rufesa da mummunan duka tareda jefasa mota anata ihu da jifansu sika tafi dashi.

Tashin hankali da kuka SANAAH takeyi mommy kuwa batama iya fitowa ba sbd ciwon kirjin daya rufeta.

Koda suka isa station da Al'amin Samad JEERAHsV aka wuce dashi da gaggawa sbd kada akaisa asibiti yan media su isa can dan labari dai kam ya fita yafara yaduwa kaman wutan daji wanda koina ya dauka da gaggawa musamman daman ana neman abin fada a familyn jeerahs.

Mr S ne ya bada umarnin a toshe hanyoyin yaduwan labarin zuwa sama sosai dan kuwa yanda ma aka fidda labarin ba haka yake ba yayi muni sosai.

Hankalin familyn yayi mummunan tashin da bai taba ba a lokaci daya musamman hajiyar Samad din tana cikin mugun shock da tashin hankali dan ta kasa yadda ace danta wai ake yada an kamasa yayiwa yar mutane fyade.

Babban tashin hankalinta dayafi kowanne shine hukuncin da mahaifinsa zai dauka sbd a karan farko an kawo batanci da dalilin da wani zai nunawa ahalinsa dana iyaye da kanninsa yatsa.

Rikici sosai aka shiga gashi Al'amin yana rufe har lokacin yana shan azaba a hannun yan sanda.

Shiru sir jeerah yayi sai da aka kwana biyu tukuna ya aika neman Al'amin wanda anan suka san da yana rufe take mr S da kansa yaje har station ya karbo sa bai wuce koina dashi ba sai asibiti aka dubasa ya maidasa gida ya huta sai washe gari tinda safe ya sake zuwa ya daukesa yakaisa JEERAHsV.

A lokacinda Al'amin ya tsaya a gabansa cikin mummunan yanayin daya saka sir jeerah jin zuciyarsa ta sake daukan zafi akan abinda Samad yayi a lokacin ne Mr S ya miqa masa bayanan komai akan cikakken bayanan binciken asalin su waye Al'amin din ya karba ya bude yafara bin bayanan a natse har qarshe kafin ya dago cikin nutsuwa mai karfi ya tsayar da idanuwansa akan Al'amin sai a yanxu yake ganin kamannin NASIR dake kwance akan fuskan Al'amin.
#MAMUH
#BEST LOVE
#JEERAHS
#SANAAH KHALIL
#FLEET ADMIRAL JEERAH
#MEENAH WAHAB
#FAMMAH JEERAH
#ARRANGE MARRIAGE
#POWER
#SAMAD JEERAH
#LOVE/ROMANCE

GANIN IDO
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

34
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki  Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki  Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce  For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Al'amin da fuskansa ta sauya kamanni kansa na qasa bai dagoba sbd a yanzu kam ya gama yanke shawarar barin gari kwata kwata da ahalinsa zuwa wata duniyar inda zasuyi rayuwa cikin nutsuwa sbd zan iya zama makashi matiqar yana garin da Samad zai iya cigaba da zuwa gurin SANAAH.

Dad jeerah jin kansa yayi yai nauyi sosai sbd ganin ahalin Nasir a gabansa cikin hali na tsananin baqin ciki da ukubar zalinci,
Ahalin da Nasir ke tsananin so fiyeda kansa,
Shin Ahalin Nasir basuda haqqi ma akansu kuwa?

Idanuwansa sauya sukai shima da wani irin sabo kuma zazzafan bacin rai da fushin daya gaurayesa gabaki daya dan haka yaji laifin Samad ba nasa ne shi kadaiba dukansu masu laifin ne mai girman gaske.

Sunkuyar da kansa yayi a hankali yana ajiye abin dayake hannunsa na bayanan a gefensa yana hadiye numfashi mai zafi da rashin sauti.

Wasu zafafan hawaye ne masu radadi sosai suka gangaro daga idanuwan yaya Al'amin wanda sai yanzu yake tabbatarda bazai iya da power dinsu ba dan haka dole sune zasu quntatu ta hanyar shiga duniya.

Dago idanuwansa yayi hawayen nasa da suka gangaro cikeda baqin cikin da neman isar ubangiji suka sauka akan idanuwan Dad jeerah wanda take hankalinsa yayi mummunan sake tashi sbd hawayen Al'amin hawaye ne na wanda aka cuta kuma Allah bazai taba barinsu ba akan hakan ga haqqin Nasir ma da suka watsar da iyalinsa.

Al'amin ne ya bude baki a sanyaye muryansa bayyane da radadi da qunci mai tsanani yace

"Zan dauki ahalina mubar gari insha Allah"

Sake kallansa da nutsuwa da jin wani irin nauyin da babu me samun hakan daga garesa kaf sai ayau din akan ahalin Nasir dan haka yaji koma a wane yanayine bazai taba barin wannan cutatarwan da akai musu ta tafi a banza ba kuma duk inda zasu matiqar suna duniyar Samad bazai taba dena bibiyan SANAAH ba sbd ya gama bincikawa a yanzu ya tabbatarda Samad ya rasa kansa ne akan sonta ba so bane obsession ne kuma abu daya ne a yanzu shine hannunsa kawai zai dawo dasu a qarqashin kulawansa cikin gidansa tukuna Samad yayi shakkar bibiyan SANAAH din amma kuma yasan babu dalilinsa na hakan batareda hujjar zaman nasu ba a qarqashinsa na har abada.

Dagowa yayi ya sake kallan Al'amin a natse wanda rayuwarsa take a mace murus a cikin bayaninsu daya gama karancewa tsaf,
Baida ilimi baida aiki baida kwanciyan hankali ko nutsuwa duk ya qare samartakarsa a wahala da rashin nutsuwan nauyin dayake kansa.

Numfashi ya sauke kai tsaye yana cigaba da Al'amin din batareda batawa kai a kowace zancen daya saba yi a kai tsaye ba kaf rayuwarsa ya bude baki hankali kwance da nutsuwa yace

"Al'amin hukunci daya na yanke dan bawa SANAAH kariyar da daga yanxu zata rayu a cikin aminci har ranar da zata samu miji na aurar da ita da kaina da hannuna na zama uba kuma waliyin aurenta tareda alfaharin da kowane uba zaiyi idan har zaka bani su sudawo hannuna"

Da slow Al'amin ya dago jajayen idanuwansa ya kalli Dad jeerah din yana jin hawayensa na tsayawa sbd tsananin mamaki dama rashin gane inda zancen ya dosa.

Tayaya zai bada SANAAH da mommy su dawo karkashin kulawan wani bayan yana raye to shi menene amfanin rayuwarsa daga lokacin,
Me zaiyi idan baiyi kula dasu ba?

Sunkuyar da kai yayi shima kai tsaye zai bada amsar rashin Amincewa hakan Dad ya katsesa a nace da dattako da cewa

"Al'amin a yanda kakeson ka kula ka kare dik wani haqqin mahaifiyarka da qanwarka to kana buqatan fara samarwa da kanka cikakken ilimin da zai baka damar hakan wanda zai baka dama ta sanin yanda zaka fuskanci kowace irin rai dazata cutatar da kai a ilimimance koda kuwa hukuma ce,
Nasan waye mahaifinka hakama bayan Mahaifinka Nasir baida mahaifi bayan ni dan haka ka bani su a matsayin ahalin Nasir idan bazaka bani su a matsayin naka wannan shine babban adalci da tsaron da SANAAH zata samu daga duk wani namijin wanda ma ba Samad ba ni kuma ina sake maka alkwarin bata kariyar da duk duniya babu me bata ko bayan aurenta,
Zan turaka ka nema ilimin da duk lokacinda ka kammala kazo zan baka su da hannuna idan har hakan ta kama"

Shiru Al'amin yayi yana tsayar da hankalinsa da tinaninsa akan maganganun na tsoho Dad jeerah wanda kai tsaye maganganunsa suke babu kwana kwana ba bata lokaci kowace magana direct take da jiran amsarta.

Numfashi Dad din ya sauke tareda kallansa yace

"Kada ka damu da komai Al'amin kaje gida kayi tinani me kyau da shawaran da duk abinda ka yanke zan maka hakan"

Mr S ne ya kalli Al'amin din yana nuna masa hanya suka juya suka fice yana zurfafa a tinanin maganganun da duk sunma rikita tinaninsa da hankalinsa.

Har Mr S ya ajiyesa bai fito daga tinani mai tsayin daya shigaba,

Yana shiga gida dakinsa ya shige ya rufe yana tinani mai tsananin zurfi da damuwa,
Har dare baida kuzari yana daki dai magrib ya fito yayo sallah yazo ya zauna cikinsu sukaci abinci suna dan magana sama sama sbd SANAAH da a yanzu take cikin tsananin tsoron rayuwarta kwata kwata sbd Samad.

Ko Mommy a yanxu cikin tsoro da damuwan da babu ranar fita take sai taga anyiwa SANAAH aure gashi mijin ya gagara babu wanda ya taba zuwa ma yace yana sonta kuma bazasu taho dinba sbd suna shakkar Samad jeerah da a yanzu ya fito duniya yayi ikirarin hallaka dik wanda ko kallanta yayi da sunan so.

Da daddare bayan sun rufe gida kowa ya kwanta kusan karfe ukun dare Al'amin yaji ana taba kofar gidan nasu sbd dakinsa ne a kusa.

Shiru yayi yana sake saurara yaji dakyau.,

Magana yaji anayi qasa qasa da motsin daya sakasa tashi zaune daga kwancen dayake ya kasa bacci.

Kaman zai fito sai kuma ya fasa sbd jin andena motsin kwata kwata dan haka ya koma ya kwanta yana rufe idanuwansa ko baccin zai daukesa a lokacin.

Babu jimawa kuwa ya samu bacci ya dan daukesa mai nauyi....

Cikin bacci yaji hayaniya sama sama tana shiga kunnuwansa hartai karfi tareda wani irin azababben zafin dayaji numfashinsa na toshewa da sauri ya bude idanuwansa yaga gabaki daya dakin ya gauraye da wani irin hayaqi mai karfi anata ihun "Wuta Wuta" daga waje.

Miqewa yayi da wani irin rawar jiki da tashin hankali yana nufar kofa ko gani bayayi ya isa setin kofar dakin data dauki mugun zafi tafara kannewa alamar bazata budeba.

Buga kofar yafara yi da karfin gaske yana shiga mummunan tashin hankali da tsoron halinda su mommy suke,

Karfinsa yake tsanantawa yana bugun kofar da gasken gaske ga hannunwansa sun fara konewa sbd zafin da kofar ta dauka na gaske tinda ta karfe ce.

Daga wajen aka fara bugo kofar da karfi suna ambatar sunansa Mommy ne da SANAAH suka dauko tabarya suna dukan kofar dakin ga wutar sai qara karfi take kokarin yi dan harta fada dakin mommy.

Su duka cikin matsanancin tashin hankali suke gashi sunje kofar gidan su bude sbd a shigo a basu taimako amma sun kasa bude gidan sbd an saka musu padlock ta wajen gidan wanda mutane keta kokarin son bugewa a shigo a taimakesu amma kwadon kaman na kofar duniya yaqi budewa.

Mommy ce tafara gazawa ta zube qasa tana dafe kirjinta dan haka SANAAH ta sake shiga rudu itama tanajin karfinta yayi qasa gashi bata saba da wahala ba sam irin haka dan haka tayi kan mommyn tana wani irin jan numfashinta da zafi ya fara yankewa.

Haukacewa Al'amin yaji yana yi a cikin dakin ya fara buga kofar yana ihun gaske yana kiran sunayensu jin shiru...

Koda ya samu nasarar balle kofar dakin duk tafin hannuwansa sun kone sosai amma bai damuba haka yayi kansa yana wata rawar jiki ya sunkuci mommy da duka karfinsa ita kuma SANAAH ya damko hannunta ya nufi kofar ficewa duk da gurin wuta naci.

Daga can waje karfi da gaggawa aka kara gurin balle kwadon amma yaqi dan haka aka fara kokarin bude bangon gurin dan cire kofar gaba daya sbd wuta dai karfin gaske take qarasawa.

Koda aka bude kofar Dukkaninsu su ukun sun sume a maqale guri daya da junansu Al'amin din ya qanqamesu ya gama saddaqar da rayuwarsu daga nan taxo karshen da duka wahala ta qare.

Cikin gaggawa aka fiddo dasu take akai asibiti dasu hankali tashe daga nan yan anguwa suka fara kokarin kashe wutar kafin motar masu kashe wutar taxo.
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee

35
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login