Showing 114001 words to 117000 words out of 244256 words
Dr Mum ta fito daga bathroom din a shiryenta tsaf da doguwan riga baqa daman tayi wankanta alwala ta koma tayo dan bata son zama ba alwala a jikinta.
Da wata irin sakewa da kauna mai tsananin karfin gaske ta kalli SANAAH tareda bude hannuwanta tana cewa
"Y'allah habebty"
Tasowa SANAAH tayi ahankali ba rashin wayewa ta shiga jikin Dr Mum din tana cewa
"Ina kwana Mum"
Amsawa da farin ciki dr mum din tayi kaman ba itace mai fada da bacin rai ba jiyan itama ta tashi ranta fes batada sauran kowace damuwa bayan ganin SANAAH ta samu right dinta a hannu.
Shi kansa RAHEEM din albarkacin ganin SANAAH ya samu da sakewa da kulawa ta gaisa dashi tana tambayar Meenah da Fammah.
Amsawa yayi da tsanaki kafin ya kalleta lokacin datake zama tareda SANAAH a gefenta tana riqe da hannunta yace
"Maganar gurin zamanki danai miki alkwari ya kammala zaku iya shiryawa zuwa anjima kadan a kaiku"
Kallansa ta juyo tayi babu alamar nauyin komai ko tina komai hankali kwance tace
"Wane gidan kenan??
Kallanta ya dago yayi yana karantar yanayinta na dagaske take tambayar yace
"Gidan da zaki bar nan ki koma"
"Kabarshi kawai na hakura zan zauna anan din"
Kallanta ya kuma dagowa yayi ta kame fuska .
Baice komaiba jin abinda ta fada kawai yayi mata sallama ya fice yabar dakin.
Yana fita ta sake fuska tana kallan SANAAH da kulawa tafara kokarin mata tambayoyi akan karatunta da zaman Gidan.
Anan taji inda SANAAH din take zaune tayi shiru tana juya lamarin a ranta wanda kusan su dukan zasusha wuyar hakan dan gwara Meenah batasan da kishiya take zaune ba ita kuwa data san meenah matar mijinta ce zatafi shan wuyan abubuwan da idonta zai gani ba daman nuna damuwa hakama bazata taba samun daman kebewa da mijinbama.
Fitowa sukai tare tana sake magana da SANAAH din wadda take cikeda jin nauyinta.
Har lokacin Maamah waya takeyi dan haka kai tsaye dining suka nufa inda abincin da suka kawo.
Maamah na gamawa acan ta samesu dan haka acan suka gaisa suna zaunawa su duka hadda SANAAH din da Dr Mum tace ta zauna taci a cikinsu.
Suna cin abincin suna magana da SANAAH din da nuna kulawa wata kauna mai karfin gaske har suka gama.
Suna baro dining din Ms Meenah na shigowa gaida su itama tana ganin SANAAH ta fara nuna kulawa da mata fadan ta dena fita batareda ta tsaya taci breakfast dinta ba.
Da mamaki dr mum ta kalli Meenah din kafin ta amsa gaisuwan datake mata da kulawa alaman ta sauko daga bacin ranta dan haka farin ciki ya cike meenah ta zauna tana gaida Maamah da fara zuba tana nuna ita yanxu ta zama yar gari da nuna iko iko akan SANAAH a matsayin uwa.
Maamah tausayinta taji ya ciketa sosai dan haka ta ringa nuna mata kulawa da kauna sbd a yanzu kam sedai kowa yayi hakuri Dr Mum bazata iya hada kaunar SANAAH da kowaba duk da bazata taba qin Meenah ba sbd itama tatace.
Ita kanta Dr Mum din tausayin Meenah taji tana ji sosai sedai ba yanda zasu iya wata kusan tafi wata hakama soyayya da tsantsar kaunar datake wa Nasir kai tsaye daga jiya xuwa yau ta koma akan SANAAH.
Anan bangaren suka wuni gabaki dayansu sunata walwalwansu hadda mommy nan ta taho suka wuni suna shaaninsu.
Sai dare kowannensu ya watse kai tsaye Dr Mum tace abar SANAAH anan tayi zamanta tukuna.
SANAAH da daman hanya take nema take ta amince da lallaba fammah da dadin baki da shagwaba har famman ta amimce tana tsokanarta da cewa indai dr mum ce kwana biyu zata sha fadanta da saikayi kwana biyu kana zazzabi.
Wani nutsuwa da farin ciki SANAAH taji na baro bangaren dan haka ta sakewanta anan gurin su Dr Mum.
Washe gari itace ta rigasu fitowa ta isa kitchen ta saka hannu a shirin breakfast dinsu tana gama jerawa suna fitowa kusan a tare.
Sunci sun gama kenan saiga Ms Meenah tazo.
Tana gaidasu ta zauna ta kalli Maamah tace
"Maamah dan Allah kiwa fleet magana ko zai amince a bani bangare na daban sbd ko SANAAH ta kasa sakewa sosai a bangaren sbd muna guri daya da Dad din nasu inason inda zamu sake sosai"
Dr Mum dake duba sako a waya dakatawa tayi ta juyo tana kallan Meenah din cikeda mamaki dan kuwa ita kadaice haka a cikin mata tana ganin.
Maamah ma kallanta tayi dakyau kafin tace
"Kina tareda mijinki zaki nema raba guri Meenah?
Kinfi son ki ringa yawon zuwa kullum gurinsa kenan?
Gyada kai tayi tana dan nuna kwantar da kai tace
"Maamah sbd yaran kinga sun zama yan mata muna guri daya dasu gwara a bamu gurimu din zaifimin na ringa zuwan"
Kara bata shawaran tabar maganar maamah tayi tana lurar da ita illar hakan sbd zai iya zamana sun iya fara samun rashin kusanci anan din,
Sam Meenah kasa iya hakura tayi ta nacewa rokon Maamah din ta masa magana sbd itace kadai zata saka ya mata yanda takeso din tinda tayi magana bai amince ba.
Sake magana Maamah tayi amma ina bataji bata gani ita hakan kawai takeso sbd ta samu nata cikakkiyar haqqin tanada nata bangaren bawai na miji ba.
Rasa abin fada Maamah tayi ita kuwa dr mum tinda dai Meenah din ta buqata hakan anata kamota tana zillewa a zance dan haka hakan yayi mata daidai sbd zai kasance bangarensa kowa sai shi kadai sai kuma macen data samesa kenan a tsakanin ita da SANAAH Maamah zata sake tausarta tabar maganar Dr Mum ta katseta da cewa
"Abar maganar zaa mata yanda takeso tinda ita ta buqata"
Maida kallanta tayi akan meenah wadda taji dadin maganarta tace
"Ki shirya ki hada kayanki koda babu bangaren baki ki dawo nan anbar miki mu saimu koma bangaren Zainab hakan ma yafi"
Meenah na jin hakan wani sanyi ya mamaye kirjinta tace
"Ngd Dr Mum, Allah ya saka da khairan ya qara lafiya da nisan kwana"
Murmushi mai kyau Dr Mum din tayi tana saka mata albarka tareda dan kallan hanyat kitchen da SANAAH take can tareda masu aiki suna magana.
Maamah kuwa Meenah ta kuma kalla tana fatar hakan ya zama abinda bazataiwa dana saniba.
Dr Mum kuwa sake jin kwanciyan hankali da farin ciki tayi sbd hakan da meenah tayi yayi mata daidai a cikin saukin da batareda tayi abinda zata saka meenah din jin kunci ba ita da kanta ta buqata.
Tsabar zumudi da farin ciki washe gari ta gama hada kayanta hankali kwance shima baice mata komaiba akan hakan sbd Maamah tayi masa maganar dan haka ya amince.
Dad ma daya samu labarin tashin nata murmushi kawai yayi yana cewa ai shikenan tinda ita ta buqata.
Su Dr Mum basuda wasu kaya bayan suitcases dinsu dan haka take aka gyara musu dakuna fes a bangaren mommy aka kai musu kayansu suka komawansu daman sunfi ma son hakan hakama itama mommyn tayi farin ciki sosai zuwansu.
Sabon parking Ms Meenah tayi a sabon bangaren wanda taji hankalinta ya kwanta ta samu abinda take so dan haka take cikin farin ciki sosai.
Fammah da SANAAH da murna ta koma ciki na ganin ta sake dai zama gurinta dukda da sauki tinda Fleet din baya bangaren.
Da daddare ta gama shirinta bayan kwankanta ta saka kayan baccinta riga da wando bar qasa ta dora hijabinta har qasa shima akai ta fito taje kitchen ta dauko tray na tea din Dad zata fice Dr Mum dake zaune palo dayake a bangaren mum take masa tea dinsa.
"Ina zuwa ne SANAAH"
"Dad zan kaiwa tea dinsa" ta fada tana dan dakatawa cikin nutsuwa wani sanyayyan qamshinta mai sanyi yana tashi.
Maamah ma kallanta tayi cikeda yabawa yanda take girmama Dad jeerah din.
Ms Meenah dake zaune a bangaren har lokacin saka bakinta tayi da cewa kin dafa harda Fleet ko sai shima akai masa tinda yanasha sosai."
Kallanta Maamah tayi zatai magana Dr mum tace
"Idan yanaso to takai masa wannan tinda ita ta shirya,
Ke fammah kije ki dafawa kakanki saiki kai masa idan kun dawo duka saiku wuce gabaki dayanku"
Tana gama fadar hakan ta kalli SANAAH tace
"Wuce ki kai masa"
#MAMUH
09033181070GANIN IDO 2026
Mamuhgee
68
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
EID MUBARAK PROMO PACKAGE
Gara basa gara basa da 7500 dinki
duk wadda ta bari promo nan ya wuceta tayi hasara ba karamaba don wannan ya wuce duk tunanin ku kayan dake ciki ko 50k ka siyesu bakayi hasaraba bare 7500 hmm inba gurin Zuzeam ba wazai muku wannan gatan
1. Tabajen kankana
2. Gumbar aya da ridi
3. Tsimin mallaka mai maganin infection
4. Garin dadi har madiga
5. Hadin dafa kaza ko Ciccibi ko nama, Kinga yanzun sallah za ai nama ya wadaci kowa hajiya kina iya dafa nama tsoka 7 da maganin ki zai miki mallaka naban mammaki zai ciko miki da gaba zai kara miki dadi da dandano.
Sannan mutun ashirin na farko nada kyautar Turaren tsugunno na mallaka gagara badau 5k
Ina amaren bayan sallah wannan hadin ya dace daku ko mai jego wadda take shirin haihuwa ma Tana iya siya ta aje ko shekara yanayi bai komi
Ina Uwar gida maiji da kayanta wannan hadin nakine
08144015291 For more information say hi,
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
DAHUWAR KAZA
Kin taba cin DAHUWAR KAZA 5in1 wato Ni’ima,Matsi,Chikowa,MAllaka da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya.
INA MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku 08144015291 Zuzeam ventures.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set
08144015291
*********
Kokarin kasa motsawa SANAAH keyi Ms Meenah ta katseta da cewa
"Kije ko baby SANAAH"
Daqyar SANAAH ta iya daga kafarta tafara takawa tabar gurin tana jin kamam ta dauko nauyin mota ne a kan tray din hannunta.
Maamah kuwa shiru tayi tana sauraron firar da Meenah ke yi hankalinta a kwance
Mommy kuwa hanyar da SANAAH ta wuce ta dan kalla kafin ta kalli dr mum wadda fuskanta take a kame ba alaman kawo mata kowace zance tana kallan Tv tana jin firar da Meenah keta zubawa da wani alfaharin itace matar FLEE RAHEEM JEERAH.
fammah kuwa kitchen ta nufa tana kiran Safiya taxo ta tayata da fira ko aikin.
SANAAH tafiya takeyi ahankali tana sake jin kafafunta na mata nauyi ta doshi bangaren wanda babu kowa a ciki yanzu bayan mai shi babu kuma wanda zai iya zuwa ciki yanzu sai matarsa da 'yarsa gata kaddara ta kawota batareda ta a tsammanin sake zuwa bangarenba.
Tana isowa kofar bangaren shiru tayi a bakin kofar tana dan dakatawa tsawon seconds tukuna ta motsa ahankali takai hannunta ta bude kofar kai tsaye ta shige tareda rufowa sbd sanin babu kowa aciki da idan ta buga zaaji azo a bude mata sai shi kuma a daidai wannan lokacin ma tasan yana palonsa bazai taba ji ba dan haka bazata bata lokacin tsayawa bugawa.
Palon tsit ya sake samun nutsuwa da kwanciyan hankali sbd rashin kowa hakama qamshinsa ne yake dan tashi kadan kadan dayake shine kadai yake kaida kawo a bangaren yau gabaki daya dan haka gurin ya fara nutsuwa da kamshin nasa.
Tsayawa tayi tsakiyar palon tana kallan Dining da tinanin idan ta ajiye bazai taba sanin ankawoba sedai ya kwana gurin a banza hakama batajin zata taba iya zuwa har palonsa na master bedroom dinsa takai masa.
Numfashi mara sauti ta sauke ahankali tana juyowa a tsanaki ta kalli hanyar palon nasa tana dan sake riqe tray din hannunta tareda sauke numfashi mai zafi tana kokarin juyawa ta nufi dining din kofarsa ta bude yana bayyana tareda fitowa gabaki dayansa.
Dogon wandan kayan bacci ne masu santsi da tsadar gaske a jikinsa bai saka rigar ba iya wandon ne a jikinsa wanda farar fatarsa mai asalin lafiya da kyau da zallan hutu tana daukan ido..
Babu tsammani ko kadan ta sauke idanuwanta akansa zuciyarta da tsaya cak daga bugawa ta dauke idanuwanta daga gurin gabaki daya tareda daga kafafunta dake neman kasa daukanta ta juya masa baya tana riqe numfashinta a kirjinta dakyar dayake neman barin kirjinta.
Kasa juyowa tayi hakama kasa daga kafafunta da sukai nauyi tayi tafara jiyo takunsa ahankali daga bayanta kaman yana tahowa.
Kara qanqame tray din hannunta tayi sbd rawan da hannunta yakeyi ahankali yana saka tray din rawa...
Shi kuwa kafeta da idanuwansa yayi sbd bai taba tsammanin zuwan kowaba a bangaren bare ita daya tabbatarda kaman gujewa haduwa dashi ma takeyi hakama ko Meenah bai saka zuwanta a lokacin ba sai dare sosai kokuma ma kila tinda tayi parking sabon guri saita kwana kafin ta iya zuwa nan hakanne ya saka ya fito a yanda yake dan daukowa kansa ruwan shan dayake buqata.
Tanajin isowansa bayanta rawar hannunta ya tsananta tray din ya tsananta rawar data kasa tsayar da hannunta cikin wani irin tsananta bugawan kirjinta sbd tinda take ma bata taba ganin kowane namiji a tube ba sai yau hakama idanuwanta sun kasa cire abinda suka gani din...
Daga kafafunta tayi daqyar zata taka ta bar gurin subucewa kawai tray din hannunta zaiyi ta bayanta ya ziro hannuwansa duka biyu a lokaci daya ya dora akan hannuwanta dake riqe da tray din ya riqesu gabaki daya ahankali tana kasancewa a tsakiyarsa yayi mata rumfar da numfashinta ya tsaya cak sbd saukan fatar tafin hannuwansa akan fatar bayan hannuwanta ya hada da tray din yayi musu wani kyakkyawan riqo yana hana tray din subuce mata ya qonata.
Wani dumin numfashinsa ne na kansa dayake gefen fuskanta harma ya dan zarto gaba sbd a cikin jikinsa take sosai ya sauka a fatar fuskanta daga gefe tareda wani qamshin da yau ta taba jinsa na mouthwash dinsa daya saka tsigar fatar fuskanta tashi ta rintse idanuwanta ahankali zata bude numfashin nasa ya sake fitowa fin na farko take ta sake qanqame tray din shima ya sake riqe hannun nata da wani slow yana juyo da idanuwansa ya kalli gefen fuskanta data kasa bude idanuwanta ya kasa dauke idanuwansa yana jin maganganun da Dad yayi masa yau da bude basa wata zazzafar wuta akan hukuncin daya yanke yana kan bakarsa takardarta zaa basa.
Rintse idanuwansa yayi shima sbd ayau din Dad ya nuna zafi da tsayuwa akan maganarsa dan haka baice komaiba haka ya baro kansa na fara kasawa da daukan pressure dinsu da duka abubuwan da kowa yakeson saiya samu a rayuwarsa.
Bude idanuwansa yayi tareda fidda wata numfashi mai dumin gasken data sakata sake tray din gabaki daya amma sbd hannuwansa suna kan nata sai ya sake riqewa dakyau cikin kulawa yana hana tray din faduwa daga hannuwansu ya bude baki da wata sautin dayake bayyanar da wata gajiyansa akan damuwan datake kokarin shiga zuciyarsa wadda iyayensa ke naman sakasa saiti da kunnenta dayake kusa da bakinsa yace
"Kin manta kincewa fammah you don't want to burn your skin,be careful"
Bude idanuwanta tayi cikin wani irin slow dayake fita da numfashinta a slow din shima sbd kowace kalmansa fitowa takeyi da iskan dayake sauka gefen fuskanta zuwa hancinta.
Motsawa tayi tanason janye hannunta sbd tsayuwan na neman gagararta kafafunta sunyi wata irin nauyi.
Ganin ta kasa zare hannuwanta a qarqashin nasa duk da ba wani matse hannuwan yayi ba ya sakata dakatawa tana bude baki ahankali ta furta
"Dr Mum ce tace na kawo"
Yanda tayi maganar can qasa qasa ya saka idanuwansa sauka akanta da kyau ya saketa yana zare hannuwansa sbd kallan fuskanta dakyau yayi magana da ita.
Yana zare hannuwansa nata hannuwan basa sauran karfin iya riqewa dan haka tray din ya tafi gabaki daya a hijabinta yana barewa.
Wani irin radadi da azaba taji ta ratseta tayi ta rintse idanuwanta da karfi tana ja baya da dan karfin daya kasa riqeta sedai shine ya sake riqeta da dan sauri yana kallan hijabinta da wata yanayin da babu wanda zai iya gane asalin na menene.
"Shit" ya fara da sautin da ko ita bata jiba kai tsaye sai jin tayi ya yaye hijabinta gabaki daya yana kallan cikinta da silk rigar baccinta ta lafe akai da ruwan tea din.
Hannunsa yakai a gurin ba tsammani taji saukansa da wani irin shoch tayi baya tana jin azaba da tashin tsigar jiki a lokaci daya.
Ganin hakan ya dago ya kalleta yaga idanuwanta tini suka ciko da hawaye.
"Kin kone?
Kina jin zafi right??
Samun kanta tayi da daga kanta idanuwanta na sake cikowa da hawayen da kalamansa suka sakasu gangarowa bama tareda da saninga ba sbd yanda yayi tambayar.
Hannunta ya kama kawai ya wuce da ita hanyar bedroom dinsa tana ganin sun shiga palonsa zai nufi bedroom dinsa da ita tai saurin son dakatawa amma yanda takeji da yanda yaje tafiya da ita tafin hannunsa hade da nata ya saka bakinta da kafafunta kasa komai suna isa bathroom dinsa dayake tsare da luxuries tako ina kai tsaye bakin ruwa ya isa da ita yakai hannunsa ya kunna ya debo ruwan a hannunsa daya ya zuba kai tsaye a gurin da rigarta ta maqale mata da ruwa a cikinta.
Wani numfashi mai tsananin karfi da rashin sauti ta sake tana rintse idanuwanta da karfi sbd azabar dataji da kuma sanyin ruwan a Lokaci daya.
Sake debo ruwan yayi a hankali da wata irin kulawa ya zuba mata yana dora hannunsa a gurin....
Sake daukewa numfashinta yaso yi ta riqe cikin karfin hali tana sake rintse idanuwanta tareda dafasa batareda ta saniba.
Hannunta ya dago ahankali ya kalla akan gefen cikinsa data dora batareda ta saniba.
Fuskarta ya dago yayiwa wani kallo idanuwanta na rintse har lokacin tana kasa budewa.
A natse ya dawo da kallansa a inda ta kone din ya miqa hannunsa daga inda yake ya dauko cream na hana skin ya tashi bayan ruwan zafi sosai yataba ko wuta....
Ahankali yakai gwiwowinsa qasa yana yana kallan cikinta cikeda kulawa a natse yakai hannunsa ya yaye rigar daman riga da wando ne a jikinta na bacci...
Bataji yayewan rigartaba sbd zafin da gurin yake mata saida hannunsa ya sauka akan fatar cikinta zuwa gurin cibiyarta ta bude idanuwanta da wani irin sauti numfashinta na yankewa da wani irin karfi...
Baya tayi sedai already hannuwansa sun riga sun zagayota a yanda yake din gabanta kan gwiwansa ya dawo da ita cikin wani slow da dan karfin da saida mararta ta hadu da fuskanta.
Ya rufe idanuwansa ahankali batareda ta ganiba ya bude ido wani slow ya dago ya kalleta itama shi ta kalla idanuwanta na cikowa da wasu