Showing 243001 words to 244256 words out of 244256 words
take ya kasa riqe kansa daga kallanta daya kunce duk wani hakurinsa ya saka hannunsa daya cikin rigarta ta qasa yana dorawa akan mararta da kame bakinta da nasa yaja kamshinta cikin hancinsa yana zuwa kansa da buga masa wani abu mai kafin da a take towel dinsa ya fadi kasa ya dagata cak yana dorawa akan dresser da mata rumfa yana bata wani lafiyayyan kiss mai shiga kai.
A daren ya sake qarasa maidata cikakkiyar Mrs Al'amin khalil suka kasance da juna all night long cikin wata slow zazzafar soyayya.
Washe gari su SANAAH kuwa kirjinsu ya daga daga kasar zuwa America inda suka bude babin sabuwar rayuwar da babu kowa a ciki sai iya su kadai.
Suma su Al'amin daga wannan daren da suka sake kasancewa ma'auratan gaske bai iya sake daga mata kafa ba wata lafiyayyan rayuwa mai tsananin soyayya suke gudanarwa da tini suka manta baa tare ba.
Su Dr Mum basu bar qasar ba suma saida Fammah ta kammala program dinta akai graduation dasu tukuna aka fara shirin barowa da komawa Nigeria dan bikin da zaayi nan da sati biyu.
Ana fara shirye shiryen komawan Fammah ta fara rashin lafiyar da dole ya kaita asibiti sukaga Dr wanda binciken farko kai tsaye ciki ya bayyana a jikinta.
Baiji komaiba bayan farin ciki mai tsananin dabai boye ba dan bazai iyaba ya sanar dasu Dad wainda suma murna sukai duk da kunya kaman zata kashe famman amma ba yanda ta iya dan har Nigeria zancen cikin yaje dan haka aka qarasa hada tafiyar suka wuce dan biki kam ba fashi.
Ranar da suka isa Nigeria a ranar na karan farko da zasu kwana batareda juna ba dan haka da zazzabi ta kwana tinda safe yazo ya kaita asibiti da kansa.
Su SANAAH saida su fammah sukai kwana biyar da dawowa suma suka sauka a lokacin ita nata cikin ya fito fili kowa na ganinsa.
Hakanan akai gyaran Amaren kowace da ciki batareda an basu abubuwan sha ba sbd cikin kowacensu sedai akai gyaran fata da sauransu akai fara hidimar bikin.
Ana cikin bikin ne aka bugo aka sanar da rasuwar Samad wanda labarin ya saka hajiyarsa samun shanyewan barin jiki dan haka ana gama bikin Aka kai fammah babban katon gidan da Al'amin ya gina tini bangare uku nasa daya mahaifiyarsa daya Maamah daya dan haka su maamah da Mommy tarewa sukai aka bar Dr Mum gidan mijinta itama sai SANAAH a nata bangaren mijin itama.
Dad ne da Dr Mum suka fara wucewa gurin rasuwar Samad kafin Fleet daga baya shida SANAAH wadda saita haihu zasu dawo dan sun koma kenan sedai zuwa ganin gida.
Fammah sai da suka kwana biyu sosai kafin suka tattara kai tsaye suka wuce Morocco itada Al'amin zasu hade acan tareda su Dad da Dr Mum.
******Meenah tin lokacinda ta sauka a Morocco gidan abbu ta nufa acan ta zauna taso dawowa Nigeria amma ya hanata amma taqi sam yace ta zauna anan kafin komai ya lafa zai maidata dakinta amma sam taqi yadda karshe taje gidansu ta fada musu suka dauki zafi sosai sukaji sun tsani dangin fleet da fleet din kwata kwata dan haka koda ta shirya komawa kona passport dinta sukai da hanata.
Duk da hakan bata saduda ba tafara shirya wani dan bazata taba yadda ba saita koma.
Amma ce kakarta ta zaunar da ita ta nuna mata tariga tayi kuskuren da har abada bazata kuma kima a gurin fleet ba sbd uwa ba abar wasa bace da zata cinnawa uwarsa wuta dan haka ta saka mata maganganu masu girma akanta cewan ta nutsu ta zauna ta bari zuciyarta da imaninta ya fara yadda da kaddara tukuna ta san zata komawa aurenta da tsaftatacciyar zuciya idan kuma ta kasa iya yadda da kaddarar auren gwara ta hakura dashi ta ciresa har abada arai zaifi mata akan ta koma ta zama mahaukaciyar da kowa zai ringa wulaqantawa.
Wannan ne yasaka wata irin nutsuwa shiga alamarinta da kuma adduar da suke mata sosai dan haka ta hakura ta fasa komawa sbd a yanxu dai batajin zuciyarta zata iya xaman kishi da kowa fleet dan haka tinda bazata iyaba zata jira har lokacin zuciyarta zata karba kaddara ta iya saita koma dakinta.
Da su fammah suka sauka Moroccon gurin mahaifiyarta takeson sauka dan haka Dad da kansa yakaita itaca mijinta yayi magana da dangin Meenah din ya basu hakuri ya sanar masu komai da dalilinsu na boye mata sbd ansan bazata taba yadda ba ta aminta.
Shiru tayi tana jin tagama da zuriar jeerahs har abada sbd wannan abin da sukai mata shime blow din karshe da bazata taba mantawa a aurar mata yarta tilo daya da kowace uwa ke burin ganin auren yarta batareda saninta ba sai dai ganin ciki a jikin yarta.
A karan farko har cikin ranta dataji ta tsani jeerahs da bata fatar ma sake komawa cikinsu har abada ta gama da fleet.
Gani yanda Al'amin yake tsananin son yarta a bayyane ya sakata jin bata buqatan tsanarsa dan haka saita rungumi kaddararta data yarta.
Fammah kuwa dadi taji tareda yankewa kanta zata roki mahaifinta babu kwana kwana ya maida mahaifiyarta idan zuciyar Mum din ta sake sanyi dan sauyinta a bayyane yake a fili..
A nan villah dinsu Mum din Al'amin ya zauna da fammah a lafiyayyan bangaren da aka qare masa suka nuna masa kauna da tattali sosai wanda ya sakasa jin shi kansa yana son Mum ta komawa mijinta suke suyita hakuri da SANAAH matiqar mum din ta sake warware ta amsa kaddarar da zuciya daya tsarkakkiya.
Su Dad sati uku sikai a Morocco suka koma koda suka koma su Mommy na Umrah itada Maamah da safiya dan haka su Fammah basu dawoba saida su Maamah din suka dawo tukuna suka koma.
Komawansu da Wata uku SANAAH ta haihu a America ta haifi yan biyu mace da namiji wainda suka saka jeerahs din kaman basu taba haihuwaba dan haka su mamaah ne da fammah suka fara sauka America sai daga baya Dr Mum da dad suka iso.
A ranar su fleet sukai wani babban gagarumin taron navy soldiers na US a ranar ya radawa yayansa suna NASIR(Ameer) da FATIMA(Little Maamah) akai sunan da iya family dinner ne ta asalin masu juya abun duniya a hannunsu da wata dukiyar da kaman baasan zafintaba.
Sati uku akai da sunan suka tattara suka dawo hadda SANAAH wadda sai yayanta sunyi wayo zai taho su koma.
Su Ameer na cika wata uku a duniya fammah ta haifi Baby boy itama wanda yaci sunan Khalil little.
Dad dinta ya taho sunanta dan haka ana gamawa da sati biyu suka juya matarsa da ayanzu bazai iya rayuwa ita anan ba sbd irin rayuwar dasuke zamansu su kadai a dik inda suke shine best ga kowa.
Itama fammah suna wata biyi Al'amin ya dawo ya daukesu suka koma Italy aka bar iyaye da binsu da adduar kariya da farin ciki mai dorewa har abada a cikin zuriarsu.
ALHAMDLLH
#MAMUH
#GANIN IDO 2026
09033181070
INA MIQA GODIA GA MASOYANA MABIYANA DA SUKAI BI NI A WANNAN TAFIYAR TA GANIN IDO TIN DAGA FARKO HAR KARSHE
ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRINSA YA BAR KAUNA.
KADA KUCE BAKUSO AKA GAMA BA SBD KAMAN KOYAUSHE GWARA MU GAMA MUNA MARMARINSA BATAREDA KUN GAJI NIMA NA GAJI BA.
LABARIN GANIN IDO PLAIN LABARI NE NA NISHADI KAWAI
INA ROKON INDA NAYI KUSKURE AMUN AFUWA
ALLAH YA YAFE MANA KURAKUREN DAKE CIKI
IDAN AKWAI ABINDA NA MANTA BAN SAKABA KO BAN WARWAREBA AYI MUN AFUWA SHIMA AJIXANCI NE NA DAN ADAM.
YAN DIARIES DINA I LOVE YOU GUYS MY YAN AMANA,
AREWAPEN GEES DINA KUMA ONE LOVE,
TELEGRAM MEMBERS I SALUTE YOU ALL..
SAI MUN HADE A SABO KUMA WANDA ZAN TAHO MUKU DA SABON SALON DABAI TABA ZUWA BA.
THANK YOU.