Showing 210001 words to 213000 words out of 244256 words

Chapter 71 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

476

shiga jin nauyinsa da kasa sakewa kaman baya da suke a waya dashi amma taji dadin fitar da kuma yanda yake mata din dan haka shirin baccinta tayi ta kwanta kawai.

Washe gari busy Fleet zai zama sosai dan haka tana fara rokonsa saiya saka aka kaita gidan tana zuwa kuwa ranar fammah bata fita koina dan haka cikin tsananin nauyi ta ringa dan kame kame jiki a mace tana kasa kallan fammah hardar suka wuni a hakan anan ta kwana washe gari da ita suka fita class din dan haka sai Al'amin yabarsu tare kawai ya tafi aikinsa.

Sai da suka gama da yamma shine ya aiko mota ta daukesu ta maidasu gida.

Suna zuwa gida SANAAH jin tayi ta gaji sosai sbd daman hutu take buqata dan haka washe gari bata iya binta ba sedai yaya Al'amin ya jirata.

Da daddare Imran ne da kansa yazo ya kawo mata waya sabuwa dal daga fleet din dan haka bata kwanta ba sai da sukai waya tana masa kaman zatai kuka wai jikinta ke ciwo ita sam batama jin daidai.

Daqyar ya iya riqe kansa ya rarrasheta tai bacci batareda ya iso gidan ba sbd ayyukane a gabansa sosai kuma kowane lokaci zasu bar qasar ma su wuce Miami da ita.

Fammah data fara jin wani irin babban sauyi akan Ya Al'amin da gabaki daya kulawansa da tattalinsa ya sakata a wani tight spot na batasan meke damunta ba dole SANAAH ta koma tana tarairayanta sbd ganin yanda duk tayi sanyi batada wani hayaniyarta irin ta baya kaman ba fammanta ba dan haka basu ankara ba sika samu kansu da komawa kaman yanda suke a baya musamman yanda fammah ce kaman baby din duk da SANAAH dinma tana missing mijinta Fammah take narkewa kaman yanda ta saba.

Dad din yana zuwa ya dubasu yana kuka kama hannun matarsa ya fita har waje da ita ta rakasa ta dawo daga baya dena zuwa yayi kwata kwata sedai a waya su jisa sbd SANAAH itace kadai abinda baya iya controlling a jininsa kaf rayuwarsa and yarsa kuma itace wadda bazai taba hurting ba dan haka ya barsu su zauna tare harsai sun tashi tafiya.

Sun zama yan yawo duk da karatun sosai fammah ta maida hankali akansa ga Summy da suka hadu da ita itama kusan tanada son yawon gashi itace tasan koina dan haka da ita suke fita Ya Al'amin ya sakar musu kudi duk da bayan kowace awa daya saiya kira wayan fammah yaji suna ina me sukeyi sbd baima san SANAAH tayi waya ba.

Ana cikin hakan tafiyarsu SANAAH din ta tashi suka shiga damuwa itada Fammah amma hakanan suka rabu SANAAH ta tafi tareda Dad din famman wadda saida Dad din yayi rarrashinta itama kafin yayi na SANAAH bayan sun wuce.

Miami sukai daga nan dan gama aikinsa daya bari ya tafi Nigeria wancan lokacin da SANAAH din batada lafiya.

**********
Bayan tafiyarsu SANAAH fammah ta gane SANAAH haryanxu tanada kusanci da zuciyarta duk da abinda ya faru hakama Dad dinta yayi magana da ita ta fahimta sosai ya kuma bata hakuri da komai ya mata nasihar data sake sakata rungumar kaddara ta karbi auren nasu da SANAAH dik da tanajin wani lokaci daci sbd Mum dinta amma tana kokarin addua shedan ya hanata yin abinda zatai danasani.

Kadaici da damuwa ce ya fara dawo mata sbd yanzu Ya Al'amin sedai ya jeta ya tafi gurin aiki amma kulawansa da tattalinsa ko daya be dena ba kawai dai ya zama busy.

Kullum idan ya dawo zai kirata a waya suyiga waya yana aiki yana debe mata kewa sbd fahimtar kadaicin dayake kokarin tabata ya kuma taba karatunta.

Yawan wayan da sukeyi ya saka ta saba ko karatu zatai idan ba suna waya tana karatun ba sai taji bata iyawa hakama shi kansa yanxu waya da ita ya saka kome zaiyi sai yana yi yana kallan wayarsa,

Shaquwarsu ta fara sakawa ake mata kallan matarsa kaman yanda shima ake masa kallan ita matarsa ce gashi zuwa yanxu abubuwan dake rabasu a waya kalilan ne.

SANAAH dake Miami tana wata irin rayuwar da daga ita harshi basu taba samun kansu a ciki ta fahimci shaquwan dake tsakanin Ya Al'amin din da fammah ta fara zama kaman abinda bazasu iya rayuwa sai dashiba dan haka take tausayinsu dan alaqa a tsakaninsu kaman bame yiyu bace sbd Mum din fammah tafison tayi kukan rashinta data bari Ya Al'amin ya aureta dan haka sai batama saka zancen itama a ranta ba bare ma ya tabbata.

******
Nigeria
Can baya a ranar dasu Fammah suka wuce cikin wani samun sassauci a kirjinta na wucewan yarta Ms Meenah ta kasa barin gari ya waye ta fito cikin sauran duhun asubar ta nufi kitchen ta kunna gas tabarsa a bude batareda ta kunna ashana ba rufe koina tana rufe kofar baya da masu aiki zasu shigo ta fice daga bangaren ta nufi na Fleet wanda shima kai tsaye ta bude da password ta shiga ta nufi kitchen ta kunna gas tabarsa a bude ta fito ta nufi palonsa na kurya ta bude kofar ahankali ta taka tana isa kofar bedroom dinsa idanuwanta na yin jajir da wani irin zafi da wutar dake cin jininta ta saka hannu ahankali ta bude kofar dakin kadan bata tsaya ta tabbatarda akwaisu a ciki ba ta juya ahankali ta fice tana barin bangaren gabaki daya.

Bangaren Hajiyar Samad ta nufa wadda tana isa hajiyar na fitowa daga dakinta tana waya muryanta na dan tashi da farin cikin jin labarin Fleet yabar qasar da SANAAH daga daya daga cikin securities din gidan dayake waya da ita sosai a bakinsa takejin fita da shigowan kowa villah din.

Babban farin cikinta na jin zancen shine idan Meenah taji dika kullin haukarta kuncewa zasuyi tayita haukan da babu sauki dan haka fitowa tayi dan karyawa dan daman ita tin 7 take breakfast dinta.

Ganin Meenah na shigowa palon ya sakata kallanta da dan mamaki tana kashe wayarta sauran farin cikin a fuska bayyane sosai tace

"Aa Meenah kece da Sassafe haka?
Allah yasa ba wani kika kashe?

Katseta Meenah din tayi da wani kallo da idanuwanta da har wani ruwa suke tarowa sbd jan da sukai ta bude baki tana qarasowa tace

"Ban kashe ba amma ai dole kowa zai mutu tinda mutuwan na kan kowa,
Wata mutuwan idan anyi duk yanda ake qinka ai bazaace kaine kayiba tinda baa ganka ba"

Wani kallo hajiyar Samad din tai mata tana juya zancenta da sam bai mata ba ta juya tana nufar dining da masu aikinta yan wahala tinda duhun asuba suke fara aiki tace

"Me kike nufi ne?
Kinsan dai yanxu kada ki kuma gwada kisan wani a gidan nan dan kuwa babu alkhairi a kowace aikin dan barazana ce ga nawa dan dani kaina"

Wani baqin ciki da zafin samad dinne ya taso ya danne kirjin Meenah din sbd yanda yake tsananin son SANAAH shima babu abinda bazata iya masa ba dan haka bata kalli Hajiyar ba tai shiru tana fatar a samu wanda zai kunna wuta a tsakanin bangaren biyu tasan wuyar bazata bar har bangaren Samad ba.
#MAMUH
09033181070
[22/06, 2:48 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

133
Dakatawa hajiyar tayi sbd jin zuciyarta gabaki daya ta juye da wani fargaba da zuwan Meenah din bangarenta tinda sassafen dan haka ta juyo tana sake kallanta taga yanda idanuwanta sukai muni sbd ja tasan babu abinda zai saka Meenah magana da hauka bayan jin tafiyar Fleet dan haka ta bude baki tana kallan cikin idanuwanta tace

"Kinsan FLEET da SANAAH sun bar qasar ayau din suma?"

Wani irin kallo Meenah ta sauke idanuwanta akan hajiyar tana mata idanuwanta na cikowa da wasu azababbin hawayen wutar dataji ta kama a kirjinta ta girgiza kai tana bude bakinta dayake yanke magana tace

"Bai tafi koinaba suna can kwance gas yana huda kowace iskar da suke shaqa"

Da sauri Hajiyar ta kalleta tace

"Gas kika saka musu??
Me kike nufi??
Wlh baya nan sunyi tafiya ya tafi da ita sun tafi yawon duniya"

Girgiza kai Meenah tayi da karfi tana jin tinaninta na kasa dauka zatai magana hajiyar Samad dataji hankalinta na tashi da barin jikinta tsabar neman rikicewa tace

"Gas naji kin ambata?
Kunna musu zakiyi kokuwa harkin kunna din??

Cikin zafi ta gyada kai tana cewa

"Me zaki musu?
Zaki sake zuwa ki fasa ihun neman cetone kaman yanda kikai wancan karan?
Karki manta duk abinda nayi yanxu tare muke....

Da wani sautin dayake tafe da tsantsar baqin ciki da tashin hankali hajiyar tace

"Kin kunna dai kenan kike nufi???

"Eh kuma....

Hajiyar bata jira sauran zancenba ta tureta da karfin gaske tana nufar kofa ko takarmi bata iya sanin yaya ake sakawaba sbd yanda idanuwanta suka rufe a take duka jikinta wata muguwar rawa yake dauka bakinta na furta

"Allah ya debe miki albarka Meenah ya kuma debewa larabawan kasarku gabaki daya tattalin arziki,irin masifa irin balai"

Da gudun gaske ta isa bangaren Samad dake kusa hanya daga bayan na Fleet.

Tana isa hannuwanta har rawa suke ta bude kofarsa ta fada tana shiga dakinsa ta nufa tanajin warin gas yana ratsowa har nan dan haka ko gani bataji ta fada dakinsa daidai fitowansa wanka kenan daga shi sai gajeran wandon daya saka ta damqi hannunsa tana janyosa da karfi tana cewa

"Yi sauri kowane lokaci bomb tashi zaiyi a bangaren nan"

Kwace hannunsa zaiyi tai masa wani mahaukacin riqo tana janyosa da daga harshenta cikin tsananin tashin hankali

Rigarsa ya janyo tana jansa yana sakawa ta fito dashi shima a lokacin yaji warin Gas sosai dan haka da kansa ya cira kafafunsa suna barin gurin da gudun gaske.

A cikin bangaren su Dr Mum kuwa tini gas din yafara shiga koina yana shiga cikinsu sosai take oxygen yafara kokarin yanke musu dan haka da wani irin tashin hankali da yajin idanuwa suka fara fitowa a palon sukaji abinda yafi karfin hankali dan haka tini Dr Mum ta zube kasa tana wani irin tarin dayake neman tafiya da ranta.

Maamah ce ta kamata da sauri itama tana jin numfashinta na yankewa ta fara kokarin miqar da ita.

Mommy da Safiya da suka fito ma da gudu Mommy tayi kitchen tana toshe hancinta sbd numfashinta daya fara yankewa.

Safiya kuwa kofa ta isa ta bude da karfin gaske tana dawowa ta bude windows tana jin jiri kaman zai zubar da ita ta fito da gudu ta fita cikin ihu ta nemi jaama wanda ihunta da neman agajinta ya saka securities fitowa sa sauri suna yowa nan daidai nan hajiyar Samad dashi suka fito da gudu suma take kowa ya fahimci abinda yake faruwa.

Da gudu akayo nan.

Mommy tini ta kashe gas din Amma bata iya fitowa ba da kanta sbd jiri da toshewan numfashin daya zubar da ita.

Dad jeerah dake kwance yaji ana ihu da hayaniya sarawa kansa yayi yana rintse idanuwansa da wani irin nauyin kirji sbd da alama an kusa kashesa da bugawan zuciya a cikin gidansa dan haka saukowa yayi yana zira jallabiya ya fito tinda dai baiji ana ambatar mutuwan Dr ba kaman wancan karan.

Koda ya iso tini aka fito da Dr Mum wadda numfashinta yake ya kewa kaman mai asthma.

Da tsananin mamaki da shock yake tambayar kafin ma a basa amsa yaji gas din dan haka take ya bada umarnin koina kada a kunna wuta a villah din.

Bangaren Raheem aka nufa da tashin hankali sbd jin yana fitowa harda tacanma.

Daqyar aka iya shiga aka kashe ana bude koina shima tareda sauke kowace labule sbd ya futa yabi iska da kyau.

Jikin Dr Mum rawa yakeyi sosai tana sake rasa numfashinta dan haka kai tsaye bangarensa yayi da ita yana sakawa aje da gaggawa a kawo masa doctors.

Umma dake bangaren ta shigo kawo masa breakfast kenan ta tadda Dr Mum a palonsa tana taimaka mata gurin dawo da numfashinta ta hanyar huta mata wani iska mai sanyi daga bakinsa zuwa fuskanta yana jin kaman ya sakata jikinta ya basa iskan bakinsa dakyau amma hakan ba dama.

Cak Umman ta tsaya daga inda take a tsaye da kaya a hannunta tana kallan Hakeem din da idanuwanta da sukai jajir tana jin wani nauyi na danne kirjinta wanda ya jima a kirjinta ba tin yanzu ba akan alaqar Hakeem din da Dr fammah.

Doctors biyu ne akai gaggawan tahowa dasu dake anguwan sbd dr bushrat ta riga tana asibiti.

Dubata sukai aka dawo da numfashinta daidai suka tafi aka barta a palon kwance cikin da wata irin rashin kuzari.

Dad na shigowa bayan ficewansu zaunawa yayi ya zuba mata manyan idanuwansa da sukai jajir sosai wani radadi da zafi na danne da kirjinsa dayakejin dukkanin riqewa da jarumtarsa ta shekarun tin kuruciya suna tsinkewa daya bayan daya har karshe ya bude bakinsa da wata murya mai tsananin kauri da bayyanarda radadin da kirjinsa yake ciki na abinda ya farun wanda rashin mallakarta ya saka yake kasa bata wata kariya da gaggawan datake tasowa a rayuwarsu idanuwansa a cikin nata ya saka da wannan strong voice din yace

"I cant live without you now Doc,
I can't breathe knowing muna guri daya muna rayuwa amma baa matsayin ke tawa ce ba ni hakeem jeerah....
Ayau ina rokonki Alfarmar da ban nema ba a bayaba,zuciyata bata taba haske da bugawa akan kowace sukuni na rayuwata ba saida kika dawo a cikin gidan danake rayuwa....ki bamu daman qarasa rayuwan datake rage mana a duniya da juna."

Wani irin nauyin dake kirjinta ne taji yana sauka ahankali wasu hawaye na ciko idanuwanta tana kasa dauke idanuwanta daga kansa shi kansa ita yake kalla jan idanuwansa na ciwo da radadin shekarun na dawo masa sabo fil.

Kasa cewa komai tayi sbd ta tabbatarda da son Hakeem zata mutu wanda shine ya sakata rabuwa dashi sbd bazata iya kallansa da wata macen ba amma a shekarun babu ranar da sonsa yabarta da kishinsa da haryanzu tana ji amma a yanzu datake iya ganin radadinsa na shekaru daya boye ya danne bayyane a idanuwansa zata iya basa daman samunta na rayuwar data rage musu.

Umma data kuma dawowa kunnuwanta sukaji abinda ya saka kirjinta dena bugawa daidai juyawa tayi tabar gurin tana jin dana sanin auren Hakeem a karan farko bayan shekaru masu tsayi sbd tin inda aka fito bai taba sontaba zaman auren biyayyar iyaye da hana kansa fidda zafinsa akan ciwon rabuwa da dr fammah din yayi da ita.

Hajiyar samad kuwa tana shiga palonta da Samad kwacewa yayi yana kallanta yace

"SANAAH f.....

Cikin masifaffen fushi ya katsesa da cewa

"Idan ka kira sunanta a nan gurin saina kusan tsine maka sbd zuwa yanzu na gane kaine masifar rayuwata dan tin farko daka riqe kwadayinka akanta da bamuzo nan ba"

Cikin mamaki da jin zafi sosai yace

"Shiyasa kike rufeni kaman nayi kisa?
Tin farkon da kin bari na sameta a ranar danaso samun nata ai da yanzu tawa ce,
Farko Samrah ta hanani mallakarta daga baya kece ku.........

Mari mai zafin gaske hajiyar ta sauke masa tana hanasa qarasa maganarsa sbd meenah din dake tsaye tana kallansu da jin abinda suke fada dan kada ta gane shine wanda yayi fyaden cikin zafi da bacin rai tace

"Ni mahaifiyarka kake fadawa hakan?"

Meenah kuwa da wani mamaki da shiga wani mahaukacin tinanin maganganun samad din da suka shigeta kai tsaye ta kalli Samad din wanda idanuwansa sukai jajir yana kallan hajiyar take ta gane inda zancen ya nufa wani mahaukacin sanyi ya sauka a kirjinta tana jin a karan farko allah ya bata saar da bata taba samu ba ta tarwatsa Fleet da Raheem da baisan sauran qaninsa ya auraba.
##MAMUH
09033181070
[22/06, 2:55 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

134
Dakatawa hajiyar tayi sbd jin zuciyarta gabaki daya ta juye da wani fargaba da zuwan Meenah din bangarenta tinda sassafen dan haka ta juyo tana sake kallanta taga yanda idanuwanta sukai muni sbd ja tasan babu abinda zai saka Meenah magana da hauka bayan jin tafiyar Fleet dan haka ta bude baki tana kallan cikin idanuwanta tace

"Kinsan FLEET da SANAAH sun bar qasar ayau din suma?"

Wani irin kallo Meenah ta sauke idanuwanta akan hajiyar tana mata idanuwanta na cikowa da wasu azababbin hawayen wutar dataji ta kama a kirjinta ta girgiza kai tana bude bakinta dayake yanke magana tace

"Bai tafi koinaba suna can kwance gas yana huda kowace iskar da suke shaqa"

Da sauri Hajiyar ta kalleta tace

"Gas kika saka musu??
Me kike nufi??
Wlh baya nan sunyi tafiya ya tafi da ita sun tafi yawon duniya"

Girgiza kai Meenah tayi da karfi tana jin tinaninta na kasa dauka zatai magana hajiyar Samad dataji hankalinta na tashi da barin jikinta tsabar neman rikicewa tace

"Gas naji kin ambata?
Kunna musu zakiyi kokuwa harkin kunna din??

Cikin zafi ta gyada kai tana cewa

"Me zaki musu?
Zaki sake zuwa ki fasa ihun neman cetone kaman yanda kikai wancan karan?
Karki manta duk abinda nayi yanxu tare muke....

Da wani sautin dayake tafe da tsantsar baqin ciki da tashin hankali hajiyar tace

"Kin kunna dai kenan kike nufi???

"Eh kuma....

Hajiyar bata jira sauran zancenba ta tureta da karfin gaske tana nufar kofa ko takarmi bata iya sanin yaya ake sakawaba sbd yanda idanuwanta suka rufe a take duka jikinta wata muguwar rawa yake dauka bakinta na furta

"Allah ya debe miki albarka Meenah ya kuma debewa larabawan kasarku gabaki daya tattalin arziki,irin masifa irin balai"

Da gudun gaske ta isa bangaren Samad dake kusa hanya daga bayan na Fleet.

Tana isa hannuwanta har rawa suke ta bude kofarsa ta fada tana shiga dakinsa ta nufa tanajin warin gas yana ratsowa har nan dan haka ko gani bataji ta fada dakinsa daidai fitowansa wanka kenan daga shi sai gajeran wandon daya saka ta damqi hannunsa tana janyosa da karfi tana cewa

"Yi sauri kowane lokaci bomb tashi zaiyi a bangaren nan"

Kwace hannunsa zaiyi tai masa wani mahaukacin riqo tana janyosa da daga harshenta cikin tsananin tashin hankali

Rigarsa ya janyo tana jansa yana sakawa ta fito dashi shima a lokacin yaji warin Gas sosai dan haka da kansa ya cira kafafunsa suna barin gurin da gudun gaske.

A cikin bangaren su Dr Mum kuwa tini gas din yafara shiga koina yana shiga cikinsu sosai take oxygen yafara kokarin yanke musu dan haka da wani irin tashin hankali da yajin idanuwa suka fara fitowa a palon sukaji abinda yafi karfin hankali dan haka tini Dr Mum ta zube kasa tana wani irin tarin dayake neman tafiya da ranta.

Maamah ce ta kamata da sauri itama tana jin numfashinta na yankewa ta fara kokarin miqar da ita.

Mommy da Safiya da suka fito ma da gudu Mommy tayi kitchen tana toshe hancinta sbd numfashinta daya fara yankewa.

Safiya kuwa kofa ta isa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login