Showing 159001 words to 162000 words out of 244256 words

Chapter 54 - GANIN IDO COMPLETE BOOK BY MAHMUGEE

MAHMUGEE   

08 Aug 2026

489

tsanani da samun wata nutsuwa ta bude baki da wani sautin farin ciki tace

"Thank you thank you"

Hannu takai ta saka ta dauki spoon mai kyau ta saka a cikin wata white rice da sauce din kidney dayake da dandano da kamshin girkin da zata iya ci takai bakinta taci ta lumshe idanuwanta da wani jin dadi tana dagowa ta kallesa da wata yanayin da saida ya dauke idanuwansa daga kanta sbd barinta taci abincin dayake ganin farin cikinta a bayyane.

Couscous da aka daga fa veggies shima ta saka spoon ta diba taci batasan lokacinda ta sake murmushi mai tsananin kyau ba tana sake kallansa da wata sanyayyar son dayake cinta tace

"Thank you"

Ruwa ya bude mata na roba yakai bakinta tasha tana sake debo abincin taci.

Wata lafiyayyan moimoi ta bude itama ta saka spoon ta debo taci ta bude doya da aka soya fara da egg sauce itama taci kadan tanaci yana kai mata ruwa bakinta tana sha kadan tana jin zuciyarta cikeda farin ciki sai murmushi takeyi wanda yana kallanta bai dauke idanuwansa daga kanta ba harta koshi tasha juice kadan dan bata wani son zaqi.

Goge bakinta tayi da tissue tana kallansa da sauran murmushin a fuskanta tace

"Na koshi"

Tissue ya sake dauka ya goge mata gefen bakinta tareda miqewa ya kama hannunta suka nufi kofa.

Yana bude kofar ya fito suka tinkaro harabar gidan wanda securities dinsa suka share kusan awa uku suna jira suna hango tahowansa Imran dake waya tin dazun wanda kiran ya hana uban kiran dasu Ms Meenah ke masa shigowa wayarsa yana ganin Fleet din ya kashe wayar yana tinkarosu ya miqa hannu ya amshi suitcase din dayake janye da ita da hannu daya fuskansa a asalin kame da babu annuri ko daya a cikinta.

Sake nutsuwa kaf securities din sukai imran na karban suitcase din ya miqawa daya daga cikinsu yana bude musu motar tin basu iso daf ba.

Daman tini Imran ya saka aka fiddo kayansu suna mota tini dan yasan ba lallaima su kwana a wannan villah dinba.

Suna shiga aka tada motocin suka bar harabar gidan tini wanda SANAAH ta dauka gurin bikin suka nufa saida suka hau titi da wani lafiyayyan speed taji muryan Fleet din ta ratsa motar cikin nutsuwa da kamewa tareda bada umarnin kai tsaye da cewa imran

"Ka siya tickets din Fammah da Mum dinta na wucewa America a daren yau ko zuwa asuba"

Juyowa SANAAH tayi da dan sauri ta kallesa sbd jiyo wani irin zazzafan hukunci a umarnin nasa sbd mum zata iya zarewa idan akace tabar qasar batareda jibi an daura aure ba"

Daidai nan kiran Mum din ya sake shigowa wayarsa da jajayen idanuwa da suka kasa boye bacin ran daya danne a kirjinsa ya kashe wayar gabaki daya wanda imran na jin bai daga wayarsa ba ya kashe tasa a take yana ajiyewa gefen motar ya qara taka motar da dan karfi suna hawa babban titi da kyau.
#MAMUH
09033181070
[08/06, 9:12 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

96
Ms Meenah da wayarta ke hannunta kallo tabi wayar dashi tana mamakin rashin ganinsa da kuma rashin sanin ina SANAAH itama gashi bikin yariga ma yayi nisa.

Sake saka kiransa tayi amma bata shigaba ta koma ta saka kiran imran wanda shima kai tsaye akace a kashe wayar take.

Mamaki ta shiga da tinanin meyake faruwa amma kuma batada lokacin duka tsayawa wannan dan haka ta sake jefa wayar jaka tana shiga busy.

Su kuwa suna sake nisa a tafiyar Zuciyar SANAAH kasa nutsuwa tayi da abinda taji ya fada sbd batason a kuntatawa su fammah din akan hakan hakama tana shakkar su dawo su san batanan kuma su san tana tareda shi dan haka haka ta sake dan juyowa ta kallesa a karo na kusan hudu amma ta kasa iya bude baki tai masa magana sbd yanda fuskansa take a kame tsaf babu alaman sassaucin da kowa zai iya masa wata maganar.

Kai tsaye gidan Abbu motocin suka nufa suna hawa layin gidan imran ya saka kiran mai gadin dan haka suna kawowa ana bude gate suka shige aka rufe gate din ruf.

Parking akai Imran ya bude masa da kansa kafin ya budewa SANAAH itama wadda zuciyarta ta sake shiga damuwa da fargaba ma ta ziro kafafunta ta fito sbd ganin ya fita kuma tanason magana dashi amma dole tasan sai ta bisa

Ciki suka wuce tana gefensa kai tsaye bangarensa suk nufa tinda ba kowa a gidan bayan masu aiki ba amfanin akaita ciki.

Suna shigewa babban palonsa mai tsananin tsari da kyau da komai yake kashe shine yaje da kansa ya kunna komai yana wucewa cikin bedroom dinsa tana biye dashi duk ta sake shiga mutuwan jiki sbd bataga alaman ma kowane zancen zai shiga ba amma tanason yi gaskia.

Suna shiga bedroom din wanda kamshinsa yayiwa mugun kamu komai kaman kusan bedroom dinsa na Nigeria.

Yaga alaman magana takeson yi kuma yasan akan me baya buqatan kowace hayaniyar da zata damesu a daren dan haka ko fuskanta bai kalla ba ya kasa bata daman maganar ya ajiye wayoyinsa dake hannunsa ya nufi closet batateda ya juyo ya kalleta ba sbd taba biye dashi.

Yana isa cikin closet dinsa da zai sauya kayansa zuwa na bacci tinda yanxu sukai wanka bada jimawa ba ta kasa hakura daga inda take tsaye sbd kada a siya tickets din ta danne shakkarta da fargabanta ta iso gurinsa ta tsaya bayansa daya gama bude gaban rigarsa zai zare tareda bude baki zatai magana ya juyo da karfi tareda kamata ya dawo da ita gabansa ya manneta da jikin hanger din da kayansa suke a jere kayan suka rufesu ta sama ya dago idanuwansa da suke a wani irin har lokacin basu koma daidai duka ba ya sauke mata su a fuska yana mata wani lafiyayyan kallan daya sakata jin zuciyarta tana sauya bugawa ta motsa bakinta da rashin son motsawan ko kadan da sautin dayake tona asirin bugawan zuciyarta akansa tace

"Kayi hakuri" qarasa maganar tayi kasa kallansa tana dauke idanuwanta ya sakasa dauke nasa idanuwan daga kanta shima yana sakinta batareda yace komaiba ya zare rigarsa ya jefa yana janyeta ahankali daga gabansa ya ciro kayan baccin da zai saka yana dora hannunsa akan doguwan wandonsa zai zare ta juya baya ahankali tana daga kafafunta zata bar gurin ya dawo da ita da hannunsa daya ya hada bayanta da kirjinsa yana qarasa zarewa ya jefar yana saka bakinsa a kunnenta yace

"Ba magana kikeson yi ba uhummm,ina jinki"

Dan rufe idanuwanta yayi tana motsa gefen fuskanta dan yanda maganar tasa ta fita har bakinsa na gogan fatan kunnenta ta gyada kai ahankali tana kasa bude baki tai maganar sbd jinsa a jikinta.

Gaba ta danso yi kadan amma ya zagayeta yana cewa

"Kin fasa maganar ne??
Shikenan"

Sakinta yayi yana juyawa da saka doguwar wandon silk kayan baccinsa black tana ganin ya bar girin ya koma bedroom ta sake biyosa a natse tana isowa gabansa ta dago cikin karfin kuzari da bayyanarda damuwanta sosai ta bude baki ta sake basa hakuri tana rasa abinda zata dora dashi akan bada hakurin sbd kaman ba hurumin shigarta bane shiga maganarsa da Mum din dan haka tayi shiru.

Miqewa yayi ya kama hannunta ya sake komawa closet din da ita ya zaro kayansa na bacci da sam bazasu iya zama a jikinta ba ya saka mata a hannu sbd ta shirya ta kwanta tayi bacci kawai.

Numfashi ta sauke tana kallan kayan tareda rasa duka sukuni da nutsuwanta sbd da alama anan yake nufin xata kwana to me zata cewa su fammah?
Yaya zata fuskancesu?

Ta jima a cikin closet din tana rasa tinanin kamawa har kafafunta sukai sanyi sosai da tsayuwar ta zare kayan jikinta ta saka rigar daya bata wadda iyakacinta cinyarta danma ta mata yawa ne sosai ta sauka.

Kasa fitowa tayi ta durqusa a gurin tsawon lokaci shima kafin ta miqe a sanyaye ta shiga bathroom dinsa ta dauka sabon brush ta wanke bakinta ta tayi alwalan bacci ta fito.

Tana fitowa a sanyaye ta fito bedroom din daya ragewa haske sosai yana kwance a gadon idanuwansa a rufe.

Kasa hawa tayi ta tsaya tsakiyar dakin tana kasa cire tinanin abinda zai iya faruwa da safe idan akasan tana tareda shi.

Zurfi tayi a tinanin da batasan yaushe ya bude idanuwansa ba sai hannunsa daya kawai ya miqo ya kama hannunta daya ya janyota ta fado kansa ya birkita da ita dayan gefen ya kwantar yana juya mata baya ahankali sbd da alama rigima take son masa.

Hakan da yayi ya sakata kallansa da idanuwanta tana jin damuwa na sake rufeta sai kawai itama ta juya bayan ahankali tana rufe idanuwanta jikinta a mace sbd ta rasa yaya zatai ta iya fada masa abinda zai iya faruwa da safe idan ta kwana anan.

Bata ankara ba bacci mai karfi da nutsuwa ya dauketa a hakan wanda yanajin alaman tayi baccin ya juyo a natse cikin kwanciyan hankali ya zira hannunsa daya ya janyota jikinsa yana rungumeta da wata irin nutsuwa tareda saka kansa wuyanta ya rufe nasa idanuwan da shima ba jimawa baccin ya daukesa.

Acan kuwa gurin biki mantawa gabaki daya da SANAAH Mum tayi tasha hidimarta cikin farin ciki da walwala da wata irin murna,
Fammah ce ta damu sosai da rashin ganin SANAAH din amma sbd yanda itama aka ringa daukan hankalinta ya saka hankalin nata ya kasu gida biyu hakama tasan zuwa yanzu dole SANAAH na gida bata zo ba kenan.

Bikinsu suka sha har tsakar dare sosai kusan karfe boyi da rabi aka tashi aka fara watsewa kowa na tafiya da motocinsa.

Sai karfe uku da kusan mintina suka iso gida a lokacin kowa a matiqar gajiye yake dan haka Mum dakinta kawai ta shige ta cire komai ta fada toilet tayo wanka tana kokarin saka kayan bacci ta nufi gurin Fleet fammah ta shigo dakin tana kallan Mum din tace

"Mum SANAAH bata nan fa banganta a koina ba"

Qarasa fesa wani turare Mum din tayi tana ajiyewa tace

"Tana gurin Amma inaga tinda ba kowa a gidan dole can zata ta kwana"

Ficewa fammah tayi ta nufin dakin Amman ita kuma Mum ta qarasa shirinta ta fito tana kokarin ficewa Fammah ta sake dawowa gurinta damuwa na fara kamata tace

"Bata can"

Itama Mum din fara shiga shakka tayi ta juyo ta kalli koina a palon babu alaman inda mutum yake a kwance tace

"Kaman yaya wai bata nan? Ina zata tafi? Ina ta sani kowafa bata saniba,kuma Maleek yace baima ganta ba koda yaxo na dauka ai ta fasa zuwanne tayi kwanciyanta"

Qarasa maganar tayi zuciyarta na neman rikicewa dan tasan wlh Dad jeerah akan a rasa SANAAH tsaf zai datse aurenta da Fleet wanda da hakan ya sameta gwara ayi mata mutuwa.

Juyawa tayi tana bazama dakunan gidan daya bayan daya tana saka kiran wayar fammah da wayarta hankalinta na mugun tashi.

Fammah ma hankalinta mugun tashi yayi ta fara jin kirjinta na bugawa dan kuwa akwai matsala ne sosai ita kanta ai zuciyarta bazata iya daukan wani abi ya samu SANAAH dinta ba.

Wasa wasa sai ga gidan kaf a tsaye cikin tashin hankalin daya saka gajiyan kowa bacewa da shiga fargaban sace 'yar mutane a gidan.

Kasa iya sanarwa Fleet sukai sbd basusan yaya lamarin zai kasance ba dan Mum batama fatar abinda zai saka Koda wasa Zancen ya fita.

Kasa riquwa hawayen Fammah sukai sbd tinin aka fita harda motoci gurin nemanta a tsakar daren babu ji ba gani.

Mum jin tayi kaman Allah ya dauki ran Dad jeerah a daren kafin yaji labarin bacewan SANAAH da baasan inda zaa ganta ba babban tashin hankalinta kada wani abin ya sameta da bazai boyu ba.

Fammah kuwa jikinta har wani rawa yakeyi sbd sunyi kiran wayarta yafi so dubu bata shiga gashi babu wanda ya ganta ko a harabar gidan ko fitarta ko shigarta koina babu wanda ya ganta shi kansa mai gadi baiga fitarta ba ko wanda ya fita da ita sam dan haka kowa ya sake shiga rudu.

Kiran sallar asuba aka fara wanda ya sake sakasu tashin hankali mara misali babu wanda ya rintse a tsaye suke cikin rashin sanin mafita tsilli tsilli babu me nutsuwa.

Sabon tashin hankalin Mum gari na wayewa dole fleet zaisan abinda ake ciki dan haka ta zauna a palo ta dafe kanta cikin tsananin ciwon kai da fara jin takaicin SANAAH din data sakasu wannan tashin hankalin a daren daya kamata su kwana suna cigaba da farin cikinsu na biki.

Wayarta ce dake kusa da ita tayi ringing sbd kiran dayake shigowa.

Kallan wayar tayi da sauri tana jin kanta na sake sarawa sbd ganin numbern Imran ce mai kiran.
#MAMUH
09033181070
[08/06, 11:00 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

97
Tinanin qin daukan wayar tayi sbd kada susan abinda yake faruwa amma kuma tinanin dole akwai mugun babban dalili mai girma na saka Imran ya kirata da asubar ya sakata saka hannu ta dauki wayar tana dorawa a kunnenta ta kimtsa muryanta tace

"Yes Imran"

Cikin nutsuwa da bata girmamawa yace

"Barka da Asuba,mota na waje da zata daukeku zuwa airport jirginku zai daga karfe 6 zuwa America Umarnin Fleet ne"

Mamaki ne yaso kasheta daga zaunen ta bude baki da bayyanarda rashin fahimtarta tace

"Menene wata mota da wani ticket din tafiya kake magana,waye ne zaiyi tafiyar??

Numfashi mai nutsuwa Imran ya sake yana sake kamar da kansa da muryansa yace

"Umarninsa ne"

Wani mugun takaici ne ya taso mata mai zafi da baqin ciki akan wanda take ciki tace

"Wai nice kake maganar fleet yace nabar Morocco yau na koma America?
Da akai me?
Akan me?
Biki fa nakeyi?

Kashe wayarta tayi kawai kai tsaye tana miqewa idanuwanta rufe da wani zafaffen tashin hankalin dataji ma maganar SANAAH kwata kwata ta bace mata akai dan kuwa wannan itace asalin tashin hankalinta bata SANAAH ba.

Tana miqewa fammah ta kalleta da jajayen idanuwanta da sauri tana cewa

"Anganta ne Mum??

Ko amsa bata bawa fammah dinba ta wuce ko gabanta bata gani sosai tsabar abinda taji yana taso mata yana danne kirjinta.

Bangaren da aka sauke fleet din ta nufa kai tsaye Fammah na biyo bayanta cikin fargaba sbd ganin halinda ta shiga.

Suna isa tin daga hanyar isa da fammah bata ga alamar securities din Dad dinta ba ta sake shiga mamaki da rudu Mum kuwa kai tsaye shiga tayi bata tsaya palonba ta wuce bedroom ta bude ko kafarta bata sakaba ta fahimci baya ma villah din kwata kwata ta sauke idanuwanta akan gadon dayake a dan yamutse ta kalla taji kanta ya wani sara da karfin gaske amma buqatar dai yanzu ta gaggawa itace ganinsa da magana dashi da gaggawar gaske.

Juyowa tayi ta fito daga bangaren gabaki daya tana saka kiran numbernsa jikinta har wani rawa yakeyi.

Bata shiga ba ta sake danna kiransa tana cigaba da tafiya kamar zata kurma ihu.

Kira kusan na goma take masa amma wayar bata shiga kwata kwata dan haka ta saka kiran imran wanda yana dauka tace masa ina Fleet yake tana buqatan ganinsa kota yaya.

Shiru ya danyi kafin ya bata hakurin bazai samu cewa komaiba kawai dai driver na jiransu kada a rasa flight dinsu.

Zaginsa taso yi sbd tsananin bacin rai da tashin hankalin datake jin yana shigarta dan babu ta yanda zata bar bikin nan batareda an qarasa shi da itaba kaninta da itace uwar biki kuma ma batasan dalilin dayasa kawai zaa tado mata wannan mugun ji da ganin ba.

Fammah da jikinta ya fara bata akwai babban laifin da sukai a gurin Dad dinta wanda ya sakata fara tinanin ko ya siyawa SANAAH ticket itama ya turata Nigeria kokarin dauko wayar Ammah tayi ta fara saka kiran Dad din nata tana jin zuciyarta na wani irin tsalle.

Ms Meenah zarewa taji kaman zatai dan haka taso tafiya gidan Abbu a cikin duhun Ammah ta hanata tana cewa ta bari gari ya waye sosai.

Securities da aka aiko tareda motar daukansu kuwa kin matsawa sukai koina sai da ita da fammah dan kuwa umarni ne da suke fatan sai sun cikasa.

****A daidai wannan lokacin kuwa Sallan asuba yaje cikin nutsuwa da kwanciyan hankali ya dawo ya tadda ita ta idar da tata sallan sanye da jallabiyarsa datai mata wani irin yawa sosai daya sakata mata tai rollin mayafinta.

Kallanta yayi da fararen idanuwansa da suke fes da wani zallan nutsuwan kwarjini da steez da babu wanda zai taba iya kallansa ya kuma ya maimaita a lokaci daya baiji komaiba a zuciyarsa.

Dagowa tayi itama a natse da sanyinta ta kallesa lokacinda ya iso ya miqa mata hannu a natse yana bude baki zaiyi magana ta katsesa da sautinta daya shigesa da kyau da cewa

"Ina kwana"

Bai amsa ba sai data miqa masa hannunta a cikin nasa daya miqo ya tsayar da ita sbd kasa tashin datai da rigar datai mata yawan ya bude baki ya amsa a natse yana tayata cire rigar ahankali kaman yanda shine ya zira mata.

Yana cire mata rigar ya kalleta ganin kusan tareda rigarta ta ciki ya zare rigar tayi saurin riqe rigar tana son juya masa baya ya riqeta yana tsayar mata da rigar a kirjinta ya tayata rufe abinda takeson rufewan yana kallan idanuwanta da suka bayyanarda wata irin kunya mai tsari da tsanani.

Baya tayi ta shige closet din dakin ahankali tareda zarar towel dinsa ta daura a jikinta tana sauke ajiyan zuciya mara sauti tareda daga rigar zara cire ta cikin data kwana da ita ta sake mayarta tajisa a bayanta ya kwanto da kirjinsa abayanta yana zagayeta da hannunsa daya ya rungumota da wata irin nutsuwa hannunsa daya na zagayo wuyanta ya sake shigar da bayanta a kirjin nasa ya rungumeta tsamtsam da kyau yana sauke ajiyan zuciya mai sanyi da nutsuwan da itama tajita har kirjinta ta dan dakata bata motsaba tana jin saukan numfashinsa a natse da sanyi na saukan mata sukai shiru a hakan batareda kowannnensu ya motsa ba sai qamshi da numfashin juna da suke shaqa da wata kwanciyan hankali.

Tsawon lokaci suka dauka a hakan kafin taji tana son maganan tafiyanta data su Mum ta motsa ahankali tareda bude baki batareda ta juyo ba zatai magana ya lips dinsa suka saika akan fatar tsakiyar bayanta da babu komai take maganarta ta tsaya cak batareda ta fitoba sbd wani irin tashi da tsigar jikinta sukai ta sauke wani numfashi mara sauti ahankali.

Bai dauke lips dinsa ba daga fatar bayan nata ya sake matseta a jikinsa da hankali yana feso wani sanyayyan numfashi mai tsananin dumi ya ratsi fatar bayan nata ta qanqame hannunsa dake zagaye da ita tana dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login